UNCLE DATTI 39-40

Advertisement

   3️⃣9️⃣—4️⃣0️⃣

Shima sai kallon ta yake yi cikin wani irin yanayi marar misaltuwa…..har yanzu yana jin tsananin sonta na ratsa shi…..Ya Fu’ad dama kaine Amintacce ka b’oye min baka fad’a min ba? Me yasa ka raba ni da gida ka jefa ni cikin kunci……..me nayi maka da na deserving haka daga gare ka………., ashe dama

kiyayyar da kake nuna min har ta kaiiiii ka raba ni da gida ka kawo ni ka ajiye ni inda babu dangina………? Shin baka tausayina ne…….baka tausayin baby d’in da ke cikina ne………? Hawaye taji ya sauko mata tayi saurin bada baya tana gogewa.

        ” Kalaman ta sun hurting d’in shi sosai bai so ace ta fad’a hakan ba, even though da baya shiri da ita amma doesn’t mean cewa har abada zai tabbata da kiyayyan ta.

         Ba tare da ya furta komai ba ya kamo hannun ta tana turjewa har suka shige d’akin……….cakkkkk ta ja ta tsaya tana kallon mutanen da ke wurin bata tab’a tsammanin cewa zata sake had’u da su a wannan lokacin ba hasali ma ta cire tsammani da ganin su………,dai-dai nan suka juyo a tare, lokaci guda mamaki rikicewa da tsantsar farin ciki ya dabaibaiye su”Na…..nah, Aina ta fad’a da mugun k’arfi………dam dam dammmm zuciyar Datti ya buga……, yana had’a ido da ita a take jikin shi ya d’auki rawa…….hak’oran shi suka fara kad’awa kattt katttt kattttt.

        “Ina kika shiga Nana muka neme ki muka rasa, me yasa zaki tafi ki bar mu, sai ga hawaye na bin fuskar Aina, ita kanta ta san cewa hawayen nan na farin ciki ne domin tayi missing k’anwar ta.

          Tsohuwa tsabar farin cikin ganin y’ar jikallen ta taje da gudu zata rungume ta taji abu ya tok’are mata ciki da ja da baya dan ta ga menene wannan abun……., ido biyu tayi da zungureren cikin Nana sai ta taji gaban ta ya mugun fad’uwa ta d’ago hijabin ta doka salati da k’arfi………..ciki  Nana?Wa ya d’irka miki ciki,?

       Sai murnar su ta koma ciki” duk suka rud’e suma hankalin su ya tashi sosai. Wuta ne ya d’auke ma Ummi sai take jin har ranta da ma bata dawo ba akan ta dawo musu da muguwar tsaraba wanda basa fata samun shi…….Nana ta jawo musu abun kunya ta b’ata ma family d’in su suna…….duk irin tarbiyar da ta basu amma sai da ta ware k’afa ma wani k’ato ya d’ura mata ciki?     Nana dai sai hawaye take yi ta kasa tsaida su…….baba Karami da ya jik’e da uban gumi shataffffff ya wanka mata wani lafiyayyen mari……….ji kake tassssssss zai k’ara mata wani Fu’ad ya shiga tsakanin su sai gashi marin ta same shi a fuskar shi………

         Baba me yasa baza ka yi bincike ba kayi saurin yanke hukunci……..walahi kunfi kowa laifi domin ku kuka jefa ta cikin wannan hatsariiii……….., dama ranar da nake jiye muku kenan sai gata ta zo.

Advertisements

          A hasale baba Karami yace” Fu’ad matsa ka bani wuri idan ba haka ba zan had’a da kaiiiiiiii, 

         “Baba sai dai ka dake bazan tab’a bari ka dake nana ba, ko ku ki ko ku so cikin da kuke gani na Datti ne ina da evidence” phone d’in shi ya ciro da zumar zai nuna musu recording d’in maganar da suka Usman sai ta tarar babu”.   

       Dafe kai yayi cike da mamakin yanda aka yi aka san da recording d’in aka goge……., zufa ne ya sauko mishi duk yanda aka yi ya so ka tonawa Datti asiri amma evidence ya goge”.   

         Datti daga kwance yana kallon su cikin wani irin hali ya sauk’e wahalallen ajiyar zuciya.

        Ashe ranar suna sane da plan nashi cikin daren bayan yayi barci ya sa Usman ya bincike wayan ya goge recording d’in Fu’ad d’in bai sani ba.

       Kuka mai tsananin k’arfin gaske Nana ta fashe da shi har da majina” Ya Fu’ad dan Allah ka barshi ya dake ni……ka barshi ya kashe ni nace……nafi k’aunar mutuwa ta dauke ni a wannan lokacin fiye da rayuwar da nake ciki…….

        “Baba ko zaku kashe ni ba zan tab’a fad’a muku ko cikin wanene ba tun farko baku yarda da ni ba sai yanzu da aikin gama ya riga ya gama?

        Idanuwan ta ne ya sauka akan Datti tun farkon shigowan ta yake ruwan hawaye, yana jan jiki da kyar k’okarin mik’ewa yake yi dan ya gane ma idanuwan cewa ita ne…….., hawaye takaici taji ya zo mata tace” Uncle ka jefa rayuwa ta cikin garari……abunda kake kunyar a sani ba zan tona  ba kamar yanda ka binne kai zaka tona….. Duk da irin uban rad’ad’in zafin da yake ji a dick d’in shi amma hakan ya rarrafo ya zo har gaban ta ya fashe da kuka yana rokon ta yafiya” don Allah ki yafe min Nana na san na cutar da ke dalilin hakan ya sa na had’u da jarrabawa kala-kala…….na cutar da ke na jefa ki cikin wani hali marar misaltuwa…….ba zan tab’a yafe ma kaina ba……..baba karami kuce ta yafe min laifin da nayi mata…….

        Buge hannun shi tayi tace” ko mutuwa zaka yi ba zan yafe maka ba wallahi sai dai ka mutu….., 

         “Ganin yanda Datti yake ta kuka wiwi kamar ranshi zai fita yasa Alhaji yace” Ku fidda mu cikin rud’ani ku fad’a mana halin da ake ciki…….Nana ta zo mana da ciki wanda bamu san ko na wanene ba kai kuma Datti da bakin ka kake cewa kayi laifi laifi kana da masaniya akan cikin da take da shi ne?

          Girgiza mishi kai yayi a’a Alhaji ban san komai ba……., sannan kuma ba zan fad’a muku irin laifin da nayi mata ba………..

         Murmushin mugun Fu’ad yayi ya hard’e hannun shi ko a haka burin shi ya cika……., Datti kenan duk yanda ka so ka b’oye komai ba zaka iya ba……… Na san kana son Nana sai dai kunya ta hana ka fad’an gaskiya…….Baba ina son ku min alfarma idan ta haihu ku aura min ita…….

Advertisements

        Mugun kishi ne ya turnuke Datti har yaji haushin maganar Fu’ad……., ya fito mishi ta hanyar da baiyi zato ba…….., Sautin kukan shine ya cika ko ina muryar shi na cracking yace” wallahi baka isa ba…..nine na rik’e baby kuma ni zan aura mata mijin da zata aura……..baby ba taka bace…….., 

             “A’a Datti tunda yaji ya gani ya amince zai aure ai ya rufa mana asiri……., dan haka Fu’ad mun baka Nana halak malak.

        Saurin dafe kai Datti yayi yana mai jin rad’ad’i a ranshi…..sammm ba zai jure rashin baby a rayuwar shi ba duk da ya san ko da za’a bashi ita a halin yanzu ba tab’uka komai zai iya yi ba……..

         Haka suka fita suka bashi guri ya had’e kai da gwiwa zuciyar shi ya turirin k’una……baby d’in shi ba shi zata aura ba…….ko dai su baba basu fahimci irin son da yake mata bane zasu ba ma wani? Shi da ma mutuwa yayi da yafi mishi.

         Rana zafi inuwa k’una haka rayuwar ta zamar mishi……taimakon shi d’aya Usman na iya bakin k’orarin shi yana bashi cikakkiyar kulawa a matsayin shi na kwarren doctor!!!, tunda Nana ta dawo gidan sai abun ya k’ara tsanani fiye da na da da baya ganin ta……., bata yarda ta shigo d’akin idan ta shigo banda gatsa mishi maganganu babu abunda take yi, ko kad’an bata tausayin shi……….,kuma taki fad’a ma su Alhaji komai ta kafa hujjan hakan ne da cewa komai ta fad’a musu basa yarda shi yasa tayi shiru. Datti dai azaba tayi azaba wata rana yana kwance daga shi sai Usman ya a d’aki yace ya san yanda zaiyi ya kawo mishi Nana a lokacin dick d’in shi ya fara warkewa amma sai dai yana damun shi da kaikayi sosai.

        Idoooo Usman ya waro yana mamakin jarabar Datti” me kake tunanin zata maka idan ta zo? Idan kana tunanin cewa zata baka abunda kake so ne ka sani fa da da yanzu ba d’aya bane, yanzu ta san ciwon kanta ba irin da da kake jujjuya ta bane”.

           “Kuka ya fashe da shi” don Allah Usman ka neman min ita……anya kuwa kasan abunda yake damuna kuwa…….., 

         “Auren ta kayi da sai duk sanda kake so ka same ta zaka samu….ko ka manta an ba ma Fu’ad ita wallahi kayi ma kanka kiyamul laili ka hak’ura da bakin kuddurin ka……….ni shawata ta d’aya da kai ka fad’a ma su Alhaji abunda ya faru tsananin ka da Nana idan ba haka ba kai ka jiyo…….

          Fuuuuu ya fice daga d’akin ya basu wuri         

           B’angare  Nana kuwa haka taci gaba da zama tana rainon cikin ta da kuma baby d’in ta…….har ranta bata son maganar auren amma ganin yanda su baba suka dage mata ya sa ta hak’ura ta mik’a wa sarautar Allah ido…….,

         Tsohuwa kammm duk abun duniya ya dame ta kamar tafi kowa jin zafin abunda ya faru….a duk sanda ta d’aga ido ta ga rusheshen cikin Nana ta rushe da kuka tace” hege d’an hegiya…….,shikenan duk ta ishe kowa da kuka Nana tana jin ta ta tab’e a ranta tace” auuu ashe kina da bakin kuka”.

         Ummi ma samm basa son cikin nan, gashi Nana ta ishe su da jarabar ci sai narkar abinci take yi tana ciyar musu da shege a gida……, idan aka yi abinci ita take cinye kusan rabin shi……., suna kallo abu yafi k’arfin su ba daman hanawa.

       Da Nana ta fahimci irin kiyayyar da suke nuna ma cikin sai ta bare dukan su sun hallara a parlourn kafin nan ta fito tana tura cikin da kyar bata sako hijabi balle ya boye cikin haka zata zauna tana matse fuska irin na masu ciki idan suka ganta sai takaici ya d’ebe su musamman Ummi da Umma sai kaga sun fara wastewa da d’add’aya sun bar parlourn su barta daga ita sai tsohuwa………

        Ita kam kasa hakuri take ta yab’a ma Nana magana” anyi asara an jawo ma mutane abun kunya……., Nana ta sakar mata hararar tare da maida mata da martani” kuma dole a karb’a a matsayin tattab’a kunne ba”, tsohuwa ta rushe da kuka tana sharar kwalla tana shine ma Nana a ranta……..ta bud’e k’afa wani k’ato ya d’ora mata ciki gashi sun an barsu da rainon shege.

          Wata rana Nana na zaune a parlour ita da tsohuwa suna gatsa ma juna magana Fu’ad ya shigo da saurin shi” hearty zo muje ki rak’a ni wani waje………..

        “Cikin ta ta turo waje tana yamutsa fuska” Allah ya Fu’ad na gaji cikin nan na wahalar dani da yawa.

         Tsohuwa na kallon ta ta kasan ido tana so ta tanka mata, sanin kanta idan ta fad’a d’aya Nana zata aika mata da biyu shi yasa tayi shiru tana zumb’uro baki, ji take kamar ta mata wawan shakar da zaisa ta haifo abunda ke cikin ta murd’e wuyan ya mutu kowa ya huta.

        Muryar Fu’ad da taji ne ya dawo da ita cikin hayyacin shi yana cewa  “Kaiiii ban son raki ki taso muje”.

       Nana ta mik’e tayi gaban tsohuwa tace” please tsohuwa ki taimaka min da hijabi a d’akina kin san hawan steer case d’in nan wahala yake bani bana iya d’aga k’afafuwana ciwo suke min.

         Maganar sai ya d’ad’a kular da ita tace” jarrrrr uba a hakan kika iya ware mishi k’afa sama ya dinga danna miki kina karba har kika samo wannan kaddararren abun”. 

         “Kunyar maganar taji sosai ta jiyo tana kallon Fu’ad taga shima ita yake kallo….., taga alamar b’acin rai a tattare da shi dole yaji kishi mana tunda yana son ta…even though ya san cewa da gayya tayi maganar amma bai kamata tayi a gaban shi ba…….., ko d’azu ma da yake mata magana daurewa kawai yake yi.

           Fita yayi da da sauri zuciyar shi nayi mishi zafi……ganin haka tayi d’auki ta d’auko hijabi  ta bi bayan shi da sauri.

        A mota ta tarar da shi yana zaman jiran ta har ta shiga ta zauna baice mata komai ba ya ja motan suka bar gidan.

        Gidan da Amintacce ya kaita shine suka nufa suna isowa yace ta jira shi a parlourn yana zuwa ya haura d’akin tsohuwa suna magana wanda ni kaina ban san me suke tattaunawa ba………..tana parlour tana jiran ya fito taji shiru sai taji tana son ta shiga d’akin da ta yi rayuwa a ciki……..mik’ewa tayi da sauri ta shige ta maida k’ofa ta hau bin ko ina da kallo tana imagining irin life d’in da ta yi a gidan da yanda take rainon cikin ta……., har ranar da Amintacce wato Fu’ad yake zuwar mata a duhu…….., drawer d’inta ta nufa ta d’auko takardun yake rubuto mata notes a ciki ta cusa a cikin jakar ta ta fito parlour da sauri ta koma ta zauna.

        Ba wani dad’ewa tayi da zaman ba sai ga shi ya fito yace ta tashi su tafi, babu musu ta mik’e suka fice daga gidan.

         Gida suka koma ta shige d’akin ta ta cire hijabinta da jakarta ta ajiye a gefe, kana ta maida jakan tana maida numfashi………, takardun ta d’auko ta warware ta fara karantawa kamar haka……..” Na san zaki yi makin dalilin da ganin ki a cikin wannan gida…..kawo ki na sa aka yi domin cimma wani manufa…….dalilin da ya sa ban bayyana a gare ki ba shine a duk lokacin da na ganki kina kina kuka ko nayi ido ke sai naji kin bani tausayi kin k’arya min zuciya har na fara tunanin janye kuddurina a kan ki”.

         Dam dam dammm buguwar zuciyan ta ya yayi dai-dai da lokacin da ta kai k’arshen rubutun ta mayar ta ajiye” maganar ta mugun d’aure mata kai sosai ta kasa fahimtar komai da ke cikin takardar……..d’auko d’aya tayi ta bud’e ta fara karantawa……hotunane na guda uku aka nannad’e a cikin takardar tare da yin rubutu kamar haka” na san baki san dalilin kawo ki cikin gidan nan ba da dalilin da yanda aka yi aka d’auko ba……, shiri ne na musamman domin na cimma burina akan ki”, hotunan ta bud’e taga itace a lokacin da fad’i yashe a kasa a pakin titi, sai taji gaban ta na tsananta bugu…….., sai taji tsoro ya kama ta ta mayar ta ajiye…….,shiri wani irin shiri…..komai nashi managar buri duk abunda zai fad’a sai ya saka k’almar.

        “Takarda na uku ta d’auko ta karanta” hankalin kowa ya tashi a gida kema na san hankalin ki a tashe yake amma ki kwantar da hankalin ki duka biyu nake so nayi na cimma burina.

        Kici gaba da rainon cikin ki da shi zan yi amfani na cimma buri na”, tana gama karanta shi ta mayar ta rufe.

         Takar na hud’u ta bud’e ta fara karantawa” naji yanda kike rayuwa a cikin gidan nan karki damu na kusa na bayyana a gare ki…….., kici gaba da mu’amalar ki har zuwa ranar da burina zai cika………

       Tana bud’e takardar k’arshe taga an rubuto” mission “.

        Menene mission d’in ita dai Fu’ad ya d’aure mata kai sosai, daren ranar ta kwana tana tunanin maganaganun da ta gani a jikin takardar ne, was he gari da abun ya dame ta ta same shi a parlour tace ya gaya mata gaskiyar ma’anar burin da yake son cimmawa a kanta.

            “Cije libs d’in shi yayi yace” barina a kan ki shine na baki tsaro wato na ceto ki a hannun Datti, 

          “Nana na san halin iyayen mu ko da ace kin je musu gida cikin jini a lokacin baza su yarda da ke ba hasali ma tsoro nake jiye miki kar suyi zargin cewa bin maza kike yi, cuz a lokacin kinyi iya k’okarin ki ki fad’a musu gaskiya suka yi kunnen uwar shegu………., musamman Aina da son mijin ta ya gama rufe mata ido shine na sa aboki na Kamal ya d’auko ki ya kawo ki gidan, gida na ne babu wanda ya san mallakina ne, na Samar miki Inna a matsayin wacce zata dinga kula da ke tana d’ebe miki k’ewa.

             ” Mission d’ina a lokacin shine sai kin haihuwa na kawo musu jikan su wata k’ila a lokacin Datti zai yarda da laifin har ya furta da bakin shi, 

        da naga yanda kika d’aga hankalin ki akan lallai sai kin koma gida na shirya plan da Kamal ya kawo ki………nayi mamaki a lokacin na zata zai hakura a lokacin sai na ga ya nuna tauri  kai, shine na fito ta hanyar neman auren ki, na tabbata wannan itace kad’ai ya rage mana, ko muci shi da yak’i ko shi ya cimu da yaki.

        “Hawaye taji ya zo mata ta sa hannu ta share kana ta jefo mishi wata tambaya” yaya aka yi ma san mun tafi asubi a ranar”.

           “Gidan Aunty Aina naje na tambaye ta tace min baki da lafiya Datti ya kai ki asubiti, a lokacin sai naji ban yarda da shi ba zuciyana ya kasa hakuri na sa Kamal ya bi bayan ku kuma ya ki duk abunda ya faru ya fad’a min”.

          Wasu sabbin hawaye ne suka fara rolling a saman fuskar ta ya tsuguna a gaban ta tare da ciro hanky yana goge mata” a da na tsane ki sosai na sha alwashin ganin bayan ki daga baya tausayin halin da kike ciki ya kama ni tun daga lokacin na fara jin son ki na kudurta a raina sai na samo ki daga halin da kike ciki”. Yanzu kin fahimci dalilina na zama Amintacce kin?” Ta gyad’a mishi kai tana kuka ya rungumo ta yana lallashin.

          Lokaci na dad’a tafiya cikin Nana yanzu ya kai kimanin wata tara a lokacin ne ta ta fara nakuda ta haufo yaro namiji santalele lyakkyawa da shi. 

          Ranar sunan shi Fu’ad ne ya rad’a ta mishi suna”Sadeeq”.

         Bacin Fu’ad da Nana babu mai yarda ya d’au yaron ko da sau d’aya har ya fara girma yayi wayo yana rarrafe…..idan ya rarrafo ya zo gun tsohuwa ta buge hannun shi sai ya sa kuka daga baya ya gane ya ma daina  zuwa wurin ta, daga mamar shi sai shi. 

      Haka kawai Allah ya d’ora ma Datti son yaron idan Nana ta ajiye shi a parlour yana wasa ta tafi ta barshi sai ya turo Usman ya d’au ko mishi ya ya rungumo yaron tsammm cikin jikin shi yana kuka….laifin shi ne da yayi sanadiyar kawo shi duniya a kazamtacciyar rayuwa……., yana sane da ko wa baya son shi……ko da yake shi ma da yake uban shi bai bayyana ma duniya ba ya k’arb’e shi a matsayin shi na d’an shi ba balle wasu da ban……, tausayin kanshi da yaron yake ji………da dai bai so zuwan shi duniya ba ashe da rabon shi ma zai ajiye nashi ne yake mu’amala da Nana…….

         So tari idan ya fito parlour yana wasa Datti na jin muryar tsohuwa tana sheganta mishi d’a da marar asali…….hakan na yi mishi zafi sosai a ranshi…..amma babu yanda ya iya.

            Wata rana yana d’aki bayan Usman ya kawo mishi shi ya tafi, Datti na wasa da yaron har yayi barci a gefen kafad’an shi………Nana da taji shiru ta fito tana neman shi ta duba ko ina bata gan shi ba…….gashi babu wanda ya damu da ya san inda yaron ya tafi…….sai taji kuka ya zo mata mai tsananin k’arfin gaske” da ace d’an sunnah ne a yanda aka ji wurin shi shiru da hankalin kowa sai yafi tashi amma da yake ba ta hanyar aure aka same shi ba babu wanda ya damu duk da dai suma sun san ya b’atan.

           Dabara ne ya fad’o mata ta duba d’akin Fu’ad ko zata gan shi…., haka ta haye sama tana sharar hawaye…….ga mamakin ta tana shiga ta ganshi yana sharar barcin shi hankalin shi kwance shima baban nashi barci yake yi……da masifa ta zo zata kwace d’an ta Datti ya bud’e ido ya sauk’e su fessss akan ta.

          ” Ina zaki kai min d’a?

         “Maganar sai ya bata haushi taja tsaki” au dama kana da d’a ne ban sani ba…….,

           “Hannu ta kai zata d’auke Sadeeq yayi saurin rik’o hannun ta yana murzawa a hankali,” babyna i’m sorry na putting d’in ki through much pains kiyi hak’uri rabon yaron ne ya sa”.

        Sai ga hawaye ya fara bin saman fuskar shi” Uncle kenan baka ji kunyar fad’a min maganar ba ina ce tun yana ciki ka sheganta min shi kuma kayi niyar kashe shi at the end kuma kana beginning d’ina bayan har yanzu kana claiming baka san komai ba…….kuka ne ya kwace mata ta hau sheshshek’awa…..Uncle me jikina yayi maka kake so? Me yasa ba zaka amsa laifin cewa Jikina kake so ba………., Uncle ka saka rayuwa ta cikin bakin ciki……. Yaure tsakanina da kai bashi yihuwa ko da ace ba jinin mu d’aya bane da aunty Aina…….., kamar yanda ka d’auki lalurar ka a matsayin k’addara ina so ka d’auki rabuwa da ni a matsayin k’addara, bana son ka Uncle i hate you!!!!!!

            Yanda yaji maganar ta a ranshi kamar saukan mashi ya runtse ido da sauri zuciyan shi na mishi azabar rad’ad’i……k’almar rabuwa da baby shi ya fi komai d’aga mishi hankali a duniya…….gashi k’arfi da yaji so ake a raba shi da ita.

         “Baby da nayi miki laifi amma na tuba ki yafe min…….Sadeeq jinina ne ina k’aunar shi fiye da yanda kike tunani……wallahi baby da kin san irin k’aunar da nake mishi baki isa ki furta hakan ba”.

        Murmushin yake tayi wanda yafi kuka ciwo tace” da kana k’aunar shi tun kafin yazo duniya baka yi yunkurin hana shi zuwa ba…….., kana ganin irin tsanar da ake mishi a cikin gidan nan amma baka yi yunkurin komai ba…….., 

         “Shiru yayi yana tunani shi kan shi ya san abunda ta fad’a gaskiya ne shine wanda ya kamata ya share mishi hawaye tunda shi ya yi silar kawo shi duniya ta gurb’atacciyar hanya…….yana cikin tunanin ne har ta d’auki Sadeeq ta tafi da shi bai sani ba.

         Ba ita ta zame ko ina da shi ba sai d’akin ta da yake b’angaren tsohuwa kusa da na Aina ta dire Sadeeq akan gado time d’in har ya tashi a barci yana kuka………, nono ta bashi ya k’i k’arb’a sai kuka yake yi da ta rasa abunyi sai itama ta rushe da kuka tana mishi wasa tana wak’a ko zai yi shiru…….taho taho d’an yaro nayi maka gata………,kowa baya sonka yace kai shege……,duka hantara da kyamar ka suke yi………tunda uban…..ka ya k’i ka……ba wani mai….maka gata.

         Ta jima sosai tana wakar ta bata sani ba ashe Fu’ad ya shigo ya tsaya yana sauraren ta……haye mai uban d’umi yaji ya sauko mishi sai ya rungumo ta ta baya yana kuka kamar k’aramin yaro…….” Ni zan bashi kulawan da ya rasa a wajen mahaifin shi……ba zan bari ya wulakanta ba dai-dai da rana ba zan bari ya san cewa bani na haife shi ba……….d’an Datti nawa nima.

          “Ya Fu’ad Uncle Datti mugune…..duk da dai na san cewa ba ta hanyar aure muka same shi ba amma na tabbata babu uban da zai kyamace d’an shi……., Sadeeq bai da wani gata a gidan na, kiyayyar shi tayi yawa a gurin kowa na gidan nan………

         “Banda ni da ke Nana idan kowa ya k’i shi mu muna son shiiiiii.

       Kuka suke yi sosai daga su har yaron kamar dama can yana ya san abunda suke fad’a .

        Shirye-shiryen bukin Nana ya kankama a lokacin ne Datti ya d’aga hankalin shi ya fito musu b’aro-baro yace shi zai aure Nana…..mamaki sosai suka yi har suke zargin anya kanshi d’aya? Ya aure ya, ya aure k’anwa.

         Ana gobe d’aurin auren hakalin shi idan yayi dubu ya tashi…..da dai ya ga tabbas  da gaske ake za’a d’aura auren nan ya shiga rokon Nana akan karta amince a d’aura mata aure da Fu’ad shi zai aure ta……tace aure babu fashi da yana son ta ya zalunce ta.

       Da abu ya dame shi ya same su Alhaji yana kuka yace” zan fad’a wallahi baby d’in nan nawa…….don Allah ku karku raba ni da ita…….., daga nan ya kwashe komai ya fad’a musu har da hotel d’in da yake kaita suna hutawa duk ya fad’a musu”

         “Sosai suka firgita da jin abunda ya fad’a” da gaske ne kai ka yi wa Nana ciki”.

       “Eehhh ehhh wallahi nine don Allah ku yafe min”.

          Inalillahi wa ina ilaihiraji’un sai yanzu suke jin k’amshin gaskiya akan abubuwan da Nana take fad’a a baya……garin yaya suka yi sakaci har hakan ya faru? tambayan da kenan suke fad’a a zuciyoyin su.

        Alhaji da ya cika da tarin al’ajabi da b’akin ciki yace” kai da muke tsammanin ba lafiyayye bane yaushe ka samu lafiya ka aikata wannan b’arnar.

            “Lalura ce nima ba da son raina bane na d’aura ma kaina sha’awar ta…….

         Aina taji wani irin mahaukacin kuka ya zo mata ashe dama Datti cin amanar ta yake bata sani ba? Ina alkhawarin da ya d’aukar mata a baya na cewa ba zai cutar da ita ba? Me yasa ita da take mace ta rik’e mishi kanta shi kuma bai rik’e mata kan shi ba yayi taraiya da k’anwar ta”.

        Kallon Nana ta yi wacce tun d’azu take rusar kuka tace” Kaico na da na yarda da yaudarar d’a namiji fiye da rayuwar k’anwata……..duk irin abubuwan da Nanar take fad’a ta toshe kunnuwan ta k’arshe ma tace k’azafi take mishi ashe yaudarar ta yake da kalama ta.

         Ita dai bata ga amfanin zaman aure da shi ba bai amfane ta da komai ba……tana nan tana rik’e mishi kanta amma shi jikin wata yake so ba nata ba……….

          Tsohuwa dai baki ya mutu sai suma take yi tana farfad’owa, duk irin tsanar da take nunawa Sadeeq ashe da uban shegen a gidan, kaiiiii Datti baiyi halin bugun girma ba….. ba a banza abar shi ya dame shi da ciwo ba, a d’au yarinya a bashi k’arshen sakamakon da zai nuna musu kenan.

         Mari baba Babba ya wank’a mishi ya had’a mishi naushi da k’afa kan kace me sai ga jini ya b’alle mishi a baki………

         Ka ban kunya wallahi ban tab’a tsammanin haka daga gare ka ba……..sirrin da kake boyewa kenan da baka nuna ba ka sa muna zaluntar yar uwar ka”.

       “Umma dai kunya had’e da bak’in ciki duk ya ishe ta ace d’an da ta haifa da cikin yayi tarayya da k’anwar matar shi uwa d’aya uba d’aya? Tausayin Nana da Sadeeq ya mugun kama ta musamman Sadeeq da bai san komai ba suka d’auki k’aran tsana suka d’aura mishi.

         Hawaye taji ya soma zubo mata ta matso cike da tarin takaici tace” ba mu da muka baka amanar yarinya ka cutar ba kanka ka cutar…….., tana gama fad’a ta d’auki Sadeeq ta mik’a mishi d’auki d’an ka tafi da shi daga yau mun cire ka acikin family d’innan bama son sake ganin ka.

        “Sai a sannan ne hakan shi ya mugun tashi , don Allah Umma kiyi hakuri ta rainar min shi idan yafi haka wayo sai a dawo min da shi”.

         ” Uban ka nace, ba za ka d’auke shi ba ko har sai ka hasalini nayi maka baki…….da muka baka amanar ta mun had’a da shi ne ina ce kai ka samo shi daga baya……..don haka ka tafi ka bamu wuri.

           “Yaron kamar ya san za’a raba shi da uwar shi ya saki kuka yana mik’a mata hannu ta d’auki shi sai tausayin shi ya kama Nana taje da gudu tana kuka zata k’arb’e shi baba babba ya rik’e ta da sauri……barshi ya tafi da tsiyan shi raino kam kin gama yi mishi sai ya d’aura daga inda kika tsaya.

         Tana ji tana gani haka Datti ya tafi da Sadeeq uba kuka d’a kuka uwa kuka…….da dai sauran masu saurin kuka suma suna taya su.

         Datti na fita Fu’ad yayi saurin bin bayan shi ya sha gaban shi” yaya ka ga takun”,

        Nayi amfani da kwakwalwata na cusa maka k’iyayyar Nana a zuciyan ka………, a halin yanzu tafi kowa tsanar ka……., ka san me? Na raba ka da ita ne dan na cimma burina kuma” kana ji kana gani sai na aure Nana na cusa maka bakin ciki wanda zaka dawwama a cikin ta. 

          ” Wawan shak’a ya kai mishi da hannun shi d’aya yana huci kamar mayunwacin zaki……. Idan har ban aure ta ba kaima baka isa ka aure ta ba……., bangaje hannun shi Fu’ad yayi ya shige ciki ya barshi. 

         Haka ya ja yaron shi ya bar gidan daga bakin k’ofa ya tsaya yana k’are ma gidan kallo zuciyan shi nayi mishi zafi…….

           


*eedatou*

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like