GOBE NA 44

Advertisement

GOBE NA…*

By Khadeeja Candy 

4️⃣4️⃣

Rasa nai abunda zan yi, na bishi nai masa magana ko kuma na zauna ko na tafi gida? Ya Abdallah zai ji idan aka ce wani ya tsare masa mata saboda kuma a kamfaninmu, no ba saboda ni ba ne saboda ta yi hayaniya ne dan haka babu ruwana a ciki. 

Advertisements

   Akai akai mutane suke ta kallona, har na soma tsarguwa, tashi nai koma can wani gefe da ba a ganina sosai na zauna, wata zuciyar na fada min cewar naje nai maganar aikina sai dai kuma idan na yi maganar aikin aka koreni ba tare da an gama maganar Suwaiba fa? 

  Na kusan awa daya a gurin ina ta tunanin abun ne naje nai masa maganar Suwaiba ko ta aikina, amman ina ruwana da matar da ta ci min mutunci a bainar jama’a, ai kara a kira Abdallah din domin na san ba da saninsa ta zo nan ba. 

Ban raba daya biyu ba, aka aiko wata mai sanye da suit kirana, haka ta saka ni a gaba ina baya har muka isa office din Ahmad. A one of visitors chair na tarar da Abdallah zaune, ni kuma sai na tsaya daga bayansa tun da ba a bani izinin zama ba, juyowa Abdallah yai ya kalleni sai kuma ya kawardar fuskarsa ba tare da yace komai ba. 

“Look man aiki bake fa zaka tsayar da ni anan for more than 20 minutes, ba kallo office dinka na zo yi ba”

Abdallah ya fada a fusace, hakan yana nuna alamar Abdallah ya dade da zuwa kenan. Da hannu Ahmad yai min alama dana zauna ba tare da ya kalleni ba. Ba musu na zauna a kujerar da ke kusa da Abdallah ina ta kallonsa shi kuma sai yai kamar be san da ni a gurin. After like 5 minutes Ahmad ya kalleshi yace. 

“Aiki nake yi ko baka gani ba? So kake na aje aikin na kula ka? Kai da ka zo ganina ba appointment? And you got lucky na barka ka shigo har office dina ka zauna tare da ni, ban barka visitors room ba?”

“Ba kai na zo gani ba, Matata na zo na ji dalilin riketa da kuka a nan”

Advertisements

“Bata fada maka abunda tai ba? Ko a hanya kawai za mu ga mace a hanya mu dauko ta?”

Babu wasa a fuskar Ahmad a yayinda yake wannan maganar, kamar yadda Abdallah ma nake ganin abun ya masa zafi. 

“Matarka ta zo nan tana mana ihu na rashin tarbiya tana fada akanka, tana fada da ma’aikaciyarmu ba za mu dauki wannan ba”

“Kai kuma ka rufe ta, saboda gaka hukuma”

Ahmad ya kwanta jikin kujerar yana masawa Abdallah cikin zafin rai. 

“Yes ko akwai abunda za ka yi? Kana ta son nuna isa, bayan you are nothing wanda be isa da iyalinsa ba har ya isa yace zai fito waje yai yi takama? It’s a shame”

“Family issues ne wannan babu ruwanka a ciki”

Abdallah ya fada yana kokarin danne fushinsa. 

“Family in my company? Public place?….”

Ganin abun kamar zai zame musu fada yasa nai hanzarin cewa. 

“Na yafe ni tai wa cin mutunci na yafe mata, dan Allah ka barta ta tafi”

Ina fadar hakan Abdallah ya daga min yatsansa alamar babu ruwana a ciki, Ahmad kuma ya tari numfashina

“To ni ban yafe ba…”

Ya fada kai tsaye yana kallona. A lokacin ne Abdallah ya mike tsaye cikin bacin rai ya daka masa tsawa. 

“And who are you? Mi kake takama da shi”

Wani shegen kallo Ahmad yai ma Abdallah, mamaki ya kama shi wato a maimakon ya bada hakuri ya karbi laifin matarsa amman sai neman kareta yake, hakan ya kara tabbatar masa da cewar Halima bata da gata domin da tana fa shi da yau ba shi zai yi fadan nan ba wani wanda ya tsaya mata ne zai yi shi.

“Kudi Alhaji……… ko baka gani ba, na isa ne isar ta isa ma matuka, kawai dan kun ga mace bata da gata sai ku yi ta taka ta any how, idan yar wani mai kudi ce ko kuma tana da wanda ya tsaya mata shashanshar matarka bata isa ta taka kofar gidansu ta fada mata bakar maganar magana ba balle har ta shigo gurin aikinta tana kiranta da suna kala kala tana cin mutuncin, so warn your wife for the last time, bilahil’azee idan ta one bad word daga bakin matarka zuwa ga Halima sai a rufeta a cell ba acikin kamfanin nan ba”

Abdallah yayi murmushi yana duba agogon hannunsa, sannan ya kalleni ya sake kallonsa. 

“Ba kai ne mutumen da yace idan yarsa ta mutu zaka rufe Halima ba? Ba kai ne mutunen da baka yarda da kaddara ba? Ba kai ka mareta har sai da ta suma ba? Kai duk abunda kai mata ai saboda kana ganin bata da gata ne, yanzu har kana da bakin da zaka fadi haka? Mi ka sani a akan Halima? Baka san komai ba akan rayuwarta fadi tashin da tai ba ka sani ba, sai a yanzu? Tsohon dan iska shiyasa ka bata wando da riga ta saka so that ka rika kallon siraicinta? So kake ka burgeta a yanzu? Shiyasa zaka fara acting kamar wani mutumen arziki… ”

Su suke fadan ni nake kuka, Ahmad be sake cewa komai ba, ya danna dan wani maballi da ke gefen teburinsa, ba a dauki lokaci ba sai ga security kamfanin sun shigo. 

“Ku fitar min da shi bana son hayaniya…. ”

Da sauri suka nufi gurin da Abdallah yake saye sai kuma suka saka rika shi sai kokarin masa magana suke.

“Karku taba shi zai fita da kanshi…. Abdallah dan Allah”

Ya fada ina masa magiya, kallo yai ya dauke kai ya juya ya fice daga office din rai a bace, sai security din suka bishi a baya. Karasa matsawa nai kusa da teburin na hade hannayena ina kuka. 

“Ka saka a saki matarsa dan Allah, na san ka tsaneni, duk abunda zaka yi Saboda ka musguna min ne  ko kuma wani na kusa da ni, idan har ya zama dole sai ka dauki mataki akan abun dan Allah ka hukunta ni ba matarsa, saboda ni komai ya faru…”

Ba tare da ya kalleni ba ya nuna min wata kujera dake can kusa da kofa. 

“Je can ki zauna”

Abun ka da mai jiran umarni sai na nufi kujerar na zauna ina kuka a hankali domin har ga Allah ban jidadin da ran Abdallah ya bace ba, kuma ban jidadin abunda Ahmad yai masa ba. 

“Idan kin gama kuka ga tissue box kusa da ke ki goge fuskarki, akwai ruwa a fridge”

Yana fadar hakan ya dauki laptop din da yake aiki da ita ya fice ya bar ni a katon office din, ni ko ban fasa aikin kuka ba har sai da nai wanda ya ishe ni na dauki tissue na goge hancina da idona sannan na bude fridge din na dauko gorar ruwa na sha, domin makoshina ya gama bushewa. Bayan na sha ruwa na koma a inda na tashi na zauna. Kalamansa na dazun ne wuka rika dawo min a rai kamar yadda na Abdallah ma suka tsaya min, na rasa ganewa Ahmad ya fara saukowa daga fushin da yake da ni ne? Da har zai ce idan Suwaiba ta sake fada min bakar magana sai ya rufe? Ya bar ni na shigo har office dinsa ya fada min idan na gama kuka na goge fuskata na sha ruwa… Ina tsaka da tunanin sai gashi ya shigo tare da Yunus yana ta murza wani karamin turare a hannunsa, kallona kawai Yunus din yai be ce komai ba ya cigaba da maganar da yake da Ahmad bayan ya gama ya fice wata matar ta shigo da kofin tea guda biyu ta aje a saman teburinsa sannan ta fice. 

  Daukar dayan kofin yai ya nufo inda nake zaune ya miko min, mamaki ne ya hana ni karbar cup din har sai da ya kalleni. Sai nai saurin girgiza masa kai na mike tsaye.

“A a na gode”

Kallo yai for few seconds sannan ya furta. 

“I’m sorry….”

Ya juya yana kurba tea ya nufi teburinsa. 

“Be kamata ka bani hakuri ba, duk abunda ya faru laifina ne, ni na ja komai sanadina komai ya faru kuma kamfaninka ne kana damar ka yi duk irin hukuncin da kake so….”

“Akan dora miki laifin kisan Baby Namra da na yi”

Ta tari numfashina, wannan karon mutuwar tsaye nai, da gaske hakuri yake ba ni? Ahmad din ne ko wani dai dabam, na dan juya na kalli bayana na sake kallona. 

“Ki yi hakuri dan Allah”

Ya maimaita min da yaren da na fi ji. Har lokacin kallonsa na ke gaba daya kaina ya gama kwancewa, mi ke faruwa ne? haka na tsura masa ido ina ta masa kallon da ban san na minene ba, mamaki kadai ko kuma har da tuannin maganar Abdallah? Da gaske hakuri yake bani ko kuma wani abun yake shirya min saboda na kashe masa ya? Kamar yadda yake zargina? 

“I say sorry”

Na hade yawun bakina. 

“Ba komai ba, wannan ma yana cikin kaddarata ne”

Ina fadar hakan na juya zan fice daga office din.

“Ina za ki je?”

“Gida”

Na fada ba tare da na juyo ba, idona na cika da hawaye.

“Aikin fa?”

“Na aje”

“Saboda me?”

“Tufafin da nake sakawa be dace da ni ba”

Na amsa cikin muryar kuka, har yanzu na kasa yadda Ahmad ya bani hakuri akan yarsa, har zuciyarsa yake bani hakurin? Miyasa? Taya yanzu ya yarda ba ni na kasheta ba? A take wasikar da na rubuta a jiya ta fado min a rai, ya fahimci ni ce kenan, kuma zuciyarsa ta bude har ya iya yarda a yanzu ban aikata ba, Al-hamdulillah akalla wani abun ya ragu daga bakincikin da yake raina, a yanzu yana kallona a matsayin marar laifi tun da har ya iya ba ni hakurin. Shigowar Yunus ne yasa nai saurin share hawayena sai dai hakan be hana shi fahimtar kuka nake ba. 

“Lafiya?”

Ya tambaya yana kallo da mamaki a fuskarsa. Ban saurari abunda Ahmad ya fadawa Yunus din ba domin har lokacin kokarin tsayarda kukan farincikina nake. 

“Biyo ni muje”

Yunus din ta fada ni kuma na juya ina rokon Ahmad amman ko kallona be yi ba. 

“Dan Allah ka saki matar can dan Allah”

Ganin Yunus din ya fice yasa nima na bi bayansa, yana gaba ina bayansa har muka isa wani guri, hannunsa ya kai ya tura kofar sai ya bude ya shiga ni kuma na tsaya a waje har sai da ya yi min izinin shiga. 

  Dan madaidaicin office ne mai dauke da desktops har biyu a teburi daya, sai dan karamin fridge da ac makale a dakin daga gefen ac window ne mai kofa biyu wanda yake bawa mutum damar hango windows din office din Ahmad kamar yadda shi ma zai iya hango na cikin office din idan an bude.

“Kin iya typing ai ko?” 

Na gyada kai. 

“Yauwa to duk emails din da za a turowa kamfanin nan anan zai shigo wanda kika ga ya dace oga ya gani sai ki masa forward kai tsaye zuwa email dinsa, idan kuma za a aika wani abu to all ma’aikatan mu ke za a bawa ki yi typing sai ki tura, sai dai daga yanzu lokacin tashi aikinki ya canja daga 3 zuwa 5pm, amman ba kamar wacan ba ne nan ana bada abinci saboda zaman da kike”

“Ban gane ba….”

Na fada a hankali cikin sanyayyiyar murya. 

“Yanzu nan ne office dinki congratulations”

“Da gaske?”

“Ga zahiri kina gani”

A take idanuwa suka kara cika da kwalla.

“Na gode”

“Oga ya kamata ki yiwa godiya”

“Dan Allah ina rokon alfarma”

“Na san kai ma oganka ne, amman kuna da kyakkyawar fahimta wata kila za ka iya yi masa magana ya ji, dan Allah ka saka ba ki ya saki matar da ya saka a ka kulle”

“Ya sake ta ai, tun dazun mijinta ya tafi da ita”

“Da gaske? Amman cewa yai ba zai barta ta tafi ba”

“Gaskiya tun dazun aka wuce da ita”

Dan murmushi nai na juya ina kallon office din. Shi kuma ya juya fice ya bar a gurin tsaye n rasa abunda zan yi murna ko kuka ko mamaki? 

  Kasa komai nai a cikin office din sai kawai nai zaune ina ta kallon office din, misalin daya da mintuna wata ta shigo da abinci ta ba aje min, takeway ne na jalof da naman kaza a ciki. Nikam ban ci ba duk kuwa da kasancewar ni kadai ce a dakin sai na saka abina a jaka. 

  Biyu na yi na shiga bandakin da ke office din nai alwala na fito nai sallah sannan na dauki wayata na kira gida na fadawa Hafiza ta fadawa Mama an canja min aiki dan haka yau sai 5pm zan dawo. 

  Har karfe uku ban duba email din ba ban kuma tura komai ba, har sai da Yunus din ya sake dawowa ya nuna min yadda ake da kuma wandanda ya kamata a turawa Ahmad din.

Karfe biyar na yi na dauki jakata na fito daga office din, ko da na fito Rilwal da Blessed basa gurin sun gama aikinsu sun tafi. 

  A lokacin da na isa gida na labartawa Mama da dukan yan gidan abunda ya faru tsakanina da Ahmd da kuma abunda Suwaiba tai, a nan Hafiza take fadar wai Suwaiba ta kirata kwanan baya tana tambayar inda nake aiki ita kuma ta fada mata ba ta yi tunanin wani abun ba ashe dan ta samu zuwa ta ci min mutunci ne.

   Su namra na bawa abincin office din, suna ta murna sun ga har da nama a cikin gurin rabon abun har ya so zame musu fada sai da Husna ta shiga tsakani.

Bayan na huta na ci abincin da aka girka gida, na watsa ruwa na sake shiryawa cikin wasu tufafin na nufi bankin da ke kusa da mu, kudin gasar da na ci nake son cirowa na samma kowa wani abu a ciki sannan nai sauran lalurorin da suke gabana. 200,000 na ciro na saka a jaka ta cikin tsoro domin a lokacin an fara kiran sallah sai nake ganin kamar akwai wasu a biye da ni duk kuwa da ba ni kadai na ciri kudi a atm din ba. 

  Ina yin gaba kadan sai wata farar mota mai bakin gilashi ta faka a gabana, na san ba zai wuce Abraham ba amman hakan be saka ni jin tsoro ba har sai da ya bude motar ya fito. 

“Ki daina cirar kudi a atm idan yamma yayi, wani zai iya sa miki ido wasu ma ba diban kudin suka je yi ba kallon masu cire kudin suka je yi”

Ban ce masa komai ba nai gaba kamar zan wuce sai ya saka ya cin min. 

“Kin gani jin labarin ki ya kara min kaunarki, kuma ya kara kafafa min guiwar aurenki, ni kadai zan rayu dake ba wata kyama ba wani tunani, ina da kudi zan sakar miki su ki jidadin rayuwarki”

“Ba kudi ne jindadin rayuwa ba, da su ne da masu kudin ba su shiga kunci ba, ni farinciki nake nema da kwanciyar hankali”

“Na sani shiyasa zan baki ai”

“Baka isa ka bani farinciki ba, baka isa ka keta min haddi da aurena ba har nai ciki yanzu kuma ka biyo ni kace zaka aureni, addininmu dabam al’adarmu dabam, baka san zafin da nake ji a raina ba, baka san yadda mace take ji idan an keta haddinta ba, saboda kai namiji ne, mace tana jin matukar bakinciki ko hannunta a rike balle a keta haddinta, kasan saboda me? Saboda martabarta kimarta mutuncinta jindadinta farincikinta yana a nan ne, to kai ka zubar min da duka wannan ka saka uwar mijina da mijin da ya sake ni suna min kallon karuwa wacce ta zubar da mutuncinta tai fasikanci da wani namijin har ta samu ciki, wannan tabon ba zai taba gogewa ba, idan kuma ka zo ne saboda ka kashe ni da bakincikin kallonka da nake kana da dama”

Na karasa cikin kuka. 

“Idan nisanta kaina da ke zai saka ki farinciki, i will do that, amman bana da niyar saka ki bakinciki, sai dai sama miki farinciki ada bakincikin fyaden da nai miki kawai yake damuna, amman a yanzu har da rayuwar kuncin da kike ciki, kina da zuciya mai kyau kuma kina da hakuri”

Bayan ya fadi haka ya bude motarsa ya shiga yai mata key ya bar ni a gurin tsaye. Sai da na daina hango motarsa sannan tari napep na shiga. Ko da na isa gida har an gama magariba, bayan na sallame mai napep na lura da motar Abdallah, na yi zaton yana cikin gidan ne sai ji nai ya kirani, ina juyowa na hango shi ya fito hanyar masallacin unguwar sai ya nufi gurin motarsa ya tsaya, hakan yasa nima na karasa kusa da shi na tsaya. 

“Ki yi hakuri da abunda Suwaiba tai miki, ban san yadda akai taje gurin ba kuma ban fada mata cewar kina kawo min abinci ba, kin san zuciya kowa da irin tasa ba tai tunani ba a lokacin da ta aikata abunda ta aikata dazun kuma ban jidadi ba”

“Tana da gaskiya Abdallah, tana tsoron wata ta karbe nata miji mai karamci da sanin ya kamata, mai kula, mai tausayi, mai taka tsantsan akan komai, kai kadai ka yarda da ni Abdallah baka taba yarda cewar na aikata laifi ba, kai kadai ka yarda cewar ban aikata zina, kai ne kadai ka yarda fyade ka min har na samu ciki, amman Hajiyarka da Abdulhamid ba su yarda da ni ba, kai na zarga a lokacin da aka min fyaden kuma na fada maka, amman gujeni ba baka kyamace ni ba, baka fasa so na ba, baka kasa taimaka min ba, so na be taba sa ka nemi aikata alfasha da ni ba, baka taba kyamar yayana ba, Wallahi ina son ka Abdallah ina son ka har kasan raina”

Na karasa cikin kuka mai tsanani. Har ga Allah ban taba jin son wani da namijin a raina kamar yadda nake jin Abdallah a raina ba, sai bayan komai ya lalace na gano shine mutumen da ya dace da ni. 

“Ke dai ba kya gajiya da kuka, shiga ciki Suwaiba tana jiranki”

“Ina son na fada maka wani abu, mutumen da yai min fyade, ya dawo yan so na”

“Wooo What….!”

Ya furta da karfi muryarsa na amayar da mamakin da ke cikinsa. 

“Waye? A ina ya ganki?”

“Labari mai tsawo ba zai yiyu a yanzu ba”

“Waye shi kin san shi ne?”

Na girgiza kai. 

“Ban san shi ba, sunansa Abraham, dan sanda ne, yana aiki a unguwar gwaza, kuma shi ba musulmi ba ne”

Na daga kaina sama ina shanye kuka.

“Abraham…..”

Ya maimaita sunan sannan ya jinjina kansa. 

“Shiga ciki za ku yi magana da Suwaiba”

Na gyada kai alamar gamsuwa sannan na saka hannuna na share hawayena sannan na juya na nufi gidanmu. Ko da na shiga na samu Suwaiba zaune falon mama tana ta rutsar kuka kamar ba ita ba, tana ganina ta soma bani hakuri tana fadin na yafe mata, a iya sanina Abdallah baya duka balle nace dukanta yai ya cilasta mata zuwa ta ba ni hakuri sai dai idan wani abun ya fada mata ko kuma cilastata yai.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

GOBE NA 48

Advertisement  *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  4️⃣8️⃣ Tun daga yanayin tafiyata zaka fahimci ina cikin wani irin nishadi…