DUK NISAN JIFA 49

Advertisement

 

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

          *DUK NISAN JIFA*

           _(K’asa zai dawo)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

            _RUBUTAWA_

               *SAJIDA*

Advertisements

        *SADAUKARWA*

                   *GA*

           *MASOYA NA*

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🀝

  β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ 

Advertisements

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                            49

Muryarsa a shake ya budi bakinsa a sanyaye ya ce” Kin ga fa yadda kuka ke mayar min da ke, dubi yadda jikinki ya dauki zafi kuma idan na ce allura ki tubure ki kiya, haba Mai gado me yasa kike son zame min rigimamiyar karfi da yaji ne?,  yanzun ni ne ake yiwa kukan ba’a so har haka?”

Bilkisu idannuwanta ta rintse gam domin tunda ya fara maganar a kunnnenta bai sasauta mata rikon da ya yi mata ba, gaba daya mamaki, tsoro, kunya ta hanna mata dago idannuwanta bale har ta iya dubansa, irin yadda zuciyarsa ke bugawa da irin yadda hannunsa ke dan rawa ya sakata kuma lumshe idannuwanta ta rasa ina zata tsoma ranta

A hankaki ya dago habarta yana kallon kyakyawar fuskarta ya ce” Zaki min alfarmar dakatar da kukan nan haka?, kin ga an daura ba maganar kina ko so na, Billy auren nan da aka daura wanda ya busa min numfashi kawai ya isa ya kashe shi ta hanyar kashe ni, ba zaki gane ba, ba zaki taba fahimta cewar kalmar so na zuwa ne idan da hali, nw i bg u ki saurara min haka kin ji?, kin ga fa wai rigima ce ta barke tsakanin su kin ga mamana ta ja su bangarena, da wane zan ji?”

Bilkisu ta kuma lumshe idannuwanta tana sauraronsa tana kuma kallon kirjinsa duda a rufe cikin rigar shadarsa mai ruwan sararin samaniya hakan bai hanna mata gannin fadinsa a haka ba

A hankali take binsa sakamakon jan hannunta da yake cikin nutsuwa ya yi dakin mama da ita

Saman bed ya dorata ya gyara mata kafafuwanta a sanyaye ya ce” Ina zuwa “

Ita dai bata da wani ikon da gaban jikinta da tunaninta har sai da ya fice ya bar dakin

Huci ta sauke mai zafi a hankali wani hawaye mai dumi ya fito daga gurbin idannuwanta, yannayin da take ciki mai girma ne, godiya take tiwa Allah na gannin wata igiyar aure ta hau kanta, godiya take yiwa Allah na gannin igiyar wadda take kauna ce a saman kanta, sai dai sam jikinta ba karfi idan tana kallon yadda yake aikatuwa da jikinsa da aljihunsa a kanta aman bakinsa bai furta mata kalmar nan ba, shin me tasa wasu mazan ke tunanin wai ba sai an fada ba, fadan ya zama kauyanci? Wannan shirme kennan fada ba zai taba zama kauyanci ba domin da da hali a kulun ka furtawa matarka wannan kalma jadadawa ne da tunatarwa hakan zai kara dankon zaman amana soyaya, da tausayi

Ta tabata du inda su Laila suke sun kusa zuwa, su kadai take jira su kamata ta mike dan sosai take jin zazabin nan a jikinta

Yana buda falonsa ya yi turus yana kallon ikon Allah, dan karamin yaki ne ake zubawa a cikin falon tsakanin mutanen nan baki daya

Mamansa ya bi da kallon tausayi wace ke zaune ta yi gurum tana kallon yadda Larabawan nan ke larabci kowace na fadin nata ga Tati gefe tana kada kafa ta daure fuska tamkar bata taba daria ba, ga Muhammad  Kharibullah na zaune yana bin matayen da iyayen da kallo hankali kwonce bai ce komai ba

Sai da kowace ta gama nata sannan Mama ta dan sauke ajiyar zuciya ta ce” A dai yi hakuri, duka abinda aka yi bai dace ba aman kuma hakurin shine ya fi cencenta”

Muhammad Kharibullah ya dubi mama ya ce” Bama wannan ba, wai ni Zannu ke yiwa rashin kunya? Ke zannu nine na mutun? Ai sai ki saurareni ki min uzuri ko? Da kike maganar idan na fito a mutun na fada maki gaskiyar lamari ke din nan ke ce zaki yarda ki rabu da ni bayan mutuwar da kika yi a sona? Kin ga mu yi maganar gaskiya ni bana son abinda zai daga min hankali, kin ga yaron nan ya kulanima na kasa samu yaya kike so na yi? Kin manta shi daya tak Allah ya bani ne? Ko mahaukaci dai ya kalli HISHAM ya kale ni zai gyada kai ya ce ni ubansa ne, kin ga ki daina abu kamar wata karamar yarinya mu fuskanci junna a yafewa junna dan nima kin min laifin kyaleki ne na yi, domin laifin da kika yi min kika yarda min yaro kika tafi idan da biyaki zan yi sai mun ga bakin junna a gidan nan!”

“TO mu gani mana Muhamadu?, ka ga ba ka gama abinda ya kawoka ba? Ka tashi ka kwashi nunanun ranarka da wace ta saka ka watsa mu ku yi tafiarku, da kake maganar na yarda yaronka ai ni ba cewa na yi na mutu ba, kuma wajen yayata na kaishi inda na san idan bai ci ba sai dai in bata ci ba! Kuma tarbiya irin nagartaciya ya samu, dan haka ka je ka kara gaba idan kana so daga nan ka wuce kudus!”

Mama ta ce” Toh fa “

HISHAM ya tabe baki a hankali ya idasa shiga ya ratsa su ya wuce ciki hakan ya sa du suka raka shi da ido kuma hayaniyar ta yi duf

Yana shiga cikin gagawa ya cire manyan kayan nab ya cenza wasu ya dauro alwalah ya fito ya dauki abubuwan bukatarsa ya fito daga dakin 

Da mamaki ya kalle su gannin har yanzun da alamun shi suke jira ya kuma tabe bakinsa ya zo zai wuce ya ji muryar mahaifinsa na fadin” Kuma wucewa zaka yi ba zaka saurareni ba Nur?”

Bai yi niyar tsayawa ba har ya kusan fita a tsakaninsu ya ji muryar tsohuwar na gargada ta ce” Haba mijin, ka tsaya ka dube ni shin bana baka tausayi tsufa ya kama ni so kake har na mace baka yafe min ba?”

Bai kuma yi niyar tsayawa ba hakan ya saka mama fadin” HISHAM”

Turus ya yi daga tafiar da yake, mama kuwa a hankali take nazartar yannayinsa, muryarta a sanyaye ta ce” Baka ji ana yi maka magana ne Hisham?, me ke damunka nake gannin kamar hankalinka a tashe?”

A hankali ya juyo inda take zaune ya shiga takowa cikin nutsuwa  har ya karaso kusa da ita , muryarsa ya rage sosai wanda hakan ya saka kowa kashe kunne da kuma zuba masa ido ya ce” Mama, bata da lafia sosai baki ji jikinta ba ya dauki zafi sai rawar sanyi take, kuma kin ga bata son ganina ban san yaya zan yi ba, walahi mama ina tsoron wannan sabuwar Billyn kin ga dai tawa bata fushi da ni, ita kuwa tun ranar nan da ta ganni na fito din nan shikenan sai nake fuskantar rashin yarda, rashin tausayina a tatare da ita”

Mamama ta rage muryarta sosai tana kallonsa ta ce” Kar ka biye mata, ka tsawatar mata idan kuma ta so kawo maka raini ka tatakata ta yadda zata gane kai din ba sa’anta bane yayanta ne kuma uba a gareta bale yanzu da ta dauki matsayi na matarka ta yi maka biyaya ko ta kona kanta ne!”

Dan girgiza kansa ya yi a hankali ya rike hannun mama ya ce” Na tatakata na shiga ina kuma? Ni dai ki koya min yadda zan bata hakuri ta daina fushin nan”

Mama ta ringa bin mutanen dakin da kallo domin cikinsu daya ce kawai bata jin hausa fa kyau itama tana tsintar wasu kalaman duka hausar ce bata ji sosai kowa ya kashe kunne ya zuba masu ido yana sauraronsu balema kakarsa wace har dan dukowa ta yi ta yi masu kuri da ido

Mama ta ce” Wannan itace shawarata idan ka yarda ka lalabata ka santa sarai kamar ka izata ne ba zata gane yarenka ba ni dai na fada maka”

Baki ya dan tabe a hankali ya ce” To na tafi”

Mama ta ce” Ina zaka je ne?, kana ganni zaman nan naka ne fa da Mamanka fa”

HISHAM ya ce” zuwa  zan yi na dauketa mu tafi asibiti na smduba lafiarta daga nan na kaita gidan namu ta huta kin ga fa ta gaji sosai ga hayaniyar nan da mutane ke yi ni kam ban san me kuma suke jira ba”

“haka muka yi da mamanka daga ni sai ita muka tare abinmu, aman mu an yi mana nasiha ko zaku zo nan na maku nasiha?” Ya fada a dake abinsa hakan ya sa kuma kowa ya kale shi

Hisham ya yi dan murmushi yana girgiza kansa  ya kalli mama ya ce” na tafi mamana “

Mahaifinsa ya mike tsaye wannan karron karara tashin hankalinsa ya kasa boyuwa yana kallonsa muryarsa a sanyaye yanzun ya ce” Kai baka yafiya ne?, dan Allah ina rokonka ka sasauta min haka Hisham, ka duba ka ga tun kana dan yaronka na bayana gareka, a tunanina zaka fada jikina da farin cikin bayanuwata a gareka tun da sauran numfashinka? Hisham da uba ake ado ba da riga ba, ka sani na aikata wannan abin ne dan na yiwa mahaifiyata biyaya, sannan kafin na aikata sai da na tabatar na barka a hannun uwa mahaifiya sannan na yi iya yina na bara mata dan abinda zata anfaneku da shi kafin na rarashi mamana, Hisham shin ka manta girman uwa a kan yayanta ne ko ka manta aljanata na karkashin digadigenta? So kake na yi wasa da aljanata ne ? HISHAM a yau ba ita ba ni kaina tsufa ya fara zuwar min domin a yanzu haka ina iya rantse maka ban san kan dukiyata ba, dukiyarka, Hisham dukiyar da take da ita ta ninka tawa kuma ta dora kaso mafi girma a kanka tun bata ganka ba, ka sani kowani bawa da irin tasa kadarar da irin nasa yannayin rayuwar, ka ga fa ita ta nemi a yi haka kuma daga baya ta kasa samun nutsuwa, ka duba mamana na hawaye dan kaunarka, ka dube ni ka dawo gareni na rungumeka a jikina ka fauki dukan dukiyata ka adana domin bani da wani da zai kula bayanka , kai daya na malaka, kai daya Allah ya bani yaya kake so na yi ne? “

Hisham na kallonsa shima muryarsa a sanyayen ya ce” Ni fa ban ga laifin wanda ya yiwa mahaifiyarsa biyaya ba, ban ga laifinka ba, abinda ka yi daya ne ya firgita ni shine ka kashe kanka!, ita kuwa tsohuwar nan sai ta fada min a ayar da aka haramtawa balarabe auren wani yaren bayan nasa!, ka ga ni fa zan zo da kaina har gidan  mu zauna da ku duka aman dan Allah yanzun ka barni na je na duba lafiar Bilkisu  ka ga rigima take bata son jin komai ni kuwa hankalina ya kasa kwonciya”

Murmushi ya masa ya rage muryarsa sosai ya ce” Kaima haka kake ji ko? To Allah ya kama mana domin mace idan ta gane ana sonta bata da kirki” ya karashe yana wani kai dubansa kan Tati wace take kada kafarta har yanzun kiri take jira  ta maida magana

Tunda suka fara magana sai yanzu Hisham ya ji murmushi ya zo masa tun daga zuciyarsa, a hankali ya kada kansa ya yi gaba mama kuwa ta mike da sauri tana kallon tati ta ce” Zainab kin ji wai tafia zasu yi, kin ga mutane a cike baya jin kunyar kar a yi gaba da su? “

Tati ta kaleta ta mike tsaye tana fadin” Bara na raka su dan zan fi sakewa a cen”

Sunna kallonta ta fita hakan ya sa dole mama ta dawo ta kuma zama cikin nutsuwa ta shiga basu hakurin irin dan mirdiyar dan nata da kuma halayan kanwar tata, ta dora da fadin” zasu sake ne daga sun huce in sha Allah “

Murmushi ya yi yana gyara zamansa domin ya yi niya ba zai tafi ba sai sallar juma’a , mahaifiyarsa kuwa da farko niyarta sai ta kai amarya to yanzun abin ya lalace

Zaune yake a motar yana dan duba agogon hannunsa, Kader na gefensa zaune sai mutanen dake bashi kariya na waje tsaitsaye

Kader ya kara sakin murmushi ya kuma miko masa hannu ya ce” Kai barkarmu dai oh Allah mai iko yau Hishamu ya zama mijin Nana”

HISHAM ya bi hannun da kallo wani kayatacen murmushi ya kubuce masa a fuskarsa a hankali ya ce” Alhamdulilah “

Kader ya kara gyada kai ya ce” Kuma yanzun idan muka dauketa ina zamu tafi ko irama mun tare? “

Hisham ya kale shi, wannan barkar da ya masa fa a kadan ta kai ta goma da ya dan juya ya juyi sai ya wani ce oh Allah duniya barkarsu dai, kuma yanzun ya wani tsatsare shi da tambaya bai san abinda yake ciki bane ko meye? Bai taba yi mata biyaya kai tsaye ba sai yau da ta ce da shi ya tafi mota zata kawota aman shiru a kadan sun dauki minti talatin a zaunen nan

Hango su da ya yi ya saka shi rage murya ya ce” Ka nutsu dan Allah ka gansu fa”

Kader ya gyara zamansa yana fadin” Ban taba gannin fitsararen ango irinka ba, yanzun me zaka aikata? “

Hisham bai iya bashi amsa ba har zuwan Tati ta bude baya a hankali ta saka Bilkisu dake cikin abin rufa irin lafayar nan an luluba mata ita

Wani fitinanen kanshi ne ya yi masu salama, kanshi mai hade da na turaran wuta da na ruwa, irin sansanyan kanshin nan ne mai nutsar da zuciya , sai tsintsiyar hannunta fara kal da bata dauke da zanen kunshi ko digo daya da ta fitar a hankali muryarta cen ciki ta ce” Inata, idan mun  je cen din ki ce ya dawo da ni da wuri dan Allah “

Tati ta kali Hisham da ya lumshe idannuwansa yana ta kokowa da zuciyarsa da numfashinsa ta ce” Yauwa Hisham idan kun je hayaniyar ta rage sai ka dawo da ita dan bata jin dadin jikinta na ce ta zo ka kaita cen wani wajen ta dan huta kafin taro ya watse “

Bai iya amsawa ba Allah yana gani bakinsa ya masa nauyi, sai kader ne ya amsa yana mai tayar da motar yana gumtse dariyarsa

A hankali ya dauki hanyar asibiti, cen kasa kasa Hisham ya ce” Ka tsaya pharmaci na sayi allura mu wuce gida ba zan iya zuwa a sibiti da ita ba”

Kader ya mulmula kansa ya ce” A kan wani dalili fa? “

                Na yi jiran matar mutun😭😭😭😭😭

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like