GOBE NA 55

Advertisement

 

*GOBE NA…*

By Khadeeja Candy 

5️⃣5️⃣

Idan na ce zan iya fadar kulawar da na samu a gurin Ahmad da mahaifiyarsa na yi karya, domin a kwanan da nai asibiti kullum sai na yi bachi yake tafiya gida, mahaifinyarsa kuma sai tavaiko mana da abinci safe, rana da na dare, sau uku tana zuwa duba ni asibiti, a duk lokacin da ta zo tana yi min

kalaman da suke kara min kimarta a idona kuma su kara kwantar min da hankali. Tana yawan fada min cewar nai hakuri, kuma na cigaba da yarda da kaddara kamar yadda nake, kar nai tsammanin Allah ba zai sake jarabata ba, kuma kar na tsammaci sake samun wata kadarar a gaba, na kyautata zaton kuma nai ta addu’ar, haka zata zauna tai ta fira da Mama ko Inna kamar ba matar babban mutum ba ko kuma na ce uwar babban mutum, da aka salleme mu a asibitin ma sai da ta kira ta ji muryata.

Advertisements

Yau kam na kara yarda da maganar mutane da suke cewa duk abunda ya baka tsoro wata rana zai baka tausayi, duk kuma abunda ya baka tausayi wata rana zai baka mamaki. 

Idan nai na hada kalubalen rayuwar da na fuskanta da na Aminu da Abdulhamid, sai na gane cewar ni din ban ga komai ba, domin a halin yanzu Allah ya min mafita kuma ya wanke ni, wani kalubalen a farkon rayuwa yake wani a karshe, wani a tsakiyar rayuwarsa, ba duka arziki ne na halal ba, na kuma ko wane arziki ne na haram ba, ba duka talauci ne kunci ba, ba kuma duka kunci ne takauci ba, saboda ina cikin takauci ba shi yake nufin ba zan jidadi rayuwa ba, idan kuma ina da arziki baya nufin aki jarabbatata. 

  Ta wani bangaren na kanyi mamakin abunda ya kai Abdulhamid aikata wannan mummunan abu, ko da yake ko wane bawa be isa ya wuce kaddararsa ba. Kamar yadda ban wuce komai ba sai da ya same ni. Ba ni kadai nake cika da mamaki ba har da Mama da Inna, da duk wani wanda ya san waye Abdulhamid, mutumen da magana ma bata sha masa kai ba, dole kowa yayi mamakin wannan abun, wata kila Abraham ne yaja zuwa ga mummunar rayuwa, wata kila kuma shi yaja Abraham din, gaskiyar abun yana a tsakaninsu sai kuma bincike idan ya tabbatar. 

Dago kaina nai daga kallon wayar Hafiza da nake wacce ke dauke da hotunan su Abdulhamid, da Abraham da wani wanda ban wayance shi ba, an saka musu handcuffs, police na tsaye a bayansu an jarida kuma nata aikinsu. Na mika mata wayar ina fadin. 

“Abdulhamid ya ban tausayi”

“Tausayi? Tausayi fa kika ce Halima? Haba mutumen daya sakeki har wani tausayinsa zaki ji, ke dai Wallahi kina da matsala”

Na yi shiru domin na san ba zata taba fahimta ba, sai dai abunda ya fi tsaya min a rai shine shin Abdulhamid ya san cewar Abraham ne yai min fyade? Da saninsa akai? I need to know, na fada ina sauke ajiyar zuciya a hankali. Na unkura zan tashi kenan sai ga su Namra sun shigo da gudu kowanensu rike da leda a ko wane hannu, ledan kuma ba karama ba irin babbar ledar nan ta super market. 

Advertisements

“Momy Guess what…?”

Aiman ya fada yana wani irin murmushin jindadi. 

“What it’s?”

Na tambaya da mamaki a fuskarta.

“Wannan Boss din naki, baban su Baby Namra ne ya dauke mu daga school ya je da mu wani katon shago yace mu dauka duk abunda muke so”

Wannan karon Adnan ne yake magana, sai Namra ya kyalkyale da dariya. 

“He say we should called him Daddy, wai yana jiranki a waje yana can cikin mota”

Kana kallonsu kasan suna cikin farinciki, jin cewar yana waje yasa na dauki Hijabina na saka na leka kofar gidan, sai ko na ganshi daf fa kofar ya faka motarsa. Ganina yasa ya sauke gilashin motar yana miko min murmushi.

“Lims how far”

Dan murmushi nai nima

“Mun gode Allah ya saka da alheri, kana ta dawainiya da yara”

“Bude back seat din nan akwai na ki”

Ya fada yana dauke fuskarsa kamar baya son nai masa godiyar. Na yi kamar yadda ya umarta na bude gidan baya na dauko katuwar leda na fito da ita. 

“Na siyo miki turare duk da ban san choice dinki, amman ni nafi son irin wannan wanda na siyo miki, na mata ina son na ji mace ta saka shi”

“Na gode Allah ya saka da alheri”

“Ki dai shirya komawa aiki on Monday, tun da lafiya ta samu sosai”

Na gyada masa kai sannan na ce. 

“In-Sha-Allah, amman dan Allah ina neman wata alfarma”

Kashe motar yai gaba daya, ya fito daga ciki ya zagayo inda nake ya saka hannayensa duka biyu aljihu yana min wani irin kallo wanda da ace akwai wani kusa da ni da sai na ji kunya, domin idonsa ya sako min sosai kamar zai cinye ni. 

“Name it”

Ya fada kamar mai rada. Kasa nai da kaina ina wasa da ledar da ke hannuna.

“Lims….. ”

Ya kira sunana cikin wata irin siga wacce ta saka sigar jikina tashi, da na kalleshi kuma sai na kasa jure irin kallon da yake min. 

“Okay Babe mu shiga mota sai ki fada min idan ba zaki iya fadi in public ba….”

Idan ban yi kuskuren fahimta ba kamar yace Babe right? Mistake yai ko kuma da gangan ne? 

“You know bani da wannan hurumin da zan rumgume ki na kallashe ki na tambaye ki abunda kike so, so please just tell me idan ba so kike ki wahalar da zuciyata ba”

The way da yai maganar kamar yana rokona ta shigar lallashi akan na fada masa abunda ni nake da bukata. 

“Daman ina son na tambaya ne ko ana barin mutum ya ga Abdulhamid”

Na fada cikin tsoro da fargaba, runtse ido yai ya bude ya sake kallona. 

“Abdulhamid….”

Ya maimaita sunan.

“Why?”

“Akwai tambayar da nake son masa, ina son naji amsar daga bakinsa ne kawai”

“It’s necessary?”

Na yi kasa da kaina, sai yai saurin matsawo kusa da ni. 

“Okay Okay Okay… Kin san irin criminals din nan ba kowa ake barin yana shiga ganinsu ba, saboda gudun abunda zai faru, tun da suna tare da miyagun mutane ne, but idan kina son ganinshi i can talk to my friend sai yai mana hanya ki ganshi, idan ya bada date zan fada miki sai ki shirya na kai ki”

“Thank you so much”

“No Lims dadi nake ji idan kika bukaci wani abu nai miki, so thank you so much for the offer”

Ya fada sound so serious, sannan ya zagaya zuwa side dinsa yana kallona tare da fadin. 

“But make sure ba wani kalma mai dadi za ki fada masa ba, ba zan jidadi ba idan kika furta wata kalma mai dadi ga wanin Ahmad, saboda Ahmad yana da kishi sosai idan yana da da dama ma, ko a unguwarku ba kowa za ki yi wa magana ba i swear”

Ya bude motar yana min murmushi.

“Take care of yourself”

Sannan ya shige motarsa yai mata key ya bar ni tsaye a gurin ina mamakin kalamansa. Yace Baby at first, and second to the last sentence ya fadi wasu abubuwa da ban gane ma kansa ba, i thought ba soyayya muke ba, but why yake irin wannan behaviors din? Na san ko bw fada min ba abunda yake min da kuma kulawarsa akaina tana nuna damuwarsa ne, kuma akan damune ne da abunda ake so, ko kuma ya zama muhimmin a rayuwa. Sai dai ni din a yanzu ban shirya ba ban kuma san ranar da zan shirya din ba.

  Ko da na koma cikin gidan an tarar sun bude abubuwan da ya siyo musu suna ci, sai labarin abubuwan da suka gani suke badawa, ni kuma an zauna saman tabarma na bude ledar, kananan cakes a ciki sai wata kyakyawar sarka mai ruwan zaiba, turare ya fi yawa sai man shafi cream and lotion, da shower gel, kana ganinsu kasan masu tsada ne. 

  Ina jin yadda kannen suke kamgama shi ni dai bance komai ba, har suka ci suka shude sannan na dauki kayan bayan na basu cake din na nufi daki na aje. 

Kamar wasa da dare Ahmad ya kira ni a waya ya fada min crwarna shirya gobe misalin ten zai zo ya dauke ni ya kai ni can abokinsa yace zai bar ni na shiga nai magana da shi, a lokacin kuma dai na ji kamar bana son zuwan wata zuciyar tai ta raya min cewar miyasa na bukaci haka? Ban kwanta ba sai da na fadawa Mama abunda nake da kudiri akai. 

“Amman dole ne sai kin yi magana da shi? A iya tunani na Halima, ya kamata ki nisanta kanki da yayan Hajiya, ba nuna nufin ki yanke alaka ba, a a ki yi nesa nesa daga duk wani abu da zai iya sakawa a zarge ki, iyakar cin mutuncin da nuna kiyaya Hajiya ta yi miki shi”

“Na sani Mama kawai ina son na masa wata tambaya ce, wacce nake son amsar ta daga bakinsa”

“To Allah ya tsare, tare za ku tafi da Ahmad din?”

“Eh In-Sha-Allah”

“To yayi kyau”

Shiru ne ya biyo baya kamin ta kalleni tace. 

“Ba zan matsa miki ki yi aure ba, kamar yadda ba zan hana ki sauraren kowa ba, sai dai duk wanda kika san ba aurenshi za ki yi ba, to ki sallame shi da wuri ba sai yayi ta wahala a kanki ba”

Ko bata fito fili ta fada min ba, na san Mama tana magana ne akan Ahmad kuma tana da gaskiya, ya kamata na dakatar da shi daga abubuwan da yake min ko ya fara min, kar abun yai nisa ya zame min wata sabuwar matsala. 

  Kamar yadda ya fada min zai zo da ten ya dauke ni, sai nai gaggawar yin duk wani abu da nake kamin lokacin na sallami yarana suka tafi Islamiyarsu kasacewar yau Sunday suna zuwa makarantar safe ne, sannan ni kuma na shiga nai wanka na shirya cikin bakar abaya, na yafa farin veils karama wanda ya tsaya min iya wuya, ban shafa komai a fuskata ba bayan powder sai dan man baki dana goga, na feshe jikina da turaren da Ahmad ya akwa min jiya, turare ne mai dadin kamshi ina jinsa a gurin manya mata idan na shiga buki ko office. 

Sako ya turo a waya cewar yana waje yana jirana. 

“Hey Beb ina jiranki a waje idan kin shirya”

Bayan na karanta sakon na samu kaina da faduwar gaba, ina ta jin tsoro zuwa bayan kuma ni na bukaci haka, sai da na sanarwa Mama sannan na fita ina addu’ar fita daga gida. Ina fito daga cikin gidan ya sauke gilashin motarsa yana kallona har na karaso, da kansa ya fito ya bude min motar ni kuma ban shiga ba sai da na fakaici idon mutane, bayan na zauna ya maida motar ya rufe sannan ya zagayo side dinsa ya rufe gilashin motar yana kallon. 

“Kin san Allah? Da kika fito daga gida na hango ki ji nai kamar naje na rumgume ki? And the way you’re walking wow Ma-sha-Allah”

Na yi murmushi ina kallon yadda black suit din da ke jikinsa yai masa kyau sai mu ka yi anko kamar na fada masa nima bakin kaya zan saka. Ya bata minti goma a gurin baya aikin komai sai kallona can kuma ya shaki kamshin turaren da ke jikina ya lumshe ido, kamin yai ma motar key mu kama hanya. Kamar wacce tai masa maganin kallo haka ya saka min ido yana ta kallona yana murmushi kamar ba driving yake ba, har tsoro na rika ji kar ya mu yi accident. Mun yi tafiya mai nisa sosai sannan muka isa gurin daga ba a bar mun shiga cikin ba sai da abokin nasa ya fito, the way da abokin ya rika min magana sai na fahimci cewar Ahmad ya fada masa cewar ni matarsa ce wata kila, domin a cikin kalamansa har da zancen wai mijina yana so na sosai duk yabi ya dame shi shi dai matarsa matarsa. Kallona kawai Ahmad din yai ya kashe min ido yana murmushi, can kuma muna sake hada idon sai ya sake kanne min ido daya ya leko da halshensa kadan yai min gwalo still yana murmushi. 

“Gaskiya Ma-sha-Allah ka yi dace mata, Allah….”

“Na sani, zamu iya shiga ciki?”

Tun kamin mutunen ya karasa Ahmad ya katse shi yana hade rai kamar ba shi ba. Dariya mutumen yai ya juya muka nufi cikin gurin, nesa da ni Ahmad ya tsaya dan bani damar yin sirri, ni kuma na karasa ciki na zauna a gurin da aka tanada, ta ko’ina akwai security amman hakan be hana ni jin tsoro ba, gabana sai faduwa yake, duk bayan minti daya sai ya juya na kalli Ahmad sai ya dago min hannu ya aiko min da sakon murmushi. After like 14 minutes aka fito da Abdulhamid daga shi sai vest da gajeren wando, gaba daya ya canja, daman can ba jikin ne da shi sosai ba sai ya kara ramewa fuskarsa tai kamar wanda ya shekara be ci abinci ba. Har ya zauna a kujerar dake facing dina be kalleni ba. 

  Yana ta murza wuyan hannunsa, tsakanin ni da shi sai aka rasa wanda zai fara yi ma wani magana, sai da na sake juyawa na kalli Ahmad ya dago min hannu yai min murmushi sannan na ji karfin guiwa fara ambatar sunansa. 

“Abdulhamid….”

“Miyasa kika zo nan?”

Na tari numfashina ba tare da ya kalleni ba. 

“Kin jidadin abunda ya same ni ko?”

A lokacin ne idona ya soma cika da hawaye.

“Mi zai saka na jidadi? Ko da ban san ka ba, ballantana kai din dan’uwana ne jinina”

Sai a lokacin ya dago ya kalleni. 

“Ina son nai maka wata tambaya wacce nake son jin amsarta daga bakinka”

Na hade yawun bakina sannan na ce. 

“Miya hadinka da Abraham?”

“Abokina ne more than 11 years, na hadu da shi a Lagos, a lokacin da naje gurin hutu, a hotel din da na sauka daki daya muka zauna a lokacin, kasancewar babu dakuna da yawa a hotel din, kasancewar ana bikin nada sabon sarki a garin, and hotel din da muka sauka kusan duka an kama dakunan ciki kasancewar ta babbar hotel, we share the same room and he is the one da ya biya komai, ya sake min sosai we exchange our numbers, lokaci zuwa lokaci mu kan hadu, some time kuma a waya, saboda shi police ne yana yawo gari gari, shakuwarmu tasa muka fahimcin juna sosai duk kuwa da kasancewar ba Addininmu daya ba, shi ya fara dorani akan sana’ar siyar da motoci, shi ya nada min jari duk da a lokacin ba wai bana da kudin ba ne, kawai dai bana ra’ayin abun ne, bayan mun fara sai ya sake nuna min wannan hayar, ban dubi hadarin da ke ciki ba sai na kalli yawan abunda zan samu, sannu sannu na fara tun ina yi ina jin tsoro har na daina, sai duk irin alakar da ke tsakanina da shi, ba kowa ya san muna abota ba, saboda abu ne da ke bukatar sirri idan aka ga alakar ta yi aminci sosai za a fara zarginmu, that’s why idan zamu hadu sai dai mu hadu a sirrice, har Allah yasa ya dawo garin nan da aiki”

Yayi shiru tare da kawardar da fuskarsa. 

“Amman ka san cewar  Abraham ne mutumen da yai min fyade?”

“Na Sani, ko da Abdallah ya fada min na sani”

Ya amsa ba tare da ya kalleni ba. 

“After na rabu da ke, na gano cewar shine saboda ya fada min yasan wandanda suka kashe Alhaji Sama’ila na yaddo, and you told me on that very night suka keta miki haddi, and guess what a wannan daren ya shirya kashe ni ne, saboda babu amana a tsakani, wanda ni ba zan iya hakan ba, shi yana ganin kamar na karbe masa jama’a na fishi samun kudi, domin shi wasu mutanen suna tsoron mu’alama da shi ganin cewar Jam’in tsaro ne, kai tsaye na tuhume sa da cewar shi ya keta miki haddi kuma ya amsa min da cewar yes shine, and now yana neman inda zai same ki ne, saboda kin ci ciki bayan shi be taba kwantawa da mace tai ciki ba, and he already know ni bana da lafiya”

“Amman baka taba fada min ka gano shi yai min fyade ba, baka nemi afuwar kazafin da kai min ba, ba ka wanke ni a idon mahaifiyarka ba”

“Komai ya riga ya lalace Haima, a lokacin na gano cewar Abdallah yana son ki, Hajiya tana kin ki, kuma na san ba zaki tana dawowa a gareni ba, saboda ni ba zan iya komai da mace ba, shiyasa na bukaci boye soyayyarmu tun farko bana son wannan sirrin ya bayyana, gano cewar Abdallah yana son ki shi yafi komai bata min rai, kuma lokaci ya kure Haima komai ya lalace, na kasa yarda da ke na rabu da ke, and silata abokina ya keta miki haddi”

Hawaye ya fito daga idonsa.

“A lokacin ne na gano cewar na rabu da matar da ba zan taba samun irinta ba har na mutu, na rasa komai ba ni da mata ba ni da yaya, babu irin neman maganin da ban yi ba amman na kasa samun lafiya saboda Abdallah”

Ya karasa yana murmushin bakinciki wanda hausawa ke cewa yafi kuka ciwo, sai ya kalleni. 

“You got lucky za ki auri mutunen da zai ba ki abunda ni da aminu muka kasa ba ki…. And the way da ya dage da neman tona sirrinmu i know yana son ki sosai”

Waiga nai da zimmar na kalli Ahmad amman sai ban ganshi a gurin ba. 

“Ba so na yake, abunda kai min kai da Aminu ya tsorata ni daga son wani ko aure a yanzu, murum data na yarda da shi a rayuwata Abdallah shi kadai nake da tabbacin na zai cutar da ni ba….”

“And you can’t marry him….”

Ya fada kai tsaye yana kallona da murmushi a fuskarsa hawaye na sauko masa. 

“Ba zai yiyu ki aure ni ba, kuma ki auri twina brother dina, bayan kuma ina raye, Hajiya ba zata yarda ba, hakan kuma na zai kara min komai ba sai tsanar Abdallah, and i know duk yadda za ki so shi ba zaki so shi kamar yadda ni kika so ni ba, I’m your first love i know ko yayana wata rana sai kin ji so a zuciyarki kamar yadda ni ma ba zan iya cire soyayyarki a raina ba, so you can’t marry my brother kuma ki rayu da so a zuciyarki, no matter what Abdallah zai baki Hajiya ba zata tana son ki ba, saboda tana ganin kin shiga tsakanin yayanta”

Mikewa nai tsaye sai shima ya mike. 

“Ban sani ba ko zan sake ganinki ko a a, ban sani ba ko za su yanke kin hukuncin dauri rai da rai ne ko kuma za su halbemu ne i don’t know, but i wish you all the best in your entire life, and I’m sorry for what I did”

A lokacin ne hawaye ya fara sauko min kamar ba gobe, tausayinsa ya rufe ni ya sadakar ya san cewar kashe shi za ayi kenan, maganganunsa suka rika min yawo a cikin kai, cewar ba shi da mata ba shi da yafi komai tsaya min a rai, kasa tafiya nai sai kallonsa nake ina hawaye kamar yadda shi ma ya rika waigena yana kuka kamar ba shi ba. Har na nufo inda motar Ahmad take na bude na shiga ban daina hawaye ba, yana kallona hankalinsa ya tashi. 

“Me ya faru? Mi yai miki?”

Kasa magana nai sai kokarin saida hawayen nake, hakan yasa shi fusata ya bude motar sai fita nai saurin riko rigarsa ina girgiza masa kai. 

“Be min komai ba”

“Then why are you crying?”

Na yi saurin share hawaye. 

“Ba komai”

Kallona yai for a moment sannan ya rufe motar muka kama hanya, sai da muka hau titi ya dauko ruwa ya miko min, na karba na bude ya sha ruwan sosai sannan na rufe na aje. Har muka isa gida ban ce masa komai ba shi kuma be fasa kallona ba, bayan yayi farkin na fita cikin motar. 

“Thank you”

Na furta ba tare da na jira abunda zai ce ba na shige cikin gidan, a wunin ranar sai na kasa sukuni cikin abunda nake tunani har da zancen samun lafiyarsa wanda yace Abdallah ne, kamar ya? Shi ya masa wata allurar ne ta zame masa haka? Amman Abdallah ya san da da wannan kuwa? Mi zai saka yayi masa haka?

Kamar ya san ina tunaninsa sai akai sara ka gaba, kiransa ya shigo wayata, sai dai wannan karon kasa daukar wayar nai har tai ringing ta katse sai ya sake kira sannan na dauka. After mun gaisa yace min. 

“Abdulhamid yace kin je gurinsa yau”

“Eh”

Na amsa masa a takaice duk da na san ya kira ne saboda ya san dalilin zuwana.

“Okay”

Har zai aje wayar na ce. 

“Abdallah zan iya tambayarka wani abu?”

Shiru nai na wani lokaci har sai da yace.

“Ina jin ki”

“Da gaske kai ne silar ciwon Abdulhamid?”

Shiru yai daga can cikin wayar sannan kamin ya aiko min da tambaya. 

“Kamar ya?”

“Ya fada min kai ne sila, taya?”

“Magana ce mai tsawo Halima zan na same ki gida daman akwai maganar da nake son yi da ke”

“Ka fada min dan Allah, zuciyata ta kasa yarda kuma na kasa natsuwa”

Ina jin yadda ya sauke ajiyar zuciya sannan yace. 

“Abun ya dade tun muna samari ne, na tashi da son yara musamman maza, and Abdulhamid ya san da haka, kamar wasa wata rana muna magana nace masa zan riga shi aure, shi kuma yace ko na riga shi aure ba zan haifi namijin da nake da buri ba, ni kuma na ce masa shi kuma ba zai ma taba haihuwar ba har sai na haifi namijin, and na gano haka ne after Suwaiba ta fara haihuwar Mata, and last barin da tai ma macece, yayi min kofi ne and after that Hajiya ta ba mu maganin kare kofi saboda abubuwan da suke faruwa, na shi ya kare nawa kuma ya rage kaifi that’s what i know”

***

( Wannan abun ya faru a gaske, Hasana da Husaina, Husaina tai ma Hassana kofi cewar ba zata taba aure ba, ita kuma Husaina tace mata ko tayi auren ba zata taba haihuwa ba, har yau kuma suna nan da rai sun fara manyanta Hassana ba tai aure ba Husaina kuma bata haihu ba)

***

Ajiyar zuciya na sauke ina mamakin yadda sukai wa junansu illa.

“Zan zo gobe akwai maganar da nake son yi da ke”

Ban sake ce masa komai ba na kashe wayar, a ranar na kwana da mamakin abun a zuciyata. Sai mafarka da safe kamar wata marar lafiya, haka dai na shiryawa su Amal suka tafi makaranta sannan ni kuma na shirya, yau ma abayar na saka sai dai wannan ash color ce tsabanin jiya da na saka black, sai da nai ma Inna da Mama sallama sannan na nufi gurin aikina kamar yadda Ahmad ya bukaci na dawo aiki bayan hutu daya ba ni wai sai na samu lafiya. 

  Napep na hau bata sauke ni ko’ina ba sai kofar gate din kamfanin, na gaisa da masu gadin kamar yadda na saba sannan na nufi ciki, a reception ma sai da na tsaya na gaisa da Blessed mace mai kirki da son mutane, sai da ta tambayi abunda ya hanani zuwa aiki kwana biyu na fada mata cewar bana jindadi ne, sannan na wuce na nufi office dina. Ina kai hannu na tura kofar office din gaba daya sai naga kamar ba nawa ba, hakan yasa na dawo waje da sauri na sake kallon kofar sannan na sake shiga, gaba daya an kawata office din da abubuwan kawa kamar gurin taron biki, idanuwana sama na shiga cikin ina ta kallon kyale kyalin da ke saman sai wani kamshin rose ke tashi an kuma jera fulawar rose har saman kujerar da nake zama. Ji nai kamar na taka wani abu mai tsantsi hakan yasa na kalli kasa da sauri sai nai arbar da fulawar rose an yi rubutu da ita cikin mayan haruffa. 

*WILL YOU MARRY ME…*

Wani irin faduwa gabana yai, da ni ake ko da wata abunda nake gani a fina fine nake karantawa a litattafai yau shi ne a gabana, motsin da na ji a bayana yasa na juyo da sauri kamar a rikice nai arba da mutum duke a gabana……

______________

I can advertise your business with some of my pages and status just chat me. 08036126660😊🙌

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

GOBE NA 59

Advertisement  *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  5️⃣9️⃣ Kwance take a dakinta tana kallon windows din dakinta da suke…

GOBE NA 45

Advertisement *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  4️⃣5️⃣ ABDALLAH POV.  Advertisements Zuciyarsa cike take da tunanin abunda Halima ta…

GOBE NA 48

Advertisement  *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  4️⃣8️⃣ Tun daga yanayin tafiyata zaka fahimci ina cikin wani irin nishadi…

GOBE NA 12

Advertisement  *GOBE NA…* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy  1️⃣2️⃣ “Hajiya barka da tashi ya kafafuwan?” A natse yake…

GOBE NA 49

Advertisement  *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  4️⃣9️⃣ A lokacin daya fito falon ya samu Mahaifiyar Aminu da wata…