MUGUN DUHU 1-5

Advertisement

 ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫

*SHAFIN SADAUKARWA NE GA* 👉shugabar kungiyar KAINUWA WRI ANTY fauzah yar amana alkairin Allah ya kai miki har gadon bacci, Allah ya kara tsawon rai mai anfani dattijuwar mu

Da sunan Allah mai rahma mai jin ƙai,tsira aminci daukaka su kara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam.

     *_FANS NA DAWO DA KARFI NA YANZU MA CIKIN LITTAFIN MUGUN DUHU WANDA ZAI KASANCE FREE BOOK, BANA BUKATAR KOMAI FACE HADIN KAI ,HADIN KAI DIN KUMA BAYA WUCE COMMENTS DAFATAN ZAKU BANI HADIN KAI YADDA MUKA FARA LPYA MU GAMA LPYA INA FATAN HAKAN_*

Advertisements

     

🅿️1️⃣_5️⃣

⚫….. Yammaci ne mai dauke da gajimare jfaa jifa , garin akwai zafi sosai kasancewar hadarin dake shirin haduwa da alama ruwa ne ke shirin sauka, gida ne madaidaici mai dauke da madaidaicin gate ,iya rayuwar duniya a wala a ji dadi wannan gidan ya ishi dan Adam.

       Gate din gidan na tura na shiga da alama babu mai gadi cikin gidan babban fili ne da zai dauke mota a ƙalla guda uku da ka dan yi tafiya kuma sai ginin da zai sada ka da cikin gidan ,can gefe saurayi ne da budurwa a kan plastic chair zaune tazarar dake tsakanin su a ƙalla zata kai kamu biyar ,cikin ƙaton hijabi take ita budurwar shi kuma saurayin cikin kananun kaya da suka amshi jikinshi ,gefen su yaro ne da bazai haura 8 yrs ba yana zaune yana wasan sa , zance suke cikin kwanciyar hankali,da ka gansu zaka kallon farko zaka shaida cikakkun masoya ne da suka sha soyayya suka ƙoshi ,kanta sunkuye yake ƙasa tana murmushi,cikin shaukin soyayya dake dibanshi yana watangaririya dashi yace SAHLA soyayyarki tarbiyyar ki addininki nagartarki suna matukar sani shaukin da Ni kaina nake mamaki wani lokacin ,amma hakan ba abin mamaki bane sabida nasan Allah yakan duba zuciyar mutum sannan ya bashi abinda yake muradi, keɗin ta dabance soyayyar ki na daban ne cikin raina,bayan soyayya ta aure dake tsakanin mu ji nake kamar keɗin wata jigo ne da rayuwa na jiki na , kin kasance min tauraruwa abar haska zuciyata ,niday AHLAN nace tarbiyyar SAHLA tayi min dayday har fiye da abinda nake son Allah ya azirta Ni dashi , inasonki SAHLA.

        Cikin daddadan muryarta mai sanyi da natsuwa mai saka shauƙi cikin zuciyar mai saurare tace: ya AHLAN SOYAYYA a zuciya take sai ka saba da mutum tausayi ya shigo sannan soyayya ke wanzuwa har mutum ya samu damar shiga zuciyarka ,bayan shaquwa da girmama juna SOYAYYA ta shiga zuciya ta ba way Zama tayi ba a’a kai tsaye ta dauke zuciyar tawa duka ta tafi dashi , soyayyar ka gare Ni tamkar itace cikon rayuwata ,a sannu nake jin idan babu kai ko ban mutu ba zan shiga mawuyacin hali ,zan ji kamar duka duniyar nan Ni kadai na rage cikin ta ,ina maka son so ya AHLAN,fatana a kullum Allah ya kai mu gaci Allah ya nuna mana ranan da zai kasance mu mallaki juna alkawarin farin ciki zalla ya AHLAN.

        Murmushi saurayin yayi mai kayatarwa dimple din gefen bakin shi ya lotsa hakoransa farare tas suka bayyana sannan yace ,alkawarin farin ciki zalla SAHLA Allah ya nuna mana wannan ranan ,Allah ya baki lpya ,ameen Ya AHLAN, SAHLA ta amsa itama tana murmushin.

        Dayday lokacin suka ji horn kofar gidan da sauri AHLAN ya miƙe yayi gate din,turawa yayi aka danno hancin mota cikin gidan , dukkan su gurin motar sukayi inda tayi parcking karamin yaron nan ne yaje da gudu yana faɗin Abba, da sauri dattijon da ya fito a motar mai madaidaitan shekaruun da bazasu haura 50 ba ya daga yaron yana cilla shi sama yana faɗin my boy ,shi kuma yaron dariya yake yana faɗin Abba sannu da dawowa cikin tsamin bakinsa,yawwa boy Barka 

Advertisements

     Rusunawa AHLAN da SAHLA sukayi duka suka kwashi gaisuwa sannan wadda aka kira Abba yace ya aikin day Ibrahim?

      Lpya kalau Abba yanzu ma daga can nake na yi wo nan insha Allah zan karisa gida yanzun nan ,cewar AHLAN yana sunkuyar  da kai ,masha Allah to Allah ya kaika lpya ka gaida yaya Ahmad da mutan gidan zasuji insha Allah Abba ,saida safe ,yawwa ya AHLAN sai da safe SAHLA da yaron suka amsa 

       Mashin dinshi dake kafe a can gefe cikin gidan ya dauka ya kai gate ya bude sannan ta fita da ita ya tura gate din ya wuce, 

     Juyowa mutumin yayi ya kalli matashiyar budurwar yace ya jikin kanwata? Lpya da sauki sosai Abba yanzu banijin komai ma ,masha Allah Allah ya kara afuwa kanwa ta ameen Ya Allah Abba

      Juyawa suka yi gaba daya suka wuce cikin gidan , parlou ne mai madaidaicin girma saiday ya kawatu da kaya na zamani kama daga kujeru zuwa labulaye zuwa abin bango kai harda tv ,can bangaren daga gefen hagu kuma dining area ne mai dauke da kujeru 6 ,sai hannun dama kuma kofar dakuna ne guda 4 a jere can na karshen shine yafi yin cikin parloun SOSAI,komai cikin parloun a gyare yake tsaf komai a kintse , dayday shigowar su wata mata mai kimanin shekaru 37 ta fito daga daya daga cikin dakunan fuskarta dauke da murmushi tana faɗin Barka da dawowa Abban Khalil ,yawwa Barka day umman SAHLA,dariya duka sukayi , sannan SAHLA tace ay na ɗauka cewa zakayi Barka day umman Khalil kaima,Ni na isa bazance haka ba kanwata yawwa abbanmu , cikin zolaya matar tace AHLAN din ya tafi ne? SAHLA bata ce komai ba sai Abba ne yace ya wuce dama daga aiki yake saida yazo kullum day yana hanya , ko gajiya baya yi cewar umma, ya za’ayi ya gaji Ni lokacin da nake zuwa zance ina gajiya ne? Dariya duka sukayi SAHLA tace Abba barin zo sai muci abinci ta fada tana bin hanyar da matar ta fito ,daki na daban ta shiga kai tsaye bayi ta wuce fitsari tayi tare da yin alwalar mangariba sannan ta fito saida tayi sallar magrib sannan ta fito parlou dayday lokacin kuma Abba da Khalil suka dawo daga Masallaci,duk a dining suka haɗu cin abinci bayan sunci suka taɓa dan hira sannan SAHLA ta wuce dakinsu tare da Khalil.

        Abban SAHLA biki na ta karatowa a lissafi na saura kwanaki 19 kaga sati biyu ba kwana 2 kenan ya kamata daga siyayya zuwa gyaran jikin SAHLA an fara zuwa yanzu ,tunda naga jikin nata da kwari sosia yanzu ta samu sauki aynun ko ya kake gani?

       Nima na fuskanci hakan abinda ya kamata kenan ,Ni wallahi yarinyar ma tausayi take bani ,jinyar ta lokaci daya ,wallahi kuwa Allah day ya rabamu da mummunar kaddara , ameen Hajiya ameen ,yanzu ki bari zuwa gobe sai mu karisa maganar kudi da sauransu ,karku tanbayi yaro wani kudin gyaran jiki ,dan yana fama da kansa shima aure ba wasa bane ,yaya Ahmad way saiday komai AHLAN yayi wa kansa ta haka ne zaisan zafin nema ,Ni yaron har tausayi yake ban yayi nan yayi nan ga shi shi kadai ne namiji abun sai a hankali. Wallahi kuwa Allah day ya dafa mana baki daya cewar umma tana miƙewa zuwa dakinta shima mikewar yayi ya wuce dakin dake kusa da wadda ta shiga da alama shine nashi 

🔛 washegari

Kiran sallar farko na asuba cikin kunnen SAHLA cikin sauri ta miƙe ta shige toilet,alwala tayi tayi nafilfili sannan tayi sallar asuba ,ta kwararo addu’a Allah ya nuna mata ranan aurenta lpya ,ya basu zaman lpya daga jarsehytayi addu’ar Allah ya bata lpya ya tsayar mata da wannan ciwon nata haka ,tana idarwa ta wuce kicin,abinci kawai ta ɗora da alama ta riga ta gama sabawa jikinta ya gama sabawa da aykin ko ɗar babu balle jin wani gajiya ,ɗumamen tuwon jiya da dare da tayi na shinkafa shi tayi ta dumama shi da miyar , sannan ta siya dankalin turawa da koyi sai ruwan zafi ,karfe 6 da rabi ta gama komai ta jera dining,dakinsu ta wuce sannan ta tashi Khalil dake shan bacci cikin tsokana take cewa zan saka Abba ya fara zuwa dakai asuba kawai yaron nan ka girmi salla a gida,tashi kayi wanka kayi salla break fast is ready maza muna JIRANKA a parlou,cikin tura baki yace to yaya SAHLA , parlou ta koma ta zauna dayday lokacin umma ta fito ita ma tayi wankan ta sanye da atampa sai kamshi take basu rufa minti 30 ba saiga Abba sai ga Khalil nanfa suka dunguma dining,

     Bayan sun gama cin abinci ne kuma Abba yayi shirin fita tare suke fita da Khalil ya sauke shi skull ya wuce kasuwa,umma ta fita raka su ita kuma SAHLA ta kama aykin gida.

     Abba yayi wa umma transfer kudi yadda ta gaya masa zasu isa ya wuce tana masa fatan alkairi

      Tana dawowa ta kira kawarta Hajiya zainab da ƙanwar ta anty Jamila aka tafiya kasuwa ta gaya masu tym, SAHLA saida ta gama komai ta share komai t goge komai sannan ta shiga wanka ,tana Fitowa kuma sai ga kawar mamarta da ƙanwar ta sunzo nan suka fara shirin tafiya kasuwa domin siyayyar biki.

Yadda labarin zaizo da sabon salo haka rubutun ,littafin bana gaggawa bane niday inason ku bini sannu kan hankali har mu kai ga gaci, wacce batada hakuri bazata iya karanta min littafi ba shine gaskiyar magana 

      MRS ABDULL ce ✍️

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MUGUN DUHU 21-22

Advertisement   ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫ _STORY BY MRS ABDULL_✍️ *_____________________________________*  *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻*  “`{United we stand and succeed;Our ambition…

MUGUN DUHU 15-16

Advertisement  ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫ 🅿️1️⃣5️⃣_1️⃣6️⃣ ”Daura hannu kawai AHLAN yayi akai yana faɗin sun kashe ta,sun kashe min mata.…

MUGUN DUHU 23-24

Advertisement  ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫ _STORY BY MRS ABDULL_✍️ https://chat.whatsapp.com/DvzXXgIpkS09c6HC71vxvf Advertisements *_____________________________________*  *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻*  “`{United we stand and succeed;Our…