WANDA BAIJI BARI BA 23-24

Advertisement

                 23&24

        Babu wanda ya lura da haka sai shi kaɗai da sauri ya zura kansa bayan Malam Liman yana cewa, ” Dan Allah kuyi haƙuri na tuba ” gabaɗaya kallo ne ya koma kan Alhaji Babba, Aramma abin ba ƙaramin dariya ya bashi ba, kallan Malam Liman yayi yace, ” Allah gafarta Malam ina ganin Idan zakayiwa Yarinyar nan ruƙiya ko zakz haɗa da Alhaji Babba? “


     Malam Liman na shirin magana Mai Unguwa yayi karaf yace, ” Kwarai kuwa domin alamu sun nuna shima Aljanu sun shige shi…” 


   Mai Unguwa shima anan maganarsa ta tsaya lokacin da kai idanunsa kan Yusra, sunkuyar da kai ƙasa yayi bai ƙara cewa uffan ba, Malam Liman ganin suna daɗa ɓata lokaci yasa ya fara magana.


     ” Assalamu alaikum, Dan Allah muyi abinda yake gabanmu tunda dukkanmu ba yara bane mu, Malam Auwalu muna jinka ” 


Advertisements

     Abba gyara zamansa yayi sannan ya fara cewa, ” _Kamar yanda kowa ya sanni a gurin nan nidai Ainihin sunana Auwalu Musa ni haifaffen garin Kano ne cikin Unguwar wailari, ina zaune cikin mahaifata nida sauran ƴan uwana, gabaɗayan ku kunsan Allah bai nufeni da haihuwa da wuri ba, ina tunanin sa’annina da mukayi aure atare suna da aurarrun ƴaƴa kusan uku ko huɗu ma, dan Aƙalla sai da muka shekara kusan goma da aure amma babu haihuw, sai daga baya Allah ya axurta mu da Yusra._”


     Abba kallanYusra yayi sannan ya cigaba da cewa, ” _Murna gurinmu bata musaltuwa, haka muka ɗauki soyayyar duniya muka ɗora akanta, musamman ma ni da ko ƙuda banasan ya taɓa ta, mahaifiyarta na nuna mata ƙauna ta daidai misali amma ni gani nake kamar bata ƙaunarta, saboda idan ta mata laifi tana mata faɗa wani lokacinma harda duka, sautari duk faɗan da zamuyi nida mahaifiyarta sai dai muyi akanta, tun tana biya mun muyi babu daɗi ganin Yusra ta girma yasa ta daina biye mun, yau da gobe itama yarinyar tun bata lura har ta ankare ya zama tafi so saboda ni nake goya mata bayan koda kuwa itace da laifi._

   _A kanta na ɓata da ƴan uwa da abokan arxiki hatta malam makarantarsu ban bari ba zuwa nake gurinsu idan wani ya dake ta, duk abinda Yusra take so nima shi nake so ko da kuwa abin nan ba mai kyau ba._”


     Numfasawa Abba yayi ya cigaba da cewa, ” _Duk wanda yasan Yusra yasan ta taso a sangarce ba kwaɓa hatta mu iyayenta bata raga mana ba, bata ganin girman kowa duk girmanka bata ƙi ta gaya maka magana tayi wucewarta ba, tun abin baya damuna har ya fara damuna a cikin zuciyat sai dai babu yanda zanyi tunda ance icce tun yana ɗanye ake tanƙwra shi, har iya yau Mahaifiyar yarinyar nan bata gajiya da mun nasiha akan makauniyar soyayyar da nake nuna mata_”



_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉



ƊANƊANO DAGA SABON LITTAFI NA

Advertisements


PAID BOOK

Littafin nan na kuɗi ne da naira 200 ki zaki karanta shi cikin nutsuwa, game buƙatar ƙarin bayani zai iya mun magana ta wannan number 0706 206 2624


ANYA BAIWA CE?

NA

AMEERA ADAM


       Free page    1

 

    Tafe take tana ɗan waige dan gudun karwani ya ganta ko taci karo da wani a hanya saboda abinda ta gano take san zuwa ta isar da shi, aikuwa batayi aune ba tana shiga soron tsakiya suka yi gware da mutum a zabure ta ja da baya tana sauke ajiyar zuciya, kallan tsaf yayi mata yana karantar yanayin ta yasan tabbas akwai abinda ke ƙunshe cikin bakin ta, aɗan diriri ce ta kalle shi ta ce.


        ” Yautai mugun tsuntsu masha miyarka sai yayi dare” 

     

        Kallanta yayi sai da yayi murmushin gefen baki ya ce, ” Tauraruwa mai wutsiya…, Kura kike ga tsoro ga ban tsoro ina zaki kike ta juye-juye haka? ” Sai da ta juya hagu da dama cikin ƙasa da murya ta ce, ” Gobara daga teku maganin ta sai Allah, wata ƙura ce take ƙoƙarin kunno kai a cikin gidan nan amma karka ce kaji daga baki na ” ta ƙarasa magana tana kuma duba gabanta da bayanta.


       ” Jakadiya Kubura kenan, ay harbi ga ɗan jaki gado ne, kuma iya ruwa fidda kai gayamun ina sauraron ki kowa ya iya allon sa ya wanke ” ya faɗa cikin son jin labarin.


     Sunkuyowa tayi dabda shi sannan ta ce, ” kasan koda girgiza kurna tafi magarya, mai tsoron a mutu shi yake maho, Ƙaramar kyauta tafi babbar rowa ” ta ƙarasa faɗa tana miƙa masa hannu alamar ya bata wani abu.


    Ya gano abinda Jakadiya ta ke nufi, dan haka ya sa hannu cikin aljihu ya ɗebo mata silallah ya zuba mata akan hannun ta yana faɗin, ” Ke dai ciki kike mai manta kyautar jiya kuma Kura kike mai manta alherin baya” 


    Juya su tayi cikin jindaɗi ta kunto bakin zaninta ta ɗauresu tana faɗin, ” Domin rana ɗaya ba’a ƙin zuguri, kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan langa, buɗe kunnen ka yanzu zaka sha labari, ashe Fulani Zaliha ciki gareta har ya girma, kasanta da shegen nunkufurci ba ta cika bada fuska a shiga sashenta ba ” zaro idanu yayi waje shima yana waigen bayansa sannan ya ce, ” Lallai tsugunne bata ƙare ba ansai da kare ansayi Mage, naji daɗin wannan albishir naki jeki anjima zan neme ki ” ya faɗa yana yin gaba abinsa.


        Jakadiya Kubura ta fahimci sarai inda maganar Galadima ta dosa har yaje bakin ƙofa ta ce masa, ” Injunan ka sammako wani tafe ya kwana, kuma hargagin ɗan damisa bashi tsorata Namijin zaki, ka taka a sannu kasan Fulani Maryama ba kanwar lasa ba ce ” kamar bazai bata amsa ba sai kuma ya juyo ya ce mata, ” Tabbas inkaji mutum na tsoron dare ba’a ɗaure shi ya ƙwance bane, Ki bar ganin allura ƙarama itama ƙarfe ce, dan haka bazan ce miki komai ba mu zuba mu gani kowa tasa ta fishsheshi ” yana gama faɗa ya sanya kai ya fice daga cikin soron.


      Bin bayansa tayi da mugun kallo sannan ta ce, ” Mai ƙafa huɗu ma ya faɗi bare mai biyu, ajuri zuwa rafi wata ran tulin zai fashe ” tana faɗa ta juya ta cigaba da tafiya, kai tsaye sashen Fulani Maryama ta nufa.


      Tana shiga ta zube ƙasa cikin salon kirari ta fara magana, ” Barka da hutawa Uwargida na bango madafar bayi, uwar marayu uwar mara gata mai iyayenma kin gamai musu komai, Ƴar sarki jikar sarki Matar Sarki kuma gaki  Uwar Sarki, Allah ya ƙara girma ya raya mana Yarima mai jiran gado, Mulki da Sarautar Masarautar Kano gaba ɗaya ta ku ce, Mai Uwa agindin murhu bazai ci miyarsa lami ba….. ” murmushi Fulani Maryama tayi saboda jin daɗin kirarin da Jakadiya tayi shiyasa ma ta katse ta da faɗin, ” Jakadiya anjima zan turo da saƙon maɗi mai ke tafe da ke??  ” russunar da kai Jakadiya tayi tana mai sauya yanayin fuskarta cikin damuwa ta ce, ” Tuba nake Uwar gijiyata banzo dan isar da mugun labarin nan dan wata manufa ba sai dan ki tashi tsaye ki ɗau mataki kuma asan abin yi, Kaico na da tuntuni ban ankare ba, har lamarin ya girmama amma ina mai neman gafarar ki saboda labarin bamai daɗi bane ” 


      Tunda Jakadiya ta fara magana Fulani Maryama gabanta ya yanke ya faɗi saboda tasan labarin bazai mata daɗi ba, shiyasa a hargitse ta wurgo mata tambaya, ” Jakadiya banasan Kewaye-kewaye tafi kanki tsaye ” 


     Jakadiya kara sauya muryarta tayi ta ce, ” Ina neman gafararki da jin kalamai na dama Fulani Zaliha ce ke da juna biyu kuma ayanayin dana lura har yayi ƙwari…..” cikin tsananin tashin hankali Fulani Maryama ta ƙunduma wani ashar sannan ta ce, ” Aikin me kike tun tuni baki sanar dani ba tunda wuri? “


     Jakadiya ta bata amsa da, ” A gafarce ni Uwargijiya ta kinsan Yarinyar da nunk……”


      Katseta Fulani tayi cikin tsawa ta na faɗin, ” Ya isa haka, Lallai Fulani Zaliha ta ɗebo ruwan dafa kanta, Samun sararin kuturu gaɗa a cikin rama, wato haka ta miƙe ƙafa da yawa? Lallai abinda ya faru a shekarun baya dole ya ƙara faruwa yanzu, Aikuwa kowa yaci tuwo dani miya yasha, tashi kije Jakadiya anjima zan neme ki bayan Sallar Isha’i ” 


       Jakadiya najin  haka ta kuma rissinawa ta ce, ” ALLAH ya huci zuciyar Fulani, Ramin kura da wuyar shiga a gayawa kare yayi hankali, tabbas bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane wace ce Fulani Zaliha da zata iya haɗa sahu da Uwar ɗakina, ni mai bin Umarnin ki ce akowanne lokaci ” Jakadiya na gama faɗa ta tashi ta fice zuciyarta fess saboda tasan ba ƙaramin alheri zata samu ba.


         Tunda Jakadiya ta fito daga ɗakin, Fulani Maryama ta kasa zaune ta kasa tsaye sai kaiwa da komawa ta ke abun duniya gaba ɗaya ya isheta, ita kaɗai sai saƙa da warwara ta ke tana san nemarwa kanta mafita, Jaririnta ɗan kimanin wata biyar da ke kwance ta je tasa hannu ta ɗauke shi tana juya shi cikin zuciyarta da shawarar da ta yankewa kanta.


     A fili ta fara surutai kamar wata zautacciya,  ” Yarima yanzu kai ake shirin yiwa kishiya a gidan nan, tabbas bazata yuwu ba tunda ban bari wata ta haifi namiji ba dole na dakatar da cikin Zaliha “


         Jakadiya tunda ta fito daga sashen Fulani Maryama kai tsaye sashen su ta wuce tana zumuɗin sauraron kiran da Fulani Maryama ta ce zata yi mata, kamar wacce a ka mintsina tashi tayi ta fito daga sashen bayi wani gida ta faɗa bakin ta ɗauke da sallama, ” Balaraba matar Ciroma dake tankaɗe ta amsa mata sallamar tana faɗin.


    ” Yau kuma Jakadiya ce da doshin magariba haka?? ” Kujera Jakadiya ta janyo ta zauna sannan ta ce, ” Eh ko bakya maraba da zuwan nawa ne?? ” cigaba da tankaɗenta tayi ta bawa Jakadiya amsa, ” Ni na isa nace banten Sarki yayi ɓurtu, ai hanyar lafiya abita da shekara, meye labari?? Dan nasan bakin ki baya rasa motsi?? “


    Murmushi Jakadiya tayi ta ce, ” Ai dama ni kujera ce dole a zauna dani, kuma abokin cin mushe ba’a ɓoye masa wuƙa, wai kuwa kinsan Fulani Zaliha na ɗauke da juna biyu?? Wa ya sani ma itama ko Namijin zata haifo ni zanso ma ta haifo Namijin naga yanda Fulani Maryama zatayi ”  ta faɗa tana ƙasa-ƙasa da murya.


     Da sauri Balaraba ta saki rariyar Hannunta waigawa bakin ƙofa tayi sannan ta cewa Jakadiya, ” Da gaske kike wannan maganar?? aikuwa muddin zancen nan yaje gun Fulani Maryama kinsan bazai mata daɗi ba, kuma kinsan dole wani abu ya biyo baya” 


      Jakadiya ƙara matse bakin zanin ta tayi ta ce, ” Ai a bakin wawa akanji magana, wai da kunne yaji muguwar magana wuya ya tsere, kinsan dai ai ciki badan tuwo akayi shi ba, bayan ke babu wanda yasan da wannan maganar ” 


      Tsuke fuska Balaraba tayi da alama bataji daɗin maganar Jakadiya ba dan haka ta maida mata da martani, ” Tafasar tukunya bata gefe ɗaya bace, haka nan abinda baki ya ƙulla hannu bashi iya kunce shi, idan kinji makaho ya ce ayi wasan dutse to tabbaci haƙiƙa ya taka dutse, Jakadiya koma dai mene ne daga bakinki wannan maganar ta fito “


    Miƙewa tsaye Jakadiya tayi tana gyara ɗaurin zaninta ta fara takawa har sai da taje wajen bakin ƙofa sannan ta juyo ta ce, ” Mutum fari ne shi ke rina kansa ya zama baƙi, bakinki dai ƙanin ƙafarki kuma harshenki linzaminki ” bata saurari mai Balaraba zata ce ba ta fice daga gidan.


     Da daddare Bayan sallar Isha’i Jakadiya ce tafe tana lalube har ta ƙarasa sashen Fulani Maryama, da sallama ta shiga  ta russuna tana cewa, ” Barka da hutawa Uwar ɗakina ance kina san ganina yanzun nan ” 


     Fulani Maryama dake tsaye hannunta ɗauke da  Salman miƙawa Jakadiya shi tayi ta ce, ” Jakadiya inasan muyi tafiyar sirri kamar yanda muka saba da ke a shekarun baya, ayau basai gobe ba zamu kai ziyara ga Boka Marduska, saboda bazan iya kwana da maganar da kika sanar da ni ba, batare da na nemi mafita ba ” 



      Riƙe Salman Jakadiya tayi tsam kamar wani zai ƙwace shi sannan ta ce, ” Duk abinda kika ce haka za’ayi, bani da ikon bijirewa umarninki, da kai da kaya duk mallakar wuya ne kuma da shuka da albarkarta duk kayan mai gona ne” 


        Fulani Maryama na gama jin haka ta juya ta shiga cikin ɗakinta, cen ƙasan adakarta ta buɗe ta ɗauko wani kurtu tasa hannu ta ɗebo waɗansu irin wuri guda biyu da wani ɗan ƙaramin zobe, maida kurtun tayi sannan ta dawo gurin da tabar Jakadiya ke tsaye.


      Miƙawa Jakadiya Wuri ɗaya tayi sannan ta fara karanta waɗansu irin ɗalasiman tsafi, ba’a ɗauki lokaci ba sai wani haske ya mamaye gurun atake suka ɓace daga cikin ɗakin.


       Tsaye suke abakin wani kogon dutsen dake cikin wani surƙuƙin daji mai matuƙar duhun gaske, Fulani Maryama runtse idanunta tayi ta fara ƙwalawa bokan kira har sau uku, ” Marduska! Marduska!! Marduska!!! ” tana gama faɗa ta buɗe idanunta.


       Ji sukayi ankece da wata mahaukaciyar dariya sai da aka ɗan ɗauki lokaci anayi sannan aka tsagaita, sannu a hankali haske ya mamaye gurin, cikin wata irin murya aka fara basu umarni, ” Ku sanya ƙafafunku cikin waccen ƴar ƙoramar sannan ku tako ku shigo ciki.


     Kamar yanda aka gaya musu haka suka bi umarnin mai magana sannan suka shiga cikin kogon dutsen, daga cen nesa suka hango shi zaune akan buzun damisa, gaba ɗaya jikinsa lulluɓe yake da gashi tamkar ba bil Adam ba, Fulani Maryama na gaba Jakadiya na biye da ita a baya.

    

        Zama sukayi sannan Fulani ta kalli bokan zata fara magana ya ɗaga mata hannu sannan ya kuma kecewa da dariya, sai da yayi mai isarsa sannan ya fara magana,


        ” Ai duk wanda ya bamu iska dole kwaɓarsa tai ruwa, Maryama kin ɗauke mana ƙafa na wasu shekaru sai da buƙatarki ta tashi zaki waiwayo mu ” 


      Fulani Maryama ta russunar da kai ta ce, ” agafarceni Sarkin bokayen duniya, nayi kuskure awancen lokacin amma yanxu baza’a sake ba ” 


       ” Na amshi tubanki kuma nasan abinda yake tafe dake, kalli nan ” ya janyo wata ƙwarya mai cike da jini yana nunawa fulani.


       Tana leƙawa Fulani Zaliha ta gani kwance akan gadon ta tana baccinta hankali kwance, jinjina kanta tayi ta cewa Boka Murduska, ” Ya babban Boka, sarkin bokayen duniya so nake a salwantar da cikin da ke jikinta inda hali ma akashe su gaba ɗaya, domin bayan Salman bana san kowacce matar sarki ta sake haihuwa acikin su saboda bansan gaba mai zasu haifo ba kuma bansan mai hakan zata haifar ba ” 


    Ƙwala-ƙwalan idanunsa ya kafe ta dasu yana ce, ” Daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaƙi, badan kinzo ayanxu ba da tuni sauran damar data rage miki ta ƙare gaba ɗaya ” A zabure Fulani Maryama ta ce, ” Ban fahimce ka ba Marduska “



INA MASOYA GA LOKACIN NUNA ƘAUNA YAZO🥰

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like