DUK NISAN JIFA 28

Advertisement

                     28

Bilkisu ta bi shi da kallon sama da kasa kafin ta shiga bin shagon da kallo a bayane ta ce” Bakama san safia ta yi ba ko? “

Da sauri ya zauna dan daga shi sai dan gajeran wando a jikinsa yana ta mamatse kafa dan har fitsaro yake ji ga tsorata shin da ta yi, dan Walahi bai taba kawowa ransa ganninta ba a duniyar bale wai har a gabanshi da safiar nan


Bilkisu ta yi tsaye jikin dogon abin da wayoyi ke ciki ta rungume hannayenta a kirjinta ta ce” To yaya zaka yi da ni? “


Kuma dubanta ya yi sai ya sada kansa hakan ya sakata da karfi karfi ta ce” Ba da kai nake ba UMARU? “


da sauri ya dago da kuma mamaki yana kallonta, muryarsa a shake ya ce”  Ban gane yaya zan yi da ke ba Bilkisu, hala Aba bai fada maki sakona ba?”

Advertisements


Bilkisu ta masa kallon uku dala ta ce” ashe vaka da kuzarin kawo min gwa da gwa sai dai ka aiko ubana ya kawo min? An fada maka nima dan ina sonka aka daura mina aure da kai? In ba dan mutuwa mai saba lamura ta dora su yanda take so ba Umar ina ni ina mijin da yayata zata aura? Mami ta so ka da zuciya daya , tana jin kunyarka tana kaunarka da a haka ka yi niyar aurenta? Ka ce da ita me? Ka halaka min ita dan bata magana? Allah daya da a lokacin zaku gane mahaukaciya ce ni baki dayanku! Ka godewa Allah da Allah bai baka damar cutar min da ita ba, da ba abinda zqi hanna ni nemanka lungu lungu ko ni ko kai!”


Kunya ce ta ringa kama shi da mamakin ashe haka ta iya masifa? Dama ta iya fada haka? Kuma ta san dalilin da ya saka shi sakinta to me ta zo yi shagonsa? Dan ta masa gargadi?


Bilkisu ta sasauta muryarta ta ce” An ce maka dan wannan abin nake iya zama da kai, ina iya zama da kai Umar ko dan soyayar da yayata ta yi maka a duniya, ni ban san komai ba bale ya dame ni! A kan me zaka watsa kin kasa a ido ka min saki irin na wulakanci har saki uku? Bama wannan ba kai kennan ba zaka rayu ba haka zaka zauna kana bakin rai da kumbiya kumbiya ba zaka nemarwa kanka magani ba ko dai da gaske ne sharin da aka ce ana maka a gari cewar da maza kake harka? “


A zabure ya kuma kallonta har wata zufa na sin keto masa ya ce” Ashe baki da kunya Nana? Kina bafilatana kina sakin magangannu haka daga bakinki me na maki to ni? Na ga dai ba soyaya muke ba bale ki ce na yaudare ki da soyaya, ko yayarki kin taba gannin mun yi kalaman soyaya da ita? Bari ki ji mahaifanmu ne zasu hada mu wai dan mu rufawa junna asiri a bar kallona a matsayin wanda ya kasa yin aure, itama a bar mata kallon ta tsufa bata samu miji ba! Ni babu yar wanda na je na yaudara na furta mata kalmar so ko na bata mata lokaci dan na san bani da lafiar da zan iya rayuwa da mace, Namiji kuwa bana cikin wa’inda Allah ya dorawa kula maza Alhamdulilah, Balki da yarintarki, da kyanki, da mutuncinki da gatanki kike fada dan na baki damad rayuwa mai kyau? Dan Allah ki yafe min idan nine na saka kika fara fada haka, idan kuwa dama mafadaciyar ce ki min hakuro kar ki yi fada da ni dan ba zan iya ba walahi”


Bilkisu ta sada kanta tana jin hawaye ya cika idannuwanta


Dago dubanta ta yi ta nuna masa wata watsetsiyar waya kirar samsung bata ce komai ba

Advertisements


Cirowa ya yi daga cikin madubinta ya miko mata yana kallonta, bai taba tsayawa ya yi mata kallon tsaf irin na yau ba, kai da ace zai samu lafia da ya ringa yiwa mata kallon tsaf har ya samu wace ta kwonta masa a zuciya, da ace bai saki Bilkisu ba da ya nemi lafia ko ta halin yayane ya zauna da yarinyar nan a matsayin mai dakinsa, ashe haka take da kyau?


Atm dinta ta miko masa bayan ta gama jujuya wayar bata ce komai ba


Amsa ya yi yana kall9n ATM din sai ya mata murmushi ya ce” Ashe hajiar mai kudi ce, to ni sai dai idan baki daya kudin ciki zan wawashe”


Dubanta ta tsaida a kansa ta kasa yin koda murmushi ne hakan ya saka jikinsa ya kara yin sanyi ya miko mata cart dinta yana kallonta


Bilkisu ta shanye kukanta ta ce” Baka anfani fa abin cirewa ne?”


Ajiyar zuciya ya sauke ya dan girgiza kansa ya ce” ina yi, aman na baki kyauta Balki, ba zan saida maki waya ba gaskiya”


Bilkisu ta kalli wayar, ta kuma kallonsa, a hankali ta kai hannunta ta ajiye wayar zata juya ya ce” Dan girman Allah ki dauki wayar nan ba dan na isa ba sai dan ina son wanke kaina, ki yafe min, ki yi min uzuri, ban yi haka dan na wulakantaki ba ko dan na lalata maki sunna ba, bama kowa ya san cewa igiyar wani ta hau kanki ba, na katse hanzarin nan ne dan karma sai kin tare duniya ta dauka kuma na dawo na rabu da ke ta yada duniya zata dauka, ke yar uwata ce , zan so mu yi zumunci mai karfi”


Bilkisu ta juyo tana kallonsa ta kuma sauke dubanta a kan wayar, bata taba amsar sako daga hannun wani namijin da ba yayanta ba, bata taba anfani da wayar da ba yayanta ya siyan mata ba


A hankali ta dora hannunta ta dauki wayar tana ji a ranta zata iya amsa ta fara anfani da abin hannun wani namijin da ba yayanta


Dubanta ta dago ta sauke a kansa ta matsa sosai dan tana wajen kofa ne bata so Laila ta jiyo sirrinsa domin abu ne  mai girman gaske, kuma ta falasa shi haka bai dace ba


Tana zuwa ta  tsaya jikin abin ta rage muryarta sosai ta ce” Akoy magani a duniya, na likita ko na hausa , ni likita ce ina so ka je a bincika lafiarka, idan da rabon ka samu lafia a baka magani ka samu lafia, Umaru baka san adadin shekarun da zaka yi a duniya ba, ba kowa zai fuskanci cewar dan baka da lafia ne ka ki yin aure, tuni an fara yi maka mugun zargi duda ba’a iyawa mutun. Aman tafia na tafia darajarka na raguwa, zaka dawo kunci ya yi maka yawa a ranka, ina anfanin ka kashe kanka da kanka? Dan Allah ka nemawa kanka magani ka yi aure, domin sunnar ma’aiki sallalahu alaihi wa salam ce , cikar mutun mutun  shine aure “


Tana gama fada ta juya ta fita a shagon ta barshi tsaye jikinsa a sanyaye yana ta auna magangannunta a kan mizani, haka kawai sai ya ji wani kwarin gwuiwa, a kasan zuciyarsa ya ringa tunani to wai me ya sa ba’a nema masa magani ba? Yaya aka yi bai kawo neman magani cikin ransa ba har yake rayuwar kunci? Rayuwar kunci mana ba damar ya saka mace a ransa dan bashi da wannan sha’awar, ba damar ya zauna cikin maza a dauko maganar mata a ringa zuzuta abubuwan da shi bai sanma akoysu a duniyar matan ba, ga abokanansa du sun haihu sun masa sunnan mai ruwan ido tuzuru


Tabas ko an masa shari ba abin mamaki bane domin dai da sana’arsa yana samu sosai Alhamdulilah kidi sunna shigo masa, aman ya kasa yin aure sam baya kuka matan ai dole a yi tunanin maza yake kulawa


Daga nan ta wajen gidan sarki suka bi, daga nesa suka tsaya sunna kallon yanda dogarai ke shiga da fita, sannan suka zagaya ta zagayen baya, a nan suka ga wasu dakaran dogarai sunna gadin kofar sai watsa watsan motocin dake shiga wa’inda sai sun nuna katin dake shaida yau suke da appointment da wajen kwaliyar sannan a basu damar shiga


Ajiyar zuciya Bilkisu ta sauke tana bin tsayin ginin da kallo nan ta kuma goyon Laila suka ringa zagayawa a saman babur kasancewar gidan a tsakiya yake du girmansa sai da Bilkisu ta zagaye aman bata ga hanyar da zata iya dirawa ba, da takaicin wannan suka je wajen mai siyar da dambu ta kofar makarantarsu suka yi zamansu sunna hira Bilkisu na fadawa Laila ta fadawa people zata hau whatsup yau, 

Ai kau murna suke , uwa uba da ta ce za’a bude mata Instagram da Facebook du sun yi mamakin yanda aka yi yayanta ya barta shiga Facebook da Instagram.Kai tsaye ya shigo office din gannin cewar ya gama duba mararsa lafia ya zauna yana kallonsa yauma bai cire takalmin kafarsa ba hakan ya sa Hisham bin kafafuwan da kallo


A hankali ya ce” wai cewa ta yi ta tsane ni fa, to me ya yi zafi in ba rigimarta ba tsakani da Allah? Abinda ya kasa gushe min a raina shine sababin hakayan da take nuna min tun daga jiya har zuwa yau, ko dai dama fada ne da ita har haka? To wai meye laifina a nan? Ko dai itama tana jin abinda nake ji? Abinda ya tsaya min a raina kuma shine a kan me zata damu da wani? Ko dai ya nuna mata wata hanyar da ban dora abina a kai ba? Da kuwa na ci uwashi!”


Kader ya hadiye dariar da yake jin tana son kwace masa ya gyara zamansa ya ce” Wai Hisham da wa kake ? Wace kake zancenta? Ko amarsusunmu ce? ” ya karashe yana dage masa gira hakan ya saka Hisham kafe shi da ido


Mikewa ya yi lokaci daya ya karasa wajen kofar ya datse kofar da ky ya juyo yana kallon Kader da ya mike tsaye yana tafa hannayensa yana kallonsa


Hisham ya ce” wani salon iskanci ne yake yawo a kwakwaluwarka da nake son ka zazago shi ko na saka kusa na kunce kan na zazago shi na gyara shi na maida Kader! Ni ka raina kake hawar min kafet da takalmi dan wulakanci? Ba dai amarsusu ba asusu!”


Kader ya yi sauri dukawa yana cire takalman kafafuwansa yana fadin” Allah dai ya baka hakuri, mugun sabo ne ba zan kuma ba”


Hisham ya karasa ya zauna ya ce” zaka bi dukan motsinta, zaka ringa bibiyarta, du wani gaulan da ya mata magana zaka sato min shu ka kawo min shi ka barni da shi, zaka ringa korar du wanda ya so rabarta, zaka ringa yi mata nasiha har sai ta cire wannan sabon hayakin dake kanta, Kader idan wani ya yi gigin yin abin dana sani zan aikata laifin dana sani  a kanta na rantse maka”


Kader dai yana gyada kansa dan baya so ya rike shi a hannunsa gaskiya, gashi ya shamace shi ya rufe kofa


Kader ya ciro takarda mai dauke da tambarin gidan sarki ya ce” Hisham, ni ban gane ba, wai so kake sarki ya zo ya kawo maka yaronsa ko gimbiya? Ka san dai ba fitowa zasu yi da rana tsakiya ba dan kawo maka shi ba ko? Kai kuwa ka ce baka aikin dare, ka duba fa rubutu ne na hankali aka rubuto maka cewar idan Har Allah ya sa ka samu lokaci ka je dan duba yaronsu dake fama da rashin lafia, da ace da garage ne zai hauka sai ka ringa masa hanya hanya, ka san da yana da damar baka umarni kuma ka bi ko? Aman sai yake lalashinka dan shi din mai mutunci ne, dan Allah ka taimaka ka je ka ga yaronsun nan an ce yaronsa na farko da ya rasu irin ciwon ya yo, wai sai ya ringa summa ga zafin zazabi “


Hisham ua sauke ajiyar zuciya ya ce” ka gane Kader, ni ba zuwan bane nake ji irin idan na tashi tafia kayan aiki zan kwasa ? Ka ga fa dole sai an bincika duda ina tunanin rashin lafiar dake saka shi hakan aman sai an auna an gani za’a iya yanke hukunci, ta yaya zan iya yin wannan aiki ba tare da kayan aikina ba, ai ba dole sai sun zo ba sunna iya turo masu yi masu hidima da yarron sai a yi binciken a gama, idan rashin lafiar ce a kan magani ne zan dora shi idan abin bai yi tsanani ba, in kuwa ya yi tsanani sai dai a yanke, ban ga anfanin zuwana ba bayan ba aikin zan gabatar ba ni kuwa bani da abin gannin a idannuwana!”


Kader ya kara yin tsam yana kallonsa ya ajiye masa takardar a nan ya juya ya je ya bude office din


Sai da ya fitar da jikinsa da kansa sannan ya leko ya ce” idan kana so kar ka je, in dai sarki Shaheed ne zaka ganshi a wajen nan shima kansa hayakin yake ai!”


Da kallo ya bi shi sannan ya dauki takardar yans karantawa


Kuri ya yi mata yana jujuyawa sai kuma ya kai dubansa kan agogo sakamakon tunawa da ya yi da ita, ya rashi da niyar zuwa ya ganta kafin ya fita aman Billy ta rikita shi ta yada ya manta da ita kwata kwata Allah yana gani


Mikewa ya yi yana cire rigar aikinsa dan ya koma har gidan ya ga yaya saukin jikinta, sannan ya ga Bilkisu 

(Shi mutumen da ya san darajar dan adam ba wai dan an maka auren hadi da mace ba zaka wulakantata, da yawa basu so ya je mata ba, da yawa basu so ya bata kukawa ba har ya tsaya ya dinketa ya taimaka mata, shin so kuke ya zama sakaran namiji wawan namijin da bashi da tausayi ko jin kai? Namijin dake take mace ya sa kai ya fice? Dan kawia haya son mace sai ya kasa bata kulawa bayan Allahn da ya halice shi ne ya bashi umarnin ya kula da ita a karkashinsa take, hakinta ne a kansa? 🌝 ku ji su, a dai linga jin tsoron Allah ah tom😁)


A lokacin da ya dawo ya tarar da Mama zaune a tsakar gida tana faman gyara miyarta wace take son yin murzajiyar miyar malifiya da kifi


Zama ya yi ya mike kafarsa yana tsince yan hakukunan da take tsincewa sunna hirarsu


Mama ta ce” Ka rafe fushi yarona ka ji? Kwana biyun nan  abu kalilan sai ya saka ka daukan fushi”


Murmushi ya yi bai ce komai ba 

Mama ta gyara zamanta ta ce” baka tambayeni jikin matarka ba, baka kuma shiga ka ga jikinta ba ka yi tafiarka”


Kansa ya sada yana jin kunyar maman, ita kuwa ta dora da fadin” Ko me zaka yi a duniya ka ringa kiyaye hakin mutanen da kake tare da su, bale hakin iyalinka, Hisham du wanda ya kasance  yana muzantawa iyalinsa ina mai tabatar maka bashi  da rabo duniya da kiyama domin Allah ba zai barshi ba”


…………….kumu ci gaba

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like