DUK NISAN JIFA 31

Advertisement

                               31

Sai da Hisham ya mike tsayinsa da kyau ya dan gyara tsayuwarsa a kasan zuciyarsa kuwa fadi yake’ Da ba dan Allah ya ce na girmama sarkina ba da na juya domin irin haka na hauda min jinina sama’

A hankali Bilkisu ta kuma kallonsa a karro na biyu, tsarin shigarsa sai yanzun take kara kawatuwa a cikin idannuwanta domin sanye yake da wani danyen yadi ruwan blue an masa dinki simple aman tsayinsa da tsarin jikinsa ya saka yadin wani irin daukansa, a kasan zuciyarta take fadin ‘to shi hama a kan me bai duka ba tunda muka shigo?’ Gashi dai da wannan mutumen ya yi ihu sai da ta ji uwa ta

rukunkume yaya Kader, shima Kader din kallonsa kawai yake, anya Hisham bai shafi jinnin sarauta ba? Wannan na biyu kennan da ya ga irin haka, yau gashi ya yi a gaban mai kankat din watau mai damagaram, uwa uba irin yanda Hisham ke saka idannuwansa a cikin na Shaheed sai abin ya ringa bashi mamaki, idannuwan shaheed da ake tsoro? Shi dai fatansa su gama su tafi kar ya yi abinda mai damagaram zai kule su walahi!


Wajen da ya nuna masa ya karasa ya zauna saman kujerar 


Muryarsa ya sanyaya ya ce” Barka da warhaka Sultan “


Shaheed ya saki murmushi a hankali ya dan gyara rawaninsa ta wajen bakinsa ya miko masa hannunsa ya furta” Barka da aiki likita, ya fama da jama’a? “

Advertisements


Hisham ya kuma dagowa ya kale shi sai ya sakar masa murmushin shima ya ce” Alhamdulilah “


Sultan Shaheed ya kai dubansa wajen da Nadia take sannan ya kai dubansa kan sarkin bulala


Da sauri sarkin bulala ya karasa ya duka daga nesa da ita kadan hakan ya sa ta mikar da yaron dake sanye da wani rawani a kansa ta matso masa da shi


Daukansa ya yi ya kaiwa Hisham shi


Hisham na  kallonsa da tausayawa ya shiga warware masa nadin da aka dafka masa 


Sai da warware masa shi tsaf, sannan ya cire masa katuwar rigar da aka saka masa mai uban zubi

Advertisements


Dubansa ya dan dago ya ga kowa shi yake kallo hakan ya saka shi yatsina kyakyawar fuskarsa ya kai dubansa wajen kader ya ce” Baka dauko jakar aikin ba “


Kader ya mike da sauri ya  fita


Jim kadan ya dawo hakan ya sa Hisham shinfida rigar yaron a nan kusa da mahaifinsa sannan yana kallonsa da sakin fuska ya ce da shi ” Zaka iya kwontawa na duba ka? “


Yaron dake ta langwabewa saboda azabar da yake ji na ciwo ya kama hannun Hisham ya taimaka masa ya kwontar da shi saman rigar


Sai da ya cire masa suturar jikinsa tsaf sannan ya shiga ciro abubuwan da ya zo da su dan auna yaron iya abinda ake iya dauka na aikin


Tun  bai je ko’ina ba ya gane cutar dake damun yaron, hakan ya saka shi daukan takarda ya yi rubutu mai dan tsayi sannan ya mikawa sarkin bulala wanda ya duka ya mikawa Shaheed


A hankali ya ce” A kawo min ruwa da tawul,aman ruwan mai dumi, kuma a kawo min maganin da na rubuta a kasa, na samanma a samo su dan sai an yi kwana uku ana saka masa ruwa safe, rana , da dare sannan ya sha magungunnan nan in sha Allah ba sai an masa aiki ba dan ciwon bai shige shi sosai ba aman a maida hankali kan traitment din “


Da sauri Sarkin Bulala ya amsa ya fice da karsashinsa a falon


Yana fita Najeeba ta kasa hakuri ta kuma dago dubanta a karro na ba adadi ta ce ” Kana nufin zai samu lafia irin na kowa?” 


Bai kalleta ba, yana maidawa yaron kayansa ya gyada kansa kawai sai cen kasan makoshinsa ya ce” In sha Allah “


Sai da ya saka masa mararsa nauyin sannan ya dago suka kuma hada ido da Sultan, ‘Ikon Allah, meye haka a idannuwansa shi kuwa?’ Shine abinda Hisham ya fada a kasan zuciyarsa, aman ya basar bai wani nuna alamun tsoro ko cire dubansa a cikin nasa ba, ko ba komai shi mai buda kai da kwakwaluwa yana tunanin abinda zai saka shi firgita ba nan kusa ba


A hankali ya kara gyara zamansa tsaf ya sauke dubansa kan Bilkisu wanda hakan ke dadada ran Shaheed, sai kawai yake gannin kamar shi a da idan yana zaune haka kawai idannuwansa basu da wajen sauka sai kan abokiyar fadansa kuma farautarsa gabansa ya ringa faduwa kamar ya ga abin tsoronsa 


A hankali ya ce” A daina saka masa rawanin nan da du wani abu mai nauyi, a barshi ya ringa samun iska har ya warke daga baya sai a masa koma menene “


Shaheed ya dan gyada kansa a hankali ya ce” Kennan ba sai mun kaishi asibitinka ba? “


Hisham ya dan juyo yana kallonsa ya ce” Akoy wanda zai ringa saka masa karin ruwan a nan? “


Nadia sai da ta saki baki dan mamakin mutumen, shima Shaheed sai ya samu kansa da sakin murmushi yana gyada kansa a ransa ya ce’Yau ga wani tsayayen irina, aman ba komai ni ke nema dole na yi hakuri kuma ko ba komai ga mai haukata tunaninsa’


Hisham bai san daga ina Shaheed ya samu tambayar nan ba, sai ji suka yi ya gyara zama cikin isar nan tasa ya ce” ITA DIN IYALINKA CE? “


Su dukansu kallonsa suka yi, ciki harda Bilkisu, 


Hisham idannuwansa ya zaro yana duban Sultan sai kuma ya daidaita yannayinsa yana sauke ajiyar zuciya a hankali ya dan girgiza kansa ya ce” Kanwata ce, tana jin zan zo shine ta tada rigima ita dai burinta Gimbiya ta kiya mata mak up “


Kuma dubansa ya yi ido cikin ido ya ce” Kana nufin kanwarka uwa daya uba daya ko kai ba muharaminta bane? “


A hankali ya kara wara dubansa a idannuwan Sultan wanda ya tsatsare shi da duban da idan da ace sun san junna yana iya rantsewa da Allah sone yake ya kure shi ko dariarsa yake, sai dai ya san ba sanninsa ya yi ba, shima hakanan kawai wani lamari ne ko dai ta birge shi ne?


Gyaran Muryar da Najeeba ta yi ya saka sultan kallonta


Kasa kasa ta gala masa hararar da du wani wanda ya kaleta da kyau ya kula da hakan, sannan ta maida dubanta wajen Hisham ta dan gyara muryarta ta ce” Ai ba damuwa, dan makup akoy masu koyarwa sosai zasu kula da ita “


HISHAM ya maida dubansa kan Bilkisu ya ce” Haka na ce da ita, sai ta ce aa ita Gimbiya Najeeba zata koya mata, burinta ta iya daga hannunta”


NAJEEBA ta maida  dubanta kan Bilkisu


Ido hudun da suka yi da Bilkisu ya sakata kara kallonta


A hankali ta kara gyara zamanta tana kallon Bilkisu ta ga baki daya tana irin yannayin nan da ake shiga idan ana matukar son wani abin


A hankali ta ce” Taso “


Bilkisu da ta san da ita ake ba wani yanga ba komai ta mike ta nufo wajenta


Tana zuwa ta nemi zubewa hakan ya saka Najeeba lumshe idannuwanta ta saka hannunta ta tareta


Bata bata damar zubewar ba ta matso da ita kusa da ita, muryarta ta rage sosai irin yanda du wanda ya ji maganarsu lale mai mugun ji ne ta ce” Shikenan daga cewa taso, ban ambaci sunnanki ba, ban nuna maki da hannuna ba, banma nuna alamun da ke nake ba sai ki taso ba tare da kin ja aji ba baki nuna ke din mace ce mai isa da takama ba kika zo kike kuma son zube min a gabama shin ni mamanki ce?” 


Da mamaki Bilkisu ta kaleta hakan ya saka Najeeba kara rage muryarta sannan ta yaye mayafin da Bilkisu ta luluba tamkar wata matar aure ta shiga kunce daurin dake kanta


Mikewa ta yi tsaye ta zaunar da ita saman kujerarta hakan ya saka baki daya su suke kallo, Najeeba ta mikar da dan kwalin sosai ta dan ninka gabansa kadan ta kama hannayen Bilkisu da ta zama tamkar wata status dan mamaki da tabatarwa kanta abinda ake fada a kan Najeeba tana biye da ita sau da kafa


Najeeba ta dora mata shi gaba sosai da goshinta sannan ta yi baya da shi bayan ta yi sama da hannun hagu din ta bi kasa da na damar a hankali ta ce” Mace kike, a gaban magauta kike, kar ki ga yayanki ne, daukarsa a matsayin abin harinki, abin farautarki, aman ba ta hanyar rashin da’a ko rashin mutunci ba sai ta hanyar da zai kasa motsin kirki a kan gadonsa, koda kuwa duniya ya aura domin an fada mana ya yi aure shi yasa bai zo da wuri neman da sultan ke masa ba, rike da kyau kar ya kunce?”


Da sauri Bilkisu ta tare domin sauraronta da take ya sakata yin sakayau zata saki dan kwalin


Sai da ta nanade dayan hannun mai tsayi ta nuna mata shi da kyau sannan ta zagaya da shi bayan ta soke mata shi sosai ya shiga ya zauna das da shi


Dan baya ta ja ta dago habarta tana kallonta sai kuma ta kunce mata shi gaba daya ta bata a hannunta ta ce ” Daura na gani “


Bilkisu ta hadiye yawu, hannayenta dake rawa rawa Najeeba ta bi da kallo


Habarta ta kuma dagowa tana kallonta tar ta ce” Kin aikata mugun laifi ne? “


Bilkisu ra yi gagawar girgiza kai tana kallonta ta ce” To a kan me jikinki yake bari bayan ke din budurwa ce dake iya tsaida jinnin tsoho ko yarro a lokacin da hakan ta raya maki? Samarinki nawa ?”


Bilkisu ta kuma hadiye yawu ta dan girgiza kanta ta ce” Ba ko daya “


Najeeba sai da ta zarro ido, a hankali ta saci kallon Sultan ta ga sai murmushi yake dokawa irin abin na saka shi nishadi, ta tabata dan ya ga irin halin da Hisham ya shiga ne abin ke saka shi nishadi ta dan yi murmushi ta saci kallon Hisham

Duda yana rungume da yaron aman gaba daya so yake ya ga me suke ko me suke fada


Najeeba ta ce” Hala tsoronsa kike? “


Bilkisu ta dan sada kanta da dan kwalin a hannunta ta ce” Yayana ne ai “


Najeeba ta tabe bakinta ta ce” Ki yi hakuri da maganar da zan yi walahi bana hanna kaina ko a gaban bako ne, yaya sunnanki dan Allah yar kanwata? “


Bilkisu ta ce” Sunnana Bilkisu “


Najeeba ta kara matsawa kusa da ita sosai ta ce” Kece fa mai gadon zinari, ke ce Nana uwar manya, kece mace mai sunnan mace, ke ce farar mace alkyabar mata, ke ce gold ke ya dace a haukacewa, da kike tsoronsa Ubankine shi? “


Sai da Bilkisu ta dago da sauri hakan ya saka Najeeba sakar mata murmushi ta ce” Sai da na baki hakurin zagin ai kau? “


Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya tana sada kanta


Najeeba ta ce” Daura “


Bilkisu ta shiga bin yanda ta yi mata ta dora saman kanta ta shiga daurawa Najeeba na dan gyara mata wajen da bai hau da kyau ba


Sai da ya dauru das da shi sannan Najeeba ta juya ta dauko jan bakin cikin yar karamar jakar dake ajiye gefe ta bude shi ta dan murda shi ya fito


Habarta ta dago ta goga mata kadan sannan ta nuna mata cewar ta hade lebunnanta


Sai da ta hade da kyau ya hadu sannan ta saka mata shi cikin hannunta ta ce” Ko kina gudu ki ringa yi da shi, koda kin ci abinci sai dan gyagyara dan kuwa dama gareki wace idan kina da wayau zaki dama!”


Bilkisu ta ringa dan gyada kanta Najeeba ta dauki mayafin nata ta ce” Tashi tau daga kujerar tawa “


Bilkisu ta mike tana kallon Najeeba,


Najeeba ta yi murmushi ta warware mayafin ta yafa mata shi a kafadarta ta ciro mata gashinta dake kasan mayafin ya hau saman mayafin sannan ta ce” Ki daina sauri ko a gaban waye, ko wa ya yi kiran ki, sannan ki fara zuwa ranar litinin karfe uku na yama dan na san kina makaranta ko? Idan kin zo ki nuna wannan takardar za’a kawo ki inda nake”


Tana fada ne tana bata yar takardar gayatar aman wannan mai saka hannun Najeebar ne wanda idan an nuna irinta har wajen Najeeba ake kawo mutun


Gaba daya mutuwar zaune ne Hisham ya yi da kader, daidai lokacin da sarkin Bulala yake neman izinin shigowa aman Sultan bai buga sandarsa ba hakan ya saka shi dakatawa a waje


Murmushi Sultan ya kuma yi ya rage muryarsa ya ce” Kadan daga aikin da ka siyarwa kanka “

๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ sai atinin ko? Idan Allah ya sa muna cikin masu rai da lafia๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ

                        

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

DUK NISAN JIFA 56

Advertisement   ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ           *DUK NISAN JIFA*            _(K’asa zai…

DUK NISAN JIFA 64

Advertisement   ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ           *DUK NISAN JIFA*            _(K’asa zai…