DUK NISAN JIFA 29

Advertisement

                                29

Hisham ya sauke ajiyar zuciya ya dago a hankali ya ce” Mamana, wai me yasa yanzu ta koyi fada? Ko gigitar rasuwar yar uwarta ne? Wai mama wai a maidata wajen mijinta ji fa abinda take  fada ko kunya bata ji”


Mama ta yi murmushi dan sarai ta gane da wa yake ta ce” Uhum dama bata da kunyar in dai mai gado ce, ai du kai ka sangartata, ta fita fa tun dazun”


Shiru ya yi daga yannayin murmushin da yake ya ce” ta fita Mama ? Ina ta je kuma?”


Mama ta ce” Hum, ta ce zata je wajen abanta, abin na mai gado kamar wace take neman fitina kamar wace take hin haushin kowa, ka ga wai rigimar? Ita ba zata ci gaba da karatun likita ba wai kwaliya zata je ta yi”


Advertisements

Mama na fadin abin shashakai ne , shi kuwa abin ya fara shigarsa, kwaliya? Zata bar karatunta ta koma kwaliya? To me hakan yake nufi? 

Zai kuma yin magana ya hango mai gadi ya bude gidan


Tsai ya yi da dubansa yana kallo ta danno kan babur dinta, fuskarta dauke da bakin gilas 


Duda hijab ne a jikinta aman gilas din ya mahaukacin haska fuskar nata ya wani gyara fuskar


Wajen ajiye babur din ta kai abinta ta ajiye ta sauka tana rike yar karamar jakar hannunta ta cirro wayar dake ciki ta yi niyar nufa falon mama ta hango su zaune saman tabarma tsakiyarsu miya ce ana tsintarta sai wayoyinsa dake ajiye gefe 


Gabanta sai da ya fadi irin kyan da ya mata a idannuwanta


A hankali ta karasa ta sasauta daurin fuskarta ta cire gilas din ta duka muryarta na fita da sanyi ta ce” Barka da warhaka, na dawo”

Advertisements


Mama ce ta amsata shi kuwa ya zuba mata shanyayun idannuwansa yana kallonta, shagali watau ko tambayarsa ba’a yi ba, fitsararta take zubawa son ranta


A hankali ta mike ta juya tana cire hijab dinta


Kuri shi kuwa ya bita da kallo, kallo irin na kurulah wanda idannuwansa sun fi sauka a kan mazaunanta

Har ga Allah ba cen ya yi niyar bi da kallo ba , shi Allah yana gani ko a da yakan dan kalla aman baya taba kawowa ransa irin abinda ya shiga ransa a yanzu, tafiar tata a hankali take yi, mazaunanta ba wasu jibga jibga bane madaidaita ne masu tsari sai juyi suke tamkar wace aka zaunar aka koyawa


A hankali ya samu kansa da sauke ajiyar yana datse lebensa na kasa

Gaba daya sai da ta bacewa ganninsa sannan ya tuna a gaban wa yake a zaune, hakan ya saka shi juyo da dubansa a hankali


Ido hudu sukai da Mama, hakan ya saka shi kifta idonsa sai kuma ya dake ya ce” Mamana kina ji? “


Mama ta basar ta  ce” ina jinka yarona”


Hisham ya rasa meye zai ce da ita din hakan ya saka shi yin shiru yana jin yanda zuciyarsa ke bugu, kai Allah ya yiwa musulunci albarka da ya zo da tsarin da mata zasu suturce jikinsu kafin su fita , koda a cikin gida ne, shi yanzu da ina zai saka ransa ya ji dadi? Sai kuma ya tuna dukawar da ta yi bata kama sunnan kowa ba , da da ne zata ce ‘Hamana barka da gida na dawo, hamana ka ci abinci ko na kawo maka?’ Aman rabonta da ta kula shi ko ta damu da bangarensa da share share da kula da cikinsa ba har ta manta, sai mamansa dake kulawa dan safia bata wayewa dare ya shigo bata gyara masa part dinsa ba domin tun da ta turo Aisha ya nuna baya so sai take yi, aman abincinsa Aishar ke kaiwa koda yaushe


Ya kara kamar minti talatin tare da Mama domin har sai da lokacin da zai koma wajen aiki ya kusan yi ya mike ya shiga fallon


Zaune Aisha take tana kallon Bilkisu dake gefe rana hada madara da zuma a cikin kofin kwalba


Tun da ta shigo gaisawa kawai suka yi , ta shige ta yi wanka ta dawo ta zauna ta hade fuska, sam bata bata damar yi mata magana bama bale har su yi hira hakan ya sa Aishar binta da kallo ta kasa yi mata magana duda irin son da take su yi hira


Tsayawa ya yi ya kasa karasawa


Bilkisu na gannin hakan ta mike da abin shanta zata basu guri dan ta tabata wajen matarsa ya shigo


A hankali ya juya yana gannin niyarta ta ratsa shi ta tafiarta?


Ji ya yi ya kasa, bai san lokacin da ya saka hannunsa ya riko tsintsiyar hannunta ya dawo da ita baya yana kallonta ido cikin ido ya ce” Meye? A kan me kike fushi da ni? Me na maki? Dan kawai kin ganni daure da tawul shine zaki ringa fada min mugayen magangannun da ba zan iya dauka ba? Dan Alkah yaushe kika zama haka Bilki am?”


Bilkisu ta yi dan murmushi ta ce” Yayana wani irin fushi zan yi da kai kuma ni a su wa? A kan me? Ko daya ni ba fushi nake da kai ba, idan ka kula a yanzu kai mai iyali ne, ni kuwa koda mun sha nono daya akoy dan bambancin dake iya saka matarka jin ba dadi idan kusancina da kai ya ci gaba da kasancewa a haka , bana son saka matsala komai kankantarta a gidan yayana”


Kalaman dake fitowa daga bakinta daban ne da abinda yake cikin zuciyarta karara yana iya karanta hakan, a bayane yake gane komai dake fitowa daga bakinta idan daga zuciyarta ne ko ta fada dan kawai kar a takurata ne


Dan murmushi ya yi ya saka hannun nasa ya matsota sosai kusa da shi har tana jin hucin numfashinsa, yar yatsarsa ya dora wajen lebanta na kasa

A hankali ya dan shafa shi yana kallon yanda yake pink

Dan murmushi ya yi ya rage muryarsa sosai ce” Ki daina kin ji Bilki am? Ba laifina fa a nan, kuma dan kin ganni da tawul idan kin gane me na aikata sai ki saka zuciyata ta girgiza, a ina kika san yannayin nan? Kin ga na san ranki ne a bace kike haka, na san hankalinki ne a tashe kike cikin wannan yannayin, ki yi hakuri kin ji, irin haka na daga min hankali baki sani bane, kin ga dazu har tafia na yi ban duba matata ba kar ki dauki hakinta mana”


Bilkisu ta lumshe idannuwansa domin maganar da yake wata iska mai dumi dumi ke sauka a kan fuskarta daga bakinsa mai tafe da kanshin fraiz na irin turaran bakin da yake anfani da shi, dumin jikinsa walahi take ji a nata irin rikon da ya yi mata, sai uwa uba ta shiga hakkin matarsa da ya fada


A hankali ta ce” Yaya am?  “


Leben nata kawai yake kallo hakan ya sakata dago dubanta ta sauke a kan tsarariyar girarsa mai cika da shegen kyau irin girar fararan larabawan nan da dogon karan hancinsa ta ce” Yaya am, ina son Umar, ka ga ya sake ni ya mayar maka da ni karamar bazawara, ina so a hau kan maganar da malamai suka saba cewar saki uku kai tsaye a matsayin saki daya ake daukansa, ka ga a zamanin mazon Allah aka yi, daga baya ne da abin ya zama ana neman a mayar da lamarin wasa sai aka soke, aman ba wajen da ya nuna ba kyau sai dan kar batanci ya yi yawa, yaya am ina son sa sosai, ka yi magana a zauna ka mayar da auren nan ka ga kaine ubana kai kake iya tsawatawa kar a min illah” ta karashe tana mai cire dubanta daga wajen girarsa da ta ga ya hade tamkar zai hade su waje daya, sai rikon hannunta da take jin ya fara tsaurara, a hankali ta saci kallon wajen Aisha, gani ta yi bata nan hakan ya sa gabanta faduwa, watau daga ita sai shi ta zuba wannan magangannun? Tabdi


Gaba daya nema yake ya fita a hayacinsa idannuwansa kyam a kan lebunnanta, muryarsa yake son daidaitawa da kyar ya iya ciro maganarsa ya ce” ……………………………………………..

                  

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like