FURUCI 11-12

Advertisement

11-12 

Kamar zai je inda take sekuma yajuya yanufi bedroom sautin muryar ta tadakatar  dashi ” sannu da dawowa ” sake juyowa yayi yadubeta amma bece komiba yasake juyawa yashiga ciki sosai Iftahal taji babu dad’i babu jimawa yafito cikin fusata yadubeta yace ” cikin ma’ay katannan waye yahauro saman

nan yashiga bedroom d’in na bayan nahana ? ” Cikin sanyin murya tace ” babu kowa Ni kad’e nahauro saman nan mai yafaru ? ” Sosai yasake dubanta yace ” kina nufin kece kika gyara saman nan hadda canja bedsheet ? ”  Eh ” kawai Iftahal tace mishi jinjina Kai yayi cikin zuciyar shi yace ” kenan jikin nata ya warware ” amma afili baice komiba yajuya yakoma bedroom tsayin lokaci sannan yafito sanye da kayan shan iska hannun shi ri’keda sigarin shi yana Sha d’ayan hannun kuma ledar maganice zama yayi kan cushion d’in datake zaune yami’ka mata ledar sannan yace ” fatan kinci abinci Kisha wa’innan magungunan yanzu ” d’an yamutsa fuska tayi sabida itakam  tatsani magani cikin shagwa’ba tace ” banci abinciba Kai nike jira muci gashican saman dining ” sake zu’kar sigarin shi yayi sannan yace ” sekuma gashi bana ra’ayin cin abinci kije kawai kici “


Babu zato kawai yaji ta kwanto saman jikin shi tace ” tonima bazanciba idan har bakaciba d’aga kafadar shi yayi alamar rashin damuwa yace ” wannan Kuma matsalar kice ” kuka Iftahal tasaki ta amshe sigarin hannun shi takai bakinta saurin ‘kwacewa yayi cikin fushi yace ” bakida hankaline zakisha abinda zai cutar dake ? wallahi daga yau Idan kika sakeyin haka senayi mugun ‘bata miki rai ” kuka Iftahal tasaki sosai cikin kuka tace ” ashe kasan tanada had’ari Kuma zata iya cutar daduk wani mai shanta Amma shine kake sha kamayar da ita kamar abinci arana kanasha fiye da kwali haba Prince katuna halin dakake ciki amma kake ‘karama kanka wata lalurar haba Prince idan kacutar dakanka to wallahi bazamu ta’ba yafe makaba ” 


Sosai maganar ta taratsa zuciyar shi amma bayajin zai iya dena shan sigarin sabida itace take saka bugun zuciyar shi natsuwa afusace yace ” bazan bar Shan sigari ba sabida itace take ragemin rad’ad’in bugun zuciya sannan kisani babu ruwanki da rayuwata idan nacutar dakaina bai shafekiba sabida bakida asara ” kuka Iftahal tasake fashewa dashi tace ” wallahi kuwa inada asara kuma dole ne yashafeni sabida ni matarkace Kuma ko yanzu kamutu yazama dole nayima takaba idan kanason natsuwar zuciya addu’a zakari’ke ba shan sigari ba ” tureta yayi daga jikin shi yasake zu’kar sigarin shi sosai sannan yace ” waye yagayamiki cewa idan namutu yanzu zakiyimin takaba ? bayan kinsan babu abinda yashiga tsakanina dake so babu takabata akanki Koda mutuwar nayi  sannan kisani nafiki son nad’inga yin addu’a amma Ina danafa sesu ri’ke min ma’koshina Susa harshena yasar’ke nakasa furtawa yaya kike so nayi dan haka dole nasha sigari dan nasamu sassaucin bugun zuciya ta ” ya’kara she maganar cikin raunin murya cikin kuka Iftahal tasake cewa ” 


” in sha Allah zan maye maka wani abu da wannan sigarin wanda zairabaka da wannan matsalar duka nide burina kasha dan Allah muje kaci abincin kaga wannan lemon zaisaka nishad’i sosai sannan kanafad’in babu abinda yashiga tsakanina da Kai to Idan yazama kakusanceni batare da saninkabafa ? ” Wata irin tsawa yadaka mata ” keeeee wannan wace irin banzar magana ce tayaya dan ciwona yatashi nida akace ina yun’kurin kisa idan ciwona yatashi tayaya har zan iya kusantar mace Ina hakan bazai ta’ba yiwuwa ba kema kanki kiga yadda najamiki ciwon Kai amma har kike tunanin zan iya kusantar mace ahalin danike ciki wannan bazai yiwuba daga yau karki sakeyimin irin wannan banzar maganar ” 


Advertisements

Daga haka yanufi dinning d’in ranshi a matu’kar ‘bace sosai Iftahal tayi matu’kar razana cikin zuciyar ta tace ” Ya subahanallahi tayaya kenan zansanar dashi ayka aykar dayamin nashiga 3 ni Iftahal mi’kewa tayi cikin sanyin jiki tanufi dinnig d’in kafin ta’isa tuni yazuba abincin yafaraci Zama tayi tanad’an yamutsa fuska cikin sanyin jiki tazuba nata abincin ahankali takecin abincin tanad’an satar kallon shi shiko ko kallonta bayayi abin mamaki sosai yaci abincin yanaci yanashan lemon sosai hakan yasa Iftahal jin dad’i ganin hakan  yasata cin abincin sosai bayan yagama yad’an dubaita sosai yace ” waye yayi wannan abincin ? ” Murmushi tasakar mishi tace ” nice ” wani irin kallo yayi mata yace ” shiyasa naji abincin babu dad’i dan kawai inajin yunwane ” mi’kewa yayi ya d’akko ledar maganin ciro mata yayi sannan yami’ka mata shagwa’be fuska tayi  ganin hakan yasa Maher tamke fuska sosai dole ta amsa tasha babu zato taji amai yataso mata sabida Shan maganin cikin sauri yari’kota yafara  shafa bayanta Yana sannu jin batadena yun’kurin aman ba yasashi zame d’ankwalin kanta hura mata kan yashigayi sosai ya’kurama kanta ido yana ‘karema gashinta kallo ahankali yad’aura hannun shi saman gashin ta d’ayan hannun shi yasa yad’ago fuskarta yasauke  idanun shi saman kyakkyawar  fuskarta saurin rufe idonta Iftahal tayi sabida yadda yayi mata kwarjini takasa had’a ido dashi hankali yashiga hura mata siririyar iska cikin idanunta tsayin lokaci sannan cikin natsastsiyar muryar shi yace 


” Bud’e idon ki Iftiih!!!!!!! ” Sosai yadda Maher yakira sunanta yadaki zuciyar ta jitayi duk duniya babu wanda ya iya Kiran sunanta kamarshi ahankali tafara bud’e idanunta masu kamadame bacci har tabud’e su tazubasu cikin nashi murmushi tasakar mishi kamar 5 minutes suna ahaka da’kayr yad’aga lab’ban shi yace ” kinajin bacci ne Iftiih!!!! ? ” Sake lumshe idonta tayi  tabud’e tagirgiza kai cikin shagwa’ba tace ” Prince dan Allah kabar Shan sigarin nan wallahi zuciyata tanayin zafi idan naga kanashanta “


Saurin sakinta yayi yatamke fuska yajuya yanufi bedroom batare dayace mata komiba  babu jimawa yafito sanye da jallabiya zai sauka ‘kasa cikin sauri Iftahal tami’ke saurin tsayawa tayi tace wasssh saurin juyowa yayi yadubeta mi’kewa tayi tafara takowa ahankali kallon yanayin tafiyar ta yayi sosai yatsura mata ido amma kafin ta’iso yajuya yasauka ‘kasa sabida Kiran sallar dayaji yanatafiya yana tunanin maiyasamu ‘kafarta zuciyar shi tabashi amsa da ” turetan datace yayi jiyane yasa ‘kafarta samun matsala sosai yaji babu dad’i  bayan fitar Maher Iftahal tajuya takwashe kayan abincin tasakko ‘kasa kitchen tanufa ta aje sannan tafito tanufi bedroom toilet tashiga tayo alwala  sannan tafito tatada sallah kafin ta’idar wayarta tad’auki ruri har sau 4 anakira bayan ta idar tami’ke tad’auki wayar Salma ce murmushi tayi sannan takira bugu 2 Salma tad’aga kafin Iftahal tayi magana Salma tace


” Gimbiya kenan kice ansha amarci gaskiya soyayyar ku tadabance  wannan shine had’in Allah to Yaya jikin ? ” Sosai Iftahal tayi mamakin yadda su Salma sukasan batada lafiya cikin mamaki Iftahal tace ” waye yace muku banida lafiya ? ” dariya Salma tayi sannan tace ” wa kuwa hmmm Prince ne yaje yasanar ma malamai cewa ayimiki uziri bazaki samu shigowa Skul ba sabida bakida lfy dakin samu sau’ki zaki shigo to kinsan yadda kaf malaman Skul d’in nan suke matu’kar son Prince babu wani shakka ko tantama suka shiga  cewa Allah yabaki lafiya gaskiya Iftahal kindace Nan kusa Prince zaisoki so Mai tsanani to Yaya jikin ina fatan anwuce gurin ” 


Dariyar farinciki Iftahal tayi tace ” a a Salma babu wani wuce guri kawaide tashi nayi daciwon kai ” dariya kawai Salma tayi tace haka de kikace mude mungane Allah yasa ansamar mana baby  ” kafin Iftahal tayi magana Salma takashe wayar tanasakin dariya shafa cikinta Iftahal tayi had’ida zaro ido tace ” dana shiga uku  ciki ni wayyo Allah gaskiya Salma bakiyimin fatan alkairi ba ” aje wayar tafi tafito parlour dede lokacin Maher yashigo ko kallonta baiyiba yawuce binshi tayi da kallo tashiga cikin tsakiyar parlour tazauna saman cushion kunna TV tayi amma zuciyar ta tatafi duniyar tunani sosai take tuna iyayen ta dakuma rayuwar datake ciki yanzu 


Babu jimawa Maher yafito dashirin motsa jiki room d’in yashiga sosai Iftahal takoma tunanin yadda zatayi wajan taimakon Maher kamar 25 minutes dashigar shi room d’in Iftahal tami’ke tanufi kitchen freezer tabud’e tad’akko ruwa sannan ta d’akko cup ta tsiyaya sannan tayi addu’o’i cikin ruwan tanufi room d’in sosai yahad’a zufa ganin karanshi agefe yasa Iftahal tsayawa yana kallonta amma yacigaba da motsa jikinshi kayan motsa jikine kala kala cikin room d’in babu abinda babu seda tajima a tsaye sannan yasa Karan yakoma cikin room d’in sosai shiga tayi tanayi tana kallon Karan sabida tsoro gurinshi tanufa tami’ka mishi ruwan baiko kalli cup d’in ba yace ” banabu’kata bakiga duk wani abunda zan bu’kata ba akwai shi ko bakiga freezer ba ? ” 


Advertisements

Cikin shigar lallashi tace ” haba Prince dan Allah ka amsha jifa yadda kayi zufa Kuma maiye amfanina cikin wannan gidan idan banyima hidimaba ? dan Allah ” amsa yayi yashanye duka yami’ka mata cup d’in yace ” fita to banason ganin mace  a inda nike ” sake dubanshi tayi sosai lamarin shi yake bata mamaki cikin taushin murya tasake cewa ” kayi ha’kuri zanfita nima banason takuraka amma Mai kakeso nadafa maka na dinner ? ” tsayawa yayi dayin abinda yakeyi yace ” amma nace bana bu’katar wannan jagwalgwalon naki ko kibari Iya ko Alina tayi ” cikin damuwa Iftahal tace 


” Nikuma daga yau bana bu’katar kasakecin abincin kowa se nawa amatsayina na matar ka hak’kinane nayima abinci nakula dakomi naka dan haka wallahi babu abincin wadda zakasakeci muddin idan Ina cikin gidan nan ” sosai Maher yatsaya Yana kallonta yarinya amma da tsirfar ciya yafad’i hakan cikin zuciyar shi ganin bashida niyyar yin magana yasa Iftahal fashewa da kuka rumtse ido Maher yayi sabida shikam yatsani kuka a’kagare yace ” naji kiyimin duk abinda yayi miki amma marar nauyi se black tea ” jin haka yasatasakin murmushi tace ” yauwa my Ruheey Kuma dan Allah kafitar da karancan wallahi yana bani tsoro kuma Allah babu kyau zamada kare idan gadi kake so yayi maka to kakai shi waje can wajan d’ayan dake bakin get dan Allah “tajuya tafita  tsintar kanshi yayi dabinta da kallo tana fita takoma kitchen tafarayin aykin abincin babu jimawa Maher yafito yana Jaye da karan babu jimawa Shanwul yashigo bashi karan yayi yace ” kaishi can bakin get daga yau acan zekoma zama ” cikin mamaki Shanwul yace 


” Allah ya’kara maka lafiya ko lafiya ? ” Seda yajuya yafara tafiya sannan yace ” lfy sabida Iftiih!!!!! batason ganinshi cikin part d’inta daga haka yahaura sama sosai Shanwul yatsaya Yana mamaki cikin sauri Iftahal tafito tace ” Shanwul cikin ‘kasada murya nufar inda take yayi cikin girmamawa tace dan Allah ayken ka zanyi dan Allah ko anasamun ‘ya’yan habba da na na’a na’a da gyanyen na’a na’a da kanumfari haddama citta ” duban hanyar saman Shanwul yayi cikin tsoro yace ” gaskiya anan bansan inda zansamuba amma naga Iya tana amfani da irinsu bari nakira miki ita dan Allah gimbiya idan angama Ina jira wallahi abincinki yayi bakad’an bafa har seda naji kamar su Maimartaba karsu tafi sabida naitacin abincin ki ” murmushi Iftahal tayi tace ” naji jeka haryafito kasha fad’a ” 


Cikin sauri yajuya yaja Karan suka fita babu  jimawa Iya tashigo sanar da ita Iftahal tayi abubuwan datake bu’kata ayko cikin sa’a tasamu duka sabida Iya ma’abociyar amfani da irin abubuwan ce misalin 6pm Maher yasakko ‘kasa zuwa lokacin Iftahal tagama komi tashirya a tsakiyar parlour inda Maher yake Zama Yana kallon News bin gurin yayi da kallo gawani kamshi da parlour yakeyi namusamman Zama yayi yana nazarin yadda jikinshi yacanza wunin yau cikin wannan tunanin yaji ana kiran sallah mi’kewa yayi afili yace ” Allah nagode maka yau nasamu ikon bin  jam’i abinda da nafara cire rai dashi Alhamdulillah ” 


Tunda Maher yatafi masallaci bai dawoba seda akayi issha’i sannan  yashigo Iftahal dake zaune cikin parlour tasha wanka cikin ‘kananun kaya wa’inda suka fidda surar jikinta ta gyara gashinta zuwa baya tafeshe jikin ta da turaruka masu shanyin kamshi da dad’i ganin shigowar shi yasata saurin mi’kewa tanufeshi dede lokacin idanunshi suka sauka saman ‘kirjinta dole yaci burki sabida yadda yaji wani yarrrrrr take ‘kafarshi tayi nauyi yakasa d’agata yakuma kasa d’auke idonshi daga kan ‘kirjinta babu zato yajita cikin jikinshi tarungume shi sosai ta ‘kwa’kube shi tanafad’in ” barka dashigowa My Ruheey Allah katsaremin mijina kakaremin shi daga dukkan sharri Allah kacika mishi burinshi Allah kanunamin ranar da zanga cikakken barrister Prince agabana “


Batare da Maher yayi zatoba yarungumai ta sabida sosai addu’o’in datayime suka ratsa zuciyar shi zuwacan Kuma yayi saurin janye jikin shi daga nata kamar wanda yatuna wani abu cikin parlour yanufa cikikin shagwa’ba Iftahal tace ” nifa bazan iya tafiyaba ni kazo kad’aukeni seda yazauna sannan yace ‘ tokicigaba dazama anan mana dama ni banabu’katar takura ” jin hakan yasa Iftahal sakin kukan shagwa’ba ” sosai Maher yake kallonta cikin mamaki afili yace ” lalle yarinyar Nan ayko idan bakitahoba senasa Shanwul yadawo da cizooo yasake koyamiki natsuwa cikin gidan Saraki ” jin haka yasa Iftahal takowa ahankali tataho dan Kam tana matu’kar jin tsoran Karan nan ganin yadda take tafiya yasa Maher dubanta sosai har ta’karaso cikin parlour zama tayi daf dashi cikin sanyin muryar shi yace 


” Wai maiye matsalar ‘kafarki Kike d’ingishi ? ” kafin tayi magana wayar shi tashiga ruri ganin sunan Ammin yasashi sauke ajiyar zuciya d’agawa yayi gai data yayi daganan yayi shiru tambayar shi lafiyar shi tayi yace Alhamdulillah daganan tace yabama Iftahal mi’kamata wayar yayi yasauka ‘kasan carpet yazuba black tea d’in shi wanda yasha kayan had’i yafara Sha sosai yaji yayi mai dad’i sosai Iftahal da Ammin sund’ad’e suna waya daganan sukayi sallama Koda Iftahal tasauka ‘kasan carpet tuni Maher yafaracin abincin sosai yasha black tea d’in dan Kam saura kad’an yashanye kallonshi kawai Iftahal takeyi yadda taga yana lumshe ido kamar Mai baccin tashi yayi yanufi samanshi batare dayace komiba cikin sauri tami’ke tabi bayanshi tana shiga taga bashi a parlour cikin sauri tashiga bedroom d’in 


Dur’kushe taganshi hanyar toilet da alama yakasa ‘karasawa cikin toilet d’in ne wani irin amai yafarayi cikin matu’kar gigita ta’isa gareshi ri’keshi tayi tsayin lokaci yanayin wannan aman ba’ki ‘kirin ga yau’ki dagani kasan wannan aman akwai wani mugun abun da Maher yake amayarwa cikin wata irin murya yace ” Iftiih!!!! kibar nan wajan inaji kamar ciwona zaitashi kifita nace kar nakuma illataki ” kuka Iftahal tasaki tace bazan iya ba kaifa mijina ne Koda zaka kasheni bazan iya tafiya nabarka ba ” wata irin tsawa yadaka mata ” Nace kifita  kifita Iftiih!!!!! Please dan Allah banaso kimutu yanzu ” 


Cikin rawar jiki Iftahal tami’ke tafaraja baya amma kafin takai kofar taga Maher yami’ke wata irin dariya yasaki cikin waga irin murya wadda dagaji batashi bace yace ” hhhhhhhhh wato ma har yafarajin tausayin ki koooooo ? wato keeee Mai taurin Kai kinfara karyamana shiri ko to kisani yau Zaki mutuuu kinsan wannan wane irin abune kikasashi yake amayarwa to to wannan abun seda muka d’auki shekaru muna shiryashi muka sharya dashi shine kikeso ki’bata Mana komi ko to kafin kigama lalata mana shiri bari nakaiki inda ba’a dawowa ” daga haka yayi kanta wani irin bugun zuciya matsananci Iftahal tashiga ji kafin ya iso gareta tuni zufa tawanke duk ilahirin jikin ta 


Comments please

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like