WASU MATAN 9-10

Advertisement

    *Page* 9~~10 


   Wani karamin botique ne, everything akwai in banda babu.

   clothes din sa ne a gurin,shadda place,english wears,suit,jallabiya ma haka ko wane da gurinsa;baza ki iya lissafa a dadin tupapin Haidar Ba, even him baisan yawan suturarsa ba.

   every states in nigeria yana da houses da dama,even outside ma haka;like UK,India,Dubai da sauransu .

    sam baya san idan zai yi travelling wai sai ya dauki kaya,baya san haka shiyasa a ko wane gari ya tafi he have his own house.Gashi mutum ne mai yawn tafiye tafiye bcox of his father’s bussiness,kuma Allah ya had’a sa da lazy wife wacce bata damu dashi ba.

 

   part d’in jallabiya ya nufa tare da d’aukar milk colour,the same thing yadanna abun nan na d’azu sai gurin ya koma yadda yake.


Advertisements

  Bayan yasa jallabiyar sa ne ya fesa turaren sa Imperial Majesty(the most expensive male perfume in the world) ya ma jikinsa wanka da perfume kamar ba gobe bcox Allah ya yisa mutum mai masifar son kamshi;lallausan takalminsa yasa a kafarsa masu masifar laushi tare da nufar palon,gurin fridge ya nufa tare d’aukar one bottle water ya fita.


   


   Part d’in Suhailat Ya nufa ya mird’a handle din kofar ta ta yaji a kulle, dama yasan a rina (wai an sace zanen ma haukaciya).


   Suhailat Ce zata zauna a gida ba tare da ta fita ba,ya d’an tabe cute pink lips d’insa tare da cewa a ransa “whether tana nan or not duk uwarsu daya tunda bata san darajar aurenta ba”.   Fita yayi daga part d’in, because lokacin magrib ya kusanto direct masallacin da ke cikin gid’an ya nufa, a gurin ne ya hadu da ila mai gadi cikin husky voice d’insa yake tambayar sa”Suhailat ta fita ne?” “eh dazu bada jimawa ba, bayan ka koma office” “ok” yace lokacin da suka shiga masallacin.Advertisements

     “Salmat Yi sauri mana kinga time na tafiya kar muyi latti”,”gani zuwa adda littafaina ne na dauka”cewar Salmat Yayin da take fitowa daga cikin dakin su,”ko kefa,kina son muje ne mallam Nura Yamana bulalar latti?” 

   “A’a adda,kuma kinsan baida mutunci bulalarsa mugun zafi ke gareta.”

    Dariya Aleeya Tayi saida gav teeth din ta ta bayyana tana cewa”Aiko saina gaya masa abunda kikace”, “sorry Addana karki gaya masa kinji,amma gaskiya na fada ai ko?”  

      Murmushi kawai Aleeya tayi tare da jan hannun k’anwarta tace”nidai mutafi kinga time yana tafiya”, “ok” Salmat Tace suka nufi dakin inna Saude .


   Sallama Aleeya Tayi ita da Salmat,inna Saude Ta amsa musu.

   A tare suka ce “inna mun tafi makaranta” “Allah ya tsare hanya banda tsayawa, in antashi ku dawo da wuri kunga dare ne” da “toh” suka amsa tare da mikewa suka fita.   Sanye suke cikin tupapin islamiyya ash colour,riga da wando ne sai dogon hijab white colour wanda ya wuce guiwa amma na Aleeya har kasa yake,suna cikin tapiya suka hadu da kawar Aleeya mai suna Amina  Tare da k’anwarta Bilkisu Yar kimanin 13Years,suka hadu waje guda suka nufi makarantar.

       

   Bayan sun isa makarantar ne kowa ya nufi class dinsa.Aleeya Da Amina ajinsu guda a both boko and islamiyya,haka ma Salmat Da Bilkisu.Gidan su Amina yafi kusa amma basu da wani tazara tsakaninsu da su Aleeya.

          “Sallama” sukayi a ajin sauran yan class din suka amsa, sit dinsu suka nufa suka zauna tare da mikawa sauran frnd dinsu hannu suka gaisa.


   “Ai na d’auka ko yau sai kunyi lattin”cewar Ummi(Maryam) d’ai daga cikin frnds d’insu,” dariya sauran suka sa Rahma Ta ce “kinsan Aglaa(Aleeya)da shegen tsoron bulala ko kad’an bata san abin da zai taba lafiyar ta ai”, “da gaskiyarta wlh wake son a taba masa lapiyar jikinsa, hardai waccan malamin mai shegen zafin hannu” cewar Aisha, Amina tace “wlh ko” duk dariya suka sa,A lokacin kuma malami ya shigo ajinnasu.


  Aglaa shine sunan da frnds dinta ke kiranta dashi,Aglaa kalmar larabci ne ta na nufin(Mai tsada),suna kiranta da mai tsada ne saboda baiwar kyau da dirin da Allah yai mata,ga kuma nutsuwa da kaifin basirar da Allah ya bata.

    

       A yanxu haka Aglaa hizib dinta Arba’in da harda,kuma ta sauke Alqur’ani mai girma tun bayan shekara hudu da suka wuce , a cikin littafai kuwa ta kammala Usulull-fiqihu,Ahdari,Ishimawee,yanxu haka tana cikin iziya.Bangaren boko kuwa tana ajin karshe SS 3 kenan.

 

   Allah ya mata baiwar basira hakanne yaja mata farin jini ga malami maza da mata da kuma dalibai;yanxu haka ita ce food prefect (mai kula da tsaftar  abincin dalibai).      “Umma nid’ai abunda na keso dake ki tayani da Addu’a kinji..” 

     “A koda yaushe cikinta kuke dan nan,(Kabeer kennan shine d’a na fari ga mahaifansa shiyasa bata fadin sunansa)kaimakaci gaba dayi Allah ya tsare ka a ko ina kake”, da “Ameen ” ya amsa shida sauran kannensa .

     Mikewa yayi yana cewa “na wuce Umma sai da safe”,”Allah ya ta shemu lapiya”, “Ameen” yace yana amsa saida sapen da k’annen sa Fatima da Batul ke masa.

      ya fito waje kenan ya hadu da da inna Dije “inna barka da dare,an wuni lafiya?” cewar Kabeer yayin da yake durkusawa “da ban wuni lafiya ba ka ganni? banson munafurci dalla tashi ka bani guri” tafa da tana jan tsaki,tayi wucewarta daki.


   cikin ransa yake cewa daga gaisuwa “toh Allah sawwaka” ya tashi ya fita.

     Wurin abokanansa ya nufa suka d’anyi fira kafin yace” bari na tafi gida karna biye ma gwauraye”ya fada yana dariya,”mun daiji,muma ai lokaci na nan tafe”cewr daya daga cikin abokanansa,guda kuwa cewa yayi “gwara ka tafi tun bata fara cigiyarka ba tunda ka koma mijin tace” dariya sauran suka sa masa”nadaijiya kumi za kuce” ya fada yana hawan mashin din sa


    Ko da ya isa gida tsare shi da tambaya Maryama Tayi tana cewa “daga gidan ubanwa kake” “lfy dai ko?” ya tambayeta “lafiyar ce ta kawo haka” tafada tana jijiga jiki.

    yarasa ma wace amsa zai bata,wai kamar shi da gidansa dan ya fita sai an tambayeshi daga gidan uban wa yake?

     Bai san lokacin da ya ce mata ba daga gidan Uban…………………………..✍️✍️✍️


    *Zeesardaunerh ce*


         ( ~Y’ar karamar su babbar~ ~su~👧🥰🤩)


# _comment_ 

# _like__ 

# _Share_


 *Comment and vote d’inku shike* *kara min karfin guiwa*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like