DUDUWA 35

Advertisement

   *”Gashi nan!!gashi nan!!,Na dudu ya diro gareku masoya afin alfahari na, yau dai na san ba yajin aiki ko ince zanga zanga🤪nayi wuf na sambaɗa muku typing yadda kuke so,ina jin daɗin comments ɗinku da yadda ku ke ƙaunar Na dudu thanks Alot fan’s🤭*


_*Sis ba kama suna nasan ƙaunarki da littafin nan yasa kika ce ina ja muku rai,so ba haka abin yake ba ni kai na nafi son na kammalashi a ƴan kwanakin nan abubuwa suka min cha bayan da na zata ba,sannan typing ba wasa bane duk yanda kika ɗauke typing sis yafi haka dan Allah mu dinga yiwa junna uziri na gode da kulawarku akaina kuma ina jin daɗin yanda kuke love ɗin Na dudu a koyaushe😘❤️😘*_
~35~Advertisements

        Duk yanda kulu ta dauki abin yafi qarfin tunanin ta domin sai da ta kwana ta yini cir a ɗaki bata leƙo ko da ta tagaba ga masifar yunwa da ƙishirwar da ke damunta duk ta fita hayyacin ta ta rame tayi zuru zuru sai nishi take tana katantanwa a ƙarƙashin gadon ta har ta samu ta fito tsakiyar ɗakin tana nishi da ƙyar,shi ko Na dudu na kwance a ɗakin sa kan katifa wani mutum ya bayyana a kansa sak mai gari babu abinda ya banbanta kamanin su ya nemi gefe kusa da inda na dudu ke kwance ya zauna haɗe da kai hannun sa kan sumar dake kan na dudu ya shafa a hankali ya ambaci sunan Na dudu,Na dudu ya buɗe idonsa tar akan mutumin da sauri Na dudu ya miƙe ya faɗa kan mutumin yana faɗin””


“Yoyo oyoyo baba ya dawo.


ƴar dariya mutumin yayi ya kuma shafa sumar kan Na dudu ya ce.


“Kaga ɗan gidan baba ina innar taka take kazo ka kwanta kai ɗaya anan.


“ta koro ni baba yunwa nake ji ina jirgin samma na da mota ta?


    Ga su nan duk na sayo maka,mutumin ya fidda jirgi ɗan ƙarami da mota ƙarama me fitila ya miƙawa na dudu yana cewa”


Advertisements

“ajiye su a gefe kazo kaci abinci idan ka gama kaga sai ka ɗauki kayan wasanka kayi wasa har kankana na sayo maka innarka ta baka ɗayar dana bar maka kuwa?


“imm imm bata bani ba baba.


to ai ga wata na sayo maka irinta waccan kuma kabarwa inna.


to baba amma bazaka kuma tafiya kabarni ba ko baba?


eh mana babu inda zan tafi na barka yaro na amma yanzu zan koma na kuma sayo maka motarka da jirginka ka haɗa guda biyu kayi wasa maza sakko kaci abinci kaji ga shinkafa da farfesu harda kankana kaci ka ƙoshi dam na sake sayo maka wata motar da jirgin samma har da babur,mutumin me siffar mai gari ya gyarawa Na dudu zaman sa ya saka masa shinkafa da miyar zabbi da kan kana yace yayi bisimillah yasaka hannu ya ci yana murmushi wa na dudu,Na dudu yayi bisimillah kamar yanda mutumin ya koya masa yaci shinkafar kaɗan yasaka farfesun zabbin a gaba ya ci da yawwa haɗe da shanye kwallon kankanar gaba ɗaya kamar ba acikin sa Na dudu yake zubawa ba nan da nan cikin na dudu yai ƙurjaja tsabar ƙoshi sai gyatsa yake zubawa mutumin ya juya bayansa ya ɗauko ruwa a ƙoƙo ya kama hannun Na dudu ya wanke masa ya haɗa da bakin shima ya goge gefan da ya ɗan ɓaci ya sake sakarwa na dudu murmush,na dudu ya buɗe baki ya ce”


“Baba kashi zanyi.


Kashi ɗan gidan baba ai ga foo ɗinka a kusa,hannu mutumin ya kuma miƙawa baya ya zaro foo ɗin ya umarci na dudu da ya tashi ya hau da taimakon mutumin na dudu ya hau kan foo ɗin har ya gama ya wanke masa a ɗakin yace dana dudu”


Ɗauki sauran abincin ka kai wa innarka tana ɗakin ta kace ka ƙoshi kaji ni zan koma na kuma sayo maka wasu kayan wasan idan ka shiga ɗakin kayi sallama.


Kafaɗa Na dudu ya noƙe haɗe da cewa”


       “dukana inna zatayi idan na shiga ɗakin da foo.


baza ta doke kaba tace ta dena dukan ka kaji ɗan albarka.


Na dudu ya gyaɗa kai ya fara ɗaukar shinkafar ya fita dungul dungul da shi har ya nufi ɗakin kulu ya faɗa kai tsaye da sallama a bakinsa kamar yanda me kama da mai gari ya faɗa masa gaban kulu dake baje a ƙasa na dudu ya dire shinkafar ya fito daga ɗakin ya yi nashi farfesun ya ɗauka kamar zai kifar ya dai taho dashi har ɗakin kulu shima ya aje ya fito da gudu yana tsalle tsallen sa na yara ɗakin ya kuma komawa ya tadda mutumin a tsaye da fo a hannu,na dudu mutumin ya miƙawa foo ɗin yace shima ya kaiwa kulu ba musu na dudu ya ɗauka ya kaiwa kulu da ta dasawa shinkafa wawa tana ci tana fidda hawayen wahala ganin kashi a gabanta ta fara yunƙurin amai tana ƙoƙarin dawo da na bakin ta.


 

fitowa Na dudu yayi daga ɗakin a guje ya shiga inda mai garin yake ya faɗa masa murmushi mai gari yayi ya janyo Na dudu jikinsa suka koma suka zauna mai gari ya fara bawa Na dudu labari me kama da ta tsuniya da manya manyan aljanu da suka shekar dubu suna keta hazo daga daula daula har na dudu yayi bacci mutumin ya kwantar dashi haɗe da luluɓe masa ƙafa ya ɓace daga ɗakin gaba ɗaya..


……

Shiru shiru liman zai zo biko bai zoba ƴarchakare sai ware ido take tana kuma roƙon malam jibo da ban haƙuri malam jibo yace sai liman ya tako gidan da zumar biko ƴarchakare tayi ta Addu’a idan liman bai zo biko ba ta ɗau dangana,kuka ƴarchakare ta fashe dashi tana”in Allah ya yarda ma baba zai zo yau yau ɗin nan roƙona ka yi haƙuri ka ƙara haƙuri ka yafe mun na koma idan na kuma yin wani abu na yadda kayi mun komai baba ni dai yanzu na koma ɗakina,malam jobo ya amsa da”ai shikenan Allah ya kawo shin idan da rabon komawar ki tashi ki surfa geron chan kafin anjima ki tisa na dawa.


    Kuka ƴarchakare ta kuma ɓarkewa da shi sai du’a’i take tana Allah ya yanke mata ya kawo malam liman.     Zaman dije da liman abun sai son barka dan dije kulawa sosai ta ke baiwa liman haka shima liman kullum akan farantawa dije yake duk abinda ya fita ya rakito dije zai furta har yaɓen ɗakin dije ya sake mata sabo ya sayo ledar sabowa ya sanya mata a tsakar ɗaki ciki da waje har da madafa abin gwanin ban sha’awa inka shigo gidan ka iske liman da dije da su Ya’u da Adamu suna fira suna cin balangu ko tsire wani lokacin har kaza Ya’u ko Adamu suke sayowa a hanya gashsshiya su taho dashi gida,sitira sai da liman ya gaji da godiya da ɗan hassafin dasu Adamu ke bashi ko wane ƙoƙarin farantawa liman da dije yake wajan gwangwaje su ga shi har sakewa dije kayan ɗaki da kwanukan amfani suka haɗa hannu su biyun sukayi ga sutura ita ma dije ta sa wannan ta cire wannan sai Addu’a take wa yaranta da godiya sun mai da ita amaryar dole matan maƙota sai neman wajan zama suke dije ta ƙi yadda kusan lokacin da ƴarchakare ke gidan tare da ita suka ƙullawa dije komai suka haɗe mata kai har dena kula dije sukayi da anganta za afara yi da ita ido da ido akan ƴarchakare malam liman har baya son a ambaci sunan ƴar chakare a gabana tsabar kwanciyar hankali da samun komai baja baja.🤣🤣 

_*By*_

_*Maman Dr*_

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

DUDUWA 22

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…

DUDUWA 23

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…

DUDUWA 26

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…

DUDUWA 9

Advertisement  _*🧟‍♀️DÛDÛWÂ🧟‍♀️*_           _9_ Ko kawar fitowa daga cikin motar jama’a suka fara yi,tsabar…