FURUCI 15-16

Advertisement

Daga haka suka fita zuwa ‘bangaran Mama wato Kaka zaune suka sameta itada Momy dasu Aunty kurrat dasukazo duba jikin Kaka  se wata hadima dake yima mama tausa a ‘kafafu dede lokacin suka shigo zama hjy Himla tayi sannan tafad’ad’a fari’ar ta tace ” mama wani labari naji shine nace bari nazo

naji Allah yasade gaskiya ne dan tuni nake burin ganin Sarakin mu yazama babban mutun ” murmushi Mama tayi tace ” gaskiya ne Himla Saraki na yazama babban mutun in sha Allah nanda 9 months zanga d’an shi ko ‘yarshi ay Kam idan matar Saraki tahaihu tofa senaje USA Allah yasa lokacin baban ku yatashi nasan zaiyi farincikin ganin yaron Sarakin shi sosai ran hjy Himla ya’baci amma setayi saurin seta kanta tace ” gaskiya ne nima kuwa zanje dan Kam za’ayi sunan daba’a ta’ba yin irin shiba sosai Momy tasaki murmushi tace 


” Allah sarki yarona Allah yabaka Lafiya gaskiya Ina matu’kar yin farinciki nasan in sha Allah wannan matar alkairi ce atare dakai mi’kewa Aunty kurrat tayi tace ” lalle de Kam amma nifa ina ganin baikamata abar Saraki da mace ba sabida kunsan fa idan ciwon shi yatashi komifa  zai iya faruwa ” mi’kewa Aunty Sumeer tayi tadafa Aunty kurrat tace bai kamata zuciyar ki takawo miki abinda babu alkairi ba kuma kiyi na’am dashi kisani Saraki bashine yad’aura makanshi wannan muguwar lalurar ba Allah ne yad’aura mishi Kuma hakan yazama kaddarar shi ce dukda ni cikin zuciya ta inaji kamar ma’kiyane suka zagaye min ‘kanina amma in sha Allah bazasuyi nasara ba a gobe babu wani sarki cikin daular mu se Saraki Aunty kurrat kawai kiyi fatan alkairi ” 


Sosai maganar Aunty Sumeer ta’bata ran Aunty kurrat da hjy Himla murmushin ya’ke Aunty kurrat tayi afili amma cikin zuciyar ta setace ayko idan har Ina raye babu yadda za’ayi nabari Saraki yayi mulkin wannan daula tamu kenan shikenan muda Mahaifiyar mu munzama ‘yan kallo lalle hakan bazai ta’ba yiyiwa ba ” itama hjy Himla anata ‘bangaran cewa tayi ” hmmm lalle kuwa zanga yadda za’ayi mahaukaci yayi Sarauta yazama doke nakoma wajan boka ya’kara yawan aljanu su kashemin Saraki dagashi har matar tashi nahuta ” Amma afili setace ” maganar ki gaskiya ce Sumeer ay Saraki ya isa ya aje iyali sosai Momy da Mama sukaji dad’in maganar Aunty Sumeer itako Faheemat se alokacin tace ” ayni wallahi sabida farinciki jina nikeyi kamar nayi tashi na isa USA ganin Amaryar ‘kaninmu autan mu Namiji ‘kwaya d’aya tilo Saraki namu Allah yakare mana sarkin gobe ” tafi Aunty Bahijjat tayi tasaki murmushi sosai tace ” gaskiya Aunty Faheemat kamar kinshiga zuciya ta nima Kam hakan nikeji tunda Sarakin mu yayi aure tokuwa tabbas lafiyar shi tafara samuwa sosai waiyyo Allah inama zanga wannan Amaryar tamu yanzu dako sabida jin dad’i Kaka Sena d’agata sama ” 


Murmushi Mama tayi tace dawane ‘karfin kinaji da jiki kamar iska tahureki ne zaki iya d’aga wani Kinga Bahijjat kifidda miji ahad’aku keda aunty ki kindega ‘kaninki yayi auran shi amma ke  ” katseta hjy Himla tayi dafad’in ” mama dama inaso nasanar daku cewa Abdul yasanar dani yana matu’kar son Bahijjat bari nayi dama Maimartaba yadawo nasanar dashi sekuma gashi hira takawo zancan ” cikin sauri Bahijjat tadubi Abdul shima ita yake kallo murmushi yasakar mata mi’kewa Bahijjat tayi rai ‘bace tace ni gaskiya Kaka bazan iya auran Yaya Abdul ba gaskiya garama yanemi wata ” daga haka tafita daga part d’in cikin fushi afusace hjy Himla tami’ke tace 


” Iyye lalle Bahijjat kin isa shiyasa kike gayamana babu sugar hmmm kina lokaci yarinya to zanga wanda ya isa yahana wannan auran mama Allah idan ba’a aura ma Abdul Bahijjat ba to wallahi zanbar muku cikin masarautar nan dafa Abdul tayi tace ” Abdul kwantar da hankalin ka duk da cewa mahaifin ka baya yare ni nan nazamar maka duka 2 uwa Kuma uba bazakayi kukan rashin komiba ” daga haka taja hannun shi suka fita

Advertisements


Bayan fitar hjy Himla Aunty Faheemat da Aunty Sumeer sukace gaskiya mama bai kamata ayarda da wannan had’in ba kowa yasan Abdul bayaji gaskiya bai cancanci auran ‘kanwarmuba itako Momy kasama magana tayi sabida bai kamata tace komiba akan wannan maganar gaban sirika itako aunty kurrat cewa tayi ” idan bamuyarda Abdul ya auri Bahijjat ba to kenan muma nashi mun ‘kishi kenan balle wasu ” sosai maganar Aunty kurrat tasa Momy ‘bacin rai murmushi Mama tayi tace ” gaskiyar ki kuwa Kurrat ay mace tana iya canzashi babu yadda zakuyi kucire Abdul daga jikin ku kuje ku lallashi Bahijjat tayi ha’kuri watarana zatayi alfahari dashi “


Jin maganar Mama yasa jikin Momy yayi sanyi sosai domin kuwa tasan tunda Mama tayarda tofa babu makawa fita sukayi daga part d’in kowa zuciyar shi babu dad’i Amma banda Aunty kurrat itakam ranta fes sabida suna matu’kar yin shiri da Hajiya Himla


Wani katafaran gida Mai matu’kar kyau wanda kallo d’aya zakayima kasan mamallakin gidan yatara dukiya maitarin yawa bakowa bane mai wannan gidan illah Alhaji Tukur sananne cikin ‘kasar Egypt Kuma shahararran d’an kasuwa zaune yake jikin wani katafaran parlour shida wasu mutane su 4 suna tattaunawa mi’kewa d’aya daga cikinsu yayi yace ” Alhaji kaskiya akwai matsala fa banajin zamu iya shanye jinin waccen yarinyar sabida tana matu’kar yawan yin addu’a kuma ga yawan Zama da alwala gaskiya yawan addu’o’in ta yasa jininta samun kariya daga dukkan wata cuta sosai jiya mukasha wahala amma ko gashin kanta mun gagara ta’bawa dukda kuwa akwai janaba jikinta gaskiya Alhaji idan muka matsa zamu samu babbar matsala wallahi ni atawa shawarar mubar wannan yaron haka tun kafin yazama masifa atare damu kuduba munsamu dukiya maitarin yawa tasanadin shi sabida kusan mutun 9 muka shanye jinin su tasanadiyyar shi yakamata mubari haka tunda ayanzu yasamu wata garkuwa Mai ‘karfi atare dashi ” 


Tashi Alhaji Tukur yayi cikin tsawa yace rufemin baki Kai wayagayamaka cewa zanbar Maher to kasani wallahi  bazanbar Maher yahutaba Mahaifiyar shi itace tajame nasashi cikin wannan  halin a rayuwata babu macan danaso kamar Batol  har gobai Kuma babu wacce nikeso samada ita amma ta’kini taje ta auri wancan Sarkin tabarni naji zafin hakan sosai har yanzu Kuma inajin zafin haka shiyasa bazan bar Batol taji dad’in rayuwa cikin waccan masarautar ba sena gigita rayuwar ta tasanad’in d’an data haifama Sarki Zaid yazama dole waccan yarinyar tamutu duk yadda za’ayi sabida doctor yasanar dani cewa Sarki Zaid da Batol sunyi na’am da ita banaso susamu wani abinda zaisasu farinciki Kuma nafiso yarinyar tamutu sanadin Maher yadda zaikasa samun wata matar sannan barin yarinyar atare dashi wata marazanace ga cimma burina ” 


Tattaunawa sukacigaba dayi tsayin lokaci sannan sauran sukayi sallama da Alhaji Tukur suka fita babu jimawa matar shi Hajiya zubaida tashigo fruit takawo mishi tafita ko kallonta baiyiba inda sabo tasaba da wannan halin nashi yakasa bata soyayya da kulawa sabida son Batol daya mamaye zuciyar shi sede Yana matu’kar son yaranshi guda 3  zahradden da Nuhu se hamdiyya sosai yake matu’kar jidasu bayason damuwar su ko kad’an 


Nigeria 

Advertisements


Shukura ce zaune a parlour hannun ta ri’keda waya dede lokacin Zayyat yashigo d’an kallon inda inda Shukura take yayi magana yakeson yimata amma baisan ta’ina zai faraba zuwa can yanufi cushion d’in dake fuskantar ta yazauna sannan yace 


” Uktee inason magana dake ” d’ago ido tayi tadubeshi tamaida tacigaba dayin abinda takeyi a waya sakeyin magana yayi ” Uktee dan Allah kisaurareni shawara zamuyi Abba ne yabani za’bi shine naga yadace muyi shawara kafin yanke hukunci kinji ki saurareni dama cewa y….. Dakatar dashi tayi dafad’in basaikayi shawara daniba kawai kayi abinda kaga dama ” amma de Uktee maganar fa tanada matu’kar mahimmanci musamman agareki please kisaurareni ” tsawa Shukura tasakar mishi tasake cewa nace kayi duk yadda kaga dama ” mi’kewa Zayyat yayi afusace yace 


” To shikenan daga yau kisani  babuke babu ayki bana bu’katar ace matata tana fita office nayanke yadda nagadama kamar yadda kikace ” cikin sauri Shukura tami’ke tasha gabanshi tace ” baka isaba Ina lallema yaro to bazan dauki wannan shashancin ba kasani zuwa office babu fashi ” 

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

” To bari nagani ” cewar Abba dake tsaye bakin ‘kofar tun d’azu zaro ido Shukura tayi sabida sosai tarazana dan batayi cammanin zuwan Abban ba shigowa ciki Abba yayi sannan yace ” tunda yace a a to magana ta’kare nine nabashi za’bi amma sabida adalci irin nashi yazo kuyi shawara Amma Kika ‘ki to kisani Shukura idan har ba Zayyat bane yayarda kicigaba dayin ayki to daga yau babu maganar ayki nahana ” wucewa ciki Abba yayi d’an duban Zayyat tayi tace  ” yakamata kacanza wannan maganar ” murmushi yasakar mata sannan yace ” Nagama magana ” daga haka yafita a parlour cikin tashin hankali da damuwa tanufi bedroom d’in ta tana kuka 


USA 


Tun bayan tafiyar Maher skul Iftahal take barci sabida allurar da’akayi mata Kiran sauran ma aykatan Iya tayi suka shiga gyaran part d’in bayan sungama kowa yakoma mazaunin shi se Iya kad’e  komawa cikin bedroom d’in Iftahal Iya tayi  ganin Iftahal zaune yasa Iya saurin ‘karasawa gareta cikin girmamawa tace ” barka datashi gimbiya Yaya jikin naki ” amsawa Iftahal tayi cikin sanyin murya ‘ko’karin sakkowa Iftahal tafarayi sekuma tacije baki had’ida fad’in “wasssh  ” kamata Iya tayi zuwa toilet d’in har cikin toilet ganin halinda take ciki yasa Iya cewa ” gimbiya bari nahad’a Miki ruwa kishiga idan babu damuwa ” saurin kauda kanta Iftahal tayi sabida kunya batayi tunanin Iya tagane halin datake cikiba se yanzu had’a mata ruwa Iya tayi dukda tanajin kunya amma haka tabari iya tagasamata  jikinta sosai sannan tayi alwala suka fito zama bakin bed Iftahal tayi sosai taji dad’in jikinta jitayi zafin yaragu sosai cikin girmamawa Iya tace ” Gimbiya bai kike bu’kata adafa miki ? ” d’an jim Iftahal tayi sannan tace 


” Mai Prince yafiso  ? ” Gaskiya bashida takamai Mai amma bayason abu mai nauyi ” shiru Iftahal tayi tace kibarshi kawai zan shiga Kitchen d’in dakaina ” cikin mamaki Iya tace ” zaki iya kuwa gimbiya kibari nayi kingaf a jikinki babu karfi ” murmushi Iftahal tayi tace ” zan iya Iya kije kawai ” sosai Iya tajinjina ma karfin halin Iftahal fita Iya tayi bayan fitar Iya Iftahal tami’ke cikin sanyin jiki takeyi komi shiryawa tayi cikin doguwar riga Mai laushi sosai tashirya kanta  sezuba kamshi takeyi ahankali take takawa sabida zafin datakeji ahaka har tashiga kitchen tsayawa tayi tayi shiru zuwacan sannan tafara shirya abinci kafin wani lokaci parlour yadauki kamshi mai dad’i   bayan tagama tahad’a lemon kwakwa Wanda yasha Madara bayan tazuba cikin jog tanemi guri tazauna ta d’akko Jog d’in lemon bud’ewa tayi tafara karanta ayatus sufa cikin Jog d’in sosai takeyin karatun sautin Yana shiga cikin lemon bayan tagama tahad’a komi saman tire tad’auka ahankali tanufi  saman Maher da’kyar take hawa sabida ko Yaya tad’aga ‘kafarta zafi takeji


Tana shiga parlourn tanufi ‘kayataccen dining d’in shi ta aje tiran seda tad’an zauna ta numfasa sosai sannan tami’ke tashiga bedroom d’in shi komi tsaf Amma dukda haka seda tasake gyarawa tacanza bedsheet dan danan ko ina yad’auki kamshi jin ana Kiran sallar azahar yasa Iftahal d’aukar abin sallar dake bedroom d’in ta shinfid’a komawa ‘kasa tayi ta d’akko hijab d’in ta sannan takoma saman salla tatada bayan ta idar tayi addu’o’i kamar yadda tasaba titowa parlour tayi tazauna shiru tayi tana nazarin yadda zata sanar da Maher batun wannan fyad’en dayayi mata tarasa maiyasa tajejin tsoran sanar dashi jin takun haurowar shi yasata jin bugun zuciya matsananci cikin sauri ya idasa shiga cikin parlour ganin Iftahal a zaune yasashi sake dubanta sosai sannan ya’karasa ciki 


Comments please

Leave your vote

-2 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like