DUK NISAN JIFA 55

Advertisement

 

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

          *DUK NISAN JIFA*

           _(K’asa zai dawo)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

            _RUBUTAWA_

               *SAJIDA*

Advertisements

        *SADAUKARWA*

                   *GA*

           *MASOYA NA*

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🀝

  β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ 

Advertisements

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                            55

A hankali ta bude idannuwanta da suke da ja dan irin tsabar cin kukan da ta sha kama daga jiya zuwa yau tana kallonsa, 

Idannuwansa ya kuma lumshewa a hankali ya ce” Ki yi hakuri, kin ji? “

Bilkisu ta yinkura a hankali ta tashi zaune tana kallonsa, a sanyaye ta ce” Na hakura “

A bayane ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta

Bilkisu ta ce” Ina ne dakina? Ina ky? “

Hisham dake kallonta a sanyaye ya ce” Babu dakin ki, babu dakina sai dakin mu, a kowani daki shirin na mutun biyu aka yi a wane kike so mu kwana? “

Sai da gabanta ya buga , tana matukar girmama wannan rana sai dai  irin yadda aka nuna mata bata da wata daraja sai abin ya mata sanyi, du take daukan komai a baibai irin  kamar karya

Mikewa ta yi da kyar tana kallonsa ta ce” A wane kayana suke? “

Shima dake gannin yannayinta kamar bata huce ba ya saka shi mikewar yana kara kallonta ya ce” Sai nake gannin kamar baki huce ba Billy am”

Bilkisu ta kakaro murmushin yake ta yaba masa ta ce” Na huce Hamma am “

Ajiyar zuciya ya kuma saukewa ya ce” A kowani daki akoy kayanki, a wancen ne kawai aka saka iya na barcinki kadai ky din kuma sune jikin yar lokar cen “

Kanta ta gyada , sannan ta juya a nitse ta je ta dauki kys din

A hankali ta gwada a dakin dake kusa da ita, tana murdawa ta ga ya bude, sai ta shiga gwada sauran dakunan da ky din nan kadai dan gannin idan ky daya na iya bude dula dakunnan, nan ta ga kowani daki da ky dinsa hakan ya sa cikin nutsuwa ta dawo ta bude ta shige sannan ta maido kofar ta kule da ky din hannunta ta barshi a jiki

HISHAM dake tsaye ya ji karan rufe kofar bai kawo komai a ransa ba har ya dauki  kusan minti goma shiru ba motsi hakan ya saka shi mikewa ya karasa kusan kofar ya shiga kwonkwasawa

Bilkisu dake zaune kasa jikin gadon ta kurawa kofar ido, bata iya amsa shi ba har ya kara bugawa ya ce” Wai me kike haka ne? “

Bilkisu ta taso ta zo kusa da kofar ta jingina a hankali ta ce” Dakina na shigo, barci zan yi Allah ya bamu alkhairi”

Ido ya tsurawa fuskar a sanyaye ya ce” Haka kike son gina mana rayuwa? Mata na wawa sunna kama mazajensu sunna rikewa da karfinsu ko a yi sama ko a yi kasa ke so kike ki fara mana da haka?, koma me na maki ai na baki hakuri ko? Wai menene a ciki dan na jewa matata? Inace halalina ce Aisha ba haramun dina na jewa ba?, kuma abin nan kece kika kunna shi kamar yadda kika saba , kuma shikenan sai abin ya zama fitina? “

Bilkisu ta hadiyi dadacen abinda ya tsaya mata, kennan dai ba zai yarda cewa rana ce special a gareta, abu ne da yake sabo a gareta, kai koda an rakota ne idanma ba ranarta bace ta ji irin haka ai sabon shiga ce ita bata san dawan garin ba bale har a ce za’a ga laifinta a kan hakan ko?, shine yake fada yana kara jadada mata matarsa ya jewa

A sanyaye ta ce” Haka ne, matarka ce, halalinka ce, kana da damar zuwar mata, kamar yadda nima nawa tsohon mijin ya zo min a lokacin da ya yi niya kafin ya dankara min saki!”

Kamar wata wawuya ta saka hannu ta bude kofar ya kasance sun yi ido hudu da shi bayan ta gama fadar maganar da bata san cewa yana iya halakata a kanta ba

Jan kallon daya wurga mata ya kai hannu zai kamota kamar ta sani ta zille ta maido k’ofar ta rufe da k’arfi, kys tasa gabanta na fad’uwa HISHAM kuma saiya shiga jijjiga k’ofar da k’arfin tsiya, idonshi sun rufe sun kad’a sunyi jajir, jijiyoyin jikinshi duk sun bayyana rad’o rad’o, cikin tsananin bacin rai da tashin hankali na masifa ya ke fad’in “Billy ki bud’e kofar nan, ki BudΓ© na gaya miki, yau saina banbance miki aya da tsakuwa, ba dai ni kika…”

Wani tafasa da zuciyarshi ke yi yasa kawai yake girgizz kofar dakin yana mai nadamar me yasa yayi kofar nan mai karko ne.

Kader na dawowa ya ji wannan tashin hankali, sai ya rud’e yayi tunanin ko dai shawarar daya bashi ce ta harzukoshi haka ta taso musu da iskokanshi, ai da gudu gudu ya shigo yana duba wayar dan ya kira d’aya daga cikin abokan aikinshi dan su zo su taimaka mishi ko allurar bacci su mishi dan yana tsoron masifar Hisham, saidai bai kai ga kiran lambar ba ya k’araso da gudu yana fad’in “Kai kai! Subhanallah!”

Rik’eshi yayi gam da iya k’arfinshi yana cewa “Me ya faru? Me ta maka? Billyn ce kake neman halakawa haka?”

Cikin k’arajin murya mai amon b’acin rai ya finciki jikinshi yana fadin “Sakeni Kader! Sakeni na nunawa Billy na fi karfinta, ni zata mayar dan iska da baisan me yake ba? Ni zata kalli idona ta ce wai wani ya je mata? Me take ji dashi? Akan me zata dinga cizgani? Dan ina son ta?”

Sake rike shi yayi gam yana sakin ledar kazar daya siyo yace “Ka yi hakuri, yi hakuri Hisham yarinya ce, muje dan Allah ka ji wani abu.”

Fizgewa yayi a hassale yace “Kader fita a nan, babu inda zanje, ka ce mata ta bude kofar nan,  ka ce ta budeeee!!!”

Yanda yayi maganar duk gidan na amsawa yasa Bilkisu sulalewa kasa ta fashe da kuka tana mai dora hannunta saman kanta, sakinshi Kader yayi yace “Shikenan na sakeka, ka balla kofar dan Allah ka kakkarya Bilkinsun ka kaji, kaga da safe sai Mama ta zo ta kaita asibiti tayi jinyarta, ai haka ya Maka ko?”

Ficewa yayi ya barshi tsaye sai yaji ya rasa kuzarin yin komai kuma, a hankali ya matsa jikin kofar yana taushe bacin ranshi ya kai hannu ya kwankwasa kofar, shiru yaji sai sautin kukanta da take rerawa, a nutse ya saita muryarshi yace “Billy am, ki yi hakuri kinji Ki bude kofar, ki fito ki ci abinci dan Allah kar yunwa ta kamaki.” Irin yadda yake maganar dole ne ka ji gaba daya hankalinka ya tashi, tabas so so? So tashin hankali ne

Ita kanta da rarafe ta nufo kofar cikin yin watsi da dukan wani tsoro ta kama ta mike tsaye ta bude gaba daya jikinta na bari

Ido cikin ido suka kalli junna da shi a lokacin da ta ga danshin abin da ya biyo ta kumatunsa  sai jan da idannuwansa  suka yi

Zuciyarta ce kw tsintsinkewa a hankali ya duka ya dauko ledar ya miko mata yana kallonta

Hannunta na rawa ta amsa tana nan tsaye ta ga ya yi wajen kys din ya dauki guda ya juya da sauri ya yi daya daga cikin sauran dakunan ya bude sannan ya maido ya rufe da wani irin karfin da sai fa ta zabura

Gaba daya kafafuwanta na rawa har ta daga dan nufar wajen sai kuma ta ja da sauri ta tsaya cike da tsoro da fargaba , wani abin ke tunasar da ita hammanta ne fa? Sai kuma wanin ya ce da ita ai shima ya san ke dinsa ce aman ya jewa wata a ranar da take taku kuma har yana ikirarin matarsa ce

Kai kawo yake a dakin da wayarsa a hannunsa, gaba daya a birkice yake yana jin zuciyarsa na suka, a yau sai yake jin mema ya hada shi fadawa soyaya? Wai haka zai kare? Haka zai kare? A yanzu abinda ya dakatar da shi da wancen yarinyar ta ci abinci, tabas rainin hankalin d atake masa kwana biyu tsakanin daya biyun sakin da shashashashan cen ya yi mata bayan kadararen aurensa da ya hau kanta zai je ya bambancewa kansa, tunda har ta san ta yi fushi kan wannan abin zai bata isashen da sai ta ringa sakin fitsarin dake mararta!

Gyaran murya malan ya kuma yi ya ce” A tunaninku an sauke maku aure a kanku ne NANA da ZAINABa? “

A tare suka kali junnansu suka kuma kalli malan

Jauro ya ce” Ko baku da ainahin wanda zai fada maku gaskiya ko ya maku nasiha kai harma ya tirsasaku ne?, shekarunku nawa tsakaninku da maza na aure? Shin baku da lafiar raya sunnar ma’aiki ne ko bakwa kwadayin rayuwa  irin ta aure? “

Mama ta dafe habarta tana sada kai ciki da jin kunya ta ce” To kuma Malan me ya kawo wannan? “

Jauro ya dube ta ya gyara zamansa ya ce” Kya ce haka, dole ki dubeni ki ce haka mana, aman ina so ki sani Asma’u idan ke kin murje idannuwanki kina zamanki haka ba ruwanki da maganar duniya bale ta kiyama sai ki tsawatarwa kanwarki, yanzun  me take nufi? Jira take a gama biki ta juya ta koma? shekaru fa tafia suke, kowa faman da yake shine ya samu wajen da zai saka ransa ya ji sanyi, ku yau ko kunyar y’ayanku bakwa ji? Danma Allah ya wanke ya baku tsararu wa’inda suke girmama ku, suke kiyaye du wani tashin hankalinku ba zaku iya shiga dakin aure ba? Ko kun yi tsufan da ba zaku iya zaman aure ba? “

Mama ta kara sada kanta cike da jin kunyar kalamansa duda tsagwaron gaskiya ce yake fada mata

Jauro ya ce” to zancen gaskiya fa zan fada maku baki daya shine, ku gyara, ku gyara domin nan kusa zaku fara tara yan jikoki ana kada maku zawarawa, kin ga Zainabu mahaifin Hisham ya min bayanin komai, kuma na gamsu, nima a shirye nake da irin muradinsa, na ce ku shigo nan ne dan na jadada maku, da wannan salar du zaku kara daraja a kan taku, Allah ya rufa maku asiri kun samu kar ku yarda wani shashancin ya shiga kwakwaluwarku fa!”

Tati ta dago tana kallonsa, muryarta a sanyaye ta ce” Yaya, auren dole ne za’a min da tsufana? Aman yaya me zan yi da mutumen da tsabar tsanar zama da ni ya min karyar ya mutu? Ni kam ko duniya ya tara ya kara gaba, in dai aure ne zan yi aman ba dai uban Hisham ba!”

Jauro ya gyada kansa ya ce” Kafin ki yanke hukunci ina so ki yi tunani a kai, sannan ki barawa Allah zabi, idan kin kula saura wata uku biyu sallar, idan lokacin ya zo sai mu ga Abinda Allah ya yi”

Dubansa ya maida kan Mama, wace ke kallon matarsa wace kanta ke sade itama ya ce” Ke fa? “

Sai da ta zabura wollah, kasa fadin komai ta yi ta mike da sauri tana fadin” Allah dai ya bamu alkhairi, Zainaba mu je “

     Sorry nah? Bukukuwa

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like