ZAN FASA KWAI 32

Advertisement

 *ZAN FASA KWAI

               *Page 32*

……..Hajiya Mama tazo Jin abinda ya faru ga abdulkarim jikinta har Bari yake don Ubangiji ya hasko Mata lamarin amafarki inda gari na wayewa ta Kira abdulkarim take tambayar shi suna lafiya dai ko? Ya fada Mata suna lafiya sai dai abinda ya faru don haka hajiya Mama ko Karin kumallo batayi ba ta tashi direba ya kawo ta gidan AK


Dukan su suka zube gaban hajiyar tana tambayar su

“Basu dai taba kowa ba ko?

“Basu taba kowa ba hajiya hatta kudi da gwalagwalan da suka karba sun maido sai Yan Wanda ba za a rasa ba……………….

“Alhamdulillah tunda dai Basu taba kowa ba sai mu dage da addua Ubangiji yakiyayeka dukkan sharri ya Dora ka Kan makiya suka amsa da ameen da haka hajiyar ta koma gida tana ADDUAR Allah ya Kare Mata danta.


Advertisements

Hon bello Rimaye ya soma budewa sister mero bakin aljihunshi akan son auren humaira fulani inda meron ke shirya yadda zata tunkari izzatu Amma acewar ta sai ta tatsi hon yadda Koda izzatu zata nemi kawo Mata wargi 


Wilson kuwa ya kasa samun nutsuwa don muddin zai runtse idon shi to Babu shakka zai hango ummita bare kuma yace bacci zaiyi kaf burinshi da tanajin shi zai Kare ga mafarkin ummita abinda ya tabbatar sonta Bai Kama shi don ya sake shi ba yayi zaton abin nawasa ne amma ya Gane yafi karfin wasa


Gaba daya ya fice hayyacin shi har ya Daina fita ko Ina ya kwanta jinyar ciwon so 

Zuciyoyin shi sukayi ta kawo mishi shawara bi da bi har dai ya yarda ya dauki shawarar karshe ta yaje kofar gidan su ummita ko da ganinta ne yayi ya rage radadin sonta

Ai kuwa ya Mike ya fice sai gashi kofar gidan su ya faka motar can gefe ya dawo nesa kadan da gidan ya zauna Yana zubawa kofar gidan ido


Zaman shi ko minti talatin ba ayi ba ta fito cikin motar ta tafice inda ya bi motar da kallo ko ba komai yaji sanyi tunda akalla dai ya hangota inda wata zuciyar ke fada mishi yabi bayan ta zuwa inda zataje ko ba komai zai Kuma ganin ta ai kuwa ya dauki motar yabi bayanta inda suka hadu a traffic wadda ta tsaida su ya juyo Yana kallon ta inda yaga tsantsar kwarjini da haiba inda ya tabbatar ita din me kyau ce 


Jikinta ya Bata lallai ana kallon ta sai ta waigo inda idon su ya hadu yaji wani Abu me kama da Jan shock ya fizgeshi ita Kuma tana kallon shi ta tabbatar shine me kallon ta sai ta dauke kanta danjar ta Basu hannu suka wuce inda bisa Dole ya koma gida inda yakejin ya samu hanyar rage kewa


Advertisements

Da yamma ya fito da zummar siyo kayan shayi ya wuce ta kuki cafee inda ya hango ta tafito daga kukin rungume da takardu ta bude motar ta SHIGA ta ja ta nufi gida 

Atake ya Gane kuki ta fito zuwa dazun me yuwa computer take karanta 

Ya wuce abin shi itama ta wuce batare da tasan yanayi ba


Satin da gambo mafiyas ya dawo daga Lagos ya Kuma samo abin duniya Wanda suke karewa ga Matan banza da kayan maye don basa tsinana abin arziki don haka ya Isa gidan izzatu Yana zukar tabar iblis wiwi


Da sauri ta toshe hanci tana tofar da yawu

“Haba gambo meye haka zaka shigo min da wannan shegiyar tabar me warin Kashin jaki? Don Allah koma waje ka zuke abinka ko dadin me kukeji acikin zukar hayaki hayakinma irin wannan da ko dadin Shaka Babu?………..”yi hakuri hajiya kan ne in Babu hayaki fanko ne Rayuwa ta in Babu mandular Nan akwai damuwa har Rashin lafiya nake kwantawa idan ban busa ta ba


Ya murtsuke sauran ya saka aljihunshi

“Yauwa to haka dai yafi don har kaina ya soma juyawa Nima ka sakani kwalewar Dole


“Yauwa hajiya Ashe akasi aka samu wurin aiki?

“Ai shiyasa nafi yarda da aikin ka yanzu Yaya za ayi kenan?


Ki bar komai a hannu na hajjya Ina me tabbatar Miki Nan da Rana irin ta yau wancan mutumin ya SHIGA UKU ke dai ku tanadi kudi don kin San Ni bana tare da tsautsayi ko kuskure bare wani Abu Wai shi sabani…….


“Karka damu gambo idan aiki yayi kyau ma za a biyaka kudi lunki uku Kai dai baje basirar ka kayi aiki me shegen zafi don ka samu sallama me kyau….


“Angama hajiya bani sati guda Daya kacal zakiji mugun albishir da haka sukayi sallama ya fito ya Kama gabanshi inda izzatu ta Kira Kabir take sanar dashi yadda sukayi da gambo mafiyas yace yayi daidai Kuma zai biya gambon lunki hudu ma ko biyar matukar dai aikin shi yayi sanadin fakuwar eng AK


Cikar satin da gambo mafiyas ya diba yayi daidai da kammaluwar aikin shi inda ya Kira Kabir yace yaje wurin hukuma ya sanar da akwai wani da yake kisan yaran mutane yau ya kashe wata yarinya ya sako a motar shi don haka su tashi Jami ansu da binciken motocin mutane ta haka ne tarkon zai Kama eng AK.


Aikuwa atake Kabir mashi kashe arna ya Kira wayar D P O ya sanar dashi abinda gambo mafiyas ya sanar dashi inda Kuma suka tashi Jami ansu aka soma checking point Wanda duk motar da zataje ko tazo sai me ita ya fito ya bude but sun caje komai kafin su bashi izinin tafiya


Bawan Allah eng abdukarim ya taho batare da sanin mugun qullin da aka hada mishi ba ya taho inda ya iske dogon layin na checking point Wanda ake ta bincike motoci shima ya bi layi batare da sanin shi ake son ganin baya ba ba Kuma Wai idan yajuya zaiyi tafiya ba. A a ganin baya na har abada inda ake son kasa ta rufe idanun shi…………….


Ubangiji kayi Mana sutura kar ka Bari makiya suga bayanmu 🤔

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like