DUK NISAN JIFA 43

Advertisement

 

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

          *DUK NISAN JIFA*

           _(K’asa zai dawo)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

            _RUBUTAWA_

               *SAJIDA*

Advertisements

        *SADAUKARWA*

                   *GA*

           *MASOYA NA*

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🀝

  β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ 

Advertisements

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim

                           43

Tabas idan aka ce tashin hankalima an fadi kadan, domin gaba daya hankalin mama ya tashi ta taro tati a jikinta a firgice take fadin” Zainab, zainab meye haka? Ke zainab meye zaki sakawa ranki damuwa irin haka a kan namijin da ya watsar da ke? Zainab kar ki min haka, ku uku kawai nake da ku a rayuwata kar ki min haka!”

Dagowa ta yi a rikice ta ce” Malan ka yi wani abu mana “

Ajiyar zuciya ya sauke daga tsayen da yake ya juya ya nufi bangaren da ya tabata Bilkisu na cen

Tana zaune a fallo ta kurawa waje daya ido ya dan yi gyaran murya ya ce” Taso ki ja mota a kai mamanku asibiti na ga ke kadai ce shi kadirin baya nan”

Da sauri ta mike a tsorace ta ce” Aba mama? Mamana? “

Abanta ya kamo hannunta yana dan girgiza kansa ya ce” Eh dayar maman naki maman Hisham, ina makulin motar gidan naku? “

Da sauri ta juya dakinta ta shige da dan fudu duda jikinta ba wai ainahin karfinsa take ji ba ta dauko kys din motar ta fito

Tana zuwa ta tarar da mama rungume da tati tana ta hawaye tana kara kiran sunnnata

A raunane ta rage tsayinta muryarta bata fita da kyau ta ce” mu kamata mu sakata motar mama “

Kai kawai mama ke gyadawa sai a lokacin ta kamata da dukan karfinta Bilkisu ta kama mata suka cicibata suka nufi mota da kyar domin jikinta ya mugun saki dole ta kara nauyi a kan ido bude

Da kyar suka daidaita mata zama Aba na rike da kofar motar sannan mama ta shige ta talabeta a jikinta Aba kuwa ya zagaya dayan bangaren ya bude ya shiga ya zauna

BILKISU ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta tayar da motar kafin ta dauki hanya

Kwata kwata sai ta rasa ina zata nufa da su, haka kawai ta juya ta nufi wata clinik da su hankali kwonce

Mama da yake hankalinta tashe bata kawo komai ranta ba, batama kula cewar tafiar ta yi wuri ba domin a clinik nandu ta kaisu haka ta talabo kanwar tata a lokacin da likitoci suka fito dab da motar domin ana bude clinik din ake shaidawa likitocin idan abin na urgence ne

Kama tati suka yi suka dorata kan gadon turawa suka gyarata da kyau sannan suka turata

Wani likita ne rike da safar hannu yana kokarin sakawa yake yiwa su mama tambayar me yake damunta, me ya sumar da ita? Shin dama tana suman haka? Da dai sauransu 

Mama gaba daya a rikice take sai juyi take ga hawaye sam bata gane cewar ba ainahin wajen aikin Hisham bane a rikice ta ce” HISHAM, ku kira min yarona HISHAM muhamad karibullah, ku shaida masa gamu nan Zainab ba lafia dan Allah”

Mutumen ne ya kara kallonta da kyau, sai kuma ya juya da sauri ya bi bayan likitocin 

Jim kadan ya fito ya yafito Aba dake tsaye da wayarsa ya gama kiran Hisham wanda da kyar ya same shi

Aba na zuwa cikin datakonsa ya masa salama

Likitan ya amsa shi da kulawa ya ce” Yauwa, muna bukatar cike dukan abinda ya dace, muna da bukatar samun dukan information na sunnanta, shekarunta da ainahin abinda yake damunta, yanzu an samu an farfado da ita aman gatacen tana kuka hasalima jinninta ke ta hauhawa ta ki yin shiru, ga kuma ita macen ta kasa daina kukan itama sai kuma na ji ta kirayi sunna complet na Professor HISHAM MUHAMMAD KARIBULLAH a matsayin yaronta  bayan idan har mamansa ce yaya aka yi suka nufo nan su dake rike da baban asibitin kasar? Nan fa na kudi ne ko shi ya fi kusa ne? “

Mama dake gefe ne ta shiga bin wajen da kallo, har ga Allah ita sai yanzu ta gane ashe ba wajen aikim Hisham suka zo ba

Dubanta ta maida wajen Bilkisu dake tsaye cen gefe da kys din motarta a hannunta fuskarta hade ba alamun kuka ba wata karaya a tatare da ita, in ba dan jin cewa Zainab ta farfado tana kuka ga jinninta ya hau ba da ta je ta kama yar cen ta wanka mata mari ta yadda zata bata kyakyawan bayani a kan kawo su nan da ta yi

Sai dai ina, bata samu wannan damar ba ta ji Aba na mata magana a sanyaye ya ce” Asma’u, ki daina hawayen nan mana ya isa hakanan, ki jajirce ki shiga ki basu dukan bayanan da suka tambaya domin jin mahaifiyar yaron nan ce gaba daya na ga sun juya sunna maganar jininta dake hawa, kece fa baba idan baki daina kukan ba wa kike so ya tsawatar mata? “

Mama ta ringa sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce” To, to “

Aba na kallonta ta juya a hankali tana cewa” A ina zan ga inda take?….”

Bai kai ga bata amsa ba wata daleliyar mota ta dano kai balbalin wajen sakamakpn budewar da mai gadin ya yi

Hasken motar da kyanta ya raja’a hankalin mutane da dama a kanta , uwa uba irin parking din da aka yi a tsakiyar wajen maimakun a kai motar cen layin motoci ya saka da yawa suke jira su ga mai tsaron nan ya zo ya kori mai motar a wajen, sai dai ba shi ba alamarshi

Kafarsa ta hagu ya fara fitarwa wace ke cikin takalmi baki sau ciki na fata mai shegen kyau wanda ya rufe yatsutsin kafar tasa da bayan kafar aman ya fitar da kadan daga jikin farar kafarsa kal kal kal da ita

A nitse ya idasa fitowa daga cikin motar sannan ya rufe yana tsaye kikam yana kallon wajen haka kuma idannuwansa na kan mama

Sanye yake da bakin dogon wando irin na lalausan yadin nan da ake yin irin kaya dinkin turawan nan na mai yar ciki da ta sama da nekti, sai dai ita din ce kawai sai wata riga baka itama mai dan tsaba tsaba sai farar rigar likitoci wace take saman kayan nasa fara kar kar da ita a goge tas hakama sai daukan ido take tsabar tsaftar mai ita

Ginanen jikinsa ya baiwa kayan damar haskawa a jikinsa, farar fatar jikinsa ta dauki kalar bakin nan da farar rigar likitoci wanda damatsunan hannunsa du irin yadda suke cikin rigar nan ta likitoci ana iya gannun girmansu da cikarsu taf da su

Kanshin turaransa yana bude motar dama shi ya fara yin salama kafin ya fito din, zuwa yanzu da yake tsaye idannuwansa sanye da bakin gilas irin bakin nan mai madubi blu wanda ya rufe kalar kwayar idon hakan ya rufe ainahin yannayin da yake ciki

Fuskarsa a hade take ba alamun ya taba sannin kalmar daria a duniyarsa

A hankali ya sada kansa da dubansa a kan mamansa dake jan hannunsa kafin ta ja ta tsaya da sauri ta shiga masa bayanan da ciki abinda ya gane kadan ne , shima kawai ya gane cewar tati ta suma ne

Turus mama ta yi tana kallonsa ta ce” HISHAM, ya kake kallona cikin wannan gilashin ina maka bayani ka zo mu je ka kama min mu yi mata nasiha wai jinninta na hawa ina take so na saka raina ne? “

A hankali ya rike hannunta sannan ya shiga tafia da ita 

Sai da ya kaita wajen zaman mutane ya zaunar da ita a hankali ya dan dafa bayan hannun nata sannan ya juya ya nufi cen cikin wajen likitoci

A hankali Bilkisu ta zauna itama a saman abin zama, kafarta ta ziro daga cikin zumbulelen hijab dinta  wace ke sanye cikin baki dogon lalausan wandonta irin wanda ake kira da sigarette damamen nan daga kasa aman kasancewar mai jayuwa ne sai ta saka hannunta ta ja kafar damar sama kadan hakan ya ba saman kafarta damar dan fitowa kadan

A hankali ta dora kafa daya kan daya ta shiga dan balancing dinta sannan ta maida kanta baya ta jinginar da jikon garun wajen ta lumshe kyawawan idannuwanta da suka dan kumbura kadan ta afka a kogin tunani

Ya dauki dan lokaci  a ciki kafin ya fito shi da wasu likitoci uku, dayan docter ne biyun kuwa infirmier ne

Da yannayin farin ciki a fuskar likitan ya kama hannun Hisham ya ce” Mun gode sosai Professor, Allah ya biya in sha Allah hajia na zuwa zamu kai mata wannan albishir Allah ya baka ikon zuwa muma kana duba mararsa lafianmu a nan”

Murmushi ya masa mai kyau wanda yanzun ba bakin gilas din a idannuwansa sannan ya nufo wajen mama dake zaune a nan din Aba kuwa na nesa da ita

Sai a lokacin ya dan rage tsayinsa yana gaishe da Aba, sannan ya zauna kusa da mama ya kamo hannunta cikin nasa ya rike a sanyaye ya ce” Mama yanzun sai ki ringa saurin kuka bayan kin san bana so”

Mama ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce” Yaya jikinta? Ta tsoratani Hisham yaya zan fuskanceta na mata bayanin tambayoyinta? “

A sanyaye ya ce” Da sauki sosai, ta yi baci mama”

Sai kuma ya dan daga dubansa yana kallon wajen kofar da ma’aikatan ke ciki ya ki ba mama amsa a kan tambayar da ta masa na shin ta yaya zata bata amsoshinta, sarai ya san wasu amsoshi tati ke so domin a lokacin da ya shiga tana kukan ne kuma ta masa tambayoyin ne, aman sai ya share domin idan zai ba mama amsa zai ce da ita ne ki bata amsa kai tsaye shin kina da wata damar bata amsa ne bayan ta kai tsayen?, sai dai ya kyaleta dan baya son ranta ya zo yana baci saboda shi

Stil da yannayin sanyin da ya riski jikinsa a yau ya ce” Yaya aka yi kuka zo nan? Ko nisa cen ta yi sosai? “

Mama ta girgiza kanta ta kai dubanta wajen da Bilkisu ke zaune ta ce” Ga ja’irar da ta kawo mu nan ban san dalili ba “

Sai a lokacin ya kaleta, ya mata duba na kirki duda jikinsa na shaida masa cewar tana wajen tun da suka sako hancin motarsu aman sai ya share ya dake ya basar du a zuwansa na ya idasa yakiceta daga rayuwarsa kwata kwata dan ya gama yarda cewar mama bata son tarayarsu shi kuwa zai mata biyaya

Kasa kasa ya kare yiwa yannayinta kallo kafin ya cire dubansa a kanta ya lumshe idannuwansa

Sun dan dauki kamar minti biyar ya ji mama na fadin” Rikemu za’a yi ne? Idan rikemu ne na koma gida na harhado abubuwan bukata Hisham? “

Hisham ya kaleta kallo irin na girmamata  har cikin zuciyarsa, lalle ana cewa tsakanin yan uwa ba’a shiga, shi shine kat, koda yake soyayar mamansa ce ta fito fili ita dayar ko zata iya duban maman bayan dukan abubuwan son kai da rashin adalci a bayane da ta aikata mata idan a kanta ne ya faru?

Kansa ya dan girgiza ya ce” aa “

Sai kuma ya kara yin shiru

Aba ne ya fara mikewa ya ce” Tunda da sauki bara na koma ga duhun magariba na karatowa “

Hisham ya mike da sauri yana kallon Aba ya ce” Aba tafia zaku yi? To bara kader ya mayar da ku gida “

Aba ya ce” Aa aa yaron nan ba za’ayi haka ba, ka ga shi din ba dorebanka bane? Kai kuwa baka da wasu aike daga nan har anguwarmu akoy nisa ga cen yan sahu da yawa sai su kaini mana”

Bilkisu da ta riga ta mike tun da Aba ya mike ne ta dan tabe bakinta gannin sunna ta gardama Hisham na fadin aa ya yi hakuri a kaishi gifa ba wani takura, shi kuwa ya dage irin kar ya shiga motar sirikin nan ta dan rage muryarta ta ce” Ma zan kai Abana gida “

Mama ta kaleta ta dan tabe baki tana kara kallonta, ita ta kulama kamar Bilkisu bata yi kukan sukar yar uwarta ba fa? , wai wani abana to da wa ya ce nasa ne? Mama ta kara tabe baki da haushi haushi ta cira kai gefe 

Bilkisu ta yi murmushi ta juya ta nufi hanyar kofa bayan ta furta” Aba mu me”

Da ido du suka bita, hijab din lale yana da tsayi aman irin mai lafewar nan ne a jikin mutun, ga wando a kasa wanda tsaf ana gane wando ne wanda ya fitar da tsarin halitarta tana rausaya cikinsa ta yi waje

Sai kuma suka kalli junna Aba da Hisham, Aba ya yi dan murmushi ya ce” to ka ga, kasancewar kai.ke tsaye a kan Zainab ka koma Hisham, ita sai ta mika ni domin akoy maganar da zamu yi da ita, idan ka samu lokacin dai ka leko kafin nan zuwa gobe in sha Allah akoy maganar da zamu yi da kai “

Hisham dake tsaye hannunsa daya na cikin farar rigarsa ta likitoci dayan kuwa na cikin na aba a ransa fadi yake ‘Shin gaba muke?’, sai kuma ya sauke nanauyar ajiyar zuciya ya gyada kansa a hankali ya ce” Aba, dan Allah kar ta jima dare ya yi, idan kuwa ta yi dare ta kwana a cen bama son tukinta na dare”

Aba ya amsa shi cike da kulawa kafin ya juya ya tafi mama na masa Allah ya tsare

Kusa da mama ya koma ya zauna kansa sade, cen ya dago yana dubanta a lokacin da take fadin” Lah Hisham, kira min number Aisha na fada masu ga inda muke kar su dawo daga asibitin bama nan”

Dan tsai ya yi da tunanin da yake, numberta? To shi ina ya ga numberta?, a hankali ya ji bakinsa na fadin” Mama wa ya batawa Bilkisu rai ne? “

Mama ta kale shi, irin yannayin da ya yi tambayar kwarai ta kula kamar maganar cikin ransa ce ta falasa kanta ta fito a lokacin da bai shiryawa hakan ba, domin sai da ya yi tambayar ne kuma sai ya hade fuskarsa ya mike tsaye yana fadin” Mama tashi a maida ke gida, wajen nan yanzu sanyi ya sauko, idan maganinta ya kare sai na kawota”

Mama ta masa wani duba mai cike da tausayi kafin ta dan kauda kanta ta ce” Zo nan “

Wajen da ta duba masa ya tsaya ya kalla sai ya kuma dubanta

A hankali ya dawo ya zauna, tun kafin mama ta yi magana ya ce” Mama, ban tambaya dan wani abu ba fa, na hakura kamar yadda kika ce mama, ba zan kuma takurawa a kan magamar ba na barwa Allah komai, na dai ga ne kamar ranta a bace kuma idannuwanta sun  kumbura sannan mama ko magana fa bata min ba shine hankalina ya tashi”

Mama ta yi murmushi ta ce” akoy wanda ya isa ya maka iyaka da ita ne? Ko ni nan sai dai na nemi shawara sannan na katse wasu abubuwa duba da yannayin rayuwa……”

Dan shiry ta yi tana tunanin shin wajen nan wajen yin maganar ne ko yaya?, aman gannin da sauki barcima take kuma tana son ya tayata rarashin kanwar tata sai ta kara gyara zamanta tana kallonsa ta ce” Harta maganar shan nono daya  dan ka mana biyaya ne, kuma ka ga Abanta sai ya  ce in dai kana sonta bata da miji sai kai “

Diro masa maganar ta yi hakan ya saka shi yin dan tsai yana kallon mama kafin da hannunsa ya nuna kansa muryarsa ta kasa fitowa sai idannuwansa da suke da ja da ya wara a kan mama still yana mai nuna kansa

Mama ta sauke ajiyar zuciya ta gyada masa kanta tana kallonsa a sanyaye ta ce” ko da ta ce ita bata so bai saurareta ba “

HISHAM gaba daya ji yake iska na neman masa kadan bayan wajen da wadataciyar iska ga sanyin AC na busawa

Da sauri ya mike ya yi cen ciki, ofice din doctern nan da suka shiga dazu ya shiga da sauri ya maida kofar ya rufe ya ringa kai kawo yana dan fifita wajen hancinsa yana rintse idannuwansa

Sai da ya cire farar rigar likitocin dake jikinsa ya bale botiran rigar sannan ya samu ya iya sauke numfashinsa yadda ya dace

A hankali ya dora jimkakun hannayensa saman table din nan ya lumshe idannuwansa kansa sade, ya kasa yarda da wadinnan kalaman da suka soki kunnayensa, fatansa Allah ya sa ba mafarki yake yi ba, haka kuma Allah ya sa a cikin maganar ta bata so din cen wasa ne, dan ya kula iyayen nasa na son yin wasa da rayuwarsa a cikin yan kwanakin nan

Buda kofar da aka yi aka shigo ne ya saka shi dan dago jajayen idannuwansa ta madubun dake jikin tagar ofice din ya zuba dubansa dan gannin ko waye

A hankali ya kuma maida duban nasa kasa sai kuma lokaci daya ya juyo da sauri ya damki hannunsa muryarsa wani iri ya ce” Mafarkin ne ko? Mafarkin ne? Me yasa? Me yasa ba zan daina wannan mafarkin ba? Ka ga fa ni ba shaye shaye nake ba”

Kader ya sakar masa murmushi yana kallonsa ya ce” Mama ta kirani, Hisham ba mafarki kake ba, Allah ne zai cika maka burinka domin da ka kai goshinka kasa zabi ka bashi a kan wannan matsananciyar soyaya taka duda kana taketa kana daneta, ka ga sai ya zaba maka Hisham alkhairin ce, soyayarku alkhairi ce”

Ajiyar zuciya a jere a jere yake saukewa, sai kuma ya ce” Wai cewa ta yi bata so in ji mama? “

Kader ya jinjina girman so idan ya yi wani rikon, a sanyaye ya ce” Ni tunda aka ce ta ce wai babanta ne kai na ce ya dace ka binciki kwakwaluwar, aman kuma wa ya sani ko Umarun take so? “

Hisham da gabansa ya buga yana kallonsa ya ce” Kader baka so na? Me na yi? “

Kader ya turo bakinsa ya ce” Ka ga ka sakeni Hisham, ni wannan abin ya fara bani tsoro rabonmu da mu yi rigima har na mance, ji wai bana sonka yo Aisha ce ni ko Billy? Ni kam kar ka tsoratar da ni na sakawa raina ko dai mala’ikun mutuwa sun shafaka ne kake kara zama wani kalau da kai ?”

Alhamdulilah Allah ya dawo da ni, Alhamdulilah jiki da sauki, in sha Allahu zamu dora daga inda muka tsaya, du ranar da ba posting to fa aure yakin mata ne zai hana sai ko jiki da jinniπŸ€£πŸ€£πŸ€£πŸ€£πŸ€£πŸ€£πŸ€£πŸ€£πŸ€£πŸ’ƒπŸΎπŸ’ƒπŸΎπŸ’ƒπŸΎπŸ’ƒπŸΎπŸ’ƒπŸΎ

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like