MUGUN DUHU 15-16

Advertisement

 ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫

🅿️1️⃣5️⃣_1️⃣6️⃣

”Daura hannu kawai AHLAN yayi akai yana faɗin sun kashe ta,sun kashe min mata.

    Da sauri Dr din ya fara kiran nurse nurse babu shiri AHLAN ya ciccibi SAHLA ya daura ta kan gadon dake office din,nan nurse suka shigo mutum biyu.

Nan da nan ya fara bata taimakon gaggawa suma tayi numfashin nan ya dauke dif babu wani motsi,sosia AHLAN ke kai komo cikin office din cikin tashin hankali ya rasa da wanne irin abu zai kwatanta wannan matsalar ciki kuma SAHLA? Kuma ga halin da take ciki innalillahi wainna ilaihirraji’un, lahaulawalaquwwata illabilla, subhanallah, allahumma ajirni fi musibaty wa’aklifni kairan minha,shi yake ta maimaitawa kawai a bakinsa.

     Can likita ya gama komai yayi mata wata allura suka daura mata ruwa sannan ya dubi AHLAN yace

   ”ka kwantar  hankalinka insha Allah zata samu sauki suma ne tayi da kuma firgici,amma abinda nake son tanbayar ka shine,ba matarka bace miyasa duka wannan tsoron haka cikin ne baku so ko kuma ba ta hanyar aure aka same  shi ba? Likita yayi tanbayr yana kallon AHLAN.

   ”Dr way da gaske kake akwai cikinnan? Yayi tanbayr idon shi na zubo da kwalla.

Advertisements

     Sosai ma kuwa akwia ciki watan shi biyu da sati Uku zo nan ma ka gani 

    Matsowa yayi gaban gadon SAHLA da yake dauke da na’urorin binkicen ciki wato (scanning) ya bude cikin ta da ya dan ɗago shi ba tumbi ba kuma bazaka ce ciki ne ba kasancewar ta ba mai jiki ba ,wani mai ya shafa sannan ya dora abin gwajin ,sosia idon AHLAN yake kan computer,bai fahimci komai ba bai san ko dan tashin hankalin da yake ciki bane oho likita ne yace ” matso nan na gani.

   Matsowa AHLAN yayi duk ya fita hayyacinsa.” kallon computer yayi ya ga day an rubata week sai baby a baby b a wajen week din yaga an saka 11 kenan hakan yana nufin cikin SAHLA sati 11 kenan ya tanbayi zuciyar sa?

   Kuka kawai ya kubce masa domin zuciyarsa nada rauni tana da matukar rauni ya gagara daukan wannan lamarin.

Kujera yaja a gaban teburin likita kawai ya kifa kansa yana shaƙar kuka mai ban tausayi,

   Zama likitan yayi sannan yace calmdown broh komai yayi zafi maganin shi Allah kayi hakuri Allah ya maka sassuci

    Ɗago kai yayi sannan yace”dr ko duka duniya zasu taru kaina bazan yarda SAHLA tayi zina ba bazan taba yarda ba kuma nasan ba’a taba yin ciki sai an sadu da namiji da mace shin ya za’a yi tayi ciki a karon haka,zuciya ta ta gagara nuna min baƙin SAHLA har yanzu gaya min take bazata aykata hakan ba shin meke faruwa kwata kwata jiya na fara sanin SAHLA ƴa mace auren mu sati guda kenan ,kuma tana al’ada shi matan dake ciki suna al’ada ne suna yi likita?

” akwia sosia ma amma sunfi karanci gaskiya wata har ta fara har tayi ciki na bata sani ba sai day a jikinta taji sauyi amma bawai ta gane da al’ada ba sai dau wajen zuwa ko ya rage lokaci ko ya kara ko kuma mace tayi sau biyu a wata duk yana yiwuwa.

    Innalillahi wainna ilaihirraji’un, hasbunallah wani’imal wakilll

   Allah karka dora mana abinda bazamu iya ba cewar AHLAN yana miƙewa ganin SAHLA na motsa Kafa.

     Bakin gadon yaje ya rankwafa yana gyara mata kwanciyar yana furta sannu SAHLA Allah ya baki lpya kinji sannu.

    Kuka ta fashe dashi sannan ta fara fadin 

Advertisements

    ”wallahi wallahi wallahi yaya AHLAN ban san cikin nan ya akayi ba bansan wannan cikin ba,wallahi ban taɓa sanin wani namiji ba bayan kai jiya wallahi dan Allah ya AHLAN kace su kara dubawa ba Ni bace mai cikin nan wallahi ,ta fada tana fashewa da kuka mai tsuma zuciyar mai saurare.

    ”na sani SAHLA amma ya akayi kika same shi? Tabbas kina da ciki na gani da idanuna na ganshi SAHLA na waye ya akayi?

    Wallahi ya AHLAN ban sani ba wallahi na shiga uku innalillahi wainna ilaihirraji’un.

     Kuka take haiƙan zuciyar ta na buga wa , wannan wanne irin abun kunya ne abin takaici abin assha ,bata yi iskanci tayi ciki ba tun tana gidan Mahaifin ta ba sai da tayi aure sati guda kenan ace tana da ciki kuma wata uku 😭

     ”matsowa likita yayi sannan yace kaɗan matsa dan Allah.

     Matsawa AHLAN yayi nurse 2 suka kama SAHLA suka wuce da ita toilet.

     Wajen 5 minutes sai gasu sun fito sun barta ciki likitan ne yace ”sadiya ki fita plazan dake titi sayo mana doguwar riga ,shiday AHLAN na zaune ya hada kai da gwiwa kawai.

”ok Dr ciro kudi yayi ya bata 6k yace ta sayo masu rigan sabida yaga AHLAN baya ma cikin hankalin sa da za’a yi mashi bayanin ya kawo kaya wadancan sun lallace da jini.

     Babu dadewa sai gata nan ta dawo kuwa ,ki bata cewar likitan.

    Toilet din ta kwankwasa SAHLA dake zaune kan toilet seat tana rizgar kuka ,kukan da bata san ranan tsayarwa sa ba way ita ce da ciki to wa yayi mata ciki ya akayi tayi ciki? Ta ina iyayen ta da sauran danginsu zasu dauki wannan lamarin me zata gaya masu da wanne yare zata musu bayani su fuskanta? 

     Tasowa tayi a hankali dan marar ta ciwo take mata sosia sosai.

    Bude kofar tayi a hankali ta karbi rigar sannan ta koma ciki.wanke jikin ta kawai tayi da fuskar ta ta saka abayar ta fito kanta a kasa.har yanzu hawaye yaki tsayawa a idonta ta gagara tsaida shi domin batada kwarin gwiwar yin hakan.

    Zama tayi kan kujerar dazu su Kuma nurses din suka fita ,likita ne ya kalle su sannan yace.

  ”da farko day Ina mai baku hakuri na wannan iftila’i abunku yazo da abin mamaki wannan shine ake kira da “`MUGUN DUHU“`. ciki a jikin mace bata san daga inda yake ba kuma auren ta sati guda ,Allah ya baku hakuri shawara ta anan shine.

    Na farko binkice ,dole kuyi binkice sosia akan hakan maganar ɓoye maganar nan bata taso ba iyaye su shiga ciki su sani , ke kuma kiyi tunanin ki tsaf ki saka a ma’aunin hankali ki gwada babu wnada zaki fadi ma baki san yadda aka yi kika yi ciki ba ya yarda ya aminta ,idan kinsan wannan “`MUGUN DUHUN“`  ta ina ya fito maza kiyi sauri ki haskaka wa mutane su fita cikin sa , ciki a jikin ki baki san na waye ba akwai ayar tanbaya kanki akwia lauje cikin naɗi dole sai kin san dashi.

     Fashe wa kawai da kuka SAHLA tayi tana faɗin wallahi wallahi wallahil’azim ya AHLAN Dr wallahi bansan dashi ba bansan cikin waye ba bansan ya akayi ba.

     Allah ya kyauta cewar likita sannan yace zaku iya tafiya Allah ya kara sauki Allah ya bayya na gaskiya 

     Kamar wadanda aka watsa wa ruwan zafi suka fita a office din tare da yiwa likita gdya.

     Dare yayi wajen tara da rabi na dare daƙyar AHLAN ya gyara parcking sannan SAHLA ta hau ya jasu.

    Kai tsaye gidan su ya nufa da ita.

”mummunan tashin hankali ne ya ziyarce ta salati ta fara da kuka tana faɗin na shiga uku innalillahi wainna ilaihirraji’un, lahaula walaquwwata illabilla, subhanallah”

    Tayi matukar bashi tausayi yaji tausayin ta aynun amma bazay yiwu ya koma gidan sa da ita ba sabida zama ma yanzu a tsakaninsu ya haramta domin ciki gareta ba’a san kuma ba waye ba kuma dole iyayen su susan Wannan kwamacalan da ya tunkaro su.

     Dayday lokacin yayi horn a kofar gate din gidan

 Mai gadi ne ya leƙo ganin sune yasa ya wangale masu gate din yana daga wa AHLAN hannu domin suna wasa da dariya sosia

   ”murmushin da yafi kuma ciwo AHLAN yayi masa kawai ya Danna kansa cikin gidan.parcking yayi sannan suka shiga cikin gidan yana gaba tana binsa a baya ,tana ta goge hawaye da katon hijab dinta da ya fita tsayi.

     Parloun suka shiga duk mutan gidan suna parloun Abba Khalil da umma.

     Gaba dayansu miƙewa suka yi ganin halin da suke ciki ,cikin tashin hankali Abban SAHLA yace Ibrahim lpya kuwa? 

 Daga aure kwana hudu sai mu ganku a gida cikin wani irin hali? 

    Da gudu SAHLA ta rungume mahaifiyar ta ta saki kuka mai tada hankali ,da gudu Khalil ya wuce daki sabida horon da akayi masa KENAN da anyi baƙi ya basu waje.( Umma ta iya tarbiyya bata da wasa akan tarbiyyar yara tana da matukar kokari ,batada fada amma idan akan tarbiyya ne zata iya dukan yaro ma dan day ya saita hanya,shiyasa ya’yan ta suka fita daban a dangi khakilyda SAHLA akwai tarbiyya da sanin ya kamata da girmama na gaba)

     ”ke lpya kuwa cewar umma? Tana daga SAHLA daga jikinta.

    Zama Abba yayi sannan yace 

”ibrahim meke faruwa ne? 

    Aljihunsa ya sa hannu ya ciro takadda da likita ya basu ya mikawa Abba ,zuciyar Abba na bugawa ya karba domin zuciyar sa ta fara raya masa abu marar dadi wani “`MUGUN DUHU“` yake hangowa ya tunkaro su.

    Bude takardar yayi abinda ya gani ne ya saka zuciyar sa bugawa da karfi zillo tayi kamar zata faɗo ta bakinshi.

     Menene wannan Ibrahim? Cewar Abban SAHLA 

” cikin shasshekar kuka AHLAN yace Abba SAHLA ne batada lpya muka wuce asibiti aka mata tambayoyi akayi mata gwaji tashin farko likita yace min ciki ne da ita wata 3 ba kwanaki,na kasa gaskata shi dan haka na dauke tana wuce da ita wani asibitin suma tambayoyin akayi da gwaji suma tashin farko aka ce ciki gareta wata uku ba sati biyu ,a nan ta sume Abba likitan a take ya mata scanning a gaba na na ga komai ciki ne da SAHLA wata 2 da sati Uku Abba , AHLAN ya karisa maganar hawayen da ya taru kasan idonsa na gangarowa

*MRS ABDULL ce* ✍️

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MUGUN DUHU 23-24

Advertisement  ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫ _STORY BY MRS ABDULL_✍️ https://chat.whatsapp.com/DvzXXgIpkS09c6HC71vxvf Advertisements *_____________________________________*  *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻*  “`{United we stand and succeed;Our…

MUGUN DUHU 21-22

Advertisement   ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫ _STORY BY MRS ABDULL_✍️ *_____________________________________*  *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻*  “`{United we stand and succeed;Our ambition…