WASU MATAN 21-22

Advertisement

  *Page* 21~~22


   Yana cema su Khaleel”kutashi mutafi kun kusa makara”mikewa sukayi suna “Umma muntafi sai mundawa”

“Allah ya tsare ya kiyayemin ku,kuyi karatu sosai banda mugun wasa da jan fada”

“tou Umma”rakiya ta musu sai da suka hau,machine din yadaka daga gidan sannan ta dawo cikin palon nata.

      Breakfast dinta ta’ida saboda d’azu bata ci abun kirki ba sannan ta fara kimtsa gidan.


      Cikin amincin ubangiji sunyi theater lami lafiya ba tare da wan problem ya afku ba,yanxu haka patient din tana bacci .

    Office d’insa ya nufa domin ya gaji sosai,ruwa ya d’auka yasha tare da zama bisa kujerar sa ya hutawa.

Advertisements

     Bayan hour guda ya kammala diba files na maras lafiya da zai dubaa sannan ya fito,bisa hanya suka hadu da Dr.Abdullahi zamau “wurinka ma zanje ashe har ka fito”

“eh inason ne na biya company “

“ok dama batun file din matar nane”

“wace matar?”

“wadda keda matsalar heart,Allah yasa dai ka duba bayananta”

“oh..!na manta ne,eh na duba bayananta now thursday sai monday za’a mata aikin”

“ok,Allah kaimu”

“Ameen”yace yana nufar motarsa 

“Dr.Haidar”bai jiyo bcox ya shaida wacece ,sake kiransa tayi ganin bai amsa ba amma ya mata shiru shi bai amsa ba kuma bai shiga motar ba.

kusa  dashi ta zo ta tsaya cikin karya murya tace “Dr.Haidar Na kiraka ka kyaleni nama wani laifine ?tafada cikin alamun tausayi.

“Kunne keji ai,if u don’t have something to say please leave here,i have something important to do “ya fada ba tare da ya jiyo ya kalleta ba,iya shaka tou Dr.Aysha Ta shaka,wulakanci da Dr.Haidar Kemata ya yi yawa amma duk da hakan bata jin zata hakura dashi,cikin dakewa da nuna abunda yace mata bai mata zafi ba tace “no dama cewa nayi idan ban ta kura maka ba ina son kad’an ragemin hanya “

“i can’t akwai abubuwan da nake son yi alot d’an haka banida time d’in westing,kina iyama Dr.Abdallah Magana sai yayi dropping dinki” ya fada yana shiga motar sa ya bata wuta.

Advertisements

     

      Wasu hawayen bakin ciki ne suka cika mata i’do,muryar Dr.Abdallah taji yana cewa muje nayi dropping d’inki “no barshi kawai Thanks ta fada tare da nufar motar ta.

    Dage kafada Dr.Abdallah yayi irin damuwarki cikin ransa kuwa cewa yake “rashin aiki ne yamiki yawa Aysha da kike tsayawa westing time d’inki akan haidar, mutum yanuna baida intress kanki amma kinki ki fahimta,

always bakya tsakanin abuja,kano,sokoto duk inda yayi sai kin bishi, taya zai so ki haka abu ba class,bansan mike damun y’an matan mu na arewa ba wlh,mata kunya aka sansu da ita amma yanzu everything sai kaji ance zamanine”wani tsaki yaja tare da komawa cikin asibitin, dama rakiya ne yayiwa Dr.Haidar.


Cikin motarta ta fada tare da bata wutaa,zuciyarta gaba daya a chinkushe take,data isa bakin wani tampatsetsen gate ta rika zuba order kamar hauka da sauri  maigadi yazo ya bude mata domin daga jin wannan order kamar za’a tadda gidan yasan cewa hajiya karama ce it daice a gidan ke irin wannan motar parking tayi cikin makeken parking space dake cikin gidan,direct room dinta ta nufa wanda ya kawatu sosai da sosai fiye da tinanin mai tinani.

      Bisa Royel bed dinta ta fada ta sake wani marayan kuka maiban tausayi,miye aibunta da Aliyu baya santa ne,mikewa tayi ta nufi glass ta tsaya taa karema kanta kallo bata wata makusa ,to miyasa shi bata burgeshi,miyasa baya santa ne ,tana da masoya da yawa a ko ina,duk abunda Haidarke mata sansa ko kadan bai ragu a zuciyarta ba sai ma haw hawa da yake yi,a ko da yaushe a ko wace sa’a.

   Ta wulakanta samari da yawa kala-kala masu kudi da diyan talakawa wadanda ke daukowa kansu abin da yafi karfinsu in bahaka ba miye hadin ta da wani talaka mstwwsss dan ya renata yace yana santa,ta wahalar da samari masu yawa amma ace wai ita Aysha Mas’ud mai nera soyayya ke wahalar suwa ,akace idan da ranka ka sha kallo amma ai Haidar yakai matsayin da kowace mace ta gansa zata iya afkuwa da sonsa .Mahaifinsa na cikin mayan masu kudin kasar nan ko ina ana damawa dashii sannan shima kansa yana cikin matasa masu kudi wad’anda suka jika da naira ga uwa uba kyau da Allah ya bashi, tabbass Haidar kyakyawane sosai shiya take bala’in sansa kuma inshaallah sai ta mallakeshi a matsayin mijin .   Har yanzu tana cikin damuwa gashi wayan ummanta yaki shiga,agoon dakin ta kalla karfe daya ta buga amma bata samu damar koda share gidan nata ba bare tayi batun aza girki,wani murmushi ne ya subuce mata,alokacin da taga…………………………………….✍️✍️✍️    *Zeesardauner ce*


          ( ~Y’ar karamar su babbar~ ~su~👧🥰🤩)


# _comment_ 

# _like_ 

# _share_ *comment and vote d’inku shike* *karamin kafin guiwar* *typing* 💋

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like