DUDUWA 36 (END)

Advertisement

                                🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

~36~

    Sai da cikin kulu ya ɗauka hankalinta da ganin ta suka dawo ta zubawa mazubin farfesun zabbin ido da kwanon shinkafar data cinye su duka har zata miƙe zaune tuno da wanda ya kawo mata kayan ya dire a gaban ta ta kuma komawa ta baje a ƙasan tana hango hoton ƙafafuwan data hanga jiya a idon ta kulu tafi sakan talatin kwance a tsakar ɗakin bata motsa ba har baci ya fara ɗaukar ta ganin zata lafke yasa ta miƙe a daddafe daga kwanchan data yi jikin ba laifi da ƙwarin sa ta samu ta rarrafo zuwa ƙofar ɗaki,kanta ta ɗan leƙo dashi kaɗan ta hangi tsakar gidan fayau babu ko mai a wajan kulu bata yadda da hakan ba tasake tura kan ta a karo na biyu nan ma bata hangi ko mai ba ta ƙarasa rarrafowa tsakar gidan cikin sauri har inda randar ta take ajiye, ƙatuwar moɗar dake kan randar ta wawura ta kamfato ruwan ciki ta maka abakin ta nan da nan kulu ta kwankwaɗe shi ta sake kamfato wani ta kuma shanye

wa,gatsa ta shiga jerawa ta waiwayo zatayi ƙofar waje ƙara da bajewa a ƙasa kulu tayi ganin guntun abu akan ta na ɓaɓɓaka mata dariya da gudu Na dudu yayi ƙofar ɗakin sa dan shima ƙarar kulun ta firgita shi sai da Na dudu ya tsaya ya zubawa kulu ido ta tabbatar da shi ɗin ne akan ta ta miƙe ta runtuma soro a guje zata fuce daga gidan turs kulu tayi a gaban tarin turɓaya da ta rufe ƙofar fita daga gidan ta shafe kamar ba hannu ne ya ƙera ta ba.

      Kuka kulu ta sake sakawa data share hawaye wani zai biyo baya gashi ta gumtse bakin ko ehim bata iya cewa saboda tsoron kar mutanan su jita ba yanda ta iya ta sake juyowa zuwa cikin gidan,tukunya ce me lamba 100 ƙatuwa akan murhu shima ƙato a tsakar gidan sai ƙamshin girki ne yake tashi lamarin daya ƙara dugun zuma hankalin kulu ta kwaɓe baki tana ihu da kuke koken ta shiga uku”yanzu yanzu na wuce babu komai a tsakar gidan yanzu kuma ga ƙatuwar tukunyar da ta bayyana a hankali kulu ta raɓa ta gefe zata shige ɗaki taji ance””


_””Kar ki take mana ƴaƴan mu._


ƙam kulun ka ta ƙame a wajan ta runtuma ihu da gunji mara daɗin sauraro haɗe da roƙon ta tuba bazata ƙara ba dariya akayi aka sake cewa””.


Advertisements

_”Kuka ba zai miki maganin komai ba tunda ke zuciyarki ɓatacciya ce bata san tausayi da taimakon marayu ba ki je ki sauƙe mana abinci kuma ki rarrabawa kowa na shi._


Ƙassa kulu tayi zata faɗi aka wanka mata wawan marin daya sa ta tsayawa dai dai tayi kan tukunyar tana kiran”


“Gwaggoooo!!!!!!!!!!!!


Duk yanda kulu taso ta sauke wannan tukunya abu yaci tura ko alamar motsawa tukunyar batayi tana gani dangi guda suka bayyana a gidan inda take ma wata ƙar guntuwar tsohuwa fara tas farin har kore kore yake me gashi tun daga kanta har ƙasan ƙafarta sai baki take wagewa kulu, kulu kuwa ganin bala’in da bata taɓa zata ba ta suma yayi sau bakwai tana farfaɗowa kukan ma kasawa tayi daga ƙarshe aka tsamo kulu aka aje a tsakiya kowa na cin abincin sa har da Na dudu daya shiga gayyar yara suna ta wasa wasu har wagewa kulu baki suke kamar zata faɗa ciki ranar dai kulu mutum mutumi ta koma ba ehim ba im im har suka gama wadaƙarsu da warshasshagale wale ɗun su suka ɓace da kayan su gaba ɗaya,da yamma Allah ya dawo da mai gari da mudi da kayan arziƙi fall a ledar daga burni da zumuɗin ganin Na dudu mai gari ya faɗa cikin gidan bayan ya gama gaggaisawa da kowa,mai gari na shiga gida ya iske kulu a summe a tsakar gida Na dudu kuma na ɗaki yana shirgar bacci ya gama kwasar ta tsotsan ƴan uwansa🤪Asibita aka kwashi kulu aka miƙa ta bayan allurai da ruwa da magungunan da kulu tasha babu wani sauƙi data samu sai ma ƙaruwar ciwo da wani irin kukan mage datake yi gwaggo ta bada shawara a koma gida ayi mata addu’a hakan kuwa akayi aka dawo gidan mai gari aka duƙufa gayawa Allah ana bawa kulu rubutu cikin ikon Allah kuma ta tashi,kulu na tashi ta zabura ta wawuri Na dudu zani ta fusga daga hannun gwaggo ta saɓa Na dudu a baya ta goya tari idan Na dudu yayi to kulu bata zama sai taji ya dena daga wannan rana kulawa da Na dudu ya dawo hannun kulu ƙarewa ma a ɗakinta ya tare ita ke masa wanka tayi masa wanki ta bashi abinci a baki siye siye kuwa babu abinda kulu bata siyawa ɗan ta acewar ta,murna sosai mai gari yayi da sauyawar kulu shima nan da nan ya shiga gwangwaje kulu yasa aka buge ɓangare ɓangare na gidan aka fara ginin bulo abin fa sai san barka komai ya dawo sabo ga rayuwa na cigaba Na dudu na girma har aka jefashi makarantar boko da islamiyya.Advertisements


******

Bayan wuyar da ƴarchakare ta sha a gidan su ranar da liman yayo biko ya maido da ita kwana tayi tana masa godiya da yiwa dije biyayya da jin bari da yi kam ƴarchakare ba a magana sau da ƙafa take bin Dije Umma samma Umma ƙassa ƴarchakare ke kiran dije,malam liman kuwa yayi kyau yayi ƙiba duk inda ya faɗa riritashi ake kamar ɗan jariri abinka da malamai lumi yayi da ƴarchakare ta dawo ya’u da adamu kuwa arziƙi ya bunƙasa sun mai da dije babbar mace har gida suka saya mata suka kuma biyawa dijen da liman kujerar hajji ita kuma ƴar chakare suka biya mata Umara.
*Alhamdulillah,anan na kawo ƙarshen alƙalami na akan rubuta wannan littafi,ina roƙon Allah ya yafe min kurakuran da suke ciki abinda yake dai dai kuma Allah yasa mu amfana,dama komai yayi farko to zai yi ƙarshe babu abinda baya wucewa sai ikon Allah,Allah ka iya mana baki ɗaya😍*


*Sannan ina miƙa godiya ta ga masoya wanda na sani dama wanda ban sani ba yadda kuke ƙaunar littafina nima haka nake ƙaunarku fatana Allah yabarmu tare ya ƙara zumunci da wadata na gode na gode sosai masoya ina alfahari da ku,ina fatan zamu yi ibada cikin ƙoshin lafiya Allah yasa muna daga cikin ƴantattun bayi yasa muga farkon Azumi da ƙarshen sa lafiya mu dage da ibada da ambaton Allah da karatun Al’Que’ani😘❤️😘*


_*ƊAN ƊANO!! ƊAN ƊANON SABON LITTAFI NA WANDA ZAI ZO MUKU INSHA ALLAH BADA JIMAWA BA MASOYA KU SHIRYA TSAF💃🤣*_

_*‍👳‍♂️👳‍♂️👳‍♂️TSANGAYAR👳‍♂️👳‍♂️👳‍♂️*_

                  _(Malam)_

                       
*Na*

_Maman Dr__*🗣️🗣️”””Ina makaranta littatafan mu, ku matso ku gyara ku kintsa da kyau kuji sabon kafce me nishaɗantar da makaranta ya mantar da kai duk wata damuwa datake damun ka cikin ƙanƙanin lokaci,wannan littafin yazo da sabon zubi da salo daban da sauran kai dai biyo ni ka kwashi garaɓasar nishaɗi da nishaɗantarwa a koyaushe,taku a kullum @Maman Dr😘*_


                1️⃣-2️⃣       “””Gauro gauro ……


gauro!!!


 “Tashi gari ya waye.………


 gauro!!!


“Mai azumin gema ge………


gauro!!!


“Mai sahur da ƙaragu………


gauro!!!


“Katashi gari ya waye…………Yara ne danƙam sun cika gari sai buge bugen kwanuka da jarkoki suke suna yawo ko ina suna waƙar gwauro musamman majalisar da samari ke zama da shagunan samari da yawancin su a buɗe suke sun taru suna fira,Ɗan malam da ke zaune cikin su baƙiru da nafi’u ne ya dubi samma da farin gajimare ya gauraye sararin samaniya ya ce”


“Wai ni ko Baƙiru anga watan azumin nan ne a garin nan ko ko ba a ganshi ba?

   ɗan malam ya karkata wuyansa yana duban baƙiru da ya mai da hankalinsa ga ɗan malam ɗin ya amsa da.“Ai ɗan malam ba a iya garin nan ka ɗai aka ga wata ba an ganshi a garuruwa har guda bakwai kuma sarkin musilmi ma ya shaida hakan insha Allahu gobe war haka mun kai azumin Ramadana ɗaya.


Haba dai baƙiru kai yaushe kaji an faɗi haka ance an ga watan azumi?


a radio naji da inna ta kunna kasan mayyar jin labarai ce safe da dare kuma naji baƙo ma yanzu da zan fito ya shigo gidan yana faɗawa inna a tsakar gida ga kuma yara na murna kaga magana ta ta gasgata yau dole katashi kayi sahur ka dauki niyar yin *AZUMI* ɗan malam.


samma ɗan malam ya hanga yana kuma ware idanuwansa duka biyun ya ce”


      “Hmmm ni dai har iyau banga watan azumin nan ba sai ware ido nake ko zan ganshi.


“,Taɓ ai wallahi ba zaka ma ganshi ba duk wani gwale gwalan idon da zakayi Azumi dole kayi shi haka zalika idon Allah bai nufeka da ganin wata yanzu ba to wasu bayan Allah sun gane maka malam ka ɗaura niyya tun daga yanzu Dan yasin bazaka ga komai ba na harbo jirgin naka inda ya nufa.amma ko Allah wadaran munafiki ɗan munafuka ɗan sa ido kai kaji NAFI’UN nan daga ji nayi magana sai ka kwaɓe baki kace wani ƴan ƴan ƴan,kaga nafi’u ban kasa da kai ba balantana ka ɗauka ko na kirayi sunan ka tunda nazo nan wajan Dan haka bana son mutum ya shiga shirgina wallahi zan maka abinda nayiwa alabaka shekaran jiya.


kai kaji wawa baho to ai sai kayi mun kaga in zaka ci riba wallahi sai na rama ni ba alabaka bane da zanji tsoron ka na kasa taɓuka komai nafi’u nake duk iya shegen ka kasan na dameka na shanye yaro.


ni ne yaron naka?


babba ma kuwa idan kana cin ƙasa to ka kiyayi shirun ta.


to shikenan ka zuba ido kaga yanda zata kwashe dani da kai Allah sai na manna maka hauka tuburan ba dai dani kake musu ina faɗa kana faɗa ba hmmm.


 kaga malamai duk ba abin tada jijiyar wuya bane kun cika mana kunnuwa da surutu duk abar maganar ma ta wuce azumi kuma gobe in Allah ya nufe mu da rai da lafiya warhaka mun idah ɗaya.


idan na haƙura shege nake baƙiru sai na mannawa wannan sokon hauka tuburan akan sa bari ma kaga ina zuwa.


haba ɗan malam daga maganar azumi sai ta zama faɗa ka tashi dan Allah ka dawo mu yi maganar da zamiyi ta gonar baba Hashimu mana.


sai dai ku je kuyi abar ku indai da wannan abun za’ayi yasin na fasa ,ɗan malam ya nuna Nafi’u da yatsa ya ɗora””tun daka ɓatan rai kaf gidan ku sai ransu ya ɓaci ni na faɗa maka.Idan baka fasa ɓatawa dangin mu kaf rai ba baka cika jinin malam ba har ni zakayiwa burgar banza da kake yiwa wasu sokayen.Ohhhhhh Allah na duk zaka amayar da zantukan nan ranar da ka ka kasa gane hanyar gidan ku ohhhhhh shatttt amma ko Nafi’u kazo da wasa ka dugunzuma zuciyata ka karkatar da lissafina akan kaf dangin ku gaba ɗaya kuma na rantse maka da Allah bazaku walwala a cikin garin nan ba mudin ina ciki,Dan malam ya juya afusace yayi qofar gidan su,yana zuwa dai dai qofar gidan ya banko ƙyauran ya faɗa kai tsaye Baƙiru sai kwara masa kira yake yana”””


“ɗan malam!! ɗan malam!! ɗan malam, ko juyowa be yi ba ya nausa kansa cikin gidansu ya na kwara kira”””


“”Malam!! malam!! fito ga tambaya me ma’ana tunda kune manyan malamai magada Annabawa.


tsuke bakin sa ɗan malam yayi ya chake akan wata dattijuwar mata ya na.


“Kaga Uwailan malam me taro da sisi yau kuma me ake shirya mana,wai shin ma ina malam yake tun da na shigo nake ta faman kwara masa kira bai amsa ba ban kuma ga ƙeyarsa ko sayyadarsa ra leƙo ba ina malam ya nufa ne Uwaila?“yatafi koyo sallama.

 

Uwaila ta bawa ɗan malam amsa ko ɗagowa batayi ba kan ta na kan tace giron da take murmushi ɗan malam ya saka ya gyara tsaiwar sa ya ce””“”Koyon sallama kuma bayan sune masu koyar da yin sallamar ko dai zakkah yatafi karɓo mana ne Uwaila sanar dani da da wuri mu fara kasafta namu rabon.

    hmmm uwalai tace ta cigaba da safgar gabanta ko ƙala bata ce da ɗan malam ba,shima ɗan malam ɗin ganin Uwaila tayi masa shiru yasa ya tsuke fuskar sa ya ɗan sunkuyo kan Uwaila ya ce””


Uwaila!! uwaila!! kenan ki amsa mini da wuri kar ki shiga layi yanzu haka rai na aɓace yake ina malam ya nufa na ce miki?*@Real Maman Dr✍️*


_*By*_

_*Maman Dr*_

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

DUDUWA 24

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…

DUDUWA 27

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…

DUDUWA 3

Advertisement _*🧟‍♀️DÛDÛWÂ🧟‍♀️*_           _3_  Fadar cike take taf da mutane wasu a zaune wasu…

DUDUWA 2

Advertisement 🧟‍♀️DÛDÛWÂ🧟‍♀️*_            _2_ Bakin rijiyar Duduwa ta nufa cikin rashin sa’a Bata iske…