MIJIN AMMINA NE SILA 3-4

Advertisement

 written by noor Eemaan 


wattpad@noorEemaan

page2-3

ganin yana tunkarasu yasa ammi kara firgita a dari ta juya domin su gudu, sai kawai suka ji  ma’aikatan gidan sun sa dariya gaba

dayansu, alhaji shima ya fara dariya gaba daya kasa motsi ammi tayi ganin  workers din gidan na dariya wanda sai yanzu ta lura dasu  dukkaninsu maza ne,  abrar kuwa kuka tasa tana cewa ” ammi kinga abunda nake ce miki ko,”? ta fada da yaren buzanci, murya alhaji ce ta katse mata amsar dataso bawa abrar “ashe hajiya ta haka kike da tsoro ?yafada yana kara fashewa da dariya domin ya kasa riketa. Ajiyar zuciya ammi ta sauke ganin ba abinda take tunani bane, nan workers din suka dinga zuwa gabanta suna gaisheta cikin sakin fuska take amsa musu kana suka nufi cikin gidan mamakin irin dukiyar alhaji   fal ranta…


*1 MONTH LATER*

zuwa yanzu ammi ta zama yar gida domin lafiya lou suke zaune da alhaji, abrar kuwa har yanzu bata sakewa da alhaji daga gaisuwa shikenan, a daki take wuni  duk yanda alhaji yaso  ya jawota jikinsa ta ki bari  ammi kuwa tun tana damuwa da halin da abrar da tsiro dashi har ta hakura domin tayi fadan tayi lallashin akan ta dauki alhaji shettima amatsayin uba amma sam ta ki yarda, da ammin ta fara maganan zata sa kuka.


Advertisements

zaune alhaji shettima da ammi suke akan hada’ddun kujeran falon da girma falon kadai ze kai 100/100.

“hajiya?”

“na’am alhaji” ammi ta amsa.

“ki sanar da abrar cewa ran monday in sha Allah zasu fara jarabawan waec da neco domin na gama mata komai na registration ga exams card dinta da uniform” ya fada yana  mika mata wani leda mai kyau.

 kasa magana ammi tayi gaba daya hawaye sun ciko idanunta tama rasa bakin godiya ashe zata samu wand ze meye gurbin musu sajeed? shiyasa akullum yaumil alhaji ke kara  matsayi aranta dalilin kaunar da yake nunawa tsoka daya a miyar ta wato(abrar).

n

“alhaji nago…. shhhhhh cewar alhaji shettima kana yadora ai abrar na dauketa tamkar yar dana haifa don uba ya sauke wa yarsa hakkin dake rataye awuyansa sai ya zama abun godiya har haka, murmushi ammi tayi kana ta bashi side hug bubbuga bayanta yayi kana yace ta kaiwa abrar kayanta domin ta fara shiri  ba musu ta mike … 

Kwance take tayi matashi da hannayenta tayi zurfi cikin tunani tamkar wata babbar budurwa mai tarin damuwa, girgiza kai ammi   dake tsaye abakin kofa tun dazu tayi kana ta karaso  bakin gadon ta zauna

 “abrar”

shiru ba amsa adan tsawace ta sake kiranta hadi da girgizata, dawowa hayyacinta tayi ganin ammi ce yasa ta fara kokarin tashi zaune hadi da cewa 

“ammina”

“abrar mekikeso ki mayar da kanki ne eyeh? Gaba daya kin daurawa kanki damuwa kina yar karamar ki dake  meye matsalarki? meye matsalarki abrar amsa min”

Advertisements

“ba…bu komi ammi ta fada muryanta na rawa” shikenan tunda haka kika zabawa kanki ,dakin ya dau shiru na mintuna uku kana ammi tacegashi inji alhaji ya biya miki waec da neco akwai uniform da wasu abubuwan dazaki bukata aciki, in kin ga dama kuma karki gode masa. Ammi ni banason wani abu daya fito daga hannunsa , toh zaki iya zuwa ki gaya masa  haka ammi ta fada cikin fushi kana ta dafa kafadarta ta cigaba da cewa koda wasa abrar kada ki bar alhaji yasan baki kaunarsa, domin zan saba miki aranar kuma ki biyoni ki masa godiya ki kuma saki fuskarki ammi ta karasa hadi da ficewa, jiki ba kwari abrar tabi bayan ammi tana kokarin daidaita yanayinta”


“da…ddy  nagode Allah ya kara arziki. Abrar ta fada kamar batason yin magana murmushi alhaji shettima yayi cikin jindadin ta kirasa da “DADDY” ameen daddy’s girl ya fada yana shafa kanta ajiyar zuciya ammi tayi ganin  bata kwabtsa mata ba. Abrar  kuwa wani iri take ji ganin ta kira mutumin data k i jiki da daddy wanda batasan dalilin tsanar ba, saidai tayi hakan ne don farinciki ammi, kuma tayi farincikin domin ta gani afuskarta mikewa tayi domin komawa dakinta alhaji shettima yace” abrar bazaki zauna tare da mu ba har yanzu dai baki gama sakin jikin ki ba, sae da ta runtse idanunta kana ta juyo tace 

“ina dan jin baccine daddy tafada  ok toh it’s alright yafada yana mai da hankalinsa wurin ammi suka cigaba da hirarsu…

ranar monday abrar tafara zuwa zana exams.

dinta kuma alhamdulillah bata samun matsalan komai domin makarantar masu kudi ce, bayan wasu watannin ta gama exams dinta sai jiran fitowar result…


*some month later*


“hajiyata ki sanar da abrar ta fara shiri na duba result dinta ya fito kuma alhamdulillah bata da matsala, na kuma samo mata admission a cyprus wanda acan nakeson ta hada degree dinta if possible har da masters ko ya kika gani” yakarasa yana girgiza kafaffunsa.  shiru ammi tayi tama rasa bakin godiya domin kullum da kyautatawar da alhaji ke musu shiyasa yake kara samun matsayi aranta domin soyaayar  dayake nunawa tsoka daya amiyarta wato abrar…

“ai alhaji abrar diyarka kana da iko da ita Allah yakara arziki, cikin jindadi yace ameen”

bayan ammi ta sanar da abrar nunawa tayi ita batason ya dinga mata komai, sai da ta ga fushin ammi kana ta hakura ta je ta masa godiya.


*******************************************

suna filin jirgi ana kiran sunan massengers har aka kira su abrar, basu wani nuna rashin sabo ko kauyanci ba tunda wanna shine karon farkon su wanda hakan dasuka yi yasa alhaji shettima jin dadi kwarai…


 “CYPRUS”

bayan duk sun gama mata komai na  karatun ta har alhaji shettima yace ze samo mata gida awajen school din amma abrar ta nuna tafison  zaman cikin campus ko nace hostel din makarantar.

 Washegari su ammi suka nufi airport domin komawa gida, abrar data rakosu sai kuka take,  ita da ammi zata zauna anan kada ta tafi alhaji sai bata baki yake amma ko kallons a bata yi, cikin kuka abrar tace “ammi ki kulamin da kanki kinji ni  ban yarda da mutumin nan daddy  ba, ki kula kinji idan ya miki wani abu  ki gayamin zan rama miki da kaina tafada cikin yarinta tana daga damtsen hannunta alamun karfi 

murmushi mai tafe da hawaye hadi da ajiyar zuciya ammi tasaki at once tana mamakin maganganun da abrar keyawan yi tamkar babba, ta kuma ji dadi daba da hausa tayi magana ba domin batason ko kadan alhaji shettima yasan cewa abrar batasonshi…

 haka abrar ta cigaba ta attending lectures har ta kai kwana shida, kamar yau  ta fara shirin zuwa makarantar sanye take da jeans trouser sai riga ta ciki pink colour sai jacket din jeans din data dora asama pink top din snickers dinta ma pink ne sai mayafin data yi rolling dashi shima pink color,babu ko digon kwalliya afuskarta amma sosai tayi kyau duk da cewa har yanzu babu komai akirjinta 🙈 jaka ta rataya tana yamutsa fuska domin kasan cikinta taji yana mata ciwo tun safe, rufe dakinta tayi da padlock domin wadanda zasu zauna adakin har yanzu basu iso bah, bata jima da shiga aji ba lecturer ya shigo yafara gabatar da lecture saidai ba komai abrar ke fahimta ba domin ciwon cikin sai gaba yake

kwas! kwas!! suka ji takun takalmi na tukaro ajin, dakatar da bayanin lecturan yayi domin ganin mai shigowa, wata farar yarinya ce ta shigo da’a shekaru zata girmewa abrar da shekara daya haka, cikin girmamawa tace” sorry for disturbing your class sir” jinjina kai yayi kana yace “its alright but why are you attending my class by this time” yafada yana nuna wristwatch din hannunsa. 

“i just resumed today, i mean right now sir”

“ok” yace kana yana mata nuni data je ta zauna  sannan yacigaba da bayaninsa, gaba daya wanna yarinyar ta kalli ajin jitayi tafison zama kusa da abrar, murmushi ta sakarwa abrar lokacin data daidaita zamanta amma sam mutuniyar batasan tana yi ba domin ciwon ciki yasata agaba, ganin abrar bata kula ta ba yasa ta dan bangaji kafadarta abrar da tata hadi da cewa “hey”  dagowa abrar tayi tana murmushin yake…

can da cikinta yayi wani azababen ciwo batare da tasaniba ta saki ihu tana zamewa kasan desk din sauri  wanna yarinyar rikota tana cewa 

 “are you okay”? 

” no am not my stomach!!!” abrar ta amsa da kyar.

lecture ya bada umarnin akaita clinic su bata drugs ba musu wanna yarinyar ta rikota hadi da daukan jakarta, yawanci yan  ajikin suka hada baki wurin furta “sorry”

suna cikin tafiya abrar tace

 “please take me to my room i will fine”

“noo you need to see a doctor” inji wanna yarinya.

“Please just take me to my room i beg you”  abrar tafada wasu siraran hawaye na zubo mata. ba musu ta gyada kanta abrar na nuna mata hanya har suka zo dakin zaro ido wanna yarinyar tayi ganin dakin aka ce zata zauna shine na abrar kara kallon dan card din hannunta mai da dauke da number dakin tayi sai tayi murmushi da ita kadai tasan ma’anarsa… 

wanna yarinyar ta dau mukulli a jakar abrar suka shiga dakin, zaunar da abrar tayi akan gado tana sakin ajiyar zuciya domin gaba daya nauyin abrar ajikinta yake har sukazo dakin  kallon farar abayar jikinta tayi zaro ido tayi hadi da cewa” blood”

” you re mensturating” azabure abrar tamike tana kallon jikinta, kallon gadon tayi sai taga shima ya cike da jini, ihu tasa hadi da fashewa da kuka itakam tun dazu take jin kamar abu na fito mata amma bata kawo cewa jini bane. cikin tausayawa wanna yarinyar ta rungumeta tana cewa” sorry don’t cry again, i guess this is your first time don’t worry i will help you through okay” ajiyar zuciya abrar tasaki still hawaye na zubo mata, cire zanin gadon wanna yarinyar tayi hadi da cewa “go and take your bath am coming” tafada tana ficewa da sauri bata ko damu da jinin dake rigar ta ba…

wanna yarinyar kuwa wurin masu kula da kayan dalibai tanufa domin daman ta ajiye kayan wurinsu ne domin ta gano dakin sai tasa akai mata kayan, tayata daukan kayan sukayi  tana gaba suna biye da ita…

bayan sun ajiye kayan ta janyo dan karamin akwati ta fito da sanitarypad hadi sabon pant ta saita pad din ajikin pant din kana ta mike ta nufi hanyar toilet din, kwankwasa kofar tayi batareda ta kalli  abrar ba ta mika mata pant din cikin kunya ta amsa, sanyawa tayi ta fito tana jinta uncomfortable, burinta kawai ta kwanta ko zata dan samu sauki, rub da ciki tayi  duk da tasan babu kyau amma tafi jin dadin hakan domin ciwon yana lafe mata babu jimawa bacci ya dauketa. wanna yarinyar  kuwa kayanta tafara jerawa asite dinta bayan tagama komai ta kwashi kayan abrar har ma da zanin gado ta saka awashing machine itama toilet ta fada tasakarwa kanta ruwa bayan ta fito ta sanya simple dress ta haye gadonta tausayin abrar fall ranta domin itama bata manta wahalar data sha akaron farkonta, bayan kamar awa biyu abrar ta farka abunda ta gani yasa ta zaro idanunta….

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like