ZAN FASA KWAI 25

Advertisement

*ZAN FASA KWAI

              *NA*

*HADIZA BARA’U GIDAN IKO*

……….”Kai Nan har Dan iska ne Kai da zaka saka shimfideden hannunka ka marar min yariya? Dama ina jiranka akan wulakancin da kayi Mata har sau uku saboda Kai Dan iska ne? Waye ubanka a duk fadin Nigeria? To zaka Gane karyar iskanci kake don sai ka Kare Rayuwar ka agidan maza. Kasan ko wacece ita da irin gatan dake gareta ? To bude kunnen ka kaji da ranta ya baci gara gara amaimsita yakin badar da tabuka  ita kadai ce gayya zakuma ka Gane gatanta ya zarce ayi Mata ko harara bare kallon banza

 


Izzatu tayi ta sababi da masifa tana wanke shi soso da sabulu Amma ko daga Kai baiyi ba bare ya tanka inda izzatu ta fiddo wayar ta ta Kira D P O na yankin ta sanar dashi tana son aturo Mata motar Yan sanda biyu suzo su wuce Mata da wani Dan iska da take son abatar dashi gaba daya 


Ta gama wayar tana mishi kallon banza inda ta dubi motar shi ta dora da sababi


Advertisements

“Dan iska da Kai ka aro mota ka shigo gari shine zaka nemi shiga hurumin yarinyata shege da ganinka ma kayi Kama da masu wankin mota wata Kil wanki aka kawo maka shine ka shigo gari don kayi bagu da barazana da motar mutane don da ganinka matsiyacine Kai zaka Gane ka tabo abinda yafi karfin ka har iyayen ka sai an kulle min su tunda Basu iya tarbiya ba……


Baice Mata komai ba har tagama cinye fuskar shi tas inda Kuma motocin na Yan sanda suka faka har mota uku cike da Yan sanda tamkar zasu Kama Yan fashi


“Kunga shegen Nan ku Kama min shi cewar izzatu inda taga kaf din Yan sandan sun wuce wurin Wanda take cewa su Kama Amma me? Sai gani tayi suna kamewa da sarawa abinda ya bawa izzatu haushi………


“Ku Kama min shege ku aje sai Naga ko uban waye yake daure mishi kugu……….


D P O ya dako Mata tsawa wadda Bata San ko ta wacece ba inda suke ta bawa  Anwar hakuri suna sarawa abinda ya daurewa izzatu Kai Bata Sha mamaki ba sai da taji Anwar din na bada umarnin Kama ta ita da fulani kawai sai gani tayi suyo musu zummuwa 


Aka garkama musu ankwa ana iza keyar su SHIGA motar Yan sandar……..


Advertisements

“Kafin ku wuce dasu kusa yarinyar tazo ta janye motar can Kuma kar abada belin su sai in Ni Naga damar hakan Kuma don yanzu kar a kirani sai Nan da bayan wata uku don inaso uwar da Yar su koyi darasi. Ita Yar Ina so ta koyi tarbiya ita Kuma uwar don idan ta sake haifar wani dan Nan gaba ta San irin tarbiyar da zata bashi


Aka dakowa fulani tsawa ta fito jiki na rawa ta janye motar ta koma cikin motar Yan sanda akaja su aka wuce dasu inda izzatu ke kallon lamarin kamar wani mafarki ko Shirin film Wai ka dauko Dan sanda ya kama maka mutum Amma sai lamarin ya juye akanka waye wannan yaron da taga Yan sandan ma kamar tsoron shi sukeji? Da sauri ta jawo wayar ta ta Kira Kabir take fada mishi abinda ya faru inda isar su station din ko minti Sha biyar ba ayi ba Kabir mashi kashe arna ya iso don yayi belin iyalan nashi 


Azaton shi ficen da yayi da sharar da kowa ya sanshi yasa yayi zaton da yazo ne za a bashi belin su izzatu Amma sai ya iske sabon Labari Wai babu batun beli sai Nan da wata uku


Yayi mamakin wannan yaro da izzatu ta fada mishi to waye? Da ya nemi sanin yaron da yayi wannan aikin D P O ya sanar dashi Anwar ne,


Mamaki ya Kama Kabir Jin Wai Anwar ne to Ina suka hadun da fulanin har sukayi wannan wautar? Da haka yayi sallama da caji ofis din ya nufi me bawa shugaban kasa shawara don ya zamo tsanin shi na ganin Mr President don ya San shi kadai ne zai saka Baki Anwar din ya fito mishi da iyalin shi don haka ya tunkari Alh uba Dan yaro Wanda ya sanar dashi abinda ya faru tsakanin yarshi da Anwar Wanda ya bada umarnin kulle su har sai bayan watannin uku shine yake son Isa wurin Mr President don asaka Baki Anwar ya hakura


Ai kuwa alh uba Dan yaro yayi mishi jagora har sukayi nasarar gani Mr President Kabir ya zayyane mishi komai inda yayi murmushi Yana cewa


“Yara ne su duka Kuma suna takama da zafin Kai kayi hakuri Kabir don Allah bansani ba Amma yanzu Nan zai zo Nan inji abinda yasa yayi hakan ya fada Yana dauko wayar shi ya latso lambar Anwar Kara biyu ya dauka inda uban yace yazo yanzu Yana son magana dashi ya amsa da gashi Nan zuwa ya aje wayar


Ya dubi Kabir “Kabir fatan ba zanyi maka shisshigi ba idan na tambaye ka bakayiwa Yar tamu miji ba? Ya amsa da baiyi Mata miji ba inda Mr President yace zaiso su hada Anwar da ita fulanin aure don wata Kil wannan tsamar tasu salon tasu soyayyar ne.


Wani Dadi da ya rufe Kabir tamkar ya shide don Yana ganin auren fulani zai zamo mishi auren jari da yadda zai dawo da kwangilolin shi da ake son yi mishi fin karfi don haka jiki na rawa ya amsa da Babu matsala duk yadda Mr President ke so hakan za ayi daga karshe ma yace ya bawa Anwar din auren fulanin idan an shirya azo ayi magana 


Mr President yaji Dadi sosai dama Yana neman Yar da zai hada da Anwar tunda shi har yanzu cewa yake Wai baiga wadda tayi mishi ba don haka ya zabi yi mishi haka don baya son yaron nashi ya bude Tasha shiyasa yake son yi mishi aure 


Mr President ya kawo kyautar girma ya bada yace akaiwa fulani ta siyi kayan kwalliya abind ya gigita Kabir mashi shi Kam zai iya cewa gara da akayi da haka Anwar yayi sallama ya shigo ya zube Yana gaishe da Kabir mashi don ya sanshi sosai Yana ganinshi agidan nasu sai dai har ga Allah Bai zaci shine uban yarinyar da tayi mishi gatsali ba. Mr President ya tambayeshi 

“Su waye kasa aka kulle a station? Ya fada mishi duk yadda abin ya faro har zuwan izzatu da irin tozarcin da tayi mishi duk ya fada musu inda Mr President yayi murmushi


“To kanwar ka da uwarka kasa aka kulle don iyalan Kabir ne sai kaje maza kasa asake su…………


Yazube gaban Kabir Yana bashi hakuri

“Kayi hakuri Abba ban sani ba ne ka gafarce Ni yanzu ne zansa akansu har gida………….

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like