GOBE NA 48

Advertisement

 *GOBE NA…*

By Khadeeja Candy 

4️⃣8️⃣

Tun daga yanayin tafiyata zaka fahimci ina cikin wani irin nishadi marar misaltuwa,  na fito daga cikin gidan na nufo inda motar Ahmad take fake ya sauke gilashin motar yana kallona har na karaso, da kansa ya miko hannunsa ya bude min motar, na shiga ciki na zauna ina gyara jakata. Sai yai motar key muka hau titi sannan ya kalleni. 

Advertisements

“Happy?”

Na gyada masa kai idanuwana suna kokarin cika da hawayen jindadi.

“Yes”

Sai yai kyakkyawan murmushin daya karawa fuskarsa kyau. 

“Thank You”

“No thank you da kika amince, hop dai kin fada musu ke za ki yi ba ni ba”

Advertisements

Na yi shiru ina kallon gorar ruwan daya dauka zai sha.

“Sun jidadi sosai, kuma sun yi supporting”

Murmushi kawai yai ya kalle ya karasa kurbe ragowar ruwan, ba mu yi wata tafiya mai nisa ba ya faka gefen titi yana kallona. 

“Bari na karbo ruwa shagon can, bana iya zama ba ruwa a mota”

Bude motar yai ya fita, da wani irin kallo na bishi na jindadin daukar nauyin duba lafiyar Kabir da yai, haka Allah yake lamarinsa idan ya zo taimaka maka sai ya maka hanyar samun abun ko ta ta silar wani ne, and farincikin dana gani a fuskar yan’uwan Kabir a yau da naje musu da labarin ya kara faranta min rai fiye da kima. Wata farar mota ce ta faka gaban ta Ahmad sam ban kawo komai a raina ba, har sai da na hango Aminu ya fito daga cikin motar a fusace ya nufo inda nake, ganin hakan yasa na bude motar na fito na rufe tun kan ya karaso. 

“Halima me kike a cikin motar nan?”

Haka ya aiko min da tambaya kamar wani ubana. 

“Ban gane mi nake a ciki ba?”

“Abunda kike be dace ba, tun dazun na hango ki a cikin motar nan ina biye da ku har kika shiga wani gida kika fito, ya kamata ki san abunda kike fa wannan ba muharramin ki bane, kuma ki rika tunawa cewa kina da yara”

“Wace irin magana kake yi haka Aminu?”

“Kin san me nake nufi”

Ya fada yana kara hade fuska, sai wani huci yake kamar ba shi ba. 

“Ya akai?”

Ahmad ya tambaya yana kallona hannunsa rike da gorar ruwa biyu.

“Ba komai”

Na fada ina dauke idona daga barin kallon Aminu. 

“Oh ba komai za ki ce masa? Malam akwai komai wannan mata ta ce, miye hadin ka da ita?”

“Who’s this?”

Ahmad ya tambaya yana kallona. Sai Aminun ya amsa masa da kansa cikin fusata. 

“Mijinta ne uban yayanta”

Wani kallon uku saura kwata Ahmad yai masa. 

“Sannu Uban yaya, da alama dai kana shaye shaye, domin mai hankali ba zai yi abunda kake yi ba”

“Ba shaye-shaye nake ba, ciye ciye nake, ka fita hanyar tun kamin dare yai ma, domin matata ce”

“Babu wani abu a tsakanina da shi Aminu, boss dina ne a gurin aiki, kuma kai baka isa ka hanani magana da wani namijin ba, domin babu igiyar aurenka a kaina”

“Amman akwai yaya a tsakaninmu ko?”

Ya fada cikin daga murya mutane har sun fara mana taro, Ahmad ya bude min front seat. 

“Shiga ki zauna”

Ina kokarin zaunawa Aminu ya fisgo Hijabina har sai da fuskata ta daki ganbun motar. 

A take Ahmad ya wulgar da gorar ruwan dake hannunsa ya zabgawa Aminu mari cikin zafin nama. 

“You’re very very stupid”

Aminu ya zaburo zai rama Ahmad ya rike masa hannu ya wulgar. 

“Ni ka mara? Ni ka mara? Na san ko ni wanene? Akan matata?”

Shine abunda yake ta fada yana nufi gurin motarsa ya dauko wayarsa daga can gurin motar ya tsaya yana wayar, kamar yadda Ahmad din ma yake waya a kusa da ni. Faruk naji ya kira sunan mutumen sannan ya fada masa abunda yake bukata tare da bashi addireshin inda mike. Sannan ya juyo ya kalli gefen goshina dake zubar da jini. Zagayawa yai ya bude motar ya dauko tissue ya mika min. 

“Sannu”

Ya fada cike da nuna danuwarsa. Sannan ya kalli Aminu dake kokarin shiga motarsa yace. 

“Indai ka cika kai dan iska ne ka tsaya nan”

A take Aminu ya rufe motar ya sake nufo inda muke. 

“Me kake nufi? Tsoronka ake ji? Uban waye kai a cikin garin nan? I warning you Wallahi Wallahi idan na sake ganinka da matata sai na halaka ka, dan iska kawai marar mutunci mai neman matar mutane”

Uffan Ahmad be sake ce masa ba, sai danna wayarsa yake. Aminu kam duk maganar daya yago sa ya yabawa Ahmad, ban tana ganin bacin ran Aminu irin na yau ba, tun da be tana fada a kaina ba, be tana nuna damuwarsa dan wani ya kula ni ba sai yanzu, jikinsa har wani rawa yake, kana kallonsa ka san kishi ne ke dawainiya da shi, kuma na banza domin a yanzu kam na masa nisa. 

“Ina kokarina ashe kai ke dauke mata hankali, wawa kawai”

Ya karasa yana kai kafarsa ya shuri motar Ahmad, har lokacin Ahmad be kula shi ba, sai da motar soja ta iso, da hannu Ahmad ya nuna musu Aminu.

“Ku masa shegen duka sai ya dawo hayyacinsa”

Ba ni kadai ba duk wanda ke a titi kallon motar sojojin yake, a yadda naga yana wayar na dauka police zai dauko ashe uban police ne, kamar sun samu nama haka suka ka kama Aminu, suka ci kwalarsa amman be daina bala’in ba. 

“Ni zaka saka a ciwa mutunci? Sai na wulakanta ka wallahi, ka shirya haduwa da ni…”

Ko da suka saka shi motar har sun fara dukanshi. Mutane sai bin motar sojojin da kallo suke kamin su juyo kan mu kallo ya dawo gurinmu. Ba mu bar gurin ba sai da Ahmad ya kira direbansa ya tafi motar Aminu sannan ya shiga tashi motar yai mata key. 

  

“Kin yi kokari haka kika zauna da mahaukacin nan? Be cancanci mata irinki ba, tun farko ya kamata ayi bincike kamin a aura masa ke, how will you face the world ki ce wannan uban yayanki ne? Wani irin hauka yake haka?”

Ni dai bance uffan ba bayan hawayen da nake. 

“Shiyasa yake cin zalinki, komai akai miki sai kuka da abun dariya dana bakinciki ko wane kuka dai i wonder how your next husband will handle you”

Ya fada da kamar fada, sannan ya faka motarsa gefen titi ya fita, ya bar ni a cikin motar ni kadai. Tun ina hawayen da gaske har ya daina zuwa sai da ya leko ta gilashin motar ya kalleni sannan ya bude ya shigo muka cigaba da tafiya. Asibitin da aka taba kwantar da ni a lokacin da Baba ya rasu ya nufa da ni, sai da ya faka motar sannan ya zagayo side dina ya bude min motar ba tare da yace min komai ba, ni kuma na saka kafafuwana waje na fito sannan ya rufe motar yana gaba ina biye da shi har muka shiga cikin asibitin, har office din likitan muke da kansa yaja min kujera ya zauna sannan ya zauna a dayar kujerar ya risino yana kallona. 

“Bari likitan ya zo yanzu kin ji? Sannu”

Ya kasa dauke idonsa a kaina ni kuma na gagara daga nawa idon na kalleshi. 

“Ji yadda ya gusar da farincikin da kika ji dazun, cikin kankanen lokaci, ina mamakin yadda akai kika auri mutunen nan tun farko….”

Ya fada yana kallon likitan daya shigo office din, wacan likitan ne dai wanda ya duba ni a wacan karon. Sai ya daga fuskata ya duba goshin nawa sannan ya tambayi abunda ya faru.

“Buguwa tai ta murfin mota”

“Ayyah sannu”

Ya fada sannan ya juya ya fita, ba dade ba ya dawo dauke da wani karamin akwaiti sai ya hanyo dayar kujerar ya zauna.

“Cire Hijabinki”

“Ba sai ta cire ba”

Ahmad amsa masa tun kamin nai wani unkuri.

“Indai gyaran kake so a mata dole sai hijabin ya matsa daga goshinta”

Doc Nura ya fada yana kallonsa, sai ya taso ya karaso kusa da ni, ya daga fuskata sama ya saka hannunsa ya janyo hijabin nawa ya raba shi da fuskata kamar zai cire sai kuma naji ya yagashi, sannan ya maida min shi a jikina ya zamana kaina na iya wucewa hijabin ya sauko saman wuyana.

Murmushi kawai likitan yai ya dauko safar hannu ya saka sannan ya soma gyara min goshin, idan naji zafi sai ya rumtse ido and Ahmad na kusa da ni yana min sannu. Bayan likitan ya gama ya saka min bandeji sannan ya rubuta mana magani.

“Zaki iya jirana a mota”

Ya fada yana mikomin key din motar, ba musu na karba na juya na fito daga office din, ina tafe ina tunanin haukar Aminu har na isa gurin motar, amaimakon na bude na shiga ciki na zauna sai kawai na zabi tsayawa har ya fito, ya dauki lokaci a ciki kamin ya fito ya nufo inda nake tsaye jikin motar, hannu ya miko min na bashi key din ya bude ya shiga sannan nima na shiga. 

“Kika yi ta tsayuwa waje? Ko baki iya budewa ba ne”

“Na iya”

Kallona yai kamar zai yi magana sai kuma ya dauke kai yai ma motar key muka kama hanya, ba kai ni gida ba sai da ya biya ta wani shopping yai min siyaya sannan ya shiga da ni cikin unguwarmu. 

“Ban san ko kina son na kai ki har kofar gida ba ko kuma na aje ki a nan”

“Nan din ma yayi na gode sosai, dan Allah kai hakuri da abunda Aminu yai maka….”

“No karki damu, ni be min komai ba”

Ya mika hannunsa baya ya dauko ledodin ya miko min.

“Ki rikawa yara wannan, and ina son na yi miki maganar karatunsu?”

Na masa kallon rashin fahimta. 

“I mean idan kin amince i will take them back to Gwarzo International school” 

“A a suna makaranta a yanzu, da na yi deciding na canja musu sai kuma na yanke shawarar kara na bari har su kai Secondary school sai na nema musu private”

“Baki son makarantarmu ne? Then i will pay su shiga wata private school din”

“Ba haka ba ne…”

“Ba haka bane minene?”

A yadda na lura Ahmad yana daya daga cikin irin mazan nan masu saurin fushi, kuma abun kankane kan iya bata masa rai, domin tun kamin na karasa ya tari numfashina cikin muryar dake nuna fusatarsa a fili, jin na yi shiru ina kallonsa sai yai sauke ajiyar zuciya ya fara magana slowly. 

“Kin dai ga mahaifinki ba wani kula zai yi da su ba, ke kuma a yanzu kina neman mai taimaka kiki ne, to miye a ciki dan na dauki nauyin karatunsu? Uba kamar wannan? Zai tsaya ya damu da rayuwarsu ne ma balle karatu? Idan mutum ne mai hankali da natsuwa zai same mu a titi ne yana ihu and called you his wife? Imagine?,  i said idan makarantar ne baki gamsu da ita ba zan iya biya su yi wata makarantar, idan kuma taimako na ne bakya so then get out of my car”

Ya karasa fuskarsa babu alamun wasa, ni kan kallonsa kawai nake mamaki cika ni, to ana taimako dole ne? Idan ya maida su a makarantar wani abu ya faru sai kuma a sake ciresu? Bana son yawo da karatunsu a yanzu domin shine rayuwarsu. Bude motar nai nai fita. 

“Okay fita kika yi? Fine…”

Jin ya fadi hakan yasa na dawo cikin motar na zauna cikin damuwa. 

“Nace ki fitar min daga mota”

Yawun bakina na hade na na kalleshi a natse nace. 

“Ba wai bana son karatun nasu ta dalilinka ba ne, bana abunda ya faru da su a baya ya sake faruwa yanzu, ko a da na dawo gida a lokacin da aurena ya mutu Abdallah ne yake kula da su ya saka su a makarantarku, daga baya kuma sai ya cire su wanda hakan be min dadi ba, a dole tasa na dawo da su makarantar gwannati”

“Sai kuma aka fada miki kowa kamar Abdallah ne idan na saka sun cire su zan yi”

“Shi ma ba da son ransa ya cire su ba, mahaifiyarsa ce ta cilasta shi saboda bata son alakar da ke tsakaninmu, bana son hakan ya sake faruwa”

“Babu abunda zai sake faruwa, Hajiya bata da matsala da ke, kusan ita ta fara min magana tun kamin na yi tunanin yin haka, so if you want zan aiko direba gobe ya dauke su, idan kin yi shawara pls let me know”

Ya karasa yana miko min katinsa. Na kalli kattin kamin na kalleshi na ce. 

“Na amince”

Murmushin yai har lokacin be janye katin daga miko min da yake ba, wata kila son yake na kira so that ya samu Number na, domin tun da nake a rayuwata be tana kirana ba bamu tana waya ba. 

Ganin na ki karba yasa ya maida katin ya aje, ni kuma na rufe masa motarsa, na kama hanyar gidanmu na barshi a gurin tsaye ni dai har na shige gida ban ga motar ta bar gurin ba. 

  Ina shiga gida hankalin kowa ya tashi ganin goshina da bandeji. A falon Inna na zauna ina labarta musu a abunda ya faru.

“Kai amman wannan mutunen ya burge ni, ai daman Aminu daidai ne ya samu mai cin ubansa….”

Hafiza da fada cikin jindadi, kamar daga sama muka ji Namra dake sanye da uniform ta fashe da kuka. Husna ta nuna da hannu tana fadin. 

“Kin ga wacan kin ga wacan munafukace, ke yanzu duk abunda ubanki nai muku har son shi kike?”

Mama ta tari numfashinta tana fadin. 

“Karki ga laifinta a duk yadda uba ya lalace ko uwa ta lalace ko da ya lalace akwai kauna a tsakani kuma baka son wani abu ya same shi, amman dai yakamata ki masa magana kar ya saka su masa mugun duka fa su ji masa ciwo ko su kashe shi ma”

Sai a lokacin wannan tunanin ya zo min, kar su masa dukan mutuwa laifi ya dawo kaina, daman kuma ga halin da nake ciki, ko kuma shi Ahmad din na ja masa matsala. 

Haka na wuni da tunanin abun, sai a lokacin na ji haushin rashin karbar number sa da ban yi ba. Bayan an sallame sallah magariba Mama take min wata magana wacce ban taba kawo ma kaina ba. 

“Halimatu, ya kamata ki daina shiga motar maza haka nan, ba mutuncin ki ba ne, yanzu ne sai ki ji mutanen unguwa sun fara magana, ni kaina ba zan so ace yau kina cikin motar wannan gobe kina wannan ba inda ba ta kama dole ba”

Gaskiya ta fada min wacce babu mai fada min ita sai mai kaunata, be kamata ina shiga ko wace irin mota ba, na sani yanxu ne sai a fara magana a unguwa ana cewa na lalace ko kuma ina jaye jayen maza barka, wasu ma kan iya dogara da cewar ganin mahaifina baya raye ne. 

“In-Sha-Allah zan kiyaye Mama, amman yana da wahala na shiga motar wani idan ba da wani dalilin ba, amman duk da haka zan kara kiyayewa”

“Hakan yayi, Allah ya fito miki da mijinki na gari ki yi aure”

“Amin”

Na amsa tare da amsa sallamar yaron dake ta doko sallama tun daga kofar gida. 

“Wai ance ana sallama da Halima”

“Je kace waye”

Yaron ya fita be dade ba ya dawo yace. 

“Yace wai Abraham ne”

“Je kace gani nan zuwa

Bayan yaron ya wuce Mama ta kalleni tace. 

“Abraham kuma? Wane irin sunana ne wannan?”

“Mama bari na dawo dai”

Na tashi already ina sanye da Hijab dina na nufi kofar waje, a inda ya saba tsayuwa ya tsaya, ni kuma na karasa gurin ina tunanin da me kuma zo wannan karon. 

“Gani”

Na fada ina kallonsa. Sai ya fito daga cikin motar da yake zaune ya kalleni. 

“Na taba fada miki ina son ki”

“Ka sha fada min”

Sai yai murmushi mai sauti. 

“Ina son ki Halima, ko da ba zaki so ni ba ni dai ina sonki, na kwanta da mata da yawa, ba su yi ciki ba sai ke da nai ma fyade, likito ma sun fada min ba zan iya haihuwa ba saboda kwayoyin halittata ba su da karfin da zasu ba mace ciki, na sha magani har na gaji, amman ji just one mistake kikai ciki, mi zai saka ba zan so ki ba? Na fada miki rayuwata tana cikin hadari zan iya mutuwa a ko yaushe, domin a duk lokacin da asirina ya tonu wow….”

Sai yai shiru yana sotsa bakinsa. 

“Na kamu da mugun son ki, ba zan iya cutar da ke ba, idan ma tsoro kike ji ki daina, ki kwantar da hankalinki ki daina sakawa ana bincike akaina, domin idan asirina ya tonu bomb….”

Ya fada yana cikawa bakinsa iska, ni kam mamaki ya gama cika ni, sakawa ana bincike akansa kuma? 

“Ni ban saka kowa yai bincike ka ba”

“To wa ya saka? Mutumen nan ko? Why kika fada masa sirrina”

“Ni ban fada masa ba”

“Ya za’ayi ya sani idan ba ki fada masa ba”

“A wasikar da na rubuta ranar children day ya ji”

“Ko mutum yaji idan be san ki ba ba zai gane waye ba just tell me the truth”

“Ban maka karya ba, labarin yarsa da kamfaninsa ya shigo ciki shiyasa ya gane cewar nice, a ranar da ya gan ni da kai kuma sai ya gane cewar kai ne mutumen da ke bibiyata”

“Okay…..”

Ya furta kamar mai nazari. 

“Saurayinki ne?”

“Why”

“Nothing”

Ya amsa ni fuska ba yabo ba fallasa.

“Miya ssmu goshinki?”

“Na ji ciwo ne”

“Garin ya?”

Na yi shiru ban amsa shi ba, be sake ce min komai ba, ya bude motarsa ya shiga, ta gilashin motar ya miko min bandir din yan 1000. 

“Zaki iya yin wani abu”

“Na gode”

Na fada ba tare da na karbi kudin ba na juya.

“Halima magana ta karshe ina rokonki dan Allah ki amince ki aure ni, i promise you zan kula da ke ba zan taba barin ki samu damuwa ba, ban ce ki so ni auren kawai nake bukata dan Allah” 

Juyowa nai na kalleshi hannayensa biyu a hade suke alamar rokona yake yi. 

“Dan alfarmar Annabinki, dan Alfarmar Addininki, dan darajar mahaifinki, i promise you zan kula da yayanki zan taimaki familynki zan saka ki cikin farinciki marar misaltuwa”

Kasa ce masa komai nai jiki a sanyaye naa juya na dawo gida, zuciyata na kyautata zaton Ahmad ne ko Abdallah yake bincike akansa.

AHMAD POV. 

Zaune yake a dakin Hajiya hannunsa rike da karamin plate wanda aka zubawa kwadon zogale da yaji kayan hadi ga tumatir da albasa a ciki. 

  

“Kasan Khadija ai ta gama karantarta”

“Wace Khadija?”

“Khadija dai, yar Hajiya Hanne”

“Okay na gane”

“Shekarar nan zata fara service”

“Okay congrats to her”

“Shine shekaranjiya na ke yi ma mahaifiyarta maganarka nace me zai hana a hada ku?”

“What?”

Ya tsaya da cin zogalen da yake yana kallon Hajiya. 

“Ni. Did i say ina son ta?”

“Tana da kyau ai”

“Ban ce bata da kyau ba Hajiya, ni ma ai ina da kyau, ammn ban ce miki ina sonta ba Hajiya”

“To ai naga ita din budurwa ce, kuma na san budurwa kake so shiyasa”

Kasa cewa komai yai kuma ya kasa hade zogalen da ke bakinsa, ya san Khadija tana da tarbiya ga kyau ga ilmin ga wayeye kuma gata budurwa amman shi har ga Allah be ji ta kwanta masa a rai ba, and taya zai yi facing mahaifintar kanwar mahaifiyarsa yace mata be amince ba? Why Hajiya zata masa haka? Siyama ce ta shigo dakin rike da waya tana latsawa.

“Yaya mutanen nan fa suna ta jiranka a falo”

“Oh ni wallahi har na manta da su, wai me suke so ne”

Hajiya ta fada tana kallon Ahmad, daker ya hade zogalen da ke bakinsa ya aje plate din yana kallon kanwarsa.

“Je ki fada musu, ba ni za su bawa hakuri ba, su je su roki Halima idan ta yafe musu then their son will be free”

Siyama ta yi wani fari da ido. 

“Wace Halima kuma?”

“Just go and tell them”

Ba musu ta juya ta fice daga dakin. 

“Wace Halima Gwarzo?”

“Halima dai matar nan mahaifiyarsu Namra, ex-husband dinta ne ya fasa mata goshi da motata”

“Garin ya”

Mikewa yai tsaye yana fadin. 

“Ina zuwa”

Ya fice daga dakin Hajiya na binsa da kallo. 

__________________

Halimatu & Aminu

Halimatu & Ahmad

Halimatu & Abdallah

Halimatu & Abraham 

Bari muga Team da suka fi yawa.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

GOBE NA 20

Advertisement  GOBE NA…* By Khadeeja Candy  2️⃣0️⃣ DEDICATED THIS PAGE TO Mai Dambu, Allah kara miki lafiya Gwanata❤…

GOBE NA 49

Advertisement  *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  4️⃣9️⃣ A lokacin daya fito falon ya samu Mahaifiyar Aminu da wata…