WASU MATAN 15-16

Advertisement

 *Page* 15~~16

   Tana cewa “k’aunata jeki ki wanke hannunki muci abincin ci”

tou Addana”ta fada tare da mikewa tsaye,bayan ta wako hannun na tane ta zauna kusa da Aglaa,bisimilla tayi suka faracin tuwon.

    

   Da suka kammala cin Abincin ne suka zauna kusa da bappa suna fira yana basu labarai kala-kala masu sa nishadi da ban dariya,salmat Sai dariya take ita ma Aglaa Murmushi takeyi.


     A duk lokacin da suke firar dare tsakaninsa da yaransa wani lokaci da inna Saude sai yaji a ransa inama tana raye,inama ace  a yanxu hakan suna tare.da zai iya dawo da hannun a gogo baya da ya gyara kuskurensa da zai sanyata farinciki fiye da misali,

Ajiyar zuciya ya sauke ya dubi su  Aglaa Yana cewa “mamana kutashi ku tapi dakinku ku kwanta da wuri kar da safe ku makara zuwa makaranta”


Advertisements

“tou bappa sai da safe komi munka yima ka yafe mana”suka ce suna mikewa tsaye


“na yafe muku,Allah muku Albarka”


“ameen bappa”


Bayan bappa ya kulle gida ya nufi dakin inna Saude,su Aglaa kuwa suka nufi nasu dakin.


 *WASHE GARII*

     Tun da bappa ya ta dasu sallar subahin bata koma bacci ba tana zaune tana azkar bayan ta idar da sallah, jin bappa ya dawo daga masallaci ne ta fito tana cewa “bappa ina kwana”


“lfy lau mamana kintashi lapiya”

Advertisements


“lpy lau na tashi bappa, kaifa?


“nima qalau nake,salamatu ko ta tashi tayi sallah?”

   

   “eh bappa tana idarwa ta koma bacci “


“yawwa, na dauka haryazun batayi sallar ba ne “yace yana shiga cikin dakinsa .

 

  Ayyukan da tasan wajib ne tayi su ta fara,dan bata san ta makara a makarantar bokon.

     Gidan ta fara sharewa ta masa tas sannan tayi wanke-wanken k’wanuka, ta daura ruwan damun kunu.Da suka ta fasa ta dama kunun sannan ta  d’aura zazafen tuwo.


   Dakin inna Saude ta nufa ta gaya mata ta gama abincin karin kumallon tazo ta raba.

       cikin dakin ta shiga da sallamarta, inna Saude ta hango tayi reshe-reshe bisa katifarta tana shakar baccinta.

     A ka’idar inna Saude ba’a tada ita bacci,kuma ko waye yayi gigin tada ita yasin sai yaga cin mutunci  kala-kala,Bappa d’ai ne dai-dai da ita dan tana shakkunsa wani lokacin amma wani lokaci inta tashi rashin arzikinta harda shi take mawa.


fita tayi a dakin ta nufi madafi, raba abun karin kumallon tayi ta sama Bappa nashi a k’wanikan shi,inna Saude Ma haka,ta dibi nasu sannan ta fito daga cikin kicin d’in.ta kai ma Bappa nashi a  dakinsa.


 Wanka taje tayi sannan ta tada salmat domin tayi wankan”Allah Addana kwanan nan bai ishe ni ba wlh kika tadanii”tafada cikin muryar bacci da shagwaba

 

  “murmushi Agla tayi tana cewa “ok sorry y’ar k’anwata tashi ki shirya sai muci abincin mu wuce makaranta kar mu makara kinjii”


“tou” tace tare da mikewa tsaye tana hamma.


  Wankan itama tayi sannan tazo ta shirya cikin uniform d’in su na *G.G.S.S mabera* ( *GOVERMENT* *GIRLS SECONDRY SCHOOL* )da ke cikin unguwarsu.Bayan ta shirya a tsakar gidan ta samu Aglaa zaune bisa ta barma,zaune tayi suka fara karya wan atare,ba wani abincin kirki Agla taci ba ta mike tare da wanko hannunta,kunun ta dan shan bada yawa ba amma yafi zazafen da taci yawa,salmat kam hani’an tayi sannan ta mike tare da wanko hannun ta tana cewa

“Alhamdulillahi Rabbil Alameen,yanxu kam naji garau Adda,zamu iya tapiya na ba mallam hakkinsa”


“wane mallam kuma salmatt?”


“lalala karki cemin baki sanshiba”tafada tana zare ido 


“a’a bansanshi ba,wai ba inna tace kibar kula samarii ba y’ar yarinya dake dudu fah bakinki 14yers “tapada cikin fada-fada amma in mutum baisanta ba bazaice fadana take hakan ba


kumshe dariyar da kesan kufce mata salmat tayi tana cewa”eh tace ,kuma Allah Adda shike damuna wai ai nabashi hakinsa idan ba haka ba yai ta damuna,kuma kinga in anka ganeni ai baza ace min yar shekara sha hudu ba ko ?”


kasa ke Aleeya tayi tana kallan salmat chan tace “hakki kuma mine ne hakkin nasa?” 


Ganin yadda Addan nata kebin ta da wani kallo yasa ta kwashewa da dariya tana cewa “yanxu Adda Aleeya Baki fahimce wane mallam nake nufi ba”


 kallo kawai Aleeya Ta bita dashi hakan yasa salmat kara kwashewa da wata dariyar tana cewa “yasinn ni ba wani malami da nake  nufi face *CIKINA*naci abunci na basa hakinsa shine nake nufi tafada cikin dariyar da take. “Murmushine ya kwacewa Aleeya tare da sauke aziyar zuciya tana cewa “lalai salamatu kin girma yanxu nizaki mayar abokiyar wasarki ko? yamiki kyau “


“sorry!sarry!!my Anty daya tamkar da dubu karkiyi fushi da yar k’anwarki mana,kiyi hakuri nasa kinyi mutuwar tsaye”ta fada har yanxun dai dariyar take tana kwatanta yadda Aleeya Tayi.

   Itama Aleeyar Saida ta dara tana cewa “zanka maki ne Salmat Harda koyon yadda nayi ko”

“Alqur’an yadda kinka yine yaban dariya sosai wlh”


“ok yayi kyau ki ci gaba da dariyar sai mun makara”tafada tana nufar dakin Bappa.

   Da gudu Salmat tabi bayan ta suka shiga dakin a tare “Assalamu Alaikum”


“Wa’alaikusallam” Bappa dake kishingide bisa katifarsa yana jan tasbaha ya fada


“Bappah barka da safiya”


“yawwa Auta kin tashi lapiya”


“lapiya lau Bappana”

Kara gaidashi Aglaa Tayi itama sannan tace “Bappa mun shirya zamu wuce makaranta”


“tou Allah yatsare ya kiyayemin ku,ya maido ku lafiya”yafada yana miko musu naira dari “ungo wannan kwasai wani abu in lokaci cin abinci yayi.”

Da ameen ameen suka amsa Aglaa(Aleeya)na cewa “Bappa mun gode Allah kara budi”


“Ameen” 


Salmat Ta bude baki zatayi magana ta hangi inna Saude zata wuce sai ta d’an daga muryarta tana cewa “Bappana mungode Allah karo arziki mai albarka ko innata na daina ma wulakanci tunda taga baka da kuddi,Allah bappa ifan kayi kuddi ka kara aure”tafada tana kumshe dariyar ta.


Murmushi Bappa Da Aglaa sukayi domin daga jin wannan maganar sun san da inna Saude ne takeyi,aiko sakon da ta isar ya isa dan inna Saude masifa ta dinga zubawa domin dai Salmat ta tsokanota.

      

    Bappa kuwa yayi kunne uwar shegu da ita domin yasan komi iskancin da takeyi mai bata kaunar ace ya karo aure,tana tsananin sonai shima haka yana santa amma halayyarta ne na son kudi ke rage santa a zuciya tai.Sanadin san da ya kema ta ne ya yasa ya tabka babban kuskure arayuwarsa da duk lokacin da ya tina yana jin ba dad’i.   Da suka ma mata sallama za su wuce masifa ta dinga yi musu hardai Salmat,tana cewa wai anya auta ba musanya min ke a asibiti akayi ba ?


“Haba inna yanzu dan nace Bappa ya kara aure zakice an musanya miki ni “tafada tana kwabe fuska


“dakuwa inna saude ta mata tacewa “kinci gidan ku nace wato  kara maimaitawa ma kike,to wuce  ki bani guri tun ban ji miki ba yar nema da bata kishina”


Hannun Salmat Aleeya taja dan wallahi suna iya kaiwa takwas ita da inna Saude sunayi kuma ba bari zata yiba tace “inna Allah ya huce zuciyarki, mun wuce makaranta”


“Allah ya kiyaye” tace ciki ciki

da Autarta ta tamata magana hita batun ta tayi,salmat ko cewa take” inna duk kishinne ko maganata baki amsawa ” 

 

  buta inna ta dauka tare da kyaro mata ita da gudu ta fita wajen gidan tana dariya,Aleeya ta bita abaya tana daura nikab dinta  ,Bappa ya bisu da fatan Alkhairi.


Gidansu Amina Suka nufa ,abakin kofar gidan suka taras dasu suka wuce makaranta salmat na basu labarin yadda sukayi da Aleeya da inna.✍️✍️✍️    *Zeesardaunerh ce*


          ( ~Y’ar karamar su babbar~ ~su~👧🥰🤩)# _comment_ 

# _like_ 

# _share_ *comment and vote dinku* *shike* *karamin karfin guiwar* *typing* 💋

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like