MIJIN AMMINA NE SILA 7-8

Advertisement


 ✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

written by noor Eemaan

watttpad@noorEemaan


page7-8

sosai yake mamakin girman datayi tamkar budurwa yar shekara 18zuwa20 daidai lokacin abrar ta iso wajensu cikin sauri ta rungumi ammina tana fashewa da kukan farinciki ” i so much miss you ammina”  tafada tana bata sumbata a kumatu itama ammi sumba ta bata a goshi cikin  kaunar tilon yarta, cikin yaren cameroon ammi tace” baki ga daddyn ki bane?”  take annurin fuskarta ya dauke ta rasa dalilin daya sa taki jinin ko da ganin alhaji shettima ne, ita kanta tarasa dalilin wanna tsanar data maza amma ya zatayi yana taka matsayin uba ne agareta yanzu, murmushi ta kakaro hadi da cewa ” daddy ina wuni na sameku lafiya”? 

dan firgigit yayi yana cewa ” abrar daddy’s girl ya studys?  welcome back home”

” thank you daddy ta fada kamar an mata dole kurawa jerarrun fararren hakoranta mai siririn wushirya atsakiya ido yayi lokacin datake magana har be san lokacin data kare maganar ba, ammi ce tace “alhaji kana jina kuwa?

Advertisements

” uhmm na’am mekika ce hajiyata?” ya fada yana wayancewa. 

“cewa nayi mutafi gida ko”

” toh toh” yafada yana dan satan kallon abrar dake kallon hanan dake nesa dasu tareda wani saurayi mai kyawun kira saidai bata ga fuskarsa ba domin ya bata baya…

tana cikin motar sai Allah-Allah take ya  juyo, domin haka kawai taji tanason ganin fuskarsa ba, amma inaa sai kwantaccen sumbarsa mai dan tsayi domin tsaf za’a iya masa parking…


” safa da marwa alhaji shettima yake abedroom dinsa, gaba daya yarasa nutsuwarsa, kyakyawar fuskarta kadai ke masa gizo tun bayan ganin daya mata airport, ga wutar sha’awarta dake sake ruruwa ajikinsa, abun har mamaki yake bashi tayaya akan wanna yar karamar yarinya mai karancin shekaru zata sashi awanna yanayin?…


“ammina wallahi naga kin kara kyau sosai, yanzu wazai ce ke kika haifeni” abrar dake kwance kan cinyar ammi tafada cikin shagwaba tana jujjuya manyan fararen idanunta. dariya mai sauti ammi tayi tana girgiza kai  “abrar zan fasa miki baki fa kin raina niko” ammi tafada tana dungure mata kai cikin wasa “sorry ammina tafada tana sake rungumeta. shafa kanta ammi tayi tana cewa “bari na saita mana dinning table muci abinci sai ki bani labarin kasar dakike karatu yama sunan kasar”?

“cyprus ammi” 

“ywwa cyprus” ammi ta maimaita bayan ammi tayi setting table tace” abrar bari na kira daddynki  muci abinci” take ta bata rai ( tofah jama’a kuji mun abrar mutum da gidansa🙄😃)

cikin nutsuwa suke cin abincinsu yayinda alhaji shettima ya kurawa lips dinta idanu har ammi ta ankara ta dan bugi kafadarsa cikin rashin gaskiya yace ” wato hajiyata sai yanzu nakara ganin kamanin ku da diyata abrar”  murmushi kawai ammi tayi bata kawa komai aranta ba, yayinda    mutuniyar taku ko dago kanta batayi ba, shikam alhaji shettima ya daina damuwa da rashin sakewa da abrar ke nuna masa ya dauka hakan yanayinta yake tunda bai taba ganin ta furta ko nuna alamun rashin son shi amatsayinsa na mijin amminta ba…


Advertisements

suna gama jin abinci sai ga kiran hanan ta wayar ammi, nan suka fara hirarsu daga karshe hanan ta bawa mummyn su waya suka gaisa da abrar…


kokawa sosai sukeyi da mutumin dako fuskarsa bata gani domin ya rufe da face mask, ganin tana bashi wahala yasa wanna mutumin kwada mata kyakyawan mari daya sa ta saki ihu… afirgice ta farka ta ihun abakin ta, gaba daya ta jike da gumi, kirjinta bugawa yake tamkar zae faso rigarta ya fito, kallon agogan bangon dakinta tayi karfe 1:30am ya nuna mata dogayen kafafunta tasauke kasa kofar bathroom ta murda ta shiga, alwala ta dauro kana ta shimfud’a sallaya salla raka’a hudu tayi bayan ta iddar  tayi karatun alqur’ani hadi da addu’a, domin sosai wanna mafarkin da take yi kwanan ke tsoratata…


“abrar dole in dinga damuwa domin basan ko yaya raheenat tareda mijinta na raye ba, ina kokarin boye damuwata domin kada alhaji yaji ko na raina kokarinsa akanmu ba”

“in sha Allah suna cikin koshin lafiya ammi idan kuma baza raye, Allah yasa sun samu rahamar Allah”

“hakane diyata ameen” inji ammi tana alfahari da yartata…


“ooh wanna yarinyar tana son haukata, alhaji shettima yafada yana dungure kansa, karshe dai haka ya baro office dinsa domin aiki bazai yu ba, sallama yayi cikin hadadd’an falon, abrar ce kadai afalo tana yankawa ammi cucumber domin wani film datake matukar so ake haskawa bataso tayi missing koda waje daya ne dalilin zamanta afalo kenan domin itakam tafison zama bedroom dinta, saboda sam bata kaunar ganin alhaji ko kadan ita kanta  batasan dalilin tsanar hakan nan taji tsanarsa aganin farko data masa… “sannu da zuwa” tafada bayan ta amsa  sallamarsa.

“yawwa daddy’s girl” yafada yana binta da kallo yayinda yake ta faman lashe labbansa tamkar tsohon maye. “ina amminki?” ya tambayeta

“tana kitchen” ta amsa masa batareda ta dago ba…


daddare da misalin karfe shadaya daidai alhaji shettima ke tsaye abakin kofar dakin abrar yana leken ta tajikin window, sanye take da pyjamas farare sai bakin hijab half sunnah akanta, cikin nutsuwa take baccinta, take alhaji  shettima yakara jin wani kwadayin kasancewa da ita, domin ayau yafara ganinta a irin wanna shigar duk da kayan basu kamata ba haka kuma basu nuna tsaraicinta ba, amma mafi yawan lokuta yafi ganinta da dogayen riguna da kuma hijabs dogaye ganin ta gyara kwanciyarta yasashi saurin barin wurin…


dakyar alhaji shettima yayi bacci awanna daren adalilin son zuciya da kwadayi daya daura wa kansa, amma ya kudurta aransa cewa agobe zae kawar da kishirwan daya dame sa, tunanin ta yanda zae bullowa al’amarin batareda an samu matsala ba.


*WASHEGARI DA YAMMA*

awani babban pharmacy alhaji shettima ya shiga can sai gashi ya fito da leda magani  ahannunsa yana sakin murmushi ganin yana daf da cimma burinsa…..

SHARE✔

COMMENT✔

VOTE✔

EDIT❌A taya ni share please🙏

 

noor Eemaan ce✍


manage pls ba yawa wallahi bana dan jin dadin jikina.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like