FURUCI 13-14

Advertisement

                *13 to 14*

 Sosai Maher yakeyin rawar sanyi hatta ha’koran bakinshi had’uwa sukeyi sake ‘kudin dinewa yayi ahaka har Allah yasa yasamu bacci abin mamaki a wannan daran sosai Maher yasamu bacci irin wanda raban dayayi irin shi har yamanta misalin 4am Iftahal tafarka sakamakon sanyin asuba daya bigeta dafe

kanta tayi sabida wani irin ciwo dayakeyi mata ga fuskar ta duk a kumbure ‘ko’karin tashi tafarayi amma takasa kuka takuma saki sosai cikin muryar kuka tace 


” Ya Allah kabani ikon tashi na gyara jikina yaushe Maher yabar bedroom d’in nan yasan abin da yayi min kuwa ko baisaniba Allah kasa yasan komi idan kuwa baisaniba nashiga 3 tayaya zan fahimtar dashi ” wasu hawayen suka gangaro saman kyakkyawar fuskarta jin anfara kiran sallah yasa Iftahal daurewa cikin ‘karfin hali da bin bango tashiga toilet ruwan d’imi ta kunna bayan yataru tashiga ciki Kara tasaki sabida rad’ad’in zafin tana zubda hawaye rumtse idon ta tayi tashiga ciki sosai dandanan tahad’a zufa sabida azabar datakeji tsayin lokaci Iftahal tana gasa jikin ta cikin juriya da karfin hali sabida ba’karamar wuya takeshaba bayan tagama sannan ta tsaftace jikin ta takawar da janabar tafito doguwar riga tajawo tasaka da hijab tashinfid’a abin salla kasayin sallar tayi a tsaye dole tazauna dukda shima zaman babu dad’i sallar issha’i tafarayi wanda batasamu yiba jiya kafin akira sallar asuba dan ayanzu kam asalatu ake Kira 


Kiran sallar asalatu yasa Maher farkawa cikin nannauyan baccin dayakeyi tashi yayi zaune yana nazarin abinda yafaru sosai yakejin damuwa tashi yayi yashiga toilet wanka yafarayi sabida yadda yakejin jikin nashi babu dad’i bayan yagama ya tsamtace jikin shi kamar yadda yasaba aduk lokacin da ciwon shi yatashi sabida gushewar hankalin shi to baisan abinda yafaru dashiba shiyasa duk lokacin da yadawo cikin hankalin shi yakeyin wankan tsarki yauma kamar kullum hakan yayi yafito jallabiya yasaka fara tas yafito daga bedroom ‘kasa yasakko yaukam yanajin zai iya zuwa masallaci sabida jin jikinshi yakeyi babu nauyi bakamar yadda yasaba jiba sede wannan muguwar bugun zuciyar Yana sakkowa ya kalli hanyar bedroom d’in Iftahal har yad’an gota sekuma yadawo nufar bedroom d’in yayi yashiga ganin ta yayi zaune kan abin sallah sekuma yadubi TV dake kunne har yanzu juyawa yayi sannan yace 


” Maiye kuma nakulla TV tunda asuba ? ” Idasa fita yayi yasauka zuwa masallaci tsayin lokaci Iftahal tana addu’a bayan idar da sallar asuba sannan tami’ke se alokacin talura da yadda zanin gadon ya’baci da jini cikin ‘karfin hali tanufi wardrobe wani bedsheet d’in taciro tayaye wancan  cikin ‘karfin hali ta shinfid’a wannan shikuma wancan takaishi toilet sannan tadawo ta kwanta tana sauke nishi mai ‘karfi sosai jikin ta yayi zafi sabida wani mugun zazza’bin daya kamata jan blanket tayi tarufe jikin ta wani saban kuka taji yazo mata  cikin kuka tace


Advertisements

” Nashiga 3 Ni Iftahal yanzu tayaya zan iya fahimtar da Maher cewa shine ya amshi budurci na ya Allah karka d’auramin abinda bazan iya ba ya ubangiji na kakawomin d’auki banida dabara ko mafita se taka ya Allah ina tuba agareka  Abba na kayafemin nasan hadda fushin ku yasa rayuwata tayimin zafi ya Allah natuba ” dede lokacin Maher yashigo jin sallamar shi yasa Iftahal yin shiru Zama yayi bakin bed saurin share hawayen ta tayi batare data waigoba tace 


” Fatan katashi lafiya ? ” Bai amsaba zuwa can sannan yace ” Wai maiye amfanin barin wannan TV a kunne ? ” Cikin dashasshiyar murya tace ” gani nayi kaine ka kunna shiyasa ban kasheba nabarshi sabida bansan nufin hakanba ” se alokacin yatuna shigowar dayayi cikin bedroom d’in amma yakasa tuna yadda yafita daga bedroom d’in balle abinda yafaru tashi yayi yakashe TV batare dayace komiba  sannan yadawo wannan karon a tsaye yatsaya fuskar nan tashi amatu’kar tamke yace ”  ina kikaje jiya nayi miki wannan tambayar jiya amma bansan wace amsa Kika baniba sabida  bazan iya tuna komiba tun daga lokacin sede nabud’e ido na ganni saman bed cikin bedroom d’ina ” 


Hannu Iftahal tasa tashare hawayen fuskar ta sannan tace ” Skul wajan su Salma ” rai ‘bace Maher yakuma cewa ” to da izinin wa ? ” Shiru Iftahal tayi sannan takuma cewa ” kayi ha’kuri bazan sakeba ” cikin muryar kuka jinjina Kai yayi yace ” naji amma idan Kika sake zuwa wani waje bada izininaba  ranki seyayi mugun ‘baci sannan kisani yazama dole kikoma kwana cikin bedroom d’ina sabida cika umarnin Ammi na kishirya inada lecture 10 duk da ciwona yatashi jiya amma yau inajin zan iya shiga Skul d’in tare zamu tafi sabida naji ke 10:30  kike da lecture ” cikin sanyin murya tace 


” Kayi ha’kuri ni bazan iya shiga Skul ba yau ” har yajuya yadawo cikin mamaki amma baice komiba jira yakeyi yaji tace wani abu amma daga haka batasake cewa komiba daurewa yayi dan yagaji dayin maganar yace ” bakida lafiya ne ? ajiyar zuciya tayi tace ” Kai ne katurani jiya nabuge Kai na shine yakemin ciwo sosai ” rumtse idon shi yayi yanajin babu dad’i cikin zuciyar shi yace 


” Gaskiya doctor ne zamada mace bai kamaceniba yanzu gashi najamata ciwon Kai da mutuwa tayifa Yaya zanyi kenan gaskiya dabazan yafe ma Kai naba ” amma afili cewa yayi ” subahanallahi zama yayi bakin bed d’in yasa hannu yata’ba kan nata saurin juyo da fuskar ta yayi sabida yadda yaji kan nata yad’auki zafi sosai ganin yadda fuskar tata takumbura sosai yasa Maher saurin jawota jikin shi cikin razana sosai yaji babu dad’i cikin sanyin murya yace


” Sannu kiyi ha’kuri kinji daga yau Idan kinga ciwona yatashi kidena zuwa inda nike idan Kuma kina gurin yatashi to kigudu kibar gurin kinji sannu bari nakira doctor yadubaki yabaki magani ” kasa magana Iftahal tayi sede wani saban kuka dataji tanason sanar dashi batun fyad’en dayayi mata Kuma tanajin tsoron Kar yakasa fahimtar ta sabida wannan zancan yafi batun bige Kai had’arin fad’i gyara mata kwanciyar yayi had’ida rufa mata blanket sannan yami’ke yafita kasancewar asubace yasa doctor baizo dawuri ba se wajan 7:30 sannan yazo kafin zuwan doctor Maher kasa zama yayi sabida damuwar halin dayasaka Iftahal doctor yana zuwa Maher yadubai shi cikin rashin fahimta yace ” amma sewa nayi katuromin doctor Sera shine Kai kazo to maiye nufinka kana nufin kana namiji ‘kato dakai zan yarda kata’bamin mata ? Ina bazai yiwuba idan har bazaka turo mace ba to gara nakaita asibiti kawai ay can dole yazama akwai mace  ” 


Advertisements

Ha’kuri doctor yashiga bashi sannan yakira wayar doctor sera yace tazo sosai Shanwul yashiga yin mamakin yadda Maher yake fad’a cikin tsawa abinda bai ta’ba ganiba itako Iftahal dake jin duk abinda ke faruwa daga bedroom tasauke ajiyar zuciya tace ” Wai yaushe Prince  yafara kishina haka ? lalle akwai damuwa shiko Shanwul cikin girmamawa yace ” Allah ya’kara maka lafiya dama cewa nayi dawace mota zakaje Skul sabida nasan wacce zankai Gimbiya Skul ” wani irin kallo Maher yawatsa mishi sigarin hannunshi yakunna yazu’ka sosai yafesar yasake zu’ka dagani cikin ‘bacin rai sosai yake zu’kar ta sannan yadubi Shanwul yace


” Daga yau bana bu’katar kasake kaita Skul ita 1 sede idan danine idan Kuma time d’in shigarmu baizo 1 ba to nine zan kaita sannan daga yau Kar nasake ganin ka cikin part d’in nan sede idan nine nakiraka jeka kacema iya tazo ” cikin sauri Shanwul yafita Yana jinjina wannan lamarin cikin zuciyar shi yace ” ko dai Prince yafara son gimbiya ne ? Ko Kuma wani taken takurar ne ” Amsar daya kasa bama kanshi babu jimawa sosai Iya tashigo zubaiwa tayi agabanshi tana kwasar gaisuwa baice komiba balle ya amsa dede lokacin doctor Sera tashigo tashi yayi yayi mata nuni data biyoshi bedroom d’in Iftahal yashiga itama doctor tashiga duban Iftahal yayi yace sanar da ita damuwar ki  ” daga haka yajuya yafito kallon Iya yayi yace ” 


” Iya kizauna anan kikula da gimbiya kafin nadawo zan shiga Skul duk abinda take bu’kata ayi mata ” daga haka ya haura sama wanka yashiga bayan fitar Maher doctor Sera tadubi  Iftahal tashiga tambayar ta maike damunta cikin sanyin murya tace ” kaina yake matu’kar ciwo dakuma zazza’bi sekuma ” kasa ‘karasawa tayi tace shikenan abinda kedamuna ” jinjina kai Doctor Sera tayi sannan tace yakamata Kisha tea sabida zanyi miki allura ” dede lokacin Iya tashigo tace to cikin sauri tafita babu jimawa tadawo hannunta ri’ke da cup d’in tea mai kauri Zama tayi bakin bed mi’kama doctor Sera cup w tea din tayi tari’ke d’an kamo hannun Iftahal tayi amma taga Ina hakan yasata saka hannu 2 tatadota zaune ” wassssa Allah ” Iftahal tace tad’an zame daga zaman  ganin haka yasa Iya jinjina Kai had’ida binta da kallo amma batace komiba se sannu datace mata 


Da ‘kyaur iya tasamu Iftahal tasha tea d’in sannan doctor tayi mata allura gyara mata kwanciya Iya tayi sannan suka fito ‘karamin parlour zama sukayi doctor najiran Maher magunguna tashiga rubutawa tsayin lokaci sannan Maher yashigo cikin shigar ba’kin suit wooow gaskiya Maher yayi matu’kar had’uwa musamman cikin wannan shigar sosai suit d’in sukayimai kyau duban doctor yayi yace ” yaya ? ” bayani tayimai kamar haka 


” Babu wata damuwa sosai da alama tasamu rashin bacci Kuma tanada damuwa sosai daganin fuskarta tasha kuka sosai nayi mata allura zata samu bacci zuwa lokacin dazata tashi zazza’bin da ciwon kan zai sauka ga wa’innan magungunan asiyo mata tashasu kwana 3 “


Amsa yayi sannan yami’ka mata kud’i masu yawa yi yayi kamar zai shiga bedroom d’in sekuma yajuya yafita tashi itama doctor tayi tayima Iya Sallama tafita sosai Shanwul yayi mamakin yadda Prince zai iya shiga Skul yau bacin jiya ciwon shi yatashi 


Egypt 


Kai komo Hajiya Himla takeyi cikin tsakiyar parlour ta sannan tadubi d’anta dake zaune sama cushion shima sefaman huci yakeyi tace ” karka damu Abdul inde ina raye to wannan masarautar takace sannan kasani wannan auran na Saraki bazai Kai labari ba hmmm watoma aure Yana mahaukacin ko wa inne sha sha shun iyayen ne suka bashi ‘yarsu hmmmm lalle kuwa sunkawo yarsu gidan mutuwa ni Hajiya Himla senaga bayan su duka wallahi dan kawai Ina macane dani namiji ne babu yadda za’ayi nabar Yaya Zaid hawa saman kujerar mulkin ‘kasarnan tokuwa tunda ni tafi ‘karfina Kai bazata gagareka ba Abdul kaine Sarkin gobe cikin wannan  katafariyar masarautar ” 


Ihu Abdul yayi yace ” se Umma ta da kyau shiyasa idan natuna inada uwa irinki nikejin dad’i sosai sabida nasan babu abinda zai gagareni cikin duniyar nan amma Kinga yadda Kaka take murna Wai Saraki yayi aure yazama babban mutun Wai lallai kuwa sun godema Allah sau’ki yasamu kumafa hadda Momy cikin masu murna ” dariyar mugunta Hajiya Himla tasaki tace barsu kawai muma muje taya murna kafin murnar tasu takoma kuka ay bazamu nuna bamuji dad’i ba ina mu nuna tamu murnar tafi tasu muje Abdul d’ina


Comments please

Leave your vote

-4 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like