DUK NISAN JIFA 45

Advertisement

 

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

          *DUK NISAN JIFA*

           _(K’asa zai dawo)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

            _RUBUTAWA_

               *SAJIDA*

Advertisements

        *SADAUKARWA*

                   *GA*

           *MASOYA NA*

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🀝

  β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ 

Advertisements

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                            45

A fili kuwa sai ya mike a hankali da ita ya nufi wajen da akwatinta take ajiye

Hijab din dake sama ya dauka ya saka mata kafin ya kama hannunta ya juya da ita a hannunsa

Cikin nutsuwa suka fito daga dakin suka zo wucewa da wajen su mama dake zaune wannan karron daga ita sai tati tati ta dora kanta a gefen kafadarta tana ta shahsekar kuka maman na share mata tana mata magana kasa kasa

Sosai ya ji ba dadi a kasan zuciyarsa, har ya so ya duka a gabanta ya rarasheta, sai dai ya tabata Allah ya fito mata da wannan lamari a yanzu ne dan ya nuna mata cewar komai yadda ta kai da tsara rayuwarta da son kanta shi ke juya mata rayuwar a lokacin da ita kanta bata sani ba, hakan ya saka a sanyaye ya ce” Mun tafi mama “

Mama kai kawai ta iya gyada masa sam batama san ina suka tafin ba har ya fice Aisha na biye a bayansa

Sunna fita mama ta kuma rike hannunta ta ce” Dan Allah ki kwontar da hankalinki Zainab, ke kin san cewa namiji na abinda ya ga dama a lokacin da ya ga dama, ban san irin tsakaninki da mutumen nan ba, ban san irin yardar da kika bashi ba, abinda na sani shine a yanzu ke ba yarinyar goye bace, ban san irin rayuwar da kika yi bayan rabonmu ba, abinda na sani shine ko wace irin rayuwa ce kin yi wace ta nuna maki cewa mafi yawancin mutane na aikata aiyukansu na yau da kulun bisa son zuciyarsu da abinda zai gyara su, wasu kan dalilin da ya dace a dube su, wasun kuwa sunna yi ne dan jin dadinsu, bana so kan wannan ki sakawa kanki rashin lafia, bana so ki saka abin a cikin zuciyarki har ya jaza maki rashin lafiar da zata damemu baki daya Zannub”

Zainab ta lumshe idannuwanta hawaye masu zafi suka shiga biyowa kuncinta tana kallonta ta ce” Aunty, ina bashi da buri da ya fi HISHAM a duniya? A ranar da na haihu kuka da hawayensa ya yi haka yake jijiga sannan ya furta min cewa a duniya bayan mahaifiyarsa bashi da wani farin cikin da ya kai Hisham da ni wace na kawo masa Hisham duniya, Aunty, dama akoy abinda ya fi mu? Ta yaya ya iya tsara mutuwarsa ya bacewa duniya? Ta yaya ya dawo cikin kasar nan ya zauna ban taba sani ba? Ta ina ya samu duka wannan? “

Mama ta sauke ajiyar zuciya jin tati ta bude bakinta a sanyaye ta  ce” Kamar yadda na fada maki wani lamarin kan zuwa aya hadasa tashin hankali mai girma haka ne, tabas mahaifin Hisham bai barshi dan wani abin ba sai dan girman umarni da soyayar uwa a kan yaronta, Mohamad kharibullah ya tafi wajen wannan yaki, hasalima da shi aka yi, su su uku suka rayu sannan cikin ikon Allah yana cikin hayacinsa, shi ya yarda galarsa da sunnansa a wajen matatun da kuma wa’inda aka koma sannan ya bar wajen, ko gwamnati bata san da yana raye ba haka aka salace shi da iyayensa wa’inda su kansu basu san da hakan ba, Zainab umarni ya bi na mahaifiyarsa a lokacin da ya kai mata labarinku, ranta ya bace, kololuwar bacewar da ta masa kwakwaran kashedi da rantsuwar mugun baki idan bai bi umarninta ba cewar ya sake ki, ya fita a harkar yaron domin duka duka aurensa bai yi jimawar da har zai wani fara hangen wasu ba, ita kuwa idan ba balarabiya ba ba zata taba yarda da wani jinsi ya zama tsatsonta ba!, wannan dalili ya saka shi bata na watani, har sai da kika bar gari ya dawo ga iyayensa , a nan suka daga suka bar kasa dan kar a gane cewar Balarabe na raye, sun jima a kasarsu ta larabawa kafin su dawo, domin a nan komai nasu yake, sun rigaya sun gina rayuwarsu a nan, uwa uba irin da suka bari wanda ya zame masu daya kwalin kwal domin bayan matar tasa an kuma aura masa wasu biyu shiru ba haihuwa bayan su dukansu lafiarsu kalau”

Da sauri Tati ta kara roke hannun mama a dan firgice ta ce” A ina kika sani, yaushe kika sani? Wa ya fada maki? Kin jima da sani ne? Ashe kin san du haka kika zuran ido? Me yasa kika kyale ni ina hauka Aunty? “

Mama ta dan ja hannunta dan ta damke shi da karfi ta ce” Ta yaya kike son na sanar maki bayan number da zan iya samunki ta ita kin yi blosck dina? Bara ki ji, a lokacin da maganar fitarsa waje ta fito abin ya bani mamaki, ba komai ya saka haka ba sai irin makudan kudin da aka ambata cewar gwomnati ta bashi, tun ban saka rai da zai samu ba har na ga abu na tafia ziryen ziryen ba gargada bayan an saba manya na danewa ko su raba tsakiya, kamar da wasa albashinsa ya fi na da yawan masu kudin dake aikatuwa sunna dauka jinna, a hakan ya sa hankalina ya tashi, na kasa zaune na kasa tsaye , shi kansa na titsiye shi kan yaya haka

A nan ne ya ringa nema min hanyar da zata sada ni da shugaban makarantarsu,

A kadan mun dauki wata muna neman kadaituwa da shi kafin muke samu, a ranar na masa bayanin ina son karrin bayani domin ba zan dauki yarona na tura shi kasar waje karatun da ban biya ba ban ga halin biya ba harma a ringa bashi albashi, a lokacin ne ya dubo takardunsa yana dubawa ya bamu labarin wai da HISHAM MUHAMMAD KHARIBULLAH? , ai mahaifinsa MUHAMMAD KHARIBULLAH shi ne a kan komai nasa, a lokacin ya zuba zunzurutun kudade na kula da shi sannan shi ya shige masa gaba a harkar fita hakinsa da kwazon yaron ya saka hankalin manya karkatowa kansa”

Mama ta dan sauke numfashi dan ta ja sheda a lokacin ta ga ashe mahaofiyqr Aisha zaune take tana karkada kafa tana kallonsu, ta dora fa fadin” Na firgita, na tsorata, na ji mamaki a lokacin da aka samu da kyar muka samu ganninsa, mahaifin Hisham naki shine ELHAJ MUHAMMAD KHARIBULLAH , mai kampanin madarar BALARABE, mai gidajen sabulai na ruwa da na omo, mai kampanin magi, shine wannan hamshakin da ganninsa aiki ne ga sauran duniya, wanda bayan dawowarsa ya komawa gwamnatinsa sanadiyar yanzun ya zamana mutuncinka aljihunka hukuncinsa na wara biyu kawai ya yi a gidan yari shima dan su tabatar idan ba aiko shi aka yi ya yi binciken kasa ba, bayan sun yarda da hujojinsa da na mahaifansa suka so bashi kaki, a nan ya kiya domin dama ya shiga aikin soja ne dan ra’ayi, sai dai kash, jinnin dake gudana a jikinsa shi yake gudana a jikin yaron cen, ba yadda bai yi ba dan ya saurare shi aman HISHAM ya kiya, karshema a cen ya baro ni sai kawo ni aka yi wancen gidan,

Ban taba sannin yana da zuciya haka ba sai da ya ce ya ajiye karatun ba zai yi ba, idan na takura zai bar min garin,

A lokacin na yi anfani da damar nan na ringa cusawa Bilkisu kaunar likitanci a zuciyarta, domin shi burinsa idan ya je ya zama soja baban soja ya gaji mahaifinsa sai dai tunda ya ga mahaifin nasa a raye shima ya tafi ya barshi ne sai kawai ya ce shi yanzun bashi da wani burin zama soja, ba zai zama ba,

Wasa wasa na samu ta dauki lamarin, ta nace har zazabi take tana ce masa hammana ina son likita, ina so na zama likita kuma idan na girma zan auri likita,

Ya sha maimaita maganar idan ta girma zata auri likita, ni dai ina gefe ina adu’a ina nasiha

A ranar da suka zo har gidan cen da tsohuwar kakarsa a ranar na ga taurin rai, domin ba yadda bamu yi ba ya dubeta aman ya kiya, karshema a gabansu ya ce shi mahaifinsa ya rasu, hakama danginsa, su barshi ya huta bashi da wani abin so a tatare da su!

Mahaifinsa na kallonsa yake tambayarsa ina mahaifiyarsa ne?, a gaban kakar ya ce “Ta ce na daina damunta da kira, na tafi na nemi na kaina itama ta kanta take, ta bara mana gida mu yi tallah mu ci abinci! Ka ga wannan……….ya nuna ni ya dora da fadin” itace uwata! , ita na sani, ita ke saurarena, ita ta san wahalata, ni dai ita na sani, itace uwata kuma ubana! Idan umarni ne nata zan bi domin ban yarda cewa ba itace uwata ba sai dan abu daya jal da nake da buri a rayuwata!”

Mama ta dago dubanta da idannuwanta da suka cika da hawaye ta ce” Ban taba jin haushinki irin ranar ba, sai naga ribar me kika tafi ci ta duniya? Shin kin manta ana haihuwar sarki da shugaban kasa ne ba shuka su ake ba? Shin kin manta cewa idan har arzikin ne ba sai kin je kin zubar da ahalinki ba in dai kina da rabon yinsa zaki yi? ZAINAB walahi sai na ji bana jin haushin mijinki dan ya yiwa mahaifiyarsa biyaya , a nan na yi anfani da damata a kan yaron nan, na yi masa umarni ina zubar da hawaye , na masa umarnin da baya so, na saka shi amsar abinda ya ce ba zai amsa ba, ya amsa yana hawaye yana cije lebensa jikinsa na rawa, a nan ne na yarda da soyayar da kika haramta bayan  Allah ya halata, domin yana kukan nan tana farawa ya ringa share hawayensa yana sakin zancecekun da sam baya cikin hayacinsa, yana fada mata ya daina ba zai kuma ba ta yi shiru zai je ya zama likita ya dawo yana sonta ta daina kuka”

Mama ta share hawayenta tana kallon Tati dake kuka kashirban ta ce” Dangi sunna da daraja, da yawa idan suka bada baya sai dai su dawo su birne nasu, wata tafiar mai daraja ce, watan kuwa asara ce, baban tashin hankalin tafiar da zaka yi ba uwar ba ribar, shi yasa wani sa’in yawon bashi da anfani, ZAINAB lafia tana da anfani a jikin dan adam, duniya kuwa na cike da abubuwan al’ajabi , a jiya na maki magana kan Bilkisu ba ita ba yaron cen ko? Na yi ne dan na dan zaburar da ke, kuma na ga ya yi anfani domin har kin gane yarena! A yanzu maganar da zan fada maki ita ce *AUREN BILKISU DA YARONA RANAR JUMA’A DA SAFE, KODA NA MACE NE A DAURA SHI KAFIN A KAINI MAKWONCINA KODA BILKISU TA MACE NE A DAURA MATA SHI IDAN ANA YI KAFIN A BIRNE TA, IDAN KUWA BAKI YARDA BA KI JA KURTU DA KAMBUNKI NA UWA MAHAIFIYA A KAN YARON CEN NA GANI!*”

tana gama fada ta mike ta bi ta gefen da mahaifiyar Aisha ke zaune ta gama cika ta yi pam tana kallon mama da wani irin kallo har ta bacewa ganninta

Tsaki maman Aisha ta ja  ta sauko kusa da Tato dake dan girgiza kai tana hawaye tana sharewa ta zauna tana kallonta ta ce” Zainab, a duniya baki da matsala sai wannan matar da yarta! Wai dama haka take maki wannan abin aman a gaban danki kamar wata zata hadiye ki tana rarashinki tana janki a jiki? Ki duba ki ga gidan nan yanda yake da girma da dakuna da arziki a cikinsa, aman kema wace ta nakudo yaron cen ta haifo shi baki da wani iko da komai , komai sai an baki yadda nake da daki daya haka kema kike da daya a gidan nan, kin ga idan baki yi da gaske ba fa tana iya korar ki a gidan nan domin idan har kika yarda kika bari aka aurawa Hisham Bilkisu kin janyowa kanki matsala, dan malake yaron nan zasu yi sai yadda suka so da shi walahi ki kiyaye!”

Tati na kallonta ido cikin ido da wani irin kallon da sam bata gane meye ma’anarsa ba, sai dai gannin kamar tatin ta tsaida kukan nata ta kuma tsura mata ido tana kallonta ya sakata gyara zamanta ta ce” Ke kike da iko da shi, ba wanda ya kaiki dama a kansa, ba wanda ya isa ya saka shi abinda kika hanna shi yi du duniya kama daga mahaifinsa har ita wannan, ta yaya zaki zauna bayan cin amana da rufe maki maganar mijinki wanda yake daya daga cikin mutun dari biyu na manyan kusoshin duniya baki daya sannan a zo ana maki wani dadin baki da magangannun da basu da kai basu da kafa a kuma maki gargadi kan kar ki yarda ki hanna? Idan kika hanna me zata iya yi maki? Ina ji ba haihuwarki ta yi ba, yau mahaifiyarki kun rabu lafia bale wani ya maki wani abin ya kama ki, dan haka ki tashi ki tsaidawa kowa ruwan miya a gidan nan a bar maki tunkaho ke da  gidan danki!”

Ta karashe tana dan daga muryarta dan mama ta jita domin ita yanzu banda haushin maman nan ba abinda take ji, ina dalili mata da shegen iya yi gashi ta isa da yaron domin daga ta fada masa yake hawa ya zauna daram a kan maganar, uwa uba abinda ya fi daga mata hankali jin wai ashe Hisham dan MUHAMMAD KHARIBULLAH daya cilo ne? Bayan nasa arzikin ashe gada ya yi? Ina zata iya bari a yiwa Aisha kishiya? Ai su yanzun likafa ta tashi idanma ana so a sauke mijinta a aiki basu da faduwa domin su suka dace da siriki!

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like