ZAN FASA KWAI 34

Advertisement

                *Page 34

*_____________________________________*

……….Bincike tamkar za a binciko yadda uwa tayi ciki har ta haife lamarin da yazo mishi da wani irin rudani har yakasa Gane inda mafita take bayan ta Allah

Yasha tambayoyi har na tashin hankali inda lamarin ya koma hannun C I D inda kuma suka rikeshi Wai sai sunyi bincike agidan shi


Wayarshi ma kasheta akayi don kar ya Kira wani ko wani ya kirashi,


Lubabatu da sukayi dashi ba zai wuce shida na maraice ba gashi har takwas da Rabi tayi mamakin abinda ya tsaidashi don ta San baya son yayi sallar magruba a waje 

Ta jawo wayar ta ta doka mishi Kira Amma abin haushi matar Nan me zakin muryar tsiya na sanar da ita sai dai ta sake Kira lokaci na gaba yanzu Wai ba za a samu layin ba

Advertisements


Haka tayi ta jaraba Kiran wayar shi Amma ta kasa samun shi Dole ta hakura ba Kuma hakura tayi ba tunanin abinda ya tsaidashi da kuma Rashin samun wayar shi don tasan ba lafiya ba  don ta San wayar shi Yana da caji 


Ummita ta shigo Mami Ina Abba ya shige yau har yanzu Bai dawo ba? 

“To Ni kuwa ina Zan sani ummita? Gaba na dai na faduwa don na fara tunanin ba lafiya ba…………


“Mami bara na Kira wayarshi naji inda ya tsaya…………….

“Wayarshi Bata shiga na Kira na kasa samun shi Ubangiji yasa dai lafiya.


Hankali ya kasa kwanciya inda ummita tace zata Kira haj mama taji ko ta San inda abban ya shiga Amma lubabatu ta ce ta saurara tukuna

Sai dai har Sha dayan dare Babu wani Abu ko da na samun wayar shi ne Dole lubabatu ta Kira wayar haj Mama wadda har ta fara bacci ta jiyo karar waya ta farka tana tambayar lubabatu lafiya kuwa?


Advertisements

“Hajiya AK ne har yanzu Bai dawo ba Kuma duka layikan shi arufe shine ko ya fada Miki zaije wani wuri? 


“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un Wallahi lubabatu bai fada min ko zaiyi tafiya ba Kuma kince duka layi kanshi basa aiki ? Eh wallahi hajiya Amma Bari na Kira abokin shi zayyan ko ya san inda yaje da haka lubabatu tayiwa haj mama sallama ta Kira wayar zayyan din take tambayar shi ko yaji AK din zaije wani wuri Amma ya sanar da ita Bai sani ba Rabon shi dashi tun la asar.


Hankalin lubabatu da ummita ya tashi matuka gaya har dai bacci ya gagari idon su suka kwana salla suna fadawa me babbar rumfa me iko akan komai me tassarufin Al amura haka suka kusa kwana zaune inda Mubarak da Ahmed da Fatima ke ta sharar bacci abinsu saboda yarinta da kuruciya


Wayewar garin na laraba yazo musu da wani irin tashin hankali domin ko Jami ai ne daga hukumar bincike ta C I D suka diro gidan eng abdukarim inda lubabatu ta rude da Ganin su suka Fara yi Mata bayani


“Karki damu hajiya tambayoyi ne kawai Zaki amsa Mana da Kuma binciken da zamuyi agidan Nan saboda an Kama me gidan Nan da part part din mitane amota…………….


“,Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un hasbunallahu wa Ni imal wakil Allahumma ajirni fee musibaty haza wa ahalufnee khairan minha.


“Abdulkarim din ne akewa wannan zargin? Ubangiji ka bashi mafita da mafitar ka……..

“Kar ki damu hajiya bincike muke tukuna ba Wai an tabbatar ba abinda kawai muke so shine ki bamu hadin Kai mu gudanar da binciken komai zai daidaita da yardar Allah,

Ta share hawayenta da habar hijabinta ta soma amsa masu duk tambayoyin su har suka Kare suka shiga bincike gidan shima Allah da ikon shi ko wata kakkaifar wuka Basu samu ba da haka suka kammala sukayi Mata sallama bayan sun sanar da ita Yana hannunku


Kuka ummita keyi tamkar zata hadiye zuciyar ta inda lubabatu ma ta ke nata kukan sai yaran ma suka dauki kukan Babu Wanda yayi kokarin rarrashin wani inda Kuma haj mama ta taho gidan don taji ko AK din ya dawo don itama ta nemi wayar shi yafi akirga Amma Bata sameshi ba sai ta iske iyalan gidan sunata rizgar kuka


Hankalin ta ya tashi inda lubabatu tayi shiru tana korawa hajiyar bayani abinda ya gigita hajiya Mama itama ta fashe da nata kukan sai da kyar lubabatu ta rarrashe ta inda tace ta bari yanzu zasuje su ganshi


Suka hada mishi kayan kalaci suka tafi su duka inda hajiya Mama ke ta sharar hawaye inda suka taho har da talai itama hawayen takeyi


Sai dai duk yadda suka so ganin abdulkarim din lamarin ya ci tura Wai ba zasu ganshi yanzu ba sai dai ko Nan gaba an dai karbi abincin an Kai mishi Amma ganin shi sunce ba yanzu ba

Kuka hajiya Mama take tana rokon su su taimaka Mata ko hango shi ne tayi in ba zatayi magana dashi ba to su nuna Mata shi ta hango lafiyar shi………………

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like