SAI A LAHIRA 7

Advertisement

 *🎀SAI A LAHIRA🎀*

              *NA*

*HADIZA BARA’U GIDAN IKO*

               *🅿️age7*

*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*

Advertisements

*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu’ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*

_ga hanyar da za’a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_

_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_

 *_____________________________________*

Advertisements

 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

Gaisuwa ga masoya gidan iko masu min fatan alkhairi Ubangiji yabiya da ALJANNAH

Haj Saliha Allah yakara lafiya ya yaye duk wani ciwo da damuwa

………Idonta akan mutumin dake doso su inda tun a kallon farko taji tsoro me tsanani ya kamata don suffar mutumin Babu alamar Yana da imani Amma duk da haka sai ta samu kanta da wurga mishi harara ya karaso Yana rusunawa alamar girmama wa garesu inda Bashir ya daga mishi hannu kawai ya riko hannun zainab zuwa cikin gidan Wanda duk kyamar da take Jin tana yiwa gidan Bai hanata bin gidan da kallo ba kasancewar duk yadda Za a bada labarin tsaruwa da haduwa irin ta gidan Dole a rage mishi armashi wurin bada Labari don Sai an rage daulolin dake shimfide agidan

Haka sukayi ta kurdawa sako da lungu har suka iso wasu kofofin inda suka SHIGA har dai suka dangano da wani katon falo me dauke da setin kujeru har kala uku bangayen falon lullube da yadin labule me kalar pink da fari ga kafet  kalar ash da Baki  Wanda har kafa ke nutsuwa wata dattijuwa sai goge katuwar TV plasma take inda taji shigowar su ta taho da sauri tana rusunawa tana musu sannu da zuwa

Ya amsa da cewa abawa zainab abinci tana Kuma bukatar hutawa shi Kuma zaije Asibiti a yi mishi treatment din goshin sa 

Ya juya da sauri  ya bar wurin inda dattijuwar me amsa sunan iya ta cika aikinta na hadawa zainab abinci da abin Sha ta dire agabanta.

Tabi tsohuwar da kallon Rashin yarda don ayanzu ita Kam a firgice da gidan bashir da duk ahalin da kaddara ta nuna Mata agidan Bashir

Sai taji hawaye na bin gurbin idon ta lallai Allah me gaggawar Sakayya ne Kuma baya barin hakkin wani akan wani nadama Kam tayi ta sama da yawan shekarunta abinda Bata sani ba kaddarar ta agidan Bashir Bata ma fara ba.

Tsohuwa iya taci gaba da aikinta ba tare da ta kulata ba dama tagama aikin ta sai tayi sauri ta fice daga falon tabata sararin yin tunanin da take son yi

Sai dai duk abinda zata tunana Babu guda daya da ta hango mafita acikin shi sai ta koma neman hanyar da zata kubuce zuwa gida saidai Nan ma Bata hango mafita ba domin kuwa ita kanta Bata San awace duniyar take ba domin ko ita din kifin rijiya CE katsina kurum ta taba zuwa bayan haka Bata taba barin garin kaduna ba sai fa Zaria

Tsayin kwana uku Amma Bata Kuma saka bashir idon ta ba sai dai iya dake ta jigilar kawo Mata abinci da dauke kwanuka Kuma har yanzu iya kar ta da ita ina kwana daga haka ko harafin A baya sake hadasu inda zainab taso raba damuwar ta da wannan tsohuwa sai dai Babu fuska har ta share sati guda batare da ango bashir ya waiwayo ta ba ita Kuma Bata nemi sanin halin da yake ciki ba inda ta tuno da wayar ta acikin jaka ta zarota inda taga caja ta jona caji 

Ta kunna wayar da son ta Kira goggo ta sanar da ita halin da take ciki sai ga Kiran kanwarta siyama

Gabanta ya Fadi ganin Kiran siyamar kamar ba zata dauka ba sai kuma ta daga

“Kai anty baby duk amarcin ne yasa aka kashe waya muna ta Kira akashe? Taja tsaki kar ki Raina min hankali kinji ko? Ta fada da tsawa siyamar ta tareta

“Allah ya Baki hakuri anty baby Ni ban San me nayi Miki ba kike min wannan abin dama goggoce tace in Kira Mata ke gashi zakuyi magana……

Ta mikawa goggon waya

“Baby Kuna lafiya? Ta bude Baki zata rattabo Mata halin da tasamu kanta akan bashir da abokan shi da Kuma kudirin da take dashi na gudowa sai kawai taji bakin ta ya rufe inda goggon ta Dora da fadan dake ta cinta arai

“Yanzu abinda kikayi kin kyauta kenan baby ace kin kwashi tsayi kinbi miji Babu rakiya? Dama tuni na kula da yadda kike ta Rawar jiki da bare bare kamar Zaki Kai kanki gidan Bashir din Nan to ki sani Babu komai acikin zaman aure sai hakuri idan kuwa Kika Faye nuna wannan Rawar jikin to namiji ne Ina Nan Zaki bani Labari..

Kamar tace na nawa kuwa goggo? Sai dai bakinta ya kasa tona asirin bashir Wanda hakan ya Bata mamaki matuka da haka goggon ta gama yi Mata nasihar da Bata tsaya anyi mata ita ba har suka gama wayar ta ajiye ta koma gefe tana rera kuka kukan da na sani banyi ba kukan tausayin Kai da hango wace Rana CE zata samu kubuta daga wannan Bala in da ta kutsa kanta da karfin tsiya 

Sai da tayi sati biyu agidan kafin bashir ya dawo inda suka shigo shi da karisha wadda akayiwa dinki a Baki

Ta kofar tagar dakin da tsohuwa iya ta nuna Mata take hango shigowar su karishar da Bashir har ma da abokanshi masu DUNIYA kamar yadda taji sunan abakin karisha mamaki ya kamata ganin abokan Bashir sun shigo gidan don hakan sai ta murzawa kofarta key tayi kwanciyar ta tana saka da warwara har bacci ya dauketa inda akarshe dai abinda ya faru ahotel ya kuma sake faruwa tamkar cikin mafarki ta Rika Jin abin kafin ta farka ta samu abin da gaske Kuma still daya daga abokan mijin nata ne tare da ita amakwancinta Wanda mijin AUREN ta ne kurum ya kasance a gurbin sai ga abokin mijin tare da ita……

Anya lamarin nan na lafiya ne❓❓❓

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like