GOBE NA 50

Advertisement

 

*GOBE NA…*

By Khadeeja Candy 

5️⃣0️⃣

TWO MONTHS LATER….. 

Advertisements

Alhamdulillah Thumma Al-hamdulillah. 

  Godiya ce abunda ta cancanci fita daga bakina na yanzu, izuwa ga mahallincina ko da kuwa ina cikin tsananin rayuwa ballantana yanzu da rayuwar ta fara sauya min. 

Abubuwa da yawa da ban zata ba daga Ahmad suna ta samu na, ni da shi a yanzu kusan mun zama abokai, yana sake min sosai yana fada min abubuwan da za su kwantar min da hankali, yana dora ni a kowace hanya ta jagoranci.

Ban tana sani haka yake da sakewa da son jama’a ba sai yanzu, a cikin abubuwan da yai minba kamar yadda ya dukufa a nemawa Kabir Lafiya, wanda farinciki ba ni kadai ya saka ba har da yan’uwansa domin na ga hakan a fuskarsu, asibiti aka maida shi suka masa duk wani gwaje gwaje daya kamata, sannan suka dora shi akan magani, duk wani abu da za a kashe masa ko aka kashe masa ta aljihun Ahmad yake fita. 

   da abun ya ki yi a nan ne suka tura asibitin sokoto wato uduth, tare da yan’uwansa biyu aka je, da kuma matarsa. 

  Bayan nemawa Kabir lafiya kuma yarana ya saka su a makarantarsa, school bus ke kaisu tana daukosu.

  Wani lokacin ina da na kalleshi sai na ji kamar na bude masa zuciyata yaga irin farincikin daya saka ni, idan kuma na tuna abubuwan da suka faru tsakaninmu sai nai dariya, farkon haduwarmu da kuma abubuwan da yai min na cin fuska kamin yanzu, da kuma yadda muke a yanzu sai wani abun ya bani dariya wani kuma ya bani mamaki. 

Kamar ko yaushe yau ma na shirya shirin zuwa aikina, cikin bakar abaya kusan abaya tafi yawa a cikin tufafi domin ina jin sakewa sosai idan na saka ta gashi babu ruwanka da wani rike hijab ko gyara gyale. 

  Ban yi kwalliya ba, hoda ce kawai na shafa bayan mai sai dan turaren da na saka, sannan na shafa dan mai a bakina na dauki bakar jakata na rayata na nufi dakin Mama nai mata sallama, a tsakar gida na samu Inna ita mai mata sai na dawo na kama hanyar zuwa office din rai na fes. 

  Na samu napep daf da kofar gidanmu ya sauke wasu sai kawai na tsayar da shi na fada masa inda zai kai ni sannan na shiga. 

Advertisements

   Misalin tara da yan mintuna na isa office din, ko da na shiga na samu komai tsaf kamar kullum, wato masu gyara office din sun gyara shi sai kamshi yake. Jaka na aje a inda na saba ajewa na nufi window ya bude abun mamaki yau Ahmad ya shigo da wuri na hango shi jikin windows sa tsaye hannunsa daya rike da mug dayan kuma a aljihunsa har yana dago min mai kofin alamar gaisuwa. Ni kuma na daga masa hannu ina murmushi sannan na juyo na zauna a kujera na fara aikina. 

Knocked akai kamin na ce komai Yunus ya turo kofar office din ya shigo.

“Good morning”

“Morning how are you sir”

“Fine, hope dai baki gaji da ni ba”

Ya fada yana murmushi kamar yadda nima nake mayar masa da murmushin.

“No haba dai Bismillah”

Na fada ina nuna masa gurin da system din take. Yau kusan kwana biyu kenan a office dina yake aikinsa saboda system din da ke office dinsa ta samu matsala kamar yadda ya fada min. 

  

“Yau ma dai kin yi kyau kamar jiya, wai kiye sirrin”

Ya fada yana nufar gurin da System din take yana aje kayan dake hannunsa. Ni kuma sai nai dariya mai sauti. 

“Na gode, sirrin aikin kamfaninku ne ka san yana karawa ma’aikatanku kyau da natsuwa”

He was laughing so hard kamar na fadi masa wani abun dariya sosai. 

“Oh wow okay zan fadawa mutanen kamfaninku haka kuwa, so that kowa ya rike aikinsa da kyau kar yai laifin da zai saka a koreshi”

Nima dariyar nai.

“Gaskiya ya kamata kam, ko ma an koresu ku makale kar su je”

“Hahaha Haima kenan”

Ya fada yana cigaba da dariyar, wani abu na ji marar dadi ya ratsa zuciyata sakamakon kirana da yai da sunan da Abdulhamid ke kirana da shi. ban sake cewa komai ba na cigaba da aikina, sai jin nai wayata ta yi kara alamar sako, a zato na mtn ne hakan yasa na share wayar ban duba.

“I think this week zan je Abuja In-Sha-Allah”

Na kalleshi. 

“Gurin me?”

“Wani aiki ne, kin san can din ma muna da branch, so idan mai gida be je ba dole ni zan je”

“Okay kace zaka leka garin manya kenan”

Dariya yai. 

“Kin tana zuwa Abuja?”

“No ni ai ban taba wuce Gusau ba”

“Oh duk wayewar nan taki? Ya kamata ace kin zagaya manyan birane ai”

“To ai ban san kowa ba, kaga ko ai ba zan tashi naje garin da ba dangi ba na zauna”

“Ba dole sai kana da dangi zaka ziyarci gari ba, idan kina da friends ko ma a karan kanki zaki iya zuwa ki huta”

“Hm da dai ace ni namiji ce zanje amman ina mace ai be kamata ba”

“Believe me akwai matan da suke zuwa garin da ba su san kowa ba, wasu idan za su yi birthday haka ko suje bikin friends dinsu”

“Tab ni kam ba zan iya ba, na je garin da ban san kowa ba? Amman masu zuwa birthday a wani garin basa celebration ko? Dan na san ba za su samu masu binsu ba”

“Irin yaran manya haka, ko manyan mata wasu ma ba su tsayawa kansu ba, so suna zuwa da friends dinsu sai a hadu can ayi ta abubuwa wasu har kasar suke bari fa, kuma kin san ba kowa ke celebration din birthday ba, like me ni ma bana bikin birthday amman a ranar zan ci na sha na yi duk abunda na so”

“Nima haka nake yi gaskiya, ban tana bikin birthday ba, ko cake ban tana ci a ranar birthday na ba sai dai na gode Allah nai saka a status shikenan”

“Ni ina ciye ciye gaskiya, kuma zan iya ma mutane abu albarka birthday na, my is 22 December”

“Mine is 4 October”

Ya kalleni.

“O really? That’s mean gobe kike birthday kenan?”

Na yi dariya ina gyada masa kai. 

“Wow ki ce ke princess ce kenan”

Dariya na sake yi, a raina ina fadin princess sai kace wata yarinya. Wayata ce tai ringing sai da na dauke kaina daga computer sannan na kai hannuna na dauko wayar ganin bakuwar ce yasa ban damu na dauka ba sai kawai na aje wayar a saman tana ringing.

“Ah gaskiya ya kamata ki yi mana celebration”

“Haba wannan kuma ai sai yara”

Na fada ina kallon number kiranta ya sake shigowa. Hannuna kai na dauka na danna picking nakara a kunne. 

“Hello Sallamu alaikum”

“Zo office dina yanzu nan”

Yana fadar hakan ya kashe wayar, ko ba a fada min ba na san mai murya, kuma na san duk a kamfanin nan shi kadai ne zai kira haka kai tsaye ya bani umarni, duk da be taba ba, be ma taba kiran wayata ba, and the way da yai maganar kamar yana cikin fushi. Hakan yasa na dan tsorata, a take na fara tunanin abunda nai wanda ba daidai tsakanin jiya zuwa yau, domin hausawa na cewa karka ji tsoron kira ka ji tsoron laifin da kai, but if i can remember ai dazun da na shigo mun gaisa da shi idan fushi yake da ni ba zai daga min hannu ba, oh maybe wani abun nai ba daidai ba, a take na fara duba sakkwanin mail din wai ko akwai wanda ya kamata na aika masa kuma ban aika ba.

“Ko a kamfanin nan ne ya kamata ki yi mana celebration”

Yunus ya fada yana danna computer dake gabansa yana murmushi, nima murmushin nai na mike tsaye rike da wayata da sai a lokacin na ke ganin sakon da ya turo min. 

“Same ni office yanzu”

Oh ashe ba mtn ba ne kenan dazun, na fada a raina sannan na nufi kofar fita ina fadin. 

“Ina zuwa Sir”

“Okay”

Ya amsa hankalinsa na gurin abunda yake, cikin faduwar gaba da fargaba na nufi office din kuwa da nasan ban yi wani abun ba, kuma a yadda nake da shi a yanzu bana tunanin akwai wata matsala a tsakaninku, sai muryarsa ta tabbatar min da ba lafiya ba.

  Na tura office din na farko na shiga har na gaisa da mutumen dake ciki, haka a na biyu har na kai a nasa office din na tura na shiga bayan na yi knocked. 

Ina shiga ya watsa min wata uwar harara, har sai da gabana ya fadi. 

“Sai yanzu kika ga damar zuwa?”

“Ban ga sakon ba ne sai yanzu, ina zaki gan shi hankalinki yana can wani guri, me Yunus yake yi a office dinki?”

“Aiki”

“Shi office dinsa kwantarsa ake a ciki?”

“System dinsa ce ta lalace”

“Kuma ba zai iya magana a gyara ba, sai dai ya zo office dinki ya zauna shi tsohon dan iska, ke kuma kin saki jiki sai dariya kike kin kebe da shi kamar wani muharraminki”

The way da yai maganar sai naga kamar ba shi ba, to miye laifi dan Yunus ya zauna a a office dina? Naga dai idan wani abu zamu aikata ai ba za mu bar windows a bude ba, kuma yana maganar Yunus din ba muharramina ba ne shi din muharramina ne da na kebe da shi a nan? I was so so confused. 

“Zauna nan”

Ya nuna min kujera, na yi zaton wani abun zan masa dan haka na nufi kujerar na zauna. 

“Look at you kuna da exchanging words, mi kuke cewa”

Kallon mamaki nai masa. 

“Magana kawai muke”

“Mi yace miki?”

Na yi shiru ina ta tunanin ta inda zan fara, ni kam yaushe rabon da ayi min haka wai a tsareni ana son na fadi wani abu da na fada ko kuma wani ya fada min. 

“Maganar zuwa Abuja ne da yai min, sai maganar Birthday, sai…. At first dai cewa yai na yi kyau sai….. Maganganu dai haka… ”

Sama sama na tsakuro abunda zan iya fada na fada masa, domin na lura ba da wasa yake tambaya ba. 

“Ji dan Allah kin saki baki kina ta magana da shi har da zancen zuwa Abuja, cewa yai ki bishi ku tafi?”

Na zaro ido ina bude baki. 

“A a Wallahi ya za ayi yace haka? Na fada masa ban taba zuwa ba ne, shine muke zancen”

Kamar hadin baki sai ga Yunus din yayi knocked.

“Yes”

Ahmad na bada umarni ya shigo rike da wasu files a hannu, kallo yai ya sakar min murmushi kamin ya karasa gurin Ahmad din yana fadin. 

“Tace gobe ne birthday ta shine nace ya kamata tai mana celebration, kuma tace bata taba zuwa Abuja ba, gaskiya ya kamata a turata ko ta hanyar aiki ne taje ta gano Abuja”

It’s normal for a friend like Yunus yai magana da friend dinsa like that kamar Ahmad, kuma ban ga wani illa a ciki ba, amman sai Ahmad yai masa banza ya karbi files din kawai ya aje. 

“Miya samu System dinka?”

“Wallahi ta tsaya ne gaba daya, ban san abunda ya same ta”

“Kuma ba kai magana ba”

“No na yi magana da Tukur yace min baya gari shiyasa”

“Kuma Tukur ne kawai yake mana gyara a kamfanin nan?”

“No na dai fi yarda da aikinsa”

“Ka dauko wata ka kai office dinka”

“Okay”

Ya amsa sannan ya juya ya fice, yadda Ahmad yake masa maganar kai ka rantse da Allah be san Yunus din ba aiki ne kawai ya hada su, domin yana masa magana ne ta sigar yaro da ubangidansa babu alamar murmushi ko wasa a duka Maganarsa, bayan kuma shi Yunus din ya fada min cewar Ahmad din childhood friend dinsa ne kuma kaf a kamfanin ba shi da aboki irinsa, saboda ya yarda da shi 100%

Haka Ahmad ya zaunar da ni a office din for more than 3 hours, ba dan na masa aikin komai ba, after every 30 minutes sai yaje gurin windows dinsa ya leko sannan ya dawo ya zauna wata kila Yunus din yana can yana aikin ne tun da ya riga ya fara. 

  Ban san abunda ya zo masa a rai ba sai ganin nai yana kallona yana murmushi. 

“I know zaki ce ni din ai ba muharraminki ba ne ko? Yes amman ni ina da karfin jini the way da zan iya controlling kaina akan wasu maganganu ko aikata wani abun ba, ba kowa zai iya haka ba, and ita mace komai shekarunta komai girmanta sai ana controlling dinta saboda karamar kwakwalwa ne da su, more especially Lims”

Ya fada still smile, ni dai ban da idon da na sakar masa babu abunda na ce, har na fara tunanin to ko dai Yunus din dan iska ne? 

“Dauko lemu ki sha”

Ya fada yana dora duka kafafuwansa saman katon tebur din, tare da kai yatsansa jikin dogon hancinsa.

“No Na gode”

Sai ya dan tabe baki. 

“Kamar kin ji haushi ko? Ke ana tausayinki kin gagara ganewa, by the way likitocin da suke uduth sun bada shawarar a fitar da Kabir india saboda a can ne za a iya masa aiki mai kyau a kwashe jinin daya kwanta a cikin kwakwalwarsa, sun ce bashi magani zai dauki lokaci mai tsawo kamin ya samu lafiya kuma za a kashe kudi sosai, amman idan an masa aikin kuma aka yi a sa’a zai iya samun sauki cikin kankanen lokaci”

“Ba za a iya yi masa a nan ba? Zuwa india ai za a kashe kudi da yawa”

“To ke zaki kashe kudin ne? Ko kudin a aljihunki za su fito? Ko kuma kudin na ki ne? Are you the money or the money is yours? Ke kin fiye son shiga uku”

Ya fada yana mikewa tsaye ya nufi fridge din ya bude ya dauko lemun ya nufo inda nake. 

“Already na fada musu su shirya komai daya kamata, kawai dai na fada miki ne just to let you know”

Ya miko min lemun, karba nai da mamaki a fuskata haka yake wani lokacin, daga abun arziki ina tausayin kudin da zai kashe sai ya ce min wai ba ni ce kudin ba, and look at him now kamar ba shi ne ya gama hade fuska dazun ba, sometimes yana abu kamar wani mai aljanu. 

“Kamar mai aljannu ko?”

Jin ya fadi haka yana murmushi yasa nai saurin mikewa tsaye ina girgiza kai, a zatona a fili nai maganar har ya ji. 

“No mai Al…. Jifai nake nufi….”

Na fada da sauri sai yai dariyar da ta bayyana hakoransa. 

“Ashe na canka daidai yadda naga kin rike lemun daman na san gulma kike a zuciyarki ki ce wannan mutume kamar mai aljanu”

Nima dariyar nai sosai har idona ya cika da kwala ashe ma ba a fili nai maganar ba, canka yai ni kuma garin kare kaina sai na fallasa kaina. Murmushi yake yana kallon yadda nake dariya kamar ba ni ba.

“Cute you, dariya na miki kyau”

Daidaita natsuwata nai, na koma na zauna na rike lemun. 

“Tashi muje mu ci abinci”

“No ana kawo min abinci a office everyday”

“Ba zaki koma office din nan ba sai gobe that’s final”

Hannunsa ya kai ya dauki keys din dake saman tebur din. 

“Amman handbag dina tana office din”

Sai ya miko min keys din. 

“Je ki jirani a mota”

Ba musu na karba keys din na juya na fice daga office din, na san inda yake aje motarsa dan haka na nufi gurin kai tsaye na tsaya a gurin ina jiransa, be jima ba ya fito tare da wata mata wacce rike da jakata ta kawo min jakar shi kuma ya karbi keys din ya bude motar ni ma na bude na shiga front seat. Tun da ya kama hanyar restaurant din be ce min uffan ba sai dai lokaci zuwa lokaci yana kallon inda nake, ni ma kuma ban ce masa komai ba, zuciyata nata raya min abubuwa da dama har muka isa gurin.

  Motar na tsayawa na bude na fito shi ma ya fito yai gaba ina binsa a baya, restaurant din da Abdulhamid ya taba cewa na tsaya a ciki na jira shi ce, wacce na shiga ciki na zauna a kujerar da Ahmad din ya rufeni da masifa saboda na zaunarna kujerar da ban san ta wacece ba a gurinsa. 

A yau ciki muka shiga har vip din inda set din yake, da kansa yaja min kujerar, sai na kasa zama kuma na gagara cewa komai and na kasa dauke idona akansa, gabana sai bugawa yake da sauri kamar zai fito. 

“Zauna mana”

Ya fada so calmly yana min wani irin kallo da na kasa natsuwa. Na zauna kamar yadda ya umarce ni amman kamar wata karago haka na zama, idan zan juya gaba daya zan juya idan zan juyo gaba daya zan juyo, kana kallo kasan bana cikin natsuwa ba kuma natsuwa irin ta wanda yake cikin tashin hankali ko zullumi ba ko fargaba ba, no natsuwa dai irin ta Wanda yake ganin wani abu kamar a mafarki. 

“Me za a kawo miki?”

“Just water”

Na fada ina kallon waiter din. 

“Kawo mana Jalof plate biyu da lemu”

Ya fada masa sannan ya kalli. 

“Is hardly na ci abinci a public place like this, bana cin abinci a awaje yawanci Hajiya ta ke girka min, sai dai ina yawan zuwa gurin nan tare da mahaifiyar Baby lokacin da take raye just to make her happy, saboda ta saba zuwa gurin tun tana budurwa, a yau ma na san sai Hajiya tace min miyasa ban ci abinci a gida ba, kuma saboda ke ne, na zamu so nan ace me zaki ci ki ce ruwa ba, you must eat with me”

Magana yake min a hankali kamar mai kokarin fahimtar da ni. Wani abu nake hangowa a idonsa wanda nake kokarin karyata kaina kansa. Ba shiri na mike tsaye ya dauki jakata na rataya. 

“I don’t think i deserve this, ya kamata ka cigaba da mutunta kujerar matarka”

Ina fadar hakan ban tsaya komai na na nufi hanyar sauka daga gurin har ina sauri kamar zan fadi. Ina fitowa gurin na tari napep na shiga, hawaye suka fara sauko min, tsoro nake ji kamar Ahmad ya bijiro min da abunda Aminu, Abdulhamid, Abdallah, Abraham suka bijiro min da shi, idan ya tambayi so a gurina na amsa masa da a a ban kyauta ba, sai dai ni ban shirya ba, na gaji da halin maza, ba zan sake aikata kurskuren auren mutunen da zan yi kuka a karkashin igiyar aurensa ba. 

  Idan na tuna Aminu da Abdulhamid duk haka suka min kamin daga baya su saka ni dakin kuka su juya min baya, babu muhallin kowa a zuciyata a yanzu, idan har akwai wanda ya cancance ni a yanzu Abdallah ne, ba kowa ba, ba zan yarda Ahmad ya yaudare ni na fada soyayyarsa, a yanayin gidansu da irin girman da suke da shi, ba lallai ne idan ya aure ni ya ga kima ta ba, domin mu talakawa ne masu rufin asiri ba masu arziki ba, idan har mahaifiyar Aminu zata raina talaucin mu ya zama silar da ya saka ta kara wulakanta ni tana cewa ina kwashe arzikin danta ina kaiwa gidanmu ina ga mahaifiyar Ahmad? 

  Secondly idan Abdulhamid be iya hakuri da ni ya zauna da ni a gidansa da aka min fyade ba taya wani zan ji labarina da rana tsaya kuma yace zai hadiye ƙashi ya zauna da ni babu kyama?  Shin idan ma na yarda wata kadarar ta sake samun a gidansa zai iya zama da ni ko kuwa shi ma juya min baya zai yi? No I’m not just ready. 

Mai napep na isa kofar gidanmu sakon kar ta kwana na shigowa wayata daga number Ahmad. 

“Miyasa kika ce baki cancanci haka ba? Miyasa kika tafi kika barni? Why kike jin tsoro? Mi zuciyarki ta raya miki a kaina?”

“Nothing, you’re just my friend”

Ita ce amsa da na bashi bayan na karanta sakon, sannan na share hawayena na fita daga napep din.

“No I’m not just your friend”

“I’m not”

Ita ce amsar da ya maido min a take. Sai kawai na goge sakon, na sallame mai napep na shige gida, kallo daya Mama tai min ta fahimci damuwa, tai ta min tambayoyi a gurin aikinki ne ko a Abraham din ne domin na dade da labarta mata komai akansa, sai kawai na ce mata babu komai. 

  Misalin tara da wani abu na dare, Aminu ya kira wayata, rabon da na ga kiransa a wayata har na manta, kusan tun da Ahmad ya saka aka mai masa duka be sake zuwa ba ko kirana ko da da sunan duba yaransa ne. Ba tare da tunanin komai ba na dauki kiran, sai ya sanar min yana kofar gida dan Allah na fito magana zai yi da ni. 

  Tashi nai na jari hijabina na saka na fadawa Inna wacce nake zaune a dakinta sannan na fita wajen, kusa da kofar gida na same shi zaune a cikin motarsa da ke fake. Tsaye nai jikin motar na ce. 

“Gani”

“Ki shigo ciki dan Allah”

“Duk abunda zaka fada ka fada a nan”

“Maganar da zan yi tana da muhimmanci dan Allah ki taimaka ki shigo”

Jin haka yasa na bude motar na shiga, ina kallonsa sai na ga idonsa sun kumbura sun yi ja sosai alamar ya ci kuka ba kadan ba har ya sauya masa kala. Mun dauki lokaci mai tsawo zaune a cikin motar be ce min komai ba kuma ya kasa kallon inda nake, ni kuma mamaki ya cika ni ina tunani yau kuma da wacce ya zo. 

“Yau ce rana ta karshe Halima, da zan daina rokon ki dawo gareni, a yau kan na yarda na rasa ki har abada, a yau na yarda na yi kuskuren da ba zai taba gyaruwa ba, a yau ina rokon Allah ya baki miji na gari wanda zai taimaki rayuwarki, wanda zai baki soyayyar da kika rasa a gidana, wanda zai nuna miki kulawa, ya fifita ki ya tausaya miki, wanda ba zai wulakanta ki ba kamar yadda nai yi…..”

Yai shiru sai kuma ya kai hannunsa ya kama hijabi ya jimkeshi sosai a hannunsa. 

“Wallahi ji nake kamar na bude bakina na dauke ki na saka a ciki na hadeye ki zauna a cikina har a bada amman babu wannan damar, na riga na rasa ki har abada, ina son ki Halima ina son ki san da wannan ko bana raye, duk abunda nake miki a baya ina yi ne kawai ba dan bana son ki ba, ina yi nw kawai saboda sharin zuciya da kuma ajizanci na dan’adam, dan Allah ki yafe min”

Wasu irin hawaye yake yana kallona numfashi na fitar masa daker, a take jikina yai sanyi. 

“A lokacin da kike fada min illar abunda nake yi, da cutar dake na ke yi ban ga hakan ba sai yanzu da lokaci ya kure min, na tuba tuba na gaskiya, amman ba ni da tabbacin idan Allah zai yafe min abunda nai, kuma ina jin tsoron haduwa da shi, shin a yanzu idan nai jinya na mutu jinyar zata zama silar kankarewar zunubaina ko kari? Saboda ni na jawa kaina”

“Ban gane wannan maganar ba…”

Na fada muryata na rawa, dayan hannunsa ya kai ya dauko farar takardar ya miko min.

“Ba kawarki kadai nai mu’alama da ita ba, amman ina da kyautata zaton ita ta laka min ciwon, domin na naji labarin kawarki Sa’adatu tana dauke da cutar bayan na tuba na daina mu’alama da ita, ban yi tunanin komai ba ban kawowa raina komai ba, har sai da wannan abun ya faru dukan da sojoji suka min da aka kai ni asibiti, sai suka min gwaje gwaje, a ciki na samu wannan, bayan na warke na koma gida na sake zuwa asibiti biyu ina samu result daya, and do you know what? Da aka saka Sadi yai gwajin sai aka samu shi ma yana dauke da ita, haka ma Murja kuma ina kyautata zaton dukansu ta dalilina suka samu….. ”

Tuni hawayena ya jika takadar da ya kunna min wutar cikin motar ina karantawa.

“Hiv Aminu?”

Ya gyada min kai yana kara jinke hijabi hawaye ma sauko masa. Ban tana jin tausayin Aminu ba tun bayan rabuwar mu sai yau.

“Zina ba tai ba Halima, bata haifar min da komai ba sai bakinciki da talauci, na yi wa yar wani an yi ma yata, na yi da matar wani kanena yayi da matata, yanzu kuma ta jefani a ramen da babu mai ceto ni, daga ni har Sadi har Hajiya ba mu da kwanciyar hankali da natsuwa tun daga lokacin da abun nan ya faru har yau ko abincin kirki Hajiya bata iya ci……”

Ya karasa yana jingina kansa jikin sitiriyarin motar ya fashe da wani irin kuka mai taba zuciya.

_______________________

Wayyo Aminu ya bani tausayi 😢😭

  To ita kuma Halima me take nufi da Ahmad? 🤔 ko da yake tana da gaske ance duk hadarin daya baka kashi….. 🤥

Har Gobe ina Team Abdallah 😘😘😘

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

GOBE NA 12

Advertisement  *GOBE NA…* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy  1️⃣2️⃣ “Hajiya barka da tashi ya kafafuwan?” A natse yake…