MUGUN DUHU 6-10

Advertisement

 

⚫“`MUGUN DUHU“`⚫

Da sunan Allah mai rahma mai jin ƙai,tsira aminci daukaka su kara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam.

🅿️6️⃣_1️⃣0️⃣

Advertisements

Tsaf suka shirya sannan suka fita harabar gidan,ita day Jamila ƙanwar umma bata ko kalli haj zainab ba ta rasa dalili ta rasa miyasa Allah ya dora mata tsanar wannan baiwar kullum kuwa ta ganta tsanar ta karuwa yake cikin ranta,a motar Hajiya zainab zasu tafi Kasancewar daga mai gadin gidan har drivern kowa ya tafi hutun salla da ake basu suke tafiya kowanne shekara,daƙyar Jamila ta shiga motar Hajiya zainab suka wuce kasuwa ,tunsafe suke can sai lokacin tasowar Khalil daga makaranta sannan suka kamo hanya kaya kam sun siye shi over motar kasuwa ce ta jido kayan zuwa gida,duk wani abin bukata da SAHLA zata nuna za’a cire kudi a siye shi babu wani damuwa babu tashin hankali, saida suka gama komai tsaf sannan suka taho ,dayday lokacin kuma Abba suka dawo da Khalil ya dauko shi daga makaranta ,Hajiya zainab taba shiga gidan ba kawai ta wuce Kasancewar tace tana da ayki a ofis da yawa,sai Jamila ne suka karisa cikin gidan da umma da SAHLA,cikin ɓacin rai umma tace.

      ”jamila banison rashin ta ido banison rashin kirki me Hajiya zainab tayi maki Ina lura dake inday zaku haɗu da Hajiya zainab sai kin nuna wani abu a fuska kuma baki mata magana balle ki gaishe ta ,shi haka ake yi ne mai tayi maki? 

        ”Nifa Yaya babu abinda tayi min kawai day haka nan nake jin haushin ta na rasa dalili wallahi Amma Ni kaina banga aybun taba tana da kirki babu laifi ,amma Ni wallahi zuciya ta taƙi aminta da ita haka kawai idan na ganta nake jin faduwar gaba kuma duk sanda na haɗu da ita na kwanta bacci sai na ga tana binki da gudu cikin bacci shiyasa kawai na tsane ta. Jamila ta karisa maganar tana kauda kai

      ”wannan ba hujja bace Jamila ba gaira babu dalili bazaki tsani mata ba haka kawai Ni baniso kuma ina addu’a ba abinda zai same Ni sai abinda Allah ya ƙaddara min kinji ko? Banison irin wannan abun.

      Umma ta karisa maganar tana kallon Jamila

        Eh naji yaya insha Allah ,yawwa to maza zo a shiga kicin rana tayi ga Abban su SAHLA ma ya dawo babu abinci.

      To yaya ,itaday SAHLA tana gefe bata ce komai ba dan tasan tsakanin mahaifiyar ta da Hajiya zainab akwai amana mai karfi bazama ta taɓa cutar da ita ba aljanun ANTY Jamila ne basu gaya mata gaskiya.

      To haka day suka gama girki zuwa la’asar kowa ya gama cin nasa sai kuma masu kaya suka iso daki guda kusa da na drivern gidan aka bude masu anan suka jibge shi tas kayan kicin ne kamar za’a bude kanti sayayya kam sun sashi 

       Da yamma kuma sai ga AHLAN yazo dan duk zancen sa da yamma ne idan ya taso ayki ko idan zai wuce yake zuwa sabida iyayensu duka basu yarda da wannan hiran daren ba.

   Sosai suka sha hiransu tare da musanyar kalamai masu tsaya wa arai na soyayya sannan sukayi sallama ya wuce ayki sabida yau aykin dare gareshi 

       Biki nat karatowa yau saura sati sosia ake gyara SAHLA dayday gwargwado duk da har yau ba dadin jikinta take ji ba amma tana karfin hali day,kawayenta 4 kwata kwata suma biyu sunyi aure NASREEN da basma NASREEN ƴaƴanta 2 twins sai basma yarta daya mace sai Hafsah da feenah sune kawayenta hafsa bata yi aure ba feenah ma ,ana ta shirye shirye babu kama hannun yaro ,saura kwanaki 6 biki babu wata bidi’a da za’a yi sai sakun lalle da za’ayi wa amarya da danginta da kawanyen ta lalle sai walima ana washegarin daura aure sai daukan amarya shikenan.

    Yau ake sakun kawayen amarya sunsha kyau sosia suma , SAHLA sai kyalli take masha Allah,ana gobe daurin aure kuwa aka yi walima an Barka kudi kasancewar babu wata bidi’a,kayan makulashe kam an cishi over.

Advertisements

     Washe gari da safe karfe 11 aka daura auren AHLAN Ahmad tinka da amaryar sa SAHLA Musa tinka,daurin auren da ya tara yan kasuwa masu ji da Naira da kudi ,nan akayi addu’ar fatan alkairi da zaman lpya da zuri’a dayyiba.

       Tunda aka daura auren SAHLA ke kuka ta rasa mai yake mata daɗi cikin duniyar ta ji take ina ma da ba’a daura auren nan ba sai yanzu take nadama ,yanzu barin umma da Abba da Khalil zatayi kenan? Innalillahi wainna ilaihirraji’un kuka kawai take ta sha,Hajiya zainab ke ta rarrashin ta daƙyar tayi wanka ta shirya ana ta bata baki kanta yana ta sarawa sabida ciwo.

      Karfe hudu yan daukan amarya suka zo kofar gida abokan AHLAN ne wasu da mota wasu da mashin gasunan day iri iri harda yan wajen aykinsu mata da maza duka suka zo,aka kai SAHLA wajen Abba

      ”yace bashida shakku bashida tantama akan SAHLA kai tsaye zai bada sheda akanta ,ba abinda zaice da ita saiday ta kara jin tsoron Allah.

     ”haka umman tama kuka ta ringa yi kawai har aka wuce da ita cikin mota, kai tsaye gidansu AHLAN aka wuce da ita inda aka ware daki guda wanda za’a sauke su sai an gama biki a wuce da ita gidanta.

      Wunin biki yayi dadi komai ya tafi yanda ake so babu wata matsala ,su Hajiya zainab dasu anty Jamila su suka gyara SAHLA tsaf zuwa gidan AHLAN 

    Kai tsaye aka wuce da ita madaidaicin gidan ta da ya kawatu da sabbin kaya da kayan more rayuwa gate dinsu dan dayday da komai masha Allah,har cikin bedrom dinta suka sauke ta ,saida suka gyara mata komai suka kimtsa komai suka saka turaruka sannan suka yi mata Sallama.

      Kuka kam SAHLA ta sashi babu adadi ,tun tana mai sauti har ta komai shassheka ,karfe 8 AHLAN ya shigo dauke da kazar sa da ya kasance al’ada ga kowane ango a daren farkon shi da amarya yakan shigo da ita ,fuskarshi dauke da madaukakin murmushi ya zauna gefenta cikin sanyin murya yace..

     ”Amincin Allah su tabbata a gareki yake ma’abociyar kunya kamewa da tarbiyya”

     Cikin shasshekar kuka tace

       ”tare da kai ya AHLAN”

     Ta bashi dariya aynun amma sai ya dake yace 

       ” Barka da zuwa duniya ta,”sunkuyar da kai tayi hawaye na ziraro mata 

     ”Kinga nifa wannan kukan ya isheni haka  tashi maza ki shiga toilet kiyi alwala kizo nan.

      Babu musu ta mike domin ita a al’adar ta babu musu ko Khalil ne yace anty SAHLA abu kaza idan yasan ba daidai bane ma bata masa musu kawai sai tace to balle kuma babban mutum haka kamar AHLAN a wajenta.

       Toilet ta shige mayafin jikin ta ta cire ta zauna kan toilet seat din tufafin jikin ta fara cirewa domin tana son kimtsawa kafin tayi salla kuma batason ruwa ya taɓa mata kaya.

      Bayan ta gama cirewa y rage saura pant Shima sauke shi tayi tana son cirewa sai taga jini jiki, she’s shock domin a lissafin ta nan gaba tana da 10days kafin jini yazo ,amma hakan ba wani matsala bane wajenta ,abin ma yayi mata matukar dadi da ya kasance haka din ,dan tana jin labarin first night sama sama dan ko yau saida ANTY zainab tayi mata gargadi sosai.

       Da yake ita ba mai yawan zuban jini bace sai kawai tayi wankan ta ta gyara jikinta tsaf ta mai da kayan ta ,kwandon da aka ijiye mata pants dasu bra ta jawo ta saka pant kawia babu pad ta fito.

      Yana zaune ya canzo kaya daga gare to jallabiya,ganin yanayin ta yasa yace..                             

     lpya kuwa? Sunkuyar da kai tayi bata ce komai ba.

     Daga kafada yayi alamar shikenan.

      ”idan kinyi alwalar zo muyi sallan to”

     Ɗago kai tayi a hankali ta zuba masa manyan idanun ta sannan ta girgiza kai.

    Babu wani kwana kwana AHLAN ya gane inda zancen ya dosa dan haka yayi murmushi yace to maza zo ki ci abinci ki kwanta 

      Hakan yayi mata daɗi sosai itafa duk abinda aka faɗa angwaye nayi na zumuɗi bata ganshi wajen AHLAN ba wallahi 

      ”shi kuma a nashi bangaren AHLAN dama yayi alƙawarin ko SAHLA bata period yau bazai mata komai ba sabida baiga amfanin hakan ba ya fi so sai sun saba sosai sannan sai ta saba da gidanshi sosia sannan ya ƙaddamar mata,to kuma sai ga period hakan yayi masa daɗi aynun”

      Kazan ta zauna ya bude mata ita ya saka mata cikin plate ta ci sosia sannan tasha faro.

     Sallama yayi mata sannan ya wuce wani dakin da ya kasance nashi a cikin gidan

     Sosia SAHLA taji dadin hakan a rannan ta kara tabbatar wa kanta cewa AHLAN dan Aljanna ne ,maza irinsa kadan ne wallahi,Da wani ne da bazasu kwan kalau ba sai ya nuna ɓacin ransa a kanta , kayan ta ta cire ta saka wasu sannan tabi lpyar gado.✍️

Yadda labarin zaizo da sabon salo haka rubutun ,littafin bana gaggawa bane niday inason ku bini sannu kan hankali har mu kai ga gaci, wacce batada hakuri bazata iya karanta min littafi ba shine gaskiyar magana 

      MRS ABDULL ce ✍️

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MUGUN DUHU 15-16

Advertisement  ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫ 🅿️1️⃣5️⃣_1️⃣6️⃣ ”Daura hannu kawai AHLAN yayi akai yana faɗin sun kashe ta,sun kashe min mata.…

MUGUN DUHU 21-22

Advertisement   ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫ _STORY BY MRS ABDULL_✍️ *_____________________________________*  *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻*  “`{United we stand and succeed;Our ambition…

MUGUN DUHU 23-24

Advertisement  ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫ _STORY BY MRS ABDULL_✍️ https://chat.whatsapp.com/DvzXXgIpkS09c6HC71vxvf Advertisements *_____________________________________*  *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻*  “`{United we stand and succeed;Our…