MUGUN DUHU 11-12

Advertisement

 ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

*_________________________________*

Advertisements

Da sunan Allah mai rahma mai jin ƙai,tsira aminci daukaka su kara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam.

1️⃣1️⃣_1️⃣2️⃣

Da asuba,kiran farko cikin kunnuwan ta , kasancewar bata salla kwanciya kawai ta gyara,bacci sosai take cikin kwanciyar hankali.

     Sai da ya dawo daga masallaci sannan ya shigo,ya sameta tana ta sharan bacci dan haka ya fice,karfe 6 ya shiga kicin bai iya dafa komai ba a rayuwar sa , dan haka ya zuba ruwa kawai a tukunya ya saka Lipton bayan ya tafasa ya juye a flask ,sannan ya fasa ƙwansa hudu ya soya su daƙyar ya juye cikin plate,kai tsaye dakin ta ya wuce,dayday lokacin ta gama shirya wa har tayi wanka,

      ”murmushi yayi sannan yace amarya kinsha kamshi,dariya kawai tayi sannan ta zauna bakin gado tace ya AHLAN ina kwana?

Advertisements

      ”lpya ƙalau alhamdulillah,dafatan kin tashi lpya?

      Lpya kalau alhamdulillah nima nake,akan bedside drawer ya ɗaura flaks din da plate din kwai, sannan ya fita madara ya dauko da milo da kofi ya dawo, karɓa tayi ta haɗa ,yana ta murmushi,mika masa kofin tayi alamar karɓa.

    ”cikin shagwaba yace ba nawa bane naki ne kuma shi kadai nayi,

     ”dariya tayi sannan ta saka cup din Bakin ta sugar kam cikin shayin ba dama ,ko a jikin ta tunda dama son sugar gareta,shanye shi tayi tas yana kallon ta,ƙwan ta janyo kamshin sa dadi ya mata sosai ,shima tas ta cinye ita fa babu wani kunya a cin abinci dan bata wasa da cikinta, saida ta gama cinye koyin kuma zuciyar ta ta fara tashi ,ta alakan ta hakan da al’ada da take yi don yana sa ta  hakan sosia. jakar da aka kawo ta dashi ta jawo cwinggum ne da wasu kalan minti a ciki bata ma san su ba , ANTY Jamila ne tace mata kawai ta ringa shan mintin duk dare ,daya ta ciro ta Sa a bakin ta,duk abinda take AHLAN yana kallon ta sonta na kara ninkuwa cikin ransa ,sai da ta shanye mintin sannan tashin zuciyar ya lafa , 

     ”ya AHLAN bari naje kicin ”

     haka kawai ta faɗi ta kama hanyar kofa ,binta yayi da kallon cikin shaukin soyayya,shima tashin yayi ya kwashe kwanukan ya bita kicin din dasu 

       A tsaye ya same ta ,ta dauko doya zata yanka ,don shi zata soya masa kasancewar breakfast ,har zata saka wuka a kai ya shigo kicin din

     Hannunta ya rike sannan yace

    ” ammi tace karkiyi girki drivern bana na kawo abinci”.

     To ya AHLAN ta fada tana daukar doyar ta mayar ta wajen zamanta.

     Parlou suka dawo, basu fi 30mint ba sai ga drivern ya iso ,shi da kanshi ya fita ta karbi flaks din abinci da kofin da ya kawo ya dawo cikin gidan

     Karɓar shi tayi suka kai kicin,plate ta dauko ta saka masa a ciki soyayyen dankalin turawa ne da plantain chips sai kunun tsamiya, 

     Parloun ta kawo masa,shima fa sosia din ya ci abincin dan baya wasa da cikin sa ko kadan. 

       Bayan sun gama breakfast duka,sai kuma suka kama ayki ,shi ya taya ta komai suka gama,a hankali yake jan ta a jiki,tunda suke da ita idan band ta na yarinya bay taɓa kama hannun ta ko ya taɓa jikin ta ba sai yau da aka kawota gidan shi ,a wasa haka sai ya dafa ta ko ya dan kama mata hannu,tun abin yana dan bata tsoro tana jin shi wani iri har kuma taji ta saba babu komai

      Haka suka wuni har dare sunyi waya da umma da Khalil duka anty Jamila ma ta kirata.

      Yau ma haka da zatayi bacci da dare dakinsa ya tafi ta kwanta a nata dakin.

         Haka kwanaki ke ja yau kwanan SAHLA uku cikin gidan AHLAN,babu wani abin da ya shiga tsakaninsu,sai day babu ruwansa idan suna ayki ko wani abu makamancin haka ,zai rike mata hannu zasuyi wasan su na guje guje ,idan sabo ne kam yanzu SAHLA tayi matukar sabo da AHLAN sabo mai tsanani ,ta sakan masa jiki over soyayya kawai suke sha son ransu.

    ”Yau tayi wanka da la’asar dan haka tanayin wanka ta maida sallan la’asar lokacin ta bai fita ba .

     Dakinta ya shigo ya iske ta tana salla,hakan ya masa daɗi dan yadda yake daukan abin wasa ba haka ya same shi ba ,ya dauka zai iya sati tare da SAHLA bai ji komai kanta ko ya neme ta da wani abu ba,amma yanzu ji yake inaaa abin ya masa nauyi ,dan zamansu na kwanaki 3 nan duk ya matsu zuciyar sa ta ƙagara da kawai ya kasance tare da matarsa.

     Addu’a suka shafa tare sannan tace

   ” ya AHLAN yanzu nake shirin fitowa Kuma sai ga ka”.

     Wallahi kuwa bebe naje salla ne da na dawo kuma baki parlou nace barin same ki a nan ashe baƙon ya tafi?yayi maganar yana murmushi.

     Hada kai da gwiwa tayi tana dariya duk kunya ta kama ta ga kuma wata bebe da yace mata ita wallahi kullum SAHLA yake kiranta ko KANWATA amma yau way bebe.

    ”me na kunyar to niday kinga tashi kizo parlou ina jiranki”.

     Cikin ladabi tace to miƙewa yayi ya fita ta bishi ds kallo kullum kamar kara ninka mata son AHLAN ake cikin ranta , SOYAYYR shi kullum girma take karawa cikin ziciyarta.

     sallayar ta ninke sannan ta bi bayansa,baya parloun dan haka ta bishi dskinshi,yana can kuwa ,kaya ne ya ciro su ya baza kan gadon duk a goge suke a ninke amma ya ƙaƙalo wannan gyaran. 

    Taya shi tayi suka gyara tsaf sannan suka dawo parlou dayday an kira magrib dan haka ya wuce masallaci,itama sallan tayi sannan ta jira isha,

     Bayan idar da Sallah sai gashi ya shigo da ledoji kala kala fruit ne da Nana m da sauransu ,

     Duk kicin ta kai ta zuba masu duka abubuwan da ya kawo ta fito masu dashi parlou komawa tayi ta dauko masu minerals a fridge ta dawo ,kafin ta zauna yace fresh milk Zaki dauko kinji?

    ”yau kuma ya AHLAN naga nine mai son fresh milk kai baka so? 

    ”eh ki dauko shi ya faɗa yana dariya,

   To ya AHLAN komawa tayi ta dauko fresh milk din ta dawo.

     Sosai suka cika tumbin su dam sannan ta tattara wajen.

      Kamar yadda suka saba dakinshi ya wuce itama haka ,wanka tayi ta gyare jikinta kamar kullum ta saba dama,sannan ta kwanta.

     Sosai bacci yayi awon gaba da ita. 

   Karfe 1 da rabi AHLAN ya mike daga aykin da yake cikin lapton yayi wo dakin SAHLA,bacci take sha sosai,kasancewar ta ba mai nauyin bacci ba yana shigowa taji amma kamar a mafarki taji karan kofa dan haka ta gyara kwanciyar ta kawai a hankali ya matso, kan gadon ya zauna ya cire takalman kafansa sannan ta hau kan gadon gaba daya jikinsa ya jawo ta duka ,witsi witsi take inda ta bude idonta tar tana shirin kwaɗa ihu ya haɗe bakinsu ,babu shiri ta kame bakinta ta shiga taitayinta,tabbas ta gane AHLAN ne amma ne haka? Me wannan yake mata mai wuyar dauka ,kanta ya mata nauyi,sosia AHLAN yake kokarin cusawa SAHLA sakonnin da ƙwaƙwalwar kanta take shirin gaza dauka,yayi kuwa nasara dan sai da ya tabbatar jikinta ya mata lakwas sannan ya fara shirin aykata abinda ya kawo shi….kofar naja na fice kasancewar ba kyau bankaɗa sirrin mutane🤣😌😎

     A parlou nayi wa kaina masauki tun ina jin hayaniya hayaniya har bacci mai dadin ya kwashe Ni,karfe 5 na asuba na farka ,naso na makara dan haka cikin azama na danna kai na cikin dakin.

      Yana zaune kan sallaya tana kan gado bacci take amma mai dauke da wahala ,dan nunfashi kawai take sauke wa da kuma ajiyar zuciya.

     Kallon ta yake da murmushi kan fuskar shi ya rasa me zai ce ya rasa wani kyauta zai bata shi wanne irin abu zai mata ya biyata kwatankwacin irin farinciki da ta saka shi, annashuwar bata da misali bazata kwatan tu ba ,batada iyaka , baki bazai iya furta wa ba,kwata kwata ƙwaƙwalwar shi ta gaza daukan wannan farincikin dole sai ya bayya na ya furta kuma ya nuna a fili kowa yasan halin da yake ciki.

     Motsi tayi nan da nan ya mike ya tafi zuwa gareta.

     ”da kuka ta farka.

Yadda labarin zaizo da sabon salo haka rubutun ,littafin bana gaggawa bane niday inason ku bini sannu kan hankali har mu kai ga gaci, wacce batada hakuri bazata iya karanta min littafi ba shine gaskiyar magana 

      MRS ABDULL ce ✍️

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MUGUN DUHU 23-24

Advertisement  ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫ _STORY BY MRS ABDULL_✍️ https://chat.whatsapp.com/DvzXXgIpkS09c6HC71vxvf Advertisements *_____________________________________*  *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻*  “`{United we stand and succeed;Our…

MUGUN DUHU 15-16

Advertisement  ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫ 🅿️1️⃣5️⃣_1️⃣6️⃣ ”Daura hannu kawai AHLAN yayi akai yana faɗin sun kashe ta,sun kashe min mata.…

MUGUN DUHU 21-22

Advertisement   ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫ _STORY BY MRS ABDULL_✍️ *_____________________________________*  *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻*  “`{United we stand and succeed;Our ambition…