Advertisement
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K’asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
Advertisements
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
Advertisements
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
48
Mama na fitowa cikin shigarta ta shada kalar orange an yi mata zubi tun daga wuya har kasa na kore da fari ta sha yar madaidaiciyar sarkarta ta sha daurinta daidai misali da abubuwan hannunta ta fara cin karro da Tati tsaye da mahaifiyar Aisha
Tati ranta a bace ta ce” Saurara Hajia, wai me kike so da ni ne? Bari ki ji na fada maki idan baki san yaren shiru ko kawaici ba, gidan nan da kike cewa gidan dana ne dan nawa shi ya ginawa mamansa shi da sunnanta, idan ita bata fada min ba dan kar hankakina ya tashi a tunaninta ya jima da ja min kurtu a kan na kiyaye hakan, bari ki ji na fada maki a yanzu ke kadai ke kirana da uwarsa kuma ina jin kunyar hakan, haihuwarsa na yi aman uwarsa yayata ce, na ajiye aurensa da yarki a matsayin *MATAR MUTUN* (Na aminiyata Samira Harun, idan baka bi ka nema ka karanta domin dadi ya barka),
Ke baki san kawaici ba? Ina mai sanar maki kaina ya dauki zafi shi yasa na kasa tambayarki shin yaushe zaki koma garinku ne? Na ga dai ya ji sauki harma ana shirin sakinsa mijinki sau nawa yana maganar komawarki kina cewa sai ta tare ai ta tare din ko? Nima ina zaune ne kan alfarma ba wai dan na isa ba, ki kiyayi sakani yiwa yayata rashin da’a, ko wanda na mata a baya ya isheni aya!”
Da mamaki hajia ta ce” Aman Zainab baki da wayau ban sani ba? Ni kike fadawa haka yau kuma? Shin kin manta wacece ni? Kin manta a karkashin mijina kike aiki? Waye ya baki damar da zaki fada min magangannu haka? “
Tati ta yi murmushi ta ce” Dadina da wanda ya tsinta bai iya ci ba, natsalar yiwa matsiyaci aiki kennan, matsalar rabewa a karkashin innuwar wani dan shan iska”
Tana gama fada ta juya itama cikin shigarta irin ta mama ta nufi waje
Da sauri mama ta daga kafarta dan dakatar da ita, sai dai wanda ya shigo ne ya saka su dakatawa su dukansu, basu gama karewa yannayin fuskarsa kallo ba mai kama da shi sai dai datijonsa sak ya shigo shima cikin gidan
A hankali mama ta ce”Tashin hankali”
Ido cikin ido suke kallon junna lokaci daya gabansu ya buga su duka biyun
Matsananciyar kunya da tashin hankali ya bayana a tatare da shi, sai dai kasancewarsa jajirtacen namiji wanda ke tsaye kan kafafuwansa sai ya dake yana kallonsu su duka ukun
A sanyaye ya ce”Asalamu alaikum ahalina”
Mama kawai ta iya amsawa tana kallon yadda tati ta yi mutuwar tsaye a lokacin da ya kara kusanta kansa da ita muryarsa still a sanyaye kamar irin yadda ta hisham ke yi idan yana cikin halin zulumi ya ce” ZANNUB shin baki fadawa yaron cen cewa abin alfahari ne ubansa ya daura masa aure? “
Makwat ta yi da busashen yawun dake makogwaronta ta ce” Baka isa ba , waye uban nasa? A sanina uban yaron nan ya jima da mutuwa dan haka baka isa ka daura auren yarona ba!”
Mama a hankali ta ce” Zaunab kin ga ku mu shiga ciki mu yi magana kina gannin mutane na kallon mu”
Aban Hisham ya yi murmushi yana kallon tati sannan ya kalli Hisham wanda tunda ya shigo fuskarsa hade ya yi murtuk bayan ya sha dakakiyar shadarsa sai maiko take ta sha zubi ta bi lafiyar jijinsa dukan jijiyoyin jikinsa sun fito radau tsabar bacin rai ya ce” Zan je na daura shi yanzu, idan da mai ja ni ba ubansa bane ya zo ya cire jinina dake jikin yarona”
Har ya juya zai fita ya ja ya tsaya sakamakon gannin mama ta yi raf da ita tana maganar ta wuce su shiga
Wani murmushin ya kuma sakar mata ya fita abinsa
Daurin auren da aka yi niyar daura shi bayan salar juma’a sai gashi ya samu karfe tara na safe a lokacin da al’uma ke cike a anguwar dan ba’a fara shiga masalaci ba duban al’uma suka shaida daurin auren HISHAM MUHAMMAD KHARIBULLAH da BILKISU JAURO bisa sadaki mai daraja da adu’o’in manyan malamai
Shiru ya yi kansa a sade tunda aka ringa shelar daurin auren a wajen da ya zauna, manyan likitoci, manyan yan kasa yan kasuwa ne, manyan mutane ciki kuwa harda mai Martaba sai busa ke tashi tamkar dan sarauta
A hankali ya dora dubansa a kan fari kal din hannun da ya dafa gefen kafadarsa a hankali ya dago dubansa ya sauke a kan fuskar mutumen, MUHAMMAD KHARIBULLAH cikin shiga ta alfarma fuskarsa mai annuri sunna kallon junna
A hankali ya cire hannun daga nan ya dan daki kirjinsa ya ce” Mijin Bilkisu ko sai na samo maka maganin zahi ne zaka mike daga zaunen nan uwa filo bayan jinnin larabawa kake?”
A hankali ya lumshe idannuwansa yana gannin yadda KADER ke tsaye da wasu mutun hudu su dukansu cikin shiga ta aikinsu sunna kakare shi domin in dai tarro zai shiga mutun biyar ne ke tatare shi ya ga yadda mutane ke yi masa fatan alkhairi daga nesa sai wa’inda ya zama wajibi su gaisa da shi ake bari su karaso inda yake
A hankali ya budi bakinsa dan ya ce a daga shi, domin kwata kwata ya kasa jin motsin kafafuwansa a jikinsa gani yake mafarki yake da wannan rana wai ga abansa ya daura aurensa da Bilkynsa? Sai dai wayarsa da ta ringa tsuwa karfi da yafi ga kuma ta kader ya saka shi zubawa Kader ido
Ta yannayin da ya amsa ne ya gane ana tambayar ky din falonsa ne dan a kai Bilkisu cen wai bata da lafia
Bai san ta yaya kafafun suka samu karfin dagashi ba, sai mikewa ya ga ya yi tsaye kan kafafuwansa sannan a hankali ya juya ya bar abansa nan tsaye yana murmushi yana binsa da kallo da godiya ga Allah wai wannan namijin nasa ne, dansa ne, jinninsa ne ya nausa cikin mutane su Kader na tatarewa ya shige ciki
Bai tsaya ko’ina ba sai falon Mama, a nan ya samu su bakwai zagaye da ita tana kuka cen cikin makogwaronta ta ce” MAMA kar a daura min auren nan, mama baya so na, nima bana son sa kar a daura auren nan mama ki hanna dan Allah”
Mama dake cike da takaicin ta yadda Bilkisu ke wannan bori bata ko jin kunyar kakarsa da Tati da mutanen da suka zo da su ta ce” ZAINAB idan baki barni na daki bakin tsiwar yar nan ba zan kai maki duka, wai meye haka kina ganni tana yiwa mutane iskancin nan ba zaki tsawatar mata ba? !”
Da sauri ya daga kafafuwansa dake rawa rawa ya karasa wajen
Irin yadda jikinta ke rawar sanyi ga kakarsa rike da ita tana dan bubuga mata baya irin rarashin nan, ga Tati na tsaye da waya ta kare mama dake son dukanta ga wasun tsaye wa’inda shi baima san ko su waye ba kowace ta sha kwaliya irin ta larabawa sunna shan yare ya rintse idannuwansa jin kalmar ki daga bakinta na kuma fitowa
A hankali ya ce” Ku barta, ku saketa ku fita dan Allah”
Cike da takaici mama ta fara juyawa tana al’ajabin irin rikicin da ranar nan ta zo mata da ita
Sauran kansu da daidaya du suka fita, Bilkisu kuwa tunda ta ji muryarsa sai ta yi gum fa bakinta aman jikinta na rawar sanyi haka kuma idannuwanta rintse
A hankali ya rage tsayinsa yana kallon rufar dake jikinta, dangalgal a falo saman kafet tana turmuka kokowa da iyayensa
A hankali ya saka hannunsa ya yaye rufar a yanzun bakar rigar ce kawai a jikinta sai kamshin turaran wutar da ya ki barin jikinta gaba daya domin ko wankan ba’a samu an yi ba aka tashi da rigingimun nan
Irin yadda ta rintse ido yake kallo, a hankali ya ringa bin dogon karan hancinta da ido har ya sauke duban nasa a irin dunkulewar da ta yi
Sai da ya cije lebensa na kasa da dan karfi sannan ya bude bakinsa muryarsa a dan dake ya mika hannunsa yana son jin zafin jijinta ke sakata rawar sanyin nan ko meye lokaci daya kuma ya budi bakinsa ya ce” BILLY AM…..” irin yadda ya so maganar ta fito a dake aman sai muryarsa ta cuce shi ta fito cen kasa sannan ya ja sunnan shi kansa sai da tsigar jikinsa ta tashi bale ita dake cikin bege da bacin rai da tsoro da firgici
A hankali ya janye hannunda jin yadda jikinta yake da zafi kafin ya dora hannunsa gaba daya ya mikar da ita tsaye
Abin rufar ne ya fadi kasa, shi kuwa da karfi ya bata wata wuwuyar runguma, irin rungumar da kana gani ka san an jima ana son aikatata ba’a samu ba sai yanzu, runguma ce da sai da ta sakata bude idannuwanta da sauri tana dan sakin kara , a tsaten da suke tsayinsa ya kere nata fadin jikinsa ya kere nata aman a haka ta jita lufluf cikin kirjinsa wani irin abu na ratsa ilahirin jikinta, hakan ya jara hadasa mata rawar jiki da digar hawaye
Muryarsa a shake ya budi bakinsa ya ce”
ππππ i’m backπππππ
GIPHY App Key not set. Please check settings