DUK NISAN JIFA 65

Advertisement

 

๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ

          *DUK NISAN JIFA*

           _(K’asa zai dawo)_

๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ

            _RUBUTAWA_

               *SAJIDA*

Advertisements

        *SADAUKARWA*

                   *GA*

           *MASOYA NA*

๐Ÿ’ซโœจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐ŸŒŸ

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_๐Ÿค

  โ˜† *[ T.M.N.A]* โ˜† ๐Ÿ“–๐Ÿ–Š๏ธ 

Advertisements

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                            65

โ˜บ๏ธโ˜บ๏ธโ˜บ๏ธโ˜บ๏ธโ˜บ๏ธโ˜บ๏ธ๐Ÿ˜Œ๐Ÿ˜Œ

Sai da ya kankance ido ya ce” To sannu fareeda, sannu yayata kai ke da alamu kinma zarce yayar  tawa sai uwata kau?”

Farida ta yi wani sakalau da baki tana kallonsa , girgiza kanta ta yi ta ce” Kader ni ban san me yake yawo a kanka ba , ka ga kai sai rigima kamar taohuwar da ta shekara dari , ka bi ka takura min ka shafa min lafia na gaji malan!”

Kader ya talabe habarsa yana kallonta kafin ya gyada kansa ya cije lebensa ya ce” Farida, da ina shafa lafia da na shafawa mararsa ita, ke yanzu abin alfaharinki ne yau a kale ni zankakededen yaro a ce naki ne? Aman sai ki ringa son wana ni? Farida idan asiri kika min ki je ki karya na tuba walahi na fara gajiya”

Farida ta kara hararansa dan har ga Allah wahala Kader yake bata, ita ba samarin ba gaba da baya ya tare ya hanna kowa kulata , shi din kuwa sai shiririta, zata yi wata rashin kunyar suka ji ana dan kwonkwasa kofar

A tare suka kai dubansu sai kuma suka zazaro ido domin baban yayan faridan ne yake kwonkwasa motar

Kader ya kaleta ta kale shi  ya rage murya ya ce” Kin san ya hanna ki shiga motata kika shiga kau? To bari ki ji na girme ahi a haife walahi idan na bude ya yi abinda ba shi ba sai na zane shi!”

Farida ta saki baki harda talabe haba bata sani ba tana kallonsa ya bude ya fita

Gaisawa suka yi a mutunce kafin yayan farida ya ce” Malan kader, ina matukar jin dadin kai ne mai neman kanwata da aure, aman dan Allah me ya sa kuke take dokar gidanmu ne? Ka ga an hannata shiga motar kowa aman yarinyar nan sai ta shige taka? Ka ga a yau shedar duniya fa abin duba ce idan aka tashi aurenku sojoji sai an yi bincike a anguwa idan aka samu yan bata gari suka ce ai tana shiga motar maza yaya zaka ji?”

Kader ya kale shi  da kyau ya ce” Yaya, motar wani take shiga bayan ni?”

Shima da mamaki ya kale ahi, yau kuma shine yayan? Lale kader sai a barshi, aman sai bai nuna ba ya ce” Aa, wai takanma ka san mutane ai”

Kader ya gyada kai yana murmushi ya ce” Shi yasa nake sonta walahi irin yadda ake mata fada a gida, ka ga idan kun shiga dan Allah ka mata nasiha, ka ga dai ni mijin da zan aureta ne ta daina yi min fada dan Allah, ka ga fa sakani take a gaba ta wankeni tas har in ringa sada kaina, aman kar ka ce inji ni dan kar ranta ya bace”

Yanzun yayan Farida tsai ya yi kawai yana kallonsa kafin ya ce” Kai kuwa a kan me zaka tsaya mace na son rainaka? Kar ka bata dama kaine fa mai gida ita kuwa uwar gida, ka ga idan baka iya tsawatar mata tun yanzu ba sai yaushe zaka fara?”

Kader ya tabe bakinsa ya ce” Ka ga idan zaka mata ka mata idan kuwa ba zaka mata ba ka barmin abina, to yau na ga ikon Allah uwar gida da mai gida daya ne? Ita fa uwar gidan ce gaba daya ka ga ni farida ta isa da ni kawai, Allah walahi, yanzun dai yaya maganar aurenmu wai ta ce Aba ya ce sai ta gama shekarar nan bayan ni na shirya”

Di kira ya yi ya sanar da ubangiji ya ce” Karya take shegiyar a nan kuwa ta ce wai inarka ta ce sai badi za’a yi bikin”

Kader ya ringa tafa hannu ya ce” Zo mu je a kwale makaryaciyar, kai Farida  ta ji kunya, ita da kawayenta banda karya basu iya komai ba, oh Allah ka rufa min asiri kar a je ta koyawa y’ayana karya ni Kadiri dan ina”

Shi dai yayanta kin binsa ya yi ya juya ya ce” Aa aba zan sanarwa kai dai sameta ni ai idan na isa cen wanwanka mata mari kawai zan yi “

Kader ya gyada kai cike da gamsuwa ya koma wajen Faridar dake zaune a mota ta yi tsuru tsuru tana cikwuikuyar hijabinta tunda ta hango sunna tafa hannu take ayana ta kade mai yiwuwa an yi da ita

Bude bangaran da take ya yi ya kama tsatsonsa ya ce” Sai a fito min a mota a shiga gida, mutun bashi fa kunya ya kirta karyar an ce sai ya samu takarda za’a masa aure, to dubu ta cika sai ki nemi gafarata na yafe maki, kuma Farida kar ki kuma yi min magana na fada maki! Karya idan abin yi ce wataran sai mutun ya sha duka”

Kafarta daya ta fitar a motar tana kallonsa ta ce” Yanzu kader korata zaka yi kuma?”

Kader ya kaleta da kyau yadda ta yi da fuskar sai da ya ji kamar ya sakar mata da murmushin kauna, kai Allah Faride akoy kyau yar dagargara abinta , sai kuma ya tuna sheka masa karya ta yi dan haka ya maze ya ce” Motar nan dai tamu ce ba taki ba, dan haka a fito a fito”

Farida ta murguda bakinta ta ce” Allahn da ya sa ai ta mijin kawata ce, idanma na ce ba inda zan fita sai Billy ta bani motar nan kuma ta badu, idan kana ja ce tak”

Kader ya ce” Farida kawancenku ya kai nawa da Hishamu? Yo ni a kaina Hishamu sai ya zane Billyn taki kuma idan kin yi gardama a gwada”

Farida ta ringa tafa hannu ta ce” Billy? Kamar a gabanta ka fadi haka zata tambayi shi hisham din mu gani, kuma ka je da wata tsami motarka zan samu mai sona mai galeliyar mota ya sakani a gaba mu sha yawo, malan baki kawai!”

Kader ya yi zuru har ta fito ta bi ta gabansa ta wuce

Bai rufe motar ba ya dan bita a hankali a sanyaye ya ce” Farida wasa kike min ko?”

Farida ta juyo ta kara murguda masa baki ta ce” yarinya ce ni da zan maka wasa? “

Kader ya kara sanyayar da muryarsa ya ce” Yanzu fa muke shiri fa, kuma sai ki tada min hankali tsakani da Allah? Ki yi hakuri kin ji? Zo mu je motar in yi yawo da ke inda kike so kin ji? Idanma garin kike so mu bari mu je Allah zai yafe mana, aman ki yi hakuri kin ji? Banda maganar saurayi”

Farida ta tabe bakinta ta kara gaba

Kader ya rike tsatso ya daga murya ya ce” Yadda muka hannaku kula kowa baku isa ku kula ba, idan kina garaje ki gwada sai na ci kakan yaron kuma ke kuma na maki Allah ya isa!”

Farida ta fitar da kanta daga soron gidansu ta ce” Kadiri sai na yi ka jima baka dauki mataki ba dilla malan a fitar mana a kofar gidanmu tun kafin na turo samari su dauke min mutun daga nan!”

Kader ya daga kafa zai bita ta arta a guje cikin gidansu tana kilkyata daria suka yi kicibus da abanta dake zaune yana kuskurar baki ya gama cin abinci  rana kennan

Da kallo ya bita kafin ya yafitota da hannunsa

Karasawa ta yi ta tsuguna yana gamawa ya ce” Ki ce da shi ya turo magabatansa kin ji?”

Farida jiki a mace ta ce” Aba aman ai sai na gama shekarar nan kau?”

Abanta ya girgiza kai ya ce” Aa, sabkon yaron nan da amininsa ya isheni haka, ku je ko a satin nan zan daura maku aure Allah ya baku abinda zaku ci ku sha ku suturta”

Kader na komawa gida tun a waje ya tambaya idan har Hisham ya je masalaci, sai dai amsar da suka bashi ce ta saka shi girgiza kai ya nufo dakin a bayane yana fadin” Na kula idan ban yi da gaske ba musuluncinma kwacewa likita zai yi ya saka yar shila a daki shi zakara ya kasa gusawa!”

Danawa ya ringa yi a jejere a jejere 

Hakan ya saka da sauri Hisham dake zaune ya gama waya da sakatariar shugaban kasa kan sakon da aka tambaye shi na rashin lafiar wani ma’aikacinsu ya bata sakon da zata sanar da su kennan ya zuba dan romon da aka kawo daga gidan mama zai fara ci kirin kirin din kuwar shigowar mutun ta saka shi mikewa da sauri ya karasa ya bude kofar suka yi ido hudu da Kader

Takalman kafarsa ya cire harda safar ya ajiye a nan kofa kafin ya raba gefen Hisham ya shige falon

Ja ya yi ya tsaya yana wani sakin murmushi kafin ya juyo wajen Hisham  da ya koma wajen kujerar ya zauna ya ce” Kai duniya, Hisham wannan daki ya ci kudi ka duba ka ga wannan uwayen TV oh kamar ba za’a mutu ba duniya kuma mutun sai ya mutu a kaishi daga shi sai likafani, mts shi yasa idan na tuna haka watarana sai in ga kamar na koma kwana cikin rami dan na saba” 

Hisham bai ce masa komai ba sai da ya gama sannan ya taka cafet din ya kuma zarro ido ya ce” Kai jama’a, ka ji laushin abin nan kuwa? Allah mai iko aman kai zaka yiwa farida kayan daki kau? Dan tabatuwar adalci, kai yauwa ina maganar adalci Hisham ina fatan dai an kamanta adalcin kayan dakin nan da aisha kau? Ka ga dai a ringa yi ana tsoron Allah ni dai amininka ne bana son abinda zai kaika wuta”

Hisham ya dafe gaban gishinsa a bayane ya ce” Ya rab, me yasa ni? Yaya aka yi na san wannan akun?”

Ya kai dubansa kan Kader da ya yi sokoko yana kallonsa ya ce” Me kake so? Wai kai dole sai ka ganni kake iya jin dadi ne? Ka ga fa yau ban ce maka kwata kwata kar ka neme ni ba? Kuma da ka tako min har falo idan matata ta fito ta sameka ko ta fito a yannayin da sai ni zan gani yaya zamu kwashe da kai kennan?”

Kader ya dafe gaban zuciyarsa da sauri ya karasa ya zauna a kasa kafin ya ringa tafa hannu ya ce” Na yarda a duniya idan baka ga abin mamaki ba mutuwa kawai ka yi, yanzu Hisham Bilkisun ce kake cewa matarka? Idan ta fito a yannayin da kai kadai ya dace ka gani, hala wai alkawarin da ka dauka cewa sai ta girma wanda nima na ce ai faride sai ta girma me ake da yan shila takewa ka yi? Na shiga uku na lalace yau zan ga abu”

Hisham ya saki murmushi yana girgiza dan kansa a bayane ya ce” Ba zaka gane ba, ba zaka taba gane cewar ashe kai wawa ne kana cutar kanka baka yi aure ba har yanzu sai ka yi ka kuma san meye auren, kai  kai  kai Kadiri idan aka ci gaba da haka ajiye aikin zan yi walahi sai in bude mana shago ka ringa tsarewa kana kawo mana masara da shinkafa sun ishemu rayuwar duniya tunda akoy soyaya”

Kader ya kara zurra masa ido kafin ya rafka tagumi da hannu bibiyu jikinsa a mace ya ce” Dan Allah ka rufan asiri ka samu ina a je a min auren nan Hisham ko na ji abinnan ka ji? Kai ka san ni ba dan iska bane da na cika yayan mutane dan Allah a rufan asiri a min aure”

Hisam ya zuba makaroni ya kara masu miya ya sauko kasa shima ya saka masu cokula ya ce” Ci abinci mu je mu samu ina, zan so a yi a gama ko zaka labe ka yi shiru ka barni da Billy ta gama haukata ni , walahi ni inma kasheni zata yi ta kasheni , sai yanzu nake jin haushin raba masu gida to idan na koma cen din yaya za’a yi na iya baci ban ganta ba?, ita kuma da ka ganta tsoronta nake na je na kwana dakin yar uwar na fito ta ringa tsatsareni da ido uwa kwarto walahi du sai na ji kamar ya dace a jefeni kamar wanda na aikata kwartanci”

Kader ya sheke da dariar da ya sa Hisham rufe masa baki kasa kasa ya ce” Baka da hankali drip ne a hannunta barci na samu ta koma , kwana biyun nan du bata da lafia “

Kader ya tabe bakinsa ya ci gaba da lodawa cikinsa domin da alama damuwarsa shima ta zo karshe tunda har Hisham ya ce zai masa aure dan ya barshi da matarsa ya huta

……………..kwonci tashi…………

Kamar yadda aka ce mai hakuri shi ke dafa dutsi, lokaci kuwa ba abinda ya bari domin da sannu za’a wayi gari duniyar ba kowa sai mutuwa wace itama wanda ya haliceta zai bata umarnin ta dauke kanta, zata dauke kanta har a kaimu ga busa kaho a nade kasa kowa ya fito, idan dan adam ya yi hakuri kanar yadda aka halice shi ba da neman shawararsa ba za’a dauki ransa a lokacin da bai shirya ko ya bada amanar yana son kaura ko a barshi ya dawama a duniyar ba, ta haka kowani bawa zai samu daidai misalin abinda ya aikata da hannaunsa a sanninsa ko a rashin sanninsa

Ta haka Allah ke bada sakamako da alamu tun a gidan duniya, zaka girba ne khairi ko shari domin a yanzun tun a duniya Allah ke nuna ishara 

Ta kasance a rayuwar Bilkisu da Hisham sun taso da muguwa fitinaniya hargitsatsiyar soyayar da take daga hankalin kowa, wace su da kansu suke tsoronta, wace kuma koda wuka aka saka dan a kashe su cewar wai za’a wayi gari wani daban ya malaki junnansu ba su ba zasu karyata ne, sai Aisha ta shigo cikinsu a lokacin da basu tsarawa junnansu karbar bakuncinta ba, duka wannan bai isheta ba kasancewarta mai kyawawan halaya aka wayi gari tana zaune daram a cikin gidan mijin Billy a matsayin uwar gidansa kuma yaya yar uwa a wajen bilkisu

Tati ta ga isharar rayuwa a lokacin da ta gane cewa shi arziki na Allah ne, kana iya tashi ka yi fashi da makami ka yi kwace ka yi karuwanci ka ci zalin aman idan Allah bai nufeka ba sai dai ka yi ka gama ka dawo  ka tsuguna komai shirkarka kuwa, idan Allah ya nufa kamar yadda yake fitar da matace a cikin rayaye kuma rayaye a cikin matace zai wanzar da ikonsa a kanka koda kuwa kana cen kuryar jejin da keke baya zuwa ka zama hamshakin da kowa ke son ganninka, kanka anfanarwa kanka dan kiyamarka ko anfanarwa kanka dan duniyarka

A lokacin da ta rasa mijin ta rasa iyaye ta kuma damki neman duniyar ba a kan tsari ba ta yarda dan mululun jaririn da ake tatsawa nonon akuya ta tafi neman na kanta ba da zuciya daya ba, sai Allah ya yi ikonsa ya ganar da ita cewa wannan dan jaririn shine alfarmarta, takamarta , jin dadinta, sai da ta dawo ta nemi alfarma a karkashinsa sannan kuma mijin da ya bartama ta kuma samunsa dominsa *DUK NISAN JIFA DAI KASA YAKE DAWOWA* ba mai cin rabon wani , kowa nasa yake ci

Mahaifiyar Aisha ta gama da samun sakamakon duniya da tsufa a kai ga saki ga ba dukiyar ga rashin daraja a idon duniya ta je ta zauna a dan kauyenta sai yadda hali ya kama………Abinda  ta shuka sai ta girba cikin aminci 

Mahaifinta da ya gane da wuri ya koma ya yiwa wanda ya isa da shi biyaya dan gamawa da duniyar lafia ya gane cewa mai sonsa dan abin hannunsa ba abokin tafia bane koma wanene

Mama ta koma dakin mijinta wanda yake mahaifin yarta da abokiyar zamanta sunna zaune kalau cikin wadatar zuci da ta arziki , ta kasance datijuwa mai farin goshi, fararen hakoranta na kara haska du wanda ya rabeta kyakyawar zuciyarta da kyawawan halayanta sun wanke da sukutun sun bata wanda ko gobe baya iya yanke shawara sai da fadar mamansa da amincewarta da amanarta da shawarta wace ke saka zani ta goye jikokinta kwaya uku reras yan mata biyu namiji guda ta tsatson billy tagwayen yan matan sai aisha mai dan saurayin jaririn da yake wajen mama har kayansa yana mai kiranta da Ummy

Kader aboki amini na gaske wanda yake a matsayin aboki baban soja mai kare lafiar amininsa da matarsa farida da yarinyarsu ISLAM sunna zaune cikin aminci da mutunta junna 

Zan iya cewa soyaya bata da alamun risinawa y’aya ko shekaru ba zasu hanna Hisham ya dauke Billy cidak ya jefa saman bed kafin a birkice a gigice a haukace ya dirar mata ya shige cikin jikinta kafin ya gama lashe dukan abinda yake gurbi na jikinta ya bata kulawa sannan ya budi baki ya yaba gardin da ya karu harma ya bada tukwuicin kyauta dan gobema a bashi mai dandano๐Ÿคง๐Ÿ˜…

Bisalam

A nan na dasa aya, kamar yadda kuka sani labari tsarawa ne, bai zama lalle yadda na gabatar da shi ya birge kowa ba, atls sakon da nake so na isar a cikinsa ya samu shiga Alhamduliah, du wanda na batawa dan Allah ya yafe min, wanda na farantawa ya min adu’ar  gamawa da duniya lafia, idan labarin ya maku gajarta kar ku damu ina da niyar yin Mage return da kuma Duk nisan jifa sabon salo da izinin Allah idan ina cikin masu rai, idan kuwa na rasu maman jariri sai ta yi domin kwakwaluwar iri daya ce, idan maman jariri  abin ya mata yawa Aminiyata, masoyiyata yar uwata Billyna sai ta rubuto shi kamar yadda zan iya rubuto shi a gefe guda mamana na taya ta, ga Yagana na zubo.mata ruwan RRRRRR, Aminene na gyaran errors  typing tana dan dangwala hannunta wajen da ya gyaru, members Grup DUK NISAN JIFA sunna bada comment ruwa ruwa ta yadda zasu haukace su zayano komai yadda ya wakana

             Sako zuwa ga masoyana

*INA SON KU, INA ALFAHARI DA KU, TABAS RUBUTU NA WAYI GARI NA GANNI A CIKINSA NE AMAN IDAN BAKU KARFAFA MIN GWUIWA KUKA KARANTA JAGWALGWALONA NA DUK KARYAR KADA, KUKA KARA BINA A YAR MAHAUKACIYA, KUKA DAGE KUKA BI NEMAN NA KAINA, BAKU GAJIYA BA KUKA SAURARI BANI DA ZABI, NA KUMA KAWO MAKU WAI SHI BAK’A CE, NA DIRO MAKU DA KUTKALE, NA SAMA MAKU MAKAUNIYA, NA KUMA CE MAKU GA MAGE YANZUN NA GAMA MAKU DA DUK NISAN JIFA BAYAN MUNA MAKU AURE YAKIN MATA, SAI NAKE BAKU ALBISHIR DIN SABON MAI SUNNA “DUTSE” GASHI KUN CE KU A GAMA MAKU NEMAN NA KAINA, TO KU MU KAMA SALATI ALLAH YA SA MU DACE YA BAMU ARON KWANA DA LAFIA DA NUTSUWA  DA KWONCIYAR HANKALI, ASUSUNMU A CIKE MU GYARA ZAMA MU SAKA VIVO DINMU A CAJI MU ANFANAR DA JUNNA SANNIN DA ALLAH YA BAMU BA DAN MU WASU BANE BA DAN MUN FI WASU BA, MUN GODE, NA GODE NA GODE NA GODE, A DUK INDA KUKE SAKON GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI YA KAI MAKU, ALLAH YA BARMU TARE CIKIN RUFIN ASIRINSA AMEN*

        GRUP DUK NISAN JIFA

Dole na yi alfahari da ku fan kun isa, kun kai , ku din na davan ne, a mage Fauzy ta min ba zata ta kawo maku shawara kuma kuka karba, a yanzun sai na wayi gari Aleesa ta bilo da wata shawarar? Ku sani bani da bakin gode maku sai dai mu yiwa junna adu’a, Allah ya kara rufa asiri duniya da kiyama ya sa mu gama da duniya lafia ya sa aljanna ce makomarmu, ya shirya mana zuri’a ya yi masu albarka amen

*NI YAR MUTAN NIJER SAJIDA RUBUTU YA MIN RANA, DA WANNAN NAKE CE DA KU One love๐Ÿ‘*

            Alhamdulilah, Alhamdulilah

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

DUK NISAN JIFA 58

Advertisement   ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ           *DUK NISAN JIFA*            _(K’asa zai…

DUK NISAN JIFA 56

Advertisement   ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ           *DUK NISAN JIFA*            _(K’asa zai…

DUK NISAN JIFA 55

Advertisement   ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ           *DUK NISAN JIFA*            _(K’asa zai…