GOBE NA 46

Advertisement

*GOBE NA…*

By Khadeeja Candy 

4️⃣6️⃣

Bayan tafiyar Aminu, Abdallah ya kira ni a waya sai na tashi na bar dakin na shiga dakin inna inda babu kowa ina amsa masa wayar, tambaya yake akan Abraham din ina fada masa abunda na sani da kuma farkon haduwarmu har abunda ya kawo isuwa yau. 

Advertisements

“Bayan ni akwai wanda ya san da wannan maganar”

“Eh ogan mu na gurin aiki”

“Halima kin amince masa da yawa, kin manta waye shi ne?”

“A a babu wani aminci a tsakaninmu, ya nemi yafiyata ne, kuma na rubuta labari ne a ranar children day a gurin ya gane cewar ni ce saboda labarin yarsa ya shigo ciki da kuma na kamfaninsa”

“Ban gane ba zuwa kikai kika fallasa kanka abayyanar jama’a”

“Aa….”

Advertisements

Daya bayan daya na bayyana masa yadda abun ya faru har da zancen siyen tikitin da Abraham yai, hakan kuma ba karamin bata masa rai yayi ba.

“Wayuya kawai taya shi Abraham din zai siya miki ticket kuma ki karba ki je”

“To ba gashi na ci gasar ba”

“Dalla can Sakarya kawai”

Ya kashe wayarsa, a iya tunanina nikam ban ga illar zuwa bukin da nai ba, to ina ruwana da shi ai ba san shi na je ba, dan yarana. Ko da na fito dakin dukansu suna zaune a tsakar gida har Mama sai zancen Aminu suke, kusa da Inna na zauna ina sauraren Mama da ke fadin. 

“Namiji dai ba shi da kunya, yanzu duk abubuwan nan da Aminu yai miki har yana iya murje ido yai miki siyayya ya kawo miki yana rokon ki koma masa?ya manta irin cin mutuncin da yai miki ne ko kuwa ya runtse ido ne ya zo?”

“Hmmm Mama ke ma dai kya fada, ni wallahi yanzu ko mai sunansa bana son ji sai na rika ganin kamar ma halinsu daya”

Na Fada ina tabe baki,Sai Inna tai dariya tace. 

“Kuma kin ga fa inda rabon shiryarwa sai a shirya tun da akwai yaya har hudu, ai ko aure kika yi a wani wajen hankalinki yana kansu, nikam da za ki bi ta tawa da kin koma masa tun dai ya gyara halinsa kuma mahaifiyarsa ma yanzu tana sonki”

Mama ta tari numfashin Inna tana girgiza kai. 

“A a wahalar da ta sha ta isa haka nan, ai ba ayi rai dan wani rai ba, wani lokacin mai hali baya fasa halinsa, Allah dai ya baki wani na kwarai wanda zai so ki tsakani da Allah, wanda zai kaunace ki har karshen rayuwarki, ya zame miki gata hawayen da kika zubar ya share miki su, kuma ya so yayanki kamar nasa, wanda zai rika jin tausayinki yana tsoron cutar da ke”

Dan murmushi nai. 

“Samun irin wannan namiji yana da wahala Mama, mutum daya na san zai iya min haka, shi kuma babu wannan damar a yanzu, nikam na yanke kauna daga yin aure a yanzu”

“Haba dai fata na gari lamiri, idan ba ki yi aure ba ki yi me? Aure ya haife ki kuma ya haifa miki yaya, ina kan fatana na ganki a dakin mijinki”

Aisha da Hafiza da Husna kamar jira suke suka hau yi mata yaya, ba ma kamar Hafiza sarkin Baki. 

“Mu da ba a kauna ai sai a kai ku kofar gida a aje, wai har wani fata ake mata ga ku zaune, ita ba kara ita ba tayi auren har ta haifi amsu yi mata addu’a, mu da ko mashinshinin ba mu da fa?”

Duk dariya muka saka har ita, sannan su ma tai musu addu’ar. Sai a lokacin na dauko siyayar da Aminu yai min na bude ina dubawa, Atamfa ce har biyu da turare da sabulun wanka da wanki sai yan kayan tande tande, komai ban dauka a gurin na rabawa Mama da Inna atamfar salubun wanka da wanki kuma na bawa kanena turaren na bawa Baba, sauran kayan tande tande kuma a nan na bar su a tsakaninsu suka raba suka cinye. 

   Ina zaune a gurin amman ko chocolate din ban ci ba, sai aikin danna wayata nake.

“Gobe idan Allah ya kaimu ina son zuwa gidan Gwaggo Ramatu”

Mama ta fada. 

“Gaskiya kam kin kwana biyu ba ki leka ta ga, gata ita kadai ta rage muku cikin Gwaggonin”

Na fada still idona yana kan wayata. 

“Shiyasa ai nake son zuwa, sai na siya mata salubu na kai mata”

Da gangan na kalli Hafiza na ce 

“Ga sabulun Hafiza nan ta baki ki kai mata”

Wata uwar harara ta watsa min. 

“Eh ni da ba kya kauna, to ba zan bayar ba, kuma Mama dakinki zan aje shi idan ma ban ganshi ba ba ruwana ni”

Ta fada tana tashi ta bar mana gurin. 

“To idan ba ruwanki ai ba ruwan kowa”

Na fada ina dariya Inna ma dariya take, haka ma Mama daman sun san Hafiza bata da na biyu a cikin gidan indai babin fada ne da matsifa, sai dai fa akwai son yan’uwanta kamar ranta, hakan yasa baka iya banbanta ni da ita kace kowa da uwarsa, mu zama kamar uwa daya daman kuma uban ne ya hada.

    Washe gari ta kama friday farar rana kuma kuraren lokaci, hakan yasa na gama shiryawa su Amal da wuri suka wuce makaranta ni kuma na shirya  a yau ma abayar na saka sai dai wannan maroon color ce, sai da nai musu sallama sannan na nufi gurin aikina.

 

  Tun daga lokacin dana fito gida nake saka ran haduwa da Abraham saboda sabon da yai min na bibiya a baya wani lokaci amman har na isa ban ganshi ba, a yau ma ban ga Kabir ba, hankali ya dan tashi daman na san Ahmad ba zai kyale shi ba bayan abunda ya faru, to amman ina ya kai shi? A wane hali yake? Har na shiga cikin kamfanin ban daina yiwa kaina tambayoyi a game da Kabir ba. Can zuciyata ta kawo min cewar na taimaka masa da kudin na da samu ko zai samu lafiya, ba karamin dadi na ji ba da wannan idea ta fado min a rai. 

  Ina isa office dina na tura kofar na shiga, kamar dai jiya yau ma na tarar an goge ko’ina an saka air freshener mai kamshi, jaka ta na fara dorawa a saman tebur din na kunna desktop din sannan na nufi window ma bude, tsaye na hango shi jikin windows din office dinsa hannunsa daya a aljihu dayan kuma rike da cup. Maida window nai na rufe na dawo na zauna na bude na fara duba abubuwan da suke kan teburin. Misalin 12pm Yunus yai knocked ya turo kofar ya shigo. 

“Halima ko?”

“Yeah”

“Kuna da meeting yau, ba ki duba takardun ba”

“Na duba amman ban gane ba, ni? Kasan ni bana zuwa meeting”

“Idan general ne dole da ke saboda mail din kamfanin na is under your control”

“A ina ake meeting din?”

“Karma hotel, ku kadai ake jira tuni sun fara taronsu ma”

Na mike tsaye da sauri. 

“To ni da wa zan je?”

“Ki dauki Laptop dinki ki samu Oga a waje, yana mota yana jiranki”

Na dan ji wani iri, da shi kuma? 

“Ba ni da Laptop”

“Shi zai baki”

“Okay”

Na fada ina daukar jakata na rataya sannan na nufi kofar fita ina gaba yana baya sai duk na ji na tsawwala ba dadi namiji ya saka ka a gaba ban san mi yake kallo a bayana ba duk kuwa da kasancewar na san abayar jikina bata matse ni ba sai dai hakan be saka na natsu ba har sai na na saka shi gaba ni na koma bayansa ina tafiya.

  A harabar kamfanin na samu motar Ahmad fake ina fitowa sai direban dake gaban motar ya fito ya bude min motar, abunda ba a tana min ba, kuma ban tana ganin Ahmad wani yana jan shi a mota ba sai dai shi yaja amman yau hakimce yake gidan baya ya saka suit dark blue, kallo daya na masa na dauke kaina a yau kam kyaunsa har wani tsoro ya bani ko dan ban taba ganinsa hakimce kamar haka bane? Ko kuwa dan ban tana ganinsa da kalar tufafin bane oho, sai kamshin turare yake.

“Ina kwana…”

Ya furta min so calmly kamar ba shi ba, ganin cewar ni ban gaishe shi ba, wata kalar kunya naji sai kaina yai girma kamar dutsen dala. 

“Ina kwana…”

Na mayar masa, be amsa ni ba ya maida hankalinsa gefen titi, har muka isa be kalli inda nake ba, nima kuma ban sake kallonsa ba har muka isa. Direban ya zagaya ya bude masa nikan ban jira a bude min na bude na fito daga motar mai sanyin ac wacce har ta fara saukar min da mura.

  Wata yar karamar laptop direban ya miko min da pen sai wani littafi mai kamar diary, sannan dauko wata jaka wacce nake kyautata zaton ta Ahmad ce yai gaba ni da Ahmad din muka rufa masa baya, kana ganin kofar shiga dakin taron kasan taro ne na manyan mutane, domin an zuba securities a gurin gwanin sha’awa. Na yi zato ko sai mun yi musu wata magana ko nuna wani abun sannan su bar mu shiga ga mamaki ne sai kawai na ga an bude mana kofa, daf da zamu shiga cikin gurin Ahmad ya risuno saitin kunnena ya rada min. 

“Ki kashe wayarki”

Yana fadar hakan yai gaba abunsa ya shiga cikin gurin, ya bar a bakin kofar tsaye da mamaki, to miye wani abun mamaki? Wata kila baya son aji muryarsa ne shiyasa yai haka. Umarninsa na bi na dauko wayar na kashe sannan na maida ta a jaka na shiga cikin gurin. 

  Ina shiga na fara rabon ido, babu mutane sosai amman kusan rabin taron duk turawa ne, wasu a taeburin manyan baki wasu a teburin masu daukar darasi irinmu, ga wani katon majigi da ke saman gurin wanda da shi suke ta nunawa mutane abubuwansu. 

  A zagayayyen tebur muka zauna ni da shi, sai dai kujerar tawa tana fuskantar tashi ne kamar yadda shi ma yake fuskanta ta, amman idonsa yana gurin abunda ake nunawa a majigin. 

   Nikam sam hankali baya gurin abunda ake fada yana gurin mutanen dake gurin ne, idan na kalli wannan na kalli wacan har na kallo Ahmad, da idon yai min alama da na maida hankalina gurin abunda ake, ba musu na tattara hankalina na maida gurin mutanen, muna zaune a gurin har kusan karfe daya. Direban dazun ne wanda ya kawo mu ya sake shigowa gurin ya nufo inda muke zaune ya kai bakinsa saitin kunnen Ahmad ya fada masa wani abu. A take na ga yanayinsa ya sauya, sai ya tashi tare da diraban suka fita, ni dai ina zaune a gurin har ya dawo a yanzu kuma baya kallon kowa sai ni, just me and me alone, har aka tashi daga taron 1,30pm bayan an bi ko wane tebur an dora takeaway da ruwa da lemu. 

  An yi mana hoto da turawan da kuma sauran wadanda suka zo taron, sannan mutane suka fara watsewa, nima na tashi ganin ogan ya tashi shi be dauki komai ba daga abunda aka kawo masa na sha da ci sai direbansa ne ya dauka ni kam na kai hannu na dauki abuna, ko ruwan ban bari ba, balle kuma yar karamar takadar da aka dora mana sama wacce nake kyautata zaton kudi ne. A kofar fitowa suke bawa mutane memo da magazine da kuma calender. 

  Sai da muka shiga motar sannan ya kalleni ya kalli kayan hannuna har na ji yar kunya.

“Ina wayarki?”

“Tana cikin jaka”

“Mu gani”

Ya zuro min farin hannunsa. 

“Na kashe ta fa”

Ganin be janye hannun ba kuma be dauke idonsa daga kaina ba yasa na saka hannu a jakar na dauko wayar na mika masa, a zato na dubawa kawai zai yi ya bani sai na ga ya zura ta aljihu, kamar nai magana sai kuma wata zuciyar ta hana ni. 

  Ba mu yi nisa sosai da hotel din na ga direban ya faka motar gafe ya fita ya zaga bayan motar ya dauki abubuwan da ya dauko a gurin taron sannan ya rufe, Ahmad kuma ya fita daga motar ya shiga mazaunin direba yaja motar, ni kam ina zaune baya abuna sai dai sanyin ac yayi min yawa har na fara jin kamar ciwon kai na son kamani. 

  A nesa da masallacin gada biyu ya faka motarsa ya bude ya fita sannan ya zagayo inda nake ya bude min. 

“Zanje nai sallah ki dawo gaba”

“Ban iya tukin mota ba”

“Ban ce ki tuka ba, a front seat zaki zauna”

Na fito na bar kayan a baya sannan na rufe motar na bude gidan gaba na zauna ina ta mamakin karbe min waya da yai, can kuma na tuna da abunda yai min jiya, wata kila dan kar ayi ta kirana ne muna tare kuma baya son hayaniyar kiran, amman ai sai ya bar min wayata yace kar na kunna. 

Ni dai ina zaune a motar har aka sauko daga sallah juma’a mutane suna ta wuce, sannan ya bude motar ya shigo yai mata key muka hau titi, a hankali yake tukun kusan ko wace mota ta zo sai ta wuce mu, kusan da mu da masu tafiya kasa duk daya idan ma akwai tazara kadan ne.

“Kin na rasa yata ko?”

Na juyo na kalleshi sai na ga ba ni yake kallo ba, amman tabbas na san da ni yake domin daga ni sai shi ne a motar. 

“Eh”

“Na rasa mahaifina ma, na rasa Matata mahaifiyar Baby”

Ya sake fada still be kalleni ba.

“Allah ya musu rahama”

Be amsa da amin ba, sai yai wata maganar ta dabam.

“You got lucky baki tana rasa kowa ba, the pain of losing someone is unforgettable, mahaifina na fara rasawa, mahaifina yana da ciwon suga, a lokacin da abun ya taso masa an fitar da shi waje, a cairo ya rasu a lokacin na shiga tashin hankali sosai, kin san saboda me?”

Na girgiza kai. 

“Saboda Hajiyata, ya mace zata ji idan ta rasa mijinta? Ya da zai ji idan ya rasa mahaifinsa? Ya yar’uwa zata ji idan ta rasa mahaifinta? A lokacin nauyin Hajiya da Siyama da nawa ni kaina sai taro duk a kaina, tausayin kaina tausayin Hajiya tausayin Siyama, mu biyu kawai Allah ya bashi, daga ni sai Siyama, Hajiya tana son yayana sosai, sai dai duk haihuwarta yaranta rasuwa suke daga ni sai Siyama muka tsaya, shiyasa take son Siyama sosai wani lokacin tana kiranta da autarta, kamar yadda nima take so na sosai har take kishina, tana ganin kamar wata macen zata karbe mata ni, lokacin da muka rasa mahaifi komai na mu ya tsaya cak, ciki har da rayuwarmu domin mahaifinmu shine komai na mu, kullum Hajiya tana cikin damuwa Siyama ma haka”

Yayi shiru ya kai hannunsa ya dauki gorar ruwan da ke cikin motar ya bude ya kurba sannan ya aje. 

“Daga lokacin na fara tunanin gina rayuwata, da ta mahaifiyata da kuma ta kanwata, a lokacin ne na fara neman aure har akai nasara na auri wata yarinya, she’s my first wife but not my first love, domin na aureta ne ba wai dan na san miye soyayya ba a lokacin, a gida daban muka tare, daga lokacin da nai aure sai rayuwa ta ta canja daga matashi wanda yake zaune a gidan mahaifinsa zuwa mai mata da yake zaune a gidansa, na aje aikin da nake na soja a lokacin na cigaba da kula da kamfanin mahaifina na zinari, a cikin na bude makaranta wa Hajiyata duk wani abu na makaranta a hannun Hajiya yake zuwa, a da kullun tare da Hajiya muke karyawa komai kusan tare muke amman da nai aure sai abubuwa suka sauya, daga lokacin sai Hajiya ta fara ganin kamar matar da na aura tana kokarin mallake ni ne, sai ta cilasta min dole sai na dawo a cikin gidan mahaifina na kama part daya na zauna da ita, ita kuma tace ba zata zauna da Hajiya ba, daker na samu kanta ta amince muka zauna tare, sai kuma ta hanani cin abincinta tana cewa zata saka min magani a ciki, ta fara takura mata ta saka abubuwan da ya kamata ace mai aiki ce zatai, da ta kasa jurewa sai ta nemi fita Hajiya tace na sake ta, a haka nai aure har uku yana mutuwa saboda takurar Hajiya, ban zamu wacce ta dade ba sai mai sunanki, mace mai hakuri kamar ke, mai kawaici da sanin ya kamata, ita ta haifa min Baby Namra, a cikinta na biyu ne ta rasu, a ranar da ya rasu ni kaina bana iya gane kaina, domin rasa abokin rayuwa yana nufin rasa wani bangare na jikinka…”

Ya karasa muryarsa na rawa, hannuna na kai na dauki daya daga cikin tissue da ke cikin tissue ibox na mika masa sai ya karba. 

“Thank you”

Ya tare gefen idonsa sannan ya sake kurba ruwan, ya bude gilashin motar iska ya shigo wata kila sanyin ac baya wadatar da shi. 

“Sai ta bar ni da Baby, after that na sake aure biyu ya mutu, dayan saboda Hajiya dayan kuma saboda matar bata son Baby sai ta rika kishin yata tana ganin kamar ina nuna mata so da yawa ne, daga lokacin sai an gimgine maganar aure a gafe, na cigaba da rayuwata da yau da kullum, sai gashi na samu kaina cikin farinciki a haka muke rayuwa da kanwata da mahaifiyata da yata sai kuma sauran dangi na yan’uwa, amman dai a familyn mu mu kadai muka rage yayan Abbah, so the day I lost Baby, ba zan iya fada miki abunda naji ba, at first ban ji komai ba sai daga baya, kuma na kasa blaming kowa sai ke saboda a gurinta ta rasu, and she always talking about her friend i mean your daughter, tace na baki hakuri be kamata nai fada da mahaifiyar abokiyarta ba, so the day that i decided zan baki hakuri….”

A nan din m shiru yai sai hawaye ya gangaro ta gefen idonsa. 

“Ina son yata sosai….”

Ya fada yana rumtse idonsa na wani lokaci kamin ya bude.

“Tana da sakewa, tana da kyauta duk da kasancewar ta karama, ga ta da wayo, ga son mutane bata da abokin shawara sai ni bata da abokin wasa daga ni sai Siyama wacce ta zame mata kamar kawa, sai kuma Hajiya wacce ta zame mata mahaifiya, Baby bata da kawa ko daya sai yarki da ta samu daga baya, that’s why take yawan damun kanta kullum sai ta ganta…. ”

Ya lumshe idonsa yana sauke ajiyar zuciya da karfi. 

“Abubuwa da yawa suna faruwa saboda ni, kai ma idan kana tare da ni wani abun zai iya samunka Dan Allah ka sauke ni a nan”

Na fada ina kawarda fuskata wasu hawaye masu zafi da radadi suna sauko min, a yau kan na manta da damuwata labarin Ahmad ya ban tausayi, domin rasa uba, ya, mata, abubuwa ne da basa fassaruwa da ko wane kalar yare. Murmushi yai ya miko min tissue da na bashi

“Take your tissue back”

Na karba na share hawayen, sannan ya miko min ruwa na karba na kurba sai na rike gorar,  ina jin kamar wani hawayen zai sauko min. 

“Can I imagine your life without your parents?”

Dam dam dam na ji gabana ya yanke ya fadi, kallonsa nai kamin na kalli gorar ruwan dake hannuna. 

“Uba wani jigone na rayuwa, bayan Allah da manzosa, iyaye ne suke da muhalli na biyu a rayuwar ko wane dan’adam, daga lokacin da ka rasa uba za a fara kiranka maraya, saboda uba gangone na gingina, shi zai nemo ya kawo a ci, shi zai tufatar ya ciyar ya shayar ya ilmantar, uba wani jigone na rayuwa, gata ne, uwa kuma ita ce gaba daya rayuwar, idan babu uwa duk farincikin da zaka samu a duniyar nan ragaggene no matter what it’s, uwa abokiyar tafiyar rayuwa ce, abokiyar shawara abokiyar kuka abokiyar dariya abokiyar farinciki abokiyar bakinciki, idan da yai kuka ka ji ba a rarrashe shi ba, to babu mahaifiyarsa a kusa ne, macen da zata dauki cikinka tun yana da second daya har yai wata tara ta haife ka ta jure kashi da fitsarinka ta rayu da kai a ciwo da ba ciwo, har ka mallaki hankalin kanka? Uwa ita ce gaba daya duniyar. No never… I can’t imagine my life without one of them they are my super supporter’s my everything”

Na karasa cikin kuka, ina jin wani irin shauki da kaunar iyayena ya kara kamami, iskar bakinsa ya busar ya jingina da kansa jikin kujerar motar yana kallona kamar bashi ba. 

“Zan kai ki gida gurin Hajiya ki yi sallah”

Na share hawayena ina kallonsa. 

“Mun tashi daga aikin ne?”

Na gyada min kai yana kokarin parking motar still idonsa na kaina. 

“Idan haka ne ai kara na wuce gida kawai”

“No gurin Hajiya za ki yi sallah”

Bance masa komai ba sai na maida dubana gurin yan yatsun hannuna, ina jin faduwar gabana yana karuwa ga wani uban ciwon kai da ya saka ni a gaba, ban san miyasa yau Ahmad ya zame min wani dabam ba shi ba. 

  Key yai ma motar muka hau titi wannan karon ba mu yi tafiya mai nisa ba muka isa gidan, horn daya ya danna aka bude masa gate, ya kunna kai a cikin gidan, be yi farkin a ko’ina ba sai bakin kofar falonsu, fita yai shi kadai yace na jira shi a motar ya shiga cikin, be jima ba ya fito ya bude min motar yace na fito, haka na fito ina jin jikina ba kwari na shiga ciki, kamar dai wacan karon wannan karon ma Hajiyar da far’a ta tarbe mu sai dai yanayin yadda take kallon fuskata tana nuna alamar tausayi. 

  Bayan mun gaisa, tai ma Kanwarsa magana tace ta kai ni ciki nai sallah, da sauri yarinyar da aka kira da Siyama ta tashi tai min jagora har dakin Hajiyar, a bathroom dinta nai alwala ko da na fito an shimfida min carpet an dora Hijabi sama, sai kawai na dauka na saka na fara sallah azahar a lokacin uku ta kusa. Ina sallah shaidan ya fara yayo min tunani kala kala, kamin na gama sallah jikina har rawa yake, ina gamawa na cire hijabin na dauki veil din abayata na yafa na fito falon inda Hajiyar take na zauna, Ahmad ma yana zaune a falon ina son nai masa magana na kasa.

“Siyama kawo mata abincin”

Ya fada yana kallon yanayi gaba daya idona ya fito fuskata ta sauya.

“Wayata ina son magana da…. ”

Tun kan na karasa ya tari numfashina.

“Zan baki anjima”

Wannan karon kallonsa nai da kyau. 

“Wa na rasa Ahmad? Uwa ko Uba, ko yaya? Ko kane? Fada min”

Mikewa tai tsaye yana kallona sai nima na mike tsaye. Can kasa kasa na jiyo Siyama na fadin. 

“Ku fada mata gaskiya mana, dole ne ta sani”

“Siyama fita ki bar falon nan”

Ahmad ya fada mata a tsawace, kamar tana jira ta juya ta fice cikin fushi. 

“Ka fada min wanda na rasa, ba zan iya dawo musu da rai ba, iyakar abunda zan yi hakuri ne”

“Muje na kai ki gida”

“Ka bani wayata”

Na daka matsa tsawa da wata irin murya daban taba sanin ina da ita ba, gaba daya jikina rawa yake. 

“Ina da kanen, idan an rasa Uba sun zama marayu wa zai kula da su, idan na rasa Uwa wa zai maye musu gurbinta shikenan sun rasa gata”

Na fada ina rufe ido kamar mai nazari.

“Allah baya barin wani dan wani duk a can muka fito iyayenmu sun tafi sun bar mu, kuma a can zamu koma gaba daya”

Mahaifiyarsa ta fada idonta cike da hawaye, takawa na fara yi sai na ji kafar ta malgwade ina neman faduwa har sai da tai saurin rike ni, a hakan na sake unguri takawa kafafuwan suka fara rawa sai ta na tsaya cak, da nai unkuri na uku sai na tafi zan fadi har sai da Ahmad ya rike ni da kanshi ya zaunar akan kujerar. 

“Ki natsu sai na kai ki gida”

“Ka kaini yanzu”

Na fada kai tsaye tare da mikewa tsaye na fara tafiya cikin karfin hali, ba shiri na ji numfashina yai sama wani hudu ya baibaye idona, jikina kuma yai arba da kasa….. 

__________________________

Allah ka jikan mahaifina kai masa Rahama ka saka aljanna ta zama makomarsa, Mahaifiyata kuma ka karasa mata lafiya da kwanciyar hankali da natsuwa ka yafe mata kurakuranta kasa ta cika da imani 🙏 da duka sauran iyayenmu musulmai 😭🙏

Rashin iyaye wani ciwo ne da ba a manta shi 💔💔💔 may Allah see us though. 🙏

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

GOBE NA 13

Advertisement  *GOBE NA…* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy  1️⃣3️⃣ “Kamar baki da gaskiya Halimatu…” Sai da na kalli…

GOBE NA 4

Advertisement  *GOBE NA…* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy  4️⃣ “Sa’adatu kenan, kwana biyu ma kin daina dan lekowa,…

GOBE NA 48

Advertisement  *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  4️⃣8️⃣ Tun daga yanayin tafiyata zaka fahimci ina cikin wani irin nishadi…