GOBE NA 51

Advertisement

 *GOBE NA…*

By Khadeeja Candy 

     Ina godiya sosai Maman Sayyed,  sakonki ya riske ni, Allah ya bar kauna kuma ya ba ni ikon yi kullum 🥰

        Gaisuwa ga duk makarantan labarin Gobena, a duk inda suke Allah bar kauna 🥰🌸❤️

Advertisements

5️⃣1️⃣

Wani lokacin Allah yana mana talala mu yi ta aikata zunubi har sai idan ya tashi kama mu sannan yai mana damkar da zata saka mana nadama da dana sani, a duniya kenan da Aminu ya fara haduwa da sakamakonsu, to ina kuma a lahira? Sai dai ina kyautata masa zato kasancewarsa musulmi kuma ya gane kuskurensa ya tuba, Allah yana son bayinsa masu tuba. 

    Na shiga gida da tunanin Aminu a raina, ba ma ni ba a halin yanzu Aminu be isa ya tunkari wata mace yace yana sonta ba, sai idan mai dauke da irin lalurarsa ce ko kuma idan boyewa zai yi, wata kila ma yayan da yake aibantawa yana cewa na haifa masa yara da yawa zam tsofar da shi sune kadai yaran da Allah zai ba shi. A ranar na kudirta a raina cewar ba zan fada musu cewar mahaifinsu yana dauke da cuta ba, fada musu ba zai haifar musu da komai ba sai tashin hankali duk kuwa da kasancewar akwai kurciya a tare da su, ba lallai ne su fahimci komai ba. 

  Har ga Allah na jidadin da cutar ta kama Sadi da Sa’adatu ko ba komai dukansu sun ci amanar aure kuma sun ci amanata, Sa’adatu kawata ce ta zabi tai mu’amala da mijina bayan kuma ita ma din tana da aure da yara, sadi kuma ya ci amanar dan’uwansa yai ma yar dan’uwansa fyade, ko da yake har da sakacina a wasan lokaci na barinsu da nake suna kebewa a tare yawan shige masa da take ban taba hanawa ba, saboda ban kawowa zuciyata komai a kansa ba, ko da yana zina ban tana ayyanawa a raina cewar zai iya lalata yar dan’uwansa ba, ashe duniyar ta dade da canjawa daga sanin da nai mata, a yanzu babu yarda a tsakanin yaranka da kowa, domin bayan Namra na yi ta ganin labarai masu sosa zuciya wasu uncles dinsu zasu lalata su wasu kuma ubansu na ciki ko makota, kai har malaman makarantar boko da islamiya ba a bari ba, hakan yasa na kara saka ido akan duk wani motsi na yayana ba mata kadai ba har mazan domin suma ba a yanzu ana lalata su, mun kai wani zamani da babu aminci a zukatan mutane kowa kokarin cutar da kai yake. 

A washe garin ranar sai na tashi kamar wata marar lafiya, ba labarin Aminu kadai daya saka jikina sanyi ba har da tunanin Ahmad abunda ban tana ba, ko da dai rana ban tana kwantawa ko tashi da tunaninsa ba. Sai dai jiya na raba dare da tunanin abunda yai min da wasu alamomi da sai a yanzu nake fahimtar inda ya dosa. 

“Hello Lims fatar kin tashi lafiya Happy birthday”

Shine farkon abunda ya fara shigo min a waya, kamin na bank dina su turo min. Ni kan har na manta da wani zancen birthday sai yanzu. 

  Aje wayar nai na fito tsakar gida na debi ruwa na shiga daki na juna a electric kettle, haka na bi yarana na zuba musu ruwa sukai wanka sannan suka karya suka saka uniform. Zuwa nai na gabansu na risina ina kallonsu wani irin farincikin marar misaltuwa ya lullube ni lallai yara rahama ne, no matter how suke rashin ji ko suke cutar da junansu. 

Advertisements

“Allah yai muku albarka ya shirya ku da duk yaran musulmi, ya tsare ku.”

Duka suka amsa da amin, daya bayan daya na busu da addu’a ina dafa kansu ina karantawa har na gama sannan school bus dinsu ta iso, da gudu suka fita daga gidan kowa yana kokarin ya riga dan uwansa gwanin sha’awa. Da kallon kauna na bisu zuciyata cike da shauki ina murmushin jindadi da yi ma Allah hamdalla. Ina juyawa sai ga Namra ta dawo tare da Adnan suna rike da wani katon kwali wanda daker ma suke iya daukarsa, an nade kwalin da fata jar leda mai kyale.

“Momy Momy gashi inji direban Bus yace wai a baki”

Jin hakan yasa nai saurin tashi na karasa na karbi kwalin. 

“To Momy bude ki sam mana abunda ke ciki”

Namra ta fada jikinta har rawa yake. 

“Kin san abunda ke ciki?”

“No”

“To kuje makaranta idan kun dawo zan ba ku nima ban san miye a ciki ba”

“Momy to waya baki?”

“Namra… Ba yanzu kika karbo sakon ba? Ni ina zan san wanda ya bani to?”

“Momy ai shi mai bus din mu ba son ki yake ba ko?”

Ta tambaya tana sako min ido, sai a lokacin na daka mata tsawa domin na fara gundira da tambayoyinta. 

“Ban sani ba, wuce kuje sarkin gulma”

Dariya tai ta nufa kofar fita da gudu daman tuni mai bus din ya danna musu horn alamar yana jiransu. 

“Daddy na yace idan wani ya zo son ki na fada masa, kuma sai na fada masa wannan”

Hafiza wacce ta nufo dakin da nake ta tari numfashinta.

“Tsohuwar munafuka ki ce tace masa i love you”

“Mama Hafiza i hate you”

Ta karasa fada sannan ta fice daman shi Adnan tun da ya aje kwalin ya koma ita ce dai ta tsaya gulma. Aje kwalin nai a tsakiyar falon Mama na gagara budewa, ko ba a fada min ba na san Ahmad ne yai domin shi yasan yau nake birthday gashi kuma direban motar scul dinsu ce. Hafiza ce ta bude kwalin sauran yan’uwana duk suka zagaye kwalin kowa yana son ya ga abunda ke ciki, katuwar kwalbar strawberry guda biyu ta fara fitarwa sai cake dan madaidaici wanda aka rubutawa happy birthday, a kasan cake din wani madaidaicin kwali ne, da kanta ta bude kwalin sai ta ciro wata farar takardar sannan ta ciro turare man shafawa da wata sarka wacce nake kyautata zaton zinari ne.

“Oh my god oh my god see love abeg duk Babban Baby Namra ne ya aiko ko?”

Ta tambaya tana kallona, sai na rasa me zan ce mata idan nace a a na yi karya tun da fa gaskiyar a bayyane, ban gama tunanin irin amsar da zan bata ba na ji ta fara karantawa wasikar dake tare da kayan. 

“On your birthday, I want to remind you that you are special, not only to me but to all those who are privileged enough to know you for the amazing person you are. People like you are hard to come by, but getting to have a woman like you is indeed a gift, People tell me that the best years are still to come. I have to agree with that because my upcoming years will be spent with the world’s most amazing woman.

Happy birthday to someone who improves every life she enters. You always know how to make an impact, but none so strong as the one you made on my heart. I will turn your black and white world into full-blown technicolor. Happy birthday to the leading actress of my life, 

If anyone is deserving of all the happiness in the world, it’s you, you are a wonderful mom, a loving woman, and a fantastic human being.

Happy birthday Lims❤️”

Kamar sautin waka haka nake jin ko wane kalami da Hafiza take karantawa a bayyane, wani irin shauki da jindadi naji ya kama ni, ba na kalaman da Ahmad yai min kadai ba har na kyautar da yai min a yau da kuma nuna min ranar haihuwata tana da muhimmanci abunda wani be tana min ba, jin ziciyata tana kokarin alakantuwa da wani abu yasa nai saurin kawarda abun a zuciyata, domin idan har na nace zan sake biyewa kalamai ko wasu abubuwan na koma dakin so to lallai ban dauki darasi akan abunda ya faru da ni ba, domin Aminu ma yana nuna son kamar ba gobe a lokacin da yake nemana, Abdulhamid ma mun yi soyayya da shi a boye kamin daga baya ya dawo min, kuma dukansu ban tsammaci haka daga garesu ba sai gashi sun juya min ba, miyasa shi ma Ahmad din ba zai juya min ba, shi ma ai namiji ne kamar su, ba a gane na gari a fuska ko a aiki har sai an zauna da mutum musamman maza. 

“Ke me kike tunani? Ni daman na san wannan rawar kafar da yake son ki yake, ya ga ruwan da ke masa wanka…. Oh wayyo ni inama ace Aminu zai ga wasikar nan yau”

Dan murmushi nai. 

“A cikin wasikar kin ji yace yana so? ku rika fahimtar abu mana”

“Ohhh se dis woman, sai ya fito ya furta miki ne? Ai su manyan mutane basa fada maka suna sonka, ke bari ma na fada miki ko zancen basa zuwa sai dai a kai musu mata, yanzu idan ya fara zance da ke sai dai ya aiko mata a dauke ki akai masa ke”

“Oh really?”

“Yes Lims”

Sai duk suka kwashe da dariya, a gurin suka gutsitsira cake din aka cirewa su Namra na su na debi kadan na ci na sha lemun sannan na tashi na shirya na nufi gurin aikina. 

  As usual ina shiga na nufi office dina kai tsaye, ina shiga office din gabana yai mugun faduwa, zuciyata ta soma bugawa da karfi kamar zata fito sakamakon arba da nai da Ahmad tsaye jikin tebur dina yana sanye da farar shadda kansa da hula sai kamshin turare yake, rikewa nai na kasa sake daga ido na kalleshi kuma na kasa juya na fita daga office din kamar yadda na kasa karasa ciki. 

“Lims shigo mana”

Kamar mai koyon tafiya haka na fara takawa na karasa cikin office din. Har na kai gurin kujerata na zauna ban iya daga ido na kalleshi ba. 

Wani dan karamin abu mai kamar akwati ya aje min yan zagaye shi da wani jan zare.

“Happy birthday, kin san on my birthday kin bani kyautar agogon da me ma?”

Ya tambaya yana yatsina fuska kamar da gaske ya manta. Muna hada ido sai ya kanne min ido daya ya sakar min kyakkyawan murmushi, sannan ya juya ya fice yana kokari saka hannayensa aljihu. Murmushi nai haka nan kawai sai na ji farinciki ya cika min zuciyata ya wanzarda nishadi da cikinta. Zaren na fara budewa sannan na bude box din mai kama da box din agogo, domin shi na fi kyautata zaton gani a ciki. 

To my surprise sai nai arba da chewing gum, irin wanda na bashi a ranar birthday sa, ban san lokacin da murmushinsa mai sauti ya subuce min ba. 

***         ****         *****

Kana kallon fuskar Abdallah kasan yana cikin tashin hankali kamar yadda Hajiyarsa ma take ciki, kusan na nashi tashin hankalin ne ke saka shi a damuwa ba kamar na Hajiya wacce ta bi ta gigice saboda batan Abdulhamid, wanda yau kwana uku kenan ba san inda yake ba kuma ba a ji duriyarsa ba, idan kuma aka kira wayarsa bata shiga shi kuma be kira ba, yawancin mutane sun fi kyautata zaton an garkuwa ne suka dauke shi duba da halin da ake ciki a kasar. 

  Hajiya kuma tana ganin kamar yan yankan kaine suka sace shi, domin idan yan garkuwa ne ba zai kwana har uku a gurinsuba, ba tare da sun kira waya sun fadi abunda suke bukata ba, yayinda dan’uwansa Abdallah kuma yake wani tunanin na dabam.

“Ya dade a nan zaune, yana ta latsa waya can kuma sai ya kalleni yai shiru kamar mai tunani, ashe yana ji a jikinsa”

Hajiya ta fada cikin kuka.

“Yana zaune aka kira sallah isha’i, a gida yai ta be je massallaci ba, har na yi mamaki dan be saba sallah a gida ba ko ta asuba balle isha’i tun tashinsu shi da Husaini ba su saba sallah gida ba saboda Alhaji ya koya musu sallah masallaci, na ce masa ga abinci yace min a a ya koshi na bashi ruwa shayi ya sha, na sa Furera ta hada masa ruwan shayi ya sha, be bar gidan nan ba sai kusan 11pm sannan yai min sai da safe ya tafi, ita ake har yau be dawo ba, kuma ya saba zuwa da safe ya gaishe ni haka da dare kamin ya wuce gida kusan ma nan yake wuni saboda ba shi da mata a yanzu, kuma dan shirye shiryen bikin nan da ake kusan kullum yana nan da shi ake duk wasu shawarwari tun da lokaci ya kusa”

“Allah dai ya bayyana shi a duk inda yake”

Wata dattijiwa dake kusa da Hajiya ta fada fuskarta dauke da damuwa. 

“Amin”

Abdallah ya amsa tare da sauran mutanen da suke falon, gaba daya idonsa da hankalinsa yana gurin Mahaifiyarsa. 

“An kai report gurin police amman har yanzu shiru”

“Ai wannan abun bana police bane kawai, ya kamata a shiga malamai ayi sadaka Allah ya bayyana shi a duk inda yake, massada babu abunda basa yi gashi ana kusan biki saura wata daya ace babu ango ina lafiya?”

“Amaryar ita ma ai tana can hankalinta tashe ance sai kuka take, ko abinci bata iya ci”

Cewar Hajiya. Hajiya Rukaiya wacce kanwace ga Hajiya ta rausayar da kai cike da tausayawa.

“Wayyo Allah, ai dole Allah dai ya bayyana shi”

A nan ma Abdallah ya sake amsawa da Amin sannan ya mike tsaye. 

“Hajiya bari na leka office na dawo”

“To Allah ya tsare ka kai ma”

“Amin, In-Sha-Allahu za a ganshi ki kwatarda hankalinki dan Allah”

Kai kawai ta gyada masa ta Lumshe idonta dake cike da damuwa. Shi kuma ya fice daga falon jiki ba kwari. 

__________

Ayi hakuri da wannan 🙏

Leave your vote

-2 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

GOBE NA 63

Advertisement  *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  6️⃣3️⃣ Mun iso Zamfara cikin aminci da farinciki, tun airport yan su…

GOBE NA 42

Advertisement   *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  4️⃣2️⃣ Da hannu daya yake tuka motar yayinda dayan hannunsa yake…