GOBE NA 49

Advertisement

 *GOBE NA…*

By Khadeeja Candy 

4️⃣9️⃣

A lokacin daya fito falon ya samu Mahaifiyar Aminu da wata yar’uwarta da dan’uwan mahaifinsa. 

  Ganin Ahmad yasa suka kara marairaice fuska, shi kuma ya mikawa namijin hannu suka gaisa. Sannan ya amsa gaisuwar da mahaifiyar Aminu ke musu. 

Advertisements

“Case din ba a hannuna yake ba, kuma ba ni aka jiwa ciwon ba, so if ita Halima tace ta yafe then ur son is free”

“To yanzu ita zamu je mu roka kenan?”

“Definitely”

Hajiyar Aminu ta marairaice fuska.

“Dan Allah dan Annabi ka taimaka mana, a saki Aminu hankalinmu duk a tashe yake”

Advertisements

“Haba Hajiya me kike so nace miki dan Allah? Idan Halima ta hafe masa Wallahi ba ni da matsala ni”

“Idan kai baka san ni ba ai ita Hajiya ta san ni, dan Allah kira min ita Yarinyar”

Ta karasa tana kallon Siyama, ba musu Siyama ta tashi ta nufi sama, bata dade ba ta sauko tana latsar waya. 

“Gata nan zuwa”

Ba a bata lokaci ba Hajiya ta sauko ta zauna saman kujera, tana yi ma Hajiyar Aminu kallon rashin fahimta. 

“Hajiya ina wuni?”

“Lafiya kalau ya gida?”

“Alhamdulillah Hajiya ba ki waye ni ba?”

“Wallahi ban gane ba, kila an kwana biyu”

“Be ke kika yi Shugabar lamurran mata ba, a lokacin Gwanna Garba Doru?”

“Eh Haka ne”

“Ni kuma ai na yi bawa matar Gwanna shawara a wacan lokacin”

“Allah sarki kin san abun da yawa, ya kwana biyu”

“Alhamdulillah, dan Allah Hajiya alfarma nake nema ki saka baki dan ki ya sako min da na Aminu, ance yana hannun sojoji dazun sun kira ta wayarshi suka sanar mana suka ce wai ya samu matsala da dan wajenki, shi kan shi Aminun na san be san Gwarzo ba da ba zai yi fada da shi ba Wallahi”

Hajiya ta kalli Ahmad. 

“Wani abun ya hada ku ne?”

“No ba komai, kawai dai ina tare da Halima ne dazun mun je yin wani abu, sai ya fito a titi yana mana ihu kamar mahaukaci, kamin nai wani abu ya buga ta da mota, that’s why na kira Faruk yasa a aka dauke min shi”

“Subhanallahi, to ita Halima ta san shi ne daman?”

Hajiyar Aminu ce ta amsa mata. 

“Eh shine baban yayanta, tsohon mijinta ne da kaddara ta raba”

“Allah sarki, Gwarzo ka kyale shi dan Allah”

Ta karasa tana kallon Ahmad, shi ma kallonta yai. 

“Ba ni da matsala Hajiya, kawai taje ta bawa Halima hakuri ita akai wa laifi idan ta hakura, shikenan ai ba matsala ba ce”

Hajiya ta sake kallonsu.

“To kuje ku ji ta bakinta idan ta amince a sake shi, ba matsala ba ne, tunda ita a kaiwa laifin yana da kyau aji ta bakinta”

“To Hajiya, bara muje indai Halima ce ai bata da matsala”

Cikin rashin jindadi Hajiya ta tashi tare da yan’uwanta suka fice. Siyama kamar jiran take su fita sai ta kalli Ahmad da sauri. 

“Yaya ina kuka je hala?”

Kallonta yai yasan ba komai ke cinta ba sai gulma, ashe duk abunda ake hankalinta na gurin amman ta fake da latsar waya. 

“Wani guri”

“Wani guri ina? Ya ganku a inda be dace ba ne?”

Tambayar da Hajiya tai masa tana kallonsa cike da son jin irin amsar da zai bata. Dan murmushi yai ya shafa kansa. 

“No akan wani marar lafiya ne da nace zan dauki nauyin maganinsa, kuma ita ta san mutunen shiyasa muka je tare tai ma familynsa magana shine kawai”

Dariya Siyama tai. 

“Oh kishi yake dan ya ga kana sonta”

“She’s just my friend”

Ya amsa ba tare da ya kalleta ba. 

“Yeah i mean friend, like friend….”

Ta maimaita tana yi ma Hajiya kallon gulma. 

“Gwarzo ai baya son bazarawa, shiyasa na nema masa auren Khadija ai, budurwa ce kuma mai tarbiya”

Kallon Hajiya kawao yai ya dauke kai be ce uffan ba. 

HALIMATU POV. 

Da tunanin Abraham na shiga gida, rokon da yai min ya karya min zuciya, indai har mutum zai hada ka da Annabi ya roki abunda kasan zaka iya masa anya ya dace na tsallake? Ko da musulunci da yace zai yi? Ko dan ya tuba da gaske? Sai dai me? Har gobe bana son jin wani kalami daga bakinsa bana kaunar ganinsa kuma bana tunanin zan koyi soyayyarsa balle har na iya kamar yadda yake tunani.

To me zanyi? Na yafe masa be bar ni ba, na san idan ma na daina kulashi hakan ba zai wadatar domin kuwa ba kyaleni zai yi ba, to ko dai na kai kararsa a wani gurin ne na fallasa sirrinsa? 

A hankali na sauke ajiyar zuciya ina ta tunanin mafita, hakika ina neman abokin shawara wata zuciyar na nace min na fadawa Mama ta wani bangaren kuma ina jin tsoron yadda hankalinta zai tashi, gashi daman ba lafiya ta isheta ba ga kuma rashin mijinta ina ganin kamar idan na labarta mata hakan zai iya janyo mata matsala, amman ai bani da abokiyar shawara sai ita bana da wanda ya fita, ko ba komai na san dole zata tambayi waye Abraham kamar yadda ta bukata dazun. Har na unkura zan tashi da zimmar shiga har uwar daka na labarta mata komai sai muk ji sallamar mata biyu tun kan na ga mahaifiyar Aminu na gane cewar ita ce saboda yanayin maganarta. 

  Bayan Inna ta amsa musu suka nufo falon Mama suna ta doka sallama, ni da Mama dake can cikin daki muka hada baki gurin amsa musu, komawa nai na zauna Mama kuma ta fito daga dakin sanye da Hijabinta. Kallo daya zaka yi ma Hajiya ka fahimce cewar tana cikin tashin hankali, daman can haka take Allah ya zuba mata son yaya musammn Aminu bata kaunar abunda ya same shi, yana daya daga cikin dalilin daya saka ko fada mukai ko na kai kararsa sai ni ta ba ni laifi. 

Sama sama suka gaisa da Mama har take mata ya karin hakuri, amman idonta na kaina tana min wani kallo kamar na mamaki. 

“Halima gurinki muka zo”

“To Hajiya Allah yasa ba laifi nai ba”

Na fada ina kallonta sai ta dan tabe baki tana murmushin da ni kaina na san be kai zuci ba. 

“Akan maganar Aminu ne da kika sa aka kama, yanzu abunda kika yi kin yi daidai kenan? Ko ba komai ai uban yayanki ne komai Aminu ya lalace sai kin fi kowa jin ciwo, haka komai Aminu yai arziki sai kin fi kowa jindadi, saboda yayan da ke tsakani, yanzu daidai ne ki saka sojoji su kama shi bayan kin san ba za su masa da sauki ba?”

Da fari murmushi nai kamin mamaki ya biyo baya ya na jin kalamanta na rainon waya da take akai.

“Aminu ba ni yai fada ba, kuma ba ni na saka a kama shi ba”

“To bakinku dai daya kenan? Shi yace ba da shi yai fada ba da ke yai, ke ma kin ce haka, yanzu ina gaskiyar magana a nan…”

Mama ta tari numfashinta tana kallona. 

“Ba haka zaki ce ba Halimatu, ki fada gaskiyar abunda ya faru, kuna hanya ne na ganku ya fara fada yana kiranta matarsa yana masifa da shi wanda suke taren, sai kuma gashi ya buga kanta da murfi mota a kokarinsa na ya jnyota daga jikin motar mutumen sandiyar haka ya fasa mata goshi dai kina gani a goshinsa, shi kuma wanda suke tare yaji haushi ya saka soja suka kama shi”

“Ah to ya isa ya raba tsakaninsu ne, tun da akwai yaya ai dole ne yai magana da ita, waya san gobe ban da Allah, aka san abunda gaba zata haifar? Ko aurenki yai ya isa ya yanke alakarku ne ai alaka Allah ya riga ya hada Wallahi”

Ba mama kadai ba ni kaina kallonta nake da mamaki, sai masifa take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba sai fada take da Ahmad din da baya nan a zatonta so na yake, a raina na ce idan kin isa ki je a gansa ki yi. Matar da suke tare wacce ita mahaifiya ce a gurin Aminu ta dakatar da ita.

“Yanzu dai ba ta wannan muke ba Hajiya, shi bazarawarin naki yace sai kin amince sannan zai saki Aminu, dan haka yanzu ki tashi muje ki fada masa cewar kin yafe”

Kallonta nai wani irin dadi ya lullube ni ko ba komai Ahmad ya mutuntani kuma ya nuna musu cewar ina da muhimmanci ba kamar yadda danta yake wulakanta ni ba. 

“Kuje ku fada masa na yafe”

“A a tare zamu tafi ki fada masa, tunda idan munje zai iya cewa sai ya ji ta bakinki ko kuma ki kira wayarsa a yanzu nan ki masa magana”

Hajiyar Aminu ta fada. Bana son na fada musu bana da number su kamar yadda bana son zuwa gidan domin kawai fada masa cewar na amince, ina kokarin yin magana Mama ta tari numfashina

“Halima tashi kuje ki fada masa da bakinki kim yafe”

“To Mama”

Na tashi na shiga ciki, Hijabin dake jikin na canza daga fari zuwa brown dogo har kasa mai gyale sannan na bisu muka fita, ashe har da namiji suke ya tsaya a waje, wanda kanen mahaifin Aminu ne. A motarsa muka shiga ya dauki hanyar gidansu Ahmad, tun da muka shiga motar babu wanda yace uffan har muka isa.

   Harabar gidan tana nan da kyauta kamar kullum, ga haske ta ko’ina gwanin sha’awa, musamman bangaren da aka zagaye da fulawoyi an saka wasu kananan gulub sun haska su gwanin sha’awa.

  Fita mukai daga motar muka nufi kofar shiga falon Hajiya ta fara knocked, ganin an dade ba a bude kofar ba ta sake yi, nan ma shiru har muka soma gajiya da tsayuwa. Hakan yasa na nufi kofar da zimmar na kwankwasa da karfi ta yadda za su ji wata kila bugawan da Hajiya take basa ji ne, tun da gidan masu kudi komai na su dabam ne. Ina kai hannuna Ahmad ya bude kofar fuska a hade alamar ransa a bacen yake kenan, sai dai muna hada ido sai ya saka min murmushi ko da wasa ba kalli mutanen da muke tare ba sai yai kamar be gansu ba idonsa na kaina ya kara wangale kofar falon. 

“Shigo”

Ni na fara shiga sannan suma suka biyo baya, da kansa ya nuna min wata one seater ya ce na zauna, ba musu na zauna ina kallon kanwarsa wacce ke kallona tana dan murmushi.

“Sannunki”

“Yauwa Sannu Halima ko?”

Na gyada mata kai. 

“Ya goshin naki?”

Ya tambaya yana kallona.

“Alhamdulillah”

“Siyama kawo mata lemu”

“No ba sai an kawo ba, daman mun zo ne akan maganar Aminu, mahaifiyarsa tace ka ce sai na amince za a sake shi”

“Yes sun miki cilas ne? ”

Mahaifiyar Aminu ta saki baki. 

“Ikon Allah wane irin cilas kuma? Akwai fa yara a tsakaninsu yara hudu ai ko ba komai a hakura tun da ba a san abunda gaba zata haifar ba, yara hudu yau a ba wasa bane komai abu ya lalace dole akwai alaka akwai wannan son a tsakani, tun da idan babu shi ba zaki rike masa yaya a hannunki ba”

A iya tunanina mahaifiyar Aminu tana fadar hakan ne saboda Ahmad ya ji cewar ina da yara hudu idan ma be sani ba ya sani, saboda ya fasa aurena ko so na kamar yadda take tunanin so na yake, ta yi hakan ne kawai dan ta muzanta ni idan ma baya son yara sai ya fasa aurena tun da ta san ba duk namiji ke son yaran da ba na shi ba. 

Kallon nai zan yi magana Ahmad ya girgiza kai alamar kar na ce komai. 

“Kin amince?”

Sai naji kamar bace a a ko dan Hajiyar amman rahamar zuciyata ta hana ni. 

“Eh na yafe”

Wayarsa ya dauka ya kira wnda nake kyautata zaton direbansa ne.

“Ga iyayen mutumen nan zasu fito yanzu, kuje tare kamfani ka dauko motarsa then ku wuce AP barack ku karbo shi gurin Faruk”

Yana sauke wayar ya kallesu yace. 

“Za ku iya fita direba na jiranku”

A dolen dolen sukai masa godiya har da addu’ar Allah ya saka da alheri.

Suna mikewa tsaye nima na mike sai yai alamar na zauna da hannu, haka kuwa akai sai na zauna din su kuma suka fita. 

“Siyama je ki kira Hajiya su gaisa”

“Ow… Owk… Owk…. ”

Ta tashi ta nufi upstairs tana wasa da wayar hannunta.

“Na gode”

Na fada ina kallonsa, sai ya juyo dubansa daga kallon Siyama izuwa gare ni. Kasa nai da kaina ina wasa da yan yatsun hannuna sosai nake son nai masa maganar Abraham domin ina kyautata zaton tsakanin shi da Abdallah ne suke bincike akansa, wanda nake ganin hakan kamar hatsari ne ga rayuwarsu. Ina zaune a gurin Siyama ta sauko tace wai na shigo dakin in ji Hajiya, kamar mai jira na tashi na nufi upstairs din Siyama na shiga dakin nima na shiga sai na zauna a saman kujerar dake gefen windows ina gaisawa da ita tana min sannu da ciwon da na ji, ta tambayi Mama sannan ta dora da ya karin hakuri. 

  Ban wani dade ba ganin dare na na yi mata sallama na taso na fito daga dakin, Ahmad na tsaye jikin stairs din yana kallon kafafuwana har na sauko.

“Muje na sauke ki”

“No zan hau Napep”

Tabe baki yai. 

“Kin fi son Napap kenan da motata okay muje na taka miki”

Tare muka jeru da shi muna kusan isa gate Siyama ta kwala min kira, a gurin muka tsaya har ta iso, ta miko min ledar hannunta. 

“Gashi in ji Hajiya”

“Wannan ba tarbiya bace ya zaki kwala mata kira kamar wacce tai sata?”

“To Yaya idan ban daga murya ba kuka fita ita Hajiya ai fada zata min tace ban ba wa Halima, yanzu kuma na bata ka fara min masifa wai ina murya da yawa”

“To ai sai ki kira wayata ko nata ki ce mu jiraki”

“Ina na ga Number ta?”

“Bata number ki”

Ya fada yana kallona sai ta miko min tsadaddiyar wayar.

“Sa min number ki”

Ba musu na karba na saka mata, sai da na mika mata wayar sannan ya ce. 

“And ta girme ki ko ba komai she deserve some respect”

“Yeah Yeah Anty Halima….”

“Lim’s”

Ya furta sannan ya juya muka cigaba da tafiya. Siyama har ta juya ta juyo tana kallonmu. 

“Wowwwwwwww”

Juyowa nai na kalleta sai yace min.

“Share ta kanwar nan tawa da kike gani bata da hankali”

Murmushi kawai nai muka fice daga cikin gidan, mike titi mukai izuwa babban titi inda ababen hawa suka fi yawa.

“Akwai maganar da kike son min ne?”

Na kalleshi ban ce komai ba.

“Na lura da yanayinki, kin san yanzu na karance ki ina iya gane yanayin damuwarki ko far’a ko makamancin haka just say it”

Na yi murmushi ina saka duka hannayena na rike ledar da nake kyautata zaton turareka ne a ciki saboda irin kamshin da suke, sai na ji duk wata kimarsa da mutunsa sun kara karuwa a idona. 

“Akan maganar Abraham ne?”

“Abraham dai? Why kike son magana akansa? Bakinsan bana son jin sunansa ba? Idan na tuna ya miki fyade sai na ji kamar na kashe shi na datsa namansa na soya shi sannan na watsa shi a cikin wuta ta kona shi”

Tsayawa nai ina kallonsa hasken dake unguwar yana haska min fuskarsa. 

“It pain me”

Ya maimaita yana yamutsa fuska. Kasa nai da kaina. 

“Saboda karka saka kanka a hatsari ne, and dazun ya zo min da wata magana ne wacce ta sanyaya min jiki, and ba zan jidadi ba idan wani abun ya same ka sanadina, yawancin mutanen da suka kusantata kaddarata ta kan shafe su”

Ban boye komai daga abunda ya faru tsakanina da Abraham ba na fada masa, sai kawai na ga yana dariya yana kallona dariya sosai fa kamar yana kallon wata yar wasan Comedy.

“Pls how old are you? Har yanzu akwai kurciya a tare da ke. And dan kawai an fada miki magana sai ki yarda? Kina saurin yarda gaskiya, and who told you idan Abraham ya aure ba ki haihu ba zai zauna da ke? How sure are you zai bayyana kansa ya daina duk abunda yake saboda ke?”

“Ba wai ina nufin na aure shi ba…?”

“Then me kike nufi? Pls karki sake min maganarsa ki bar masu bincike su bincika abunda suke so akansa, so that ki samu salama ni ma kuma hankalina na kwanta”

Na gyada masa kai. Sannan muka cigaba da tafiyar ya zuba hannayensa aljihu, da kansa ya tara min napep na shiga ya fada masa inda zai kai ni, sannan ya ciro kudin da nake kyautata zaton sun kai 3k ya bawa mai napep din. 

“Na tabbatar ta shiga gida sannan ka dawo”

“To ranka ya dade na gode sosai”

Ya amsa cike da far’a sannan yaja Napep din muka nufo gida. 

AHMAD POV. 

tsaye yai a gurin har sai da ya daina hango napep dinsu sannan ya juyo ya dawo gida, duk abunda yai a gaban mahaifiyar Aminu yayi ne just to make her feel special, wani irin tausayi take ba shi ko kallonta yai sai yaji kamar zai zubar mata da hawaye. 

  Part dinsa ya nufa a ranar kwana yai da tunani kala kala, sai sake sake yake a ransa. Misalin tara da wani abu ya shiga part din mahaifiyarsa, sai ya same ta a kitchen kamar kullum mai aikinsu kuma na jera abinci a dinning.

“Ina kwana Hajiya”

“An tashi lafiya?”

Ta amsa tana murmushi jinginawa yai jikin kofar kitchen din yana murmushi. 

“Al-hamdulillah, Hajiya ba zaki daina wahalar da kanki akan girkin nan ba”

“Na san baka son abincin mai aiki shiyasa nake girka maka da kaina, amman idan kai aure zan huta”

Murmushi yai ya kai hannunsa a kirjinsa yana shafa farar shaddar dake jikinsa. 

“Soon In-Sha-Allah”

Da sauri Hajiya ta juyo ta kalleshi. 

“Da gaske?”

Ya gyada mata kai. 

“Khadija dai?”

Sai ya bar jikin kofar ya nufo inda take yana murmushi.

“Wata ce dai wacce ta cancanci rayuwa mai kyau, wacce ta yanke kauna daga samun jindadi, wacce take bukatar tallafi ita da yayanta da yan’uwanta, wacce zuciyata ta cika da tausayinta”

“Halima ce?”

Hajiya ta tambaya tana murmushin jindadi. Sai ya rumgume ta ta baya ya dora kansa saman wuyanta. 

“Hakan nan kawai nake jin kamar idan ba ni na aureta ba, zata iya auren wani ya ci amanarta kuma ta sha wahala, and idan ta auri wani ba ni ba, zai so yayanta? Zai iya taimakonta? Zai jin tausayinta kamar ni? Kin san me take fada min jiya? Wai tana tsoron kar kaddararta ta shafe ni, tsoro rabar mutane take, ina son na cire mata wannan tsoron i want to make her feel special, and duk wani kalami da mahaifiyar mutumen tai jiya da ni take, a tunaninta ina son Halima ne, Idan har ta amince min na aureta, zan aureta ne kawai saboda in tausayinta amman ba dan ina sonta ba”

Ya sake ta ya juyo gabanta ya tsaya. 

“And ina son mace mai hakuri kamar ta, the way she talk, yadda take gudanar da rayuwarta da yadda take taka tsantsan everything is perfect i like her, and her name, ke ma kuma naga kamar ta ku zata zo daya”

“Duk macce da ta auri dana ta yi babban dace, and i believe matar na deserve a better life, ban kawo maka zancen ta bane saboda na san baka son bazawara, sai dai na lura jininku ya hadu hankalinku da tunaninku yana kokarin zama daya, zan fi kowa farinciki idan hakan ya tabbata saboda tana burgeni, daga ganinta kasan macece mai hakuri mai tarbiya mai hankali mai natsuwa da yadda da ko wace irin kaddara, irin matar nan duk namijin da ya aureta yayi sa’ar aure, abunda kake kudiri idan alheri a tsakaninku ina rokon Allah ya tabbatar”

“Amin Hajiya”

Ya amsa yana murmushi, har ga Allah shi dai kam ba son Halima yake ba, domin tuna tayi aure har biyu ga fyade yana bata masa rai, dukan wani abu da zai mata na tausayi ne kawai da kuma gudun halin da zata fada nan gaba, and the way ta Hajiya take son yai aure zai sake cika mata burinta na auren, sai dai yana jin inda har zai yi auren so Halima ce macen da tafi cancanta ya aura, ko ba komai ita kadai zata iya hakurin zaman da Hajiya, kuma a yadda ya lura da Hajiya tana son ta tan tausayinta ba zata cutar da ita kamar sauran matan ba. 

AMINU POV. 

Ko da suka isa har an fito da shi, sun zuba shi nan jikin wani siminti fuskarsa duk ta kumbura jikinsa ma kana gani kasan ya sha duka, da ido daya yake iya dagawa ya kalli mutane, jin muryar Hajiyarsa yasa shi jin sanyi, dacan kam ya dauka ko kashe shi za su yi. Hajiya da kuka da komai suka dauke shi suka saka shi a motarsa da direban Ahmad ya biyo su da ita, daga barak din suka wuce da shi asibiti, sai da suka kusa isa asibitin sannan Hajiya ta fara Allah ya isa dan can kan kasa daga ido tai ma ta kalli tarin sojijin, domin ba a bar su sun shiga ba sai da Direban ya kira Faruk din ya sanar masa sannan Faruk din ya bada umarnin a zo a tafi da da su ciki. 

  

“Wannan ai zalunci ne, to shi Bazawarin nata soja ne daman”

Kanen mahaifinsa wanda shima sai a yanzu ya samu baki ya fada, babu dai wanda ya amsa shi duk jimamin abun kawai suke. Bama kamar Hajiya da take jin kamar ita aka daka. 

“Wallahi duk inda zan shiga sai na shiga sai na ga inda za ayi auren nan, bakar azzalumar mata, da shegen bazawarin nata daman can ba son shi take da alheri ba, wannan bakin zalincin wallahi Allah ya saka muna”

Riri Hajiya take kuka tana jin kamar ace sun fi Ahmad arziki da iko da sai ta saka an wulakanta shi fiye da yadda yai ma danta amman ba dama, tun da sun fisu arziki da komai ma ciki har da sanin darajar dan’adam.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

GOBE NA 59

Advertisement  *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  5️⃣9️⃣ Kwance take a dakinta tana kallon windows din dakinta da suke…

GOBE NA 50

Advertisement   *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  5️⃣0️⃣ TWO MONTHS LATER…..  Advertisements Alhamdulillah Thumma Al-hamdulillah.    Godiya ce…