FURUCI 1-2

Advertisement

 πŸ…Ώ 1 to 2

Cikin babbar jami’ar USA babbar jami’a ce wadda tatara d’inbin dalibe kama da yan Nigeria Sudan Cameroon gana da wasu ‘kasashen dayawa cikin babbar harabar Skul d’in  Student ne kowa yana hidimar shi wasu suna gefe suna karatu wasu suna Hira wasu kam soyayya sukeyi kowa da abinda

yadame shi wasu ‘yan mata nahango su 3 suna zaune cikin lallausar ciyawa wadda tasha gyara hira sukeyi cikin nishad’in cikin farinciki d’aya daga cikin su tace 


” nikam wallahi kaf samarin cikin skul d’in nan babu wanda zan iya tsayawa nasaurara  babu wanda nabama zuciyata se yaya Zayyan ina koma gida Nigeria se aure shima ni yake jira Allah sarki yayana inanan babu mai shiga cikin zuciyata dan takace batakowa ba ” 


Shewa sauran sukayi sukace ” lalle Imtahal karfa kicika baki dayawa muga kinfad’a  dawani karki manta ko 3 month bamugama hadawa ba cikin skul d’in nan amma harkin yanke hukunci ” 


Murmushi Iftahal tayi tace ” ‘kwarai kuwa dan ni kaf cikin skul d’in nan banga wanda zai iya biyan sadakinaba ko kuna ganin akwai wanda zai iya fidda 2.1 million ayau basai gobe ba yabiya sadakina idan akwai to wallahi nikuma zan aure shi yau koda babu sanin kowa nawa ” 


Advertisements

Zaro ido salma tayi tace ” sayar dakanki zakiyi Iftahal gaskiya kibar wannan maganar yanzu idan akasamu yaya kenan dan kina yar minister kud’in Nigeria shikenan se sadakinki yakai darajar haka gaskiya nikam banta’bajin wadda akabiya sadakinta hakaba to shi yayan naki kina nufin haka zai biya? ” Murmushi Iftahal tayi tace ” ina ay shi dabanne wannan kuma dan inga wanda zai iya ne ” dariya habiba tayi tace ” ayko babu wanda zai iya dama ansa lokaci ne amma ayanzu  ay kam bab….. ” 


Maganar wani matashin saurayi tasasu saurin mi’kewa  cikin matu’kar razana dajin FURUCIN!!!!!! shi kamar haka 


” Ansamu wanda zai biya koda yakai ninkin hakan ayanzu haka malam da duk wani dalibi nacikin skul d’in nan zasu hallara wajan d’aurin auran ku ayanzu ” mi’ka mata wata bag yayi yace wannan shine adadin sadakin dakika bu’kata amma gaskiya kinyi dacen miji Namijin zaki kenan bari kiji kad’an daga cikin tarihin shi “


” Sunan shi Maher zaid d’an kasar Egypt d’aga Sarki Zaid d’an gata mai matu’kar dukiya cikakken miskili kuma fusatacce zuciya kusa shine d’ah namiji tulo gun mahaifin shi yanada yayye mata amma ‘yan uba suke shid’in d’aga amarya ne yanada hadarin gaske dan bayajin bari idan yafusata yanada masifar shan sigari wato taba babu ruwan shi damace bayason yawan magana duk arana baifi yayi magana sau 5 ba hmmm akwai babbar matsala guda 1 yanada wani ciwo wanda idan yatashi to zai iyayin kisa batare dayasani ba ciwon yafi tashi cikin dare kuma idan yayi farinciki ko yaya yake shiyasa akullum cikin kunci yake duk karshen month mahaifin shi yanazuwa da doctor shi dan duba lafiyar shi amma har yau ankasa gane maike damunshi sabida ciwon shi yasa karatun shi baya tafiya dede dan idan yatashi seya samu kwanaki 2 baishigo skul ba koda lokacin Exam ne 


Bai fiyasan magana da harshen turanciba yafison nashi harsen  wato yaran Araf ni d’ayane daga cikin  masumai hidima kuma amin taccen shi tun daga Egypt sunana Shanwul karkice zaki fasa dan ba abune mai yiyiwaba karki damu nasan bazama zaiyi dakeba kawai de wata manufarce daban wadda nima bansantaba amma tabbas FURUCIN!!  ki yazamiki bugun zuciya dan duk wanda yake tare da Maher to babu shi babu natsuwar zuciya nasan kinfara ayanzu k….. ” 


‘karasowar malaman skul din yasa Shanwul yin shiru sosai kowa yataru daga bayansu kuwa masu tsara gurine sukafara tsara wajan d’aurin aure cikin harabar skul d’in  malam Abdallah yadubi Iftahal yace ” yarinya babu shakka kinyimakanki FURUCI!!!! mafi girma ‘kila ya amfaneki ‘kila kuma kiyi nadama amma kisani ba’a wasa dakalmar aure shiyasa muka yarda dan yazama darasi ga ‘yan baya ke kikayi rantsuwa dakanki to gashi kuma ansamu wanda yabiya sadakin kamar yadda kika bu’kata gasunan ahanninki ni malam Abdallah nine zanzama waliyyin ki malam Abubakar kuma waliyyin Maher bayan wannan auran zamuturama iyayen ki maganar auran da yadda yakasance kowa anan yasheda cewa kinyi wannan FURUCIN!!!!! cikin nishad’in dan haka muna tayaki murna “


Advertisements

Daga haka malam Abdallah yajuya wani irin bugu zuciyar Iftahal tashigayi rumtse ido tayi tabud’e tana ro’kon Allah yasa mafarki takeyi suma ‘kawayen nata daskarewa sukayi awajan cikin sar’kewar Murya Iftahal tace ” dagaske nice zanyi aure babu sanin iyayena ina babu wanda zan iya aura idan ba yaya ba ‘kawayena kusanar dasu wasane kunajifa idan ciwon shi yatashi zai iya kisa kuma yafi tashi cikin dare dan Allah karku bari yakasheni wannan fa ba mutun bane kamar kowa duk cikin siffar shi babu abu mai sau’ki dan.. “


Jin anfara shirin d’aura aure yasa Iftahal juyawa aguje zuwa hostel yadda bag d’in kudin tayi cikin sauri Salma tad’auka sukabi bayanta suna shiga suka tadda tashiga had’a kaya sefaman kiran waya takeyi amma ta’ki shiga ri’keta Habiba tayi tazaunar da ita cikin muryar lallashi tace 


” haba Iftahal karki rikita kanki akan wannan abu eh gaskiya ne ba’ayin wasa da aure Iftahal kisani shi FURUCI!!!! wani babban abune dazaran kin furta shikenan bafazai komaba kuma idan kayishi abakin mala’iku sukace Ameen tofa shikenan to naki FURUCI!!!!!  shima inaga hakanne takasance amma nizan baki shawara Iftahal tunda nashigo cikin skul d’in nan naji labarin Maher yanada d’aurin ‘kugu cikin Skul d’in nan duk abinda yanema wajan malaman nan to zasuyi shi ni aganina kibari ayi auran shifa babu ruwan shi damace inada tabbacin babu abinda zai yi miki nasan yayi hakanne dan kawai yanunamiki kuskuran FURUCIN!!!! ki kuma nasan labari aka kaimishi dan shi bayazama cikin harabar skul dayagama abinda yakeyi yake fita ance wani mahaukacin gida mahaifin shi yasiya mai tabbas Maher yawuce duk yadda kike tunani kokin sanar da iyayenki tofa ayanzu babu abinda zasu iya dan kam kosun taho Maher yana iyasawa ahanasu shigowa cikin USA sabida ‘kanin mahaifiyar shi babban jakadane na wannan ‘kasar wanda a Airport se jerin sunayenku sun isa gareshi kafin abarku kinsan nan bakamar Nigeria bace to dan Allah kar kisema iyayenki cin mutunci da damuwa kibari malam Abdallah yayi musu bayani yadda zasu fahimta nasan bazasuga lefinkiba nan gaba kad’an zaku rabu seki auri yayanki kamar yadda kike so idan kuma kikace zakibar ‘kasar to bafa zai yiwuba dan ba zasubar kiba ” 


Wani irin kuka Iftahal tasaki tace ” shi kenan ina gani zan auri wancan mugun dako fuskarshi bansaniba kasheni zaiyi Salma kuma babusanin iyayena wannan wane irin abune ni za’ayima aure a cikin skul wannan wane irin mugun tarihine gaskiya malaman cikin skul d’in nan basusan mai…… “


Maganar wata d’aliba dako shigowa cikin room din batayiba tace ” shima baisan fuskarkiba haka sunanki garama kai kinsan nashi sunan hasalima yau kwana 2 bai shigo Skul ba labarin FURUCIN!!!!!!  ki kawai yaji karki damu Maher bazama zaiyi dake ba nanda 3 years zaigama karatun shi matsayin cikakken lawyer kekuma zaki gama nanda 5 years  Doctor ko to kingani na tabbatar bazaije Egypt dakeba bayan matsalar ciwon shi datuni yagama kuma dayaso ko babu karatu dayasamu sedar kammalawa amma yanada tsayayyan ra’ayi yafiso yafito lawyer nagaske kinyi sa’a nanda kwanaki 6 mahaifin shi zaizo daga Egypt idan zaki iya kisanar da mahaifin shi yasa yasakeki to tabbas idan mahaifin shi yasa to babu sakka zaiyi dan yana matu’kar jin maganar iyayen shi nasan ayanzu haka mahaifin shi yasan maganar wannan auran dan baya ‘boyemai komi Iftahal Amarya to kisakko dan ayanzu za’a kaiki gidan Yarima Maher motocin suna ‘kasa suna jiranki ” batajira mai zataceba taja hannun ta tashi su salma sukayi zasu bishi tadakatar dasu dafad’in ” prince bayason hayaniya muma iya karmu waje ita kad’ai zata shiga gidan mijinta ” 


Daga haka taja hannun ta cikin sauri Salma tace ga kud’in sadakin ta amsa wannan budurwar tayi suka fita sosai Iftahal take bin motocin da kallo tabbas tayarda Maher yanada d’aurin ‘kugu cikin skul d’in nan kowa kagani cikin walwala yake cikin lokaci kad’an anshirya gagarumin d’aurin aure cikin sauri Shanwul yabud’e mota ganin batada niyyar shiga yasa wannan buduwar janta suka shiga cikin motar ihu Students suka saki suna farinciki dan kaf cikin skul d’in babu wanda baisan prince Maher ba cikin natsuwa motar take tafiya sauran kuwa Students ne ciki wani irin bugu zuciyar Iftahal takeyi tamarasa wane irin hali take ciki har suka isa bakin get d’in katafaran gidan 


daganan kowa yasauka ciki hadda wannan budurwar sauran motocin ma iya driver bakwai akabari daganan kowa yajuya cikin parking space sukayi parking motocin fitowa kowa yayi shima Shanwul fitowa yayi mi’kamai makullan motocin sukayi suka juya budema Iftahal mota yayi kamar bazata fitoba sekuma tafito fuskarta cike da hawaye bin harabar gidan tayi da kallo babban bene ne mai hawa 6 harabar gidan kawai abin kallo ce ga security kota ina kallonta Shanwul yayi yace ” muje ko ” wani irin kallo tayi mai Murmushi yayi yace 


” garama kizo muje dan babu wanda zai barki kifita se idan Prince yace koda nine nace bazasu bariba kinga wa’incan sojojin wallahi basuda  imani ni kaina idan nayi badedeba to Prince yana gani sukecin ubana sema yace su’karamin dan shi babu ruwanshi da rashin adalci ” cikin tsawa Iftahal tace 


” ayko shine babban marar adalci tunda gashi yasaka rayuwata cikin masifa daga yin FURUCI!!!! cikin ‘kawayena shikenan yazamarmin masifa to wallahi bari kaji zan…… ” afusace wani security yazo gurin cikin zafin rai yad’aga hannu zai mareta had’ida fad’in  ” kinatsu ba’ayimana hayaniya anan cikin harshen turanci ” cikin sauri Shanwul yace ” sorry Matar oga ce fa ” saurin sauke hannunshi yayi yana gaidata cikin matu’kar tsoro tabi bayan Shanwul 


har zuwa hawa na 5 sannan suka shiga cikin wani had’add’an parlour nuna mata wajan zama yayi sannan yace 


” nan shine parlour ki zaki iya shiga kowane bedroom amma banda wancan sabida kayan motsa jikin prince ne aciki yana motsa jiki duk safiya dakuma yamma daga hawa na 6 yake sakkowa nan yana shan black tea akan wancan dining d’in kullum safiya yana sakkowa ya kalli News a wannan parlour kullum dare  idan kina bu’katar wani abu nizaki sanar mawa karki manta bayason hayaniya k…. ” 


jin takun sakkowar Prince yasa Shanwul yin shiru saurin du’kawa yayi yana kwasar gaisuwa cikin rikicewa yake nunama  Iftahal tadu’ka amma tayi ‘banza Sigarin dake hannun shi yazu’ka yabusar da haya’kin seda yakusa shanyeta sannan cikin tsadaddiyar muryar shi yace 


” Wanna fa daga ina ? ” 

Cikin sauri da rawar jiki Shanwul yace ” Allah yataimakeka wadda kace akaima sadakin 2.1 million kuma d’aura maka aure da ita ayanzu itace ” hannu yanuna ma Shanwul alamar yafita bayan fitar Shanwul Maher yasake zu’kar Sigarin shi sannan yadu’ko dede fuskar Iftahal yahura mata haya’kin Sigarin yace


 ” Welcome ” 


daga haka yami’ke yanufi d’akin motsa jikin shi bin bayanshi tayi da kallo tanasakin  tari sabida haya’kin daya busha mata gawani irin bugun zuciya datakeji sabida ganin suffar Maher cikin zuciyarta tace 


” anya wannan mutun ne tuda nike banta’ba ganin kyakkyawa kamar shiba ko acikin finafinan India gaskiya  babu kamar shi ” sekuma tace nashiga 3 yanzu yaya zanyi wai dagaske nazama matar aure ? “


Daga Al’kalamin….πŸ–Š

Leave your vote

-30 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like