SAI A LAHIRA 2

Advertisement

 *🎀SAI A LAHIRA🎀*

   

        *🅿️age 2

*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*

*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu’ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*

Advertisements

_ga hanyar da za’a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_

_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_

 *_____________________________________*

 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

Advertisements

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*I* donta taf da hawaye take kallon Bashir ganin gardin abokin shi ya Miko Mata hannu Wai su gaisa abinda Bata Saba gani ba. Ta zuba mishi ido da son ganin abinda zaiyi don asanin ta dai duk namiji me kishi ba zai taba Bari hakan ta faru ga matar da yake neman AUREN ta bare wadda aure ya zarga igiyoyin Sunnah. Sai taga yayi Mata alamar ta Mika hannun nata su gaisa da abokin nashi.

Hawayen ta ya silalo akan dakalin fuskarta cikin Rawar murya tace

“Bashir dama ka shirya wulakanta Ni ne akan tsinannun abokan ka da kace min sun fiye maka kowa da komai a DUNIYA?

“Dama don ka tozar tani ne yasa ka Hana kawaye na da Yan uwana zuwa don kar suje su bada labarin muguwar dabi ar ka da abokan ka? “Nayi nadamar sanin ka a Rayuwa ta nayi nadamar AUREN ka fiye da yawan shekaruna. Ayau na tabbatar da Ubangiji baya barin hakkin wani akan wani Kuma shi din me gaggawar Sakayya ne. “Na rantse maka da Allah Bashir na fasa AUREN ka idan har Kai kadai kayi saura a DUNIYA sai dai in mutu babu mijin aure…..

Ya tareta Yana me ruko hannuwan ta.

“Cool down my beby yi hakuri me ya Bata Miki Rai ne haka?

“Idan Kika fasa aure na in mutu kenan kike so?  Indon na Hana Yan uwanki da kawayen ki zuwa Nan ne ai nace Zan shirya Miki wani kayataccen party agida na Wanda Zaki gayyato Yan uwanki da kawayen ki ko? Nan abokai na NE suka shirya Mana shi Kuma bama bukatar kowa sai amarya tuni na fada Miki Ina girmama abokai na duk abinda suke so zanyi musu shi koda Ni din bana ra ayin shi Raina ma zai iya Zama fansa agare su indai sun bukaci hakan So kar ki damu da duk abinda zasuyi Miki da yardata da amincewa ta hakan ta tabbata…….

Tayi saurin katse shi

“Kaji matsalar farko da zamu fara samu da Kai tunda har ka bawa abokai damar da Ubangiji bai Basu ba.”Ina tsoron yadda abokan ka zasu saka abinda ba zaka Musa masu ba akaina tunda har kake fada min ranka ma fansa ne garesu ina ga Ni da Zan kasance karkashin ikon ka? Zamana da Kai da su ba zaiyuwu ba wallahi don Kai da su nayi muku wata irin tsana wanda ban taba jin irin ta ba saboda giyar da nagani a muhallan ku da Jan idon ku ya Kara jefani cikin shakku karshe Kuma yadda ka Hana Yan uwana da kawaye na zuwa don kar su Dora ayar tambaya akan ku……

Wayar ta dake ta Kara tun dazu ta isheta da Kara ta jawo pos din ta fito da wayar inda ta iske kiran da ta rasa missed call kusan arba in da biyar na Yan uwan ta da kawayen ta.

Ta daga Kiran humaira dake shigowa

“Sannu Yar duniya shine Kika shanya mu kikayi tafiyar ki ke Yar Dadi miji ana ta Kira kin share mutane ai da Baki gayyato mu ba tunda kunyi nufin watsa mu……

“Kiyi hakuri humaira wallahi ban San haka ba nima……

“A a na bar Miki hakurin don ni har na zo gida ma a tashi taro lafiya ta tsinke wayar ta. Ranta ya Kuma baci  inda matar Nan ta Kuma zuwa tana Bata hakuri akan haka suke nasu Sha anin . Abokan ango suka soma yiwa amarya kyautar girma inda kowanen su ya bawa amarya kyautar rafar dollars su goma Sha biyu haka suka dire Mata Rafa goma Sha biyu  sai dai ta karanto wani babban alamari a fuskokin su da zuciyar su al amarin da ta tabbatar ba ALHERI bane

DJ da mc suka soma hada Kayan su saboda dare ya soma har Sha biyu da kusan rabi inda abokan ango suka soma ficewa matar Nan Yar duniya wadda taji sunanta Wai karisha ta dubi abokan da cewa tana Nan zuwa su saurareta bayan ta tambaye su hotel din da suka sauka suka fada Mata barewa suka sauka.

Karisha ta tattare Mata kudin da aka Tara Mata ta zuba Mata cikin wata Yar jaka ta Mika Mata ta dubeta ta dubi kudin

“Allah ya tsareni kar bar kudin mutanen can da Raina da hankalinki na Bai kwanta dasu.

Ta Mike tana Shirin barin wurin inda karisha ta kyalkyale da dariya

“Kai bash amaryar mu fa ta Shaka dayawa Ina ga Kuma Taji aikin dake jiranta? “Aikin da Kuma ya zamar Mata Dole tunda taci abin hannunmu 

Suka biyo bayan zainab wadda ta tsaya abakin motar Bashir tana jiran yazo ya mayar da ita gida

Suka karaso shida karisha wadda zainab ke musu kallon Yan bariki wadanda Babu Allah a zuciyar su da ayukansu

“Zee kirawo gida ki fada musu mun wuce dake abawa Yan rakiya amarya hakuri tunda Kinga dare yayi….

Ta juyo arude

“Banji abinda kace ba Bashir? Da wane bakin Zan sanar da Hime hakan?

“Ba zaka Jamin abin kunya da abin fada ba kamaida Ni gidanmu gobe Yan uwa suyi min rakiya Amma ba Zan bika Ni kadai tsinken ragi ba . Karisha tace 

“Bash Bari in kaita gida goben sai muje mu dauketa.

Karisha ta bude motar ta inda Bashir yace suje shi zai wuce gida.

Wani kololon bakin ciki ya turnuke zainab bisa Dole ta SHIGA motar karisha suka dauki hanya sai dai maimakon taga sunbi hanyar gidan su sai taga akasin hakan 

Inda taga karishi ta dauki titin by pas inda ta dubi karisha a kule 

“Kin fa baro hanyar haj sai mun koma baya.

Karisha tayi murmushi

“Ina sane amarya Sha guda zamu biya Nan ne in bada sako.

Bata Ankara ba taga motar taci burki bakin kofar SHIGA hotel din barewa

Abinda ya haddasa Mata sarawar Kai me tafe da bugun zuciya………

To Bari mugani ko wace irin waina za a Toya

Ta wake CE ko ta masara

Muje zuwa gidan iko

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like