SAI A LAHIRA 1

Advertisement

 *K* ayataccen wuri ne irin holl din Nan me girma Wanda ake gabatar da party irin na bikin Aure. Wurin ya kayatu da kyakkyawan tsari kasancewar angon babban kicima ne. Hasken fitulu ya haske tarwai  ga kwalliyar

docration me burgewa inda wakar nasara ke tashi tare da wani haske me sauya launi da Dole ya burgeka Yana ta canza launi.


Wata katuwar mota me numfashi ta faka inda jerin gwanon motocin  suka faka Wanda kallo daya zakayi musu ka Gane sunci sun tada Kai  lallai bikin na manyan gwaskaye ne. Kyauren motar ya bude inda amarya da ango suka fito Atare tamkar dai antsara yadda fitowar tasu zata kasance .

Amarya cikin shigar doguwar Riga irin ta bikin aure kalar fara tana Kuma lullube da mayafi me kama da net kafarta sanye da dogon takalmi kalar silver hade da Yar jakar shi silver colour fuskarta da make up me kayatarwa sai dai fuskarta amurtuke Babu annuri ko kadan inda angon ke ta washe Baki alamar Yana murna da wannan Rana akasin amarya. Ya lura da Amaryar Bata saki ranta ba akan abinda ya fada Mata.

Don haka ya rungumo ta Yana Kara Bata hakuri Amma dai Bata saki fuskar ta ba.

Suka Isa holl din  yayinda abokan ango suka taho tarba inda wani bakin ciki ya Kara turnuke amarya  saboda ganin Babu wata kawa Tata awurin wannan party Wanda aka Hana  kawayen ta da Yan uwanta zuwa . Bata taba Jin irin wannan party ba na Hana Mata zuwa bayan amarya kawai. Ta dubi abokan angon Wanda suka zamo kamar angon nata wato masu abin hannun su kowane yanayin shi ya nuna yayi hannun Riga da talauci sai dai abinda ya Bata tsoro shine kowanen su ido jajir tamkar sun Sha wani abun maybe . Kuma Wai sunyi anko na jar shadda da bakar hula Dara. Ta lura da wani Jan zobe me girma da tagani wurin Bashir angon nata Wanda Bata taba kawowa ranta wani Abu akan zoben ba sai yanzu da taga abokan Bashir din kowane Yana sanye da shi a yatsan shi na tsakiya.

Kaf wurin party maza ne sai wata mace guda Daya da ta taho ta tarbeta cikin murna da farin ciki.ta kamo hannunta har Kan high table ta zaunar da ita.

Advertisements

Tabi matar da kallo inda taga matar tayi Mata Kama da Yar duniya farace tas irin farin Nan na bilicin fuskarta da tsagen kalangu bakin ta dauke da hakorin makka guda biyu sama da kasa. Ta sake maida hankalin ta Kan abokan angon Wanda suka zubo Mata idanu da jajayen idanunsu inda taji wani matsiyacin faduwar gaba me tsanani ya risketa ta sunkuyar da kanta tanajin wani Abu me kama da nadama na son sauko Mata. DJ ya soma sauya kida yayin da mc ke ta babatu Amma Sam amarya zainab Bata fahimta saboda zuciyar ta ta SHIGA binciken shin waye angon nata Bashir? Kuma suwaye abokan shi masu jajayen idanu da jar shaddar su da Jan zobe?

Bata gama hada lissafin 4+4 ya Bata 8 ba taji an dafata akafada ta dago da kanta inda ta ga matar Nan me kama da Yar duniya tana Mata murmushi. “Kiyi fa hakuri amarya da abubuwan da Zaki gani kin San ko yaushe ilimin yawa yake karawa mu namu salon ya Sha bambam da sauran. So kar kiyi mamaki komai Kika gani kiyi hakuri kar ki nemi ba asi ko sanin Yaya abin yake? Kafin tasamu abin cewa don tambayoyi ne fal bakin ta inda taga matar Nan ta fito da wasu kwalabe Wanda bakin kwalbar bai Bata damar ganin abinda ke ciki ba.


Ta zubawa kwalbar ido zuciyar ta na fada Mata wannan kwalbar giyace! Matar ta kware ledar da aka nade bakin kwalbar da  bincine marfin wani shegen tsami ya dira Kan hancin zainab wacce ta tabbatar da zaton ta na giyace a yau idon ta ke gani abinda Bata taba gani ba ko acikin mafarki sai gashi Wai giya abikin AUREN ta to meye hadin Bashir da abokanshi da giya?

Kafin ta samo amsar ta soma jiyo tsamin na sauka a kafatanin jikinta 


Ta dago afusace tana kallon matar dake jifar ta da murmushi ta Kuma dubu Bashir da son ganin irin matakin da zai dauka sai taga Babu alamar zai yi wani Abu sai ma murmushi da ta karanto a fuskar shi 

Zuciya ta zo Mata wuya ta Mike da son sharawa matar Mari akan yafa Mata ruwan giya  Amma sai Bashir da ya lura da abinda take nufi yayi maza ya damke hannunta ya na kyar Mata idanu.

Haka matar Nan ta juye musu kwalbar giya biyu ajikkunan su kafin ta dire kwalaben 

Inda bakin ciki ya saka Amarya kuka saboda tunda uwar ta ta haifeta ba ta taba ganin giya da idonta ba bare ace ta taba ta sai yau da ake Mata wanka da ruwan giya giyar da ta tabbatar babu abinda Hime da malam suka tsana Arayuwa irin ta.

Kanta na kasa tana shakar kuka kukan takaici da bakin ciki inda take Jun nadamar auren Bashir.

Sai Kuma ta Kuma ganin wani kayan bakin ciki inda aka soma dire musu abin tabawa Wanda ba abun tabawar ba hatta ita kanta kyamar kanta take.

Advertisements

Duk yadda matar Nan ke rarrashin ta da Bata hakuri akan taci wani Abu Amma Bata ko dubeta ba bare taci saboda bakin cikin dake damfare a ranta.

Abokan ango da mc me magana da salon ban dariya sai taji duk haushin kowa take ji mussamman Bashir da ya biye Mata ko waye shi Wanda a yanzu ita da kanta ta gama fassara ko waye shi abinda take Jin ba zata dauka ba.


Abokan ango suka taso suna bawa ango hannu suna gaisawa inda itama Daya daga cikin su ya Miko Mata hannu Wai suyi musabihar inda taji wani takaici na naushin zuciyar ta inda taso fashewa dama ta so ta amayar da abinda ke ranta akan wankan giyar da akayi Mata….Lallai abin da kulle zuciya da tunani🤔


Muje zuwa gidan iko

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like