GOBE NA 59

Advertisement

 *GOBE NA…*

By Khadeeja Candy 

5️⃣9️⃣

Kwance take a dakinta tana kallon windows din dakinta da suke bude, pillow na rumgume a kirjinta babu abunda ke fita daga idonta sai hawaye masu zafi. 

  Mai aikinsu ce Hindatu ta turo kofar dakin ta shigo da sallama. 

Advertisements

“Assalamu Alaikum, Siyama Hajiya na nemanki”

“Ki ce zan zo”

Ta amsa ta ba tare da ta juyo ta kalleta ba. After like one hour Hajiya ta turo kofar dakin ta shigo.

“Siyama….”

Sai a lokacin ta fara kokarin yin kamar bachi take, hakan yasa Hajiya ta karasa kusa da gadon ta zauna leken fuskarta da hawaye ya gama yi mata kwalliya. 

Advertisements

“Miye abun kuka kuma? Me yake damunki?”

Juyowa tai da kyau ta kalli Hajiya wasu hawayen na cika mata ido. 

“Hajiya…”

Sai kuma tai shiru ta tashi zaune tana matsar yatsun hannunta. 

“Ba ki fito kin ci abinci ba, ko yau ba kya zuwa makarantar ne?”

“Hajiya bana son na sake rasa kowa”

Ta fada cikin hawaye. 

“To wa za ku rasa?”

“Ban sani ba, amman yanzu idan ciwo ya kama wani a cikinmu sai na rika ganin kamar zan rasa shi ne, i don’t want to be alone….”

Ta fashe da kuka, tana kwantawa jikin Hajiya. 

“Babu abunda zai samu yayanki zai samu sauki In-Sha-Allah, ki daina tada hankalinki kin ga nima kina daga min nawa, da kuzari da karfin zuciya da nake da shi sai ki sa ya karye”

“Hajiya ina jin tsoro”

“Ki daina kawai ki yi masa addu’a, ki tashi ki wanke bakinki ki fito ki yi breakfast”

Ta gyada kai tana share hawayenta Hajiya ma ta yi saurin tashi tana tare hawayen da ke son zubo mata, cikin rashin kuzari ta fita daga dakin ba Siyama kadai ba ita kanta abun ya bata tsoro jin cewar ba a ga komai ba kuma gashi yace yana jin ciwo, tun daga lokacin da ciwon ya same shi baya iya komai daga zaune sai tsaye sai kwance wani lokacin kuma ya kan dan zagaya cikin asibitin amman fa sai idan am masa allurar kashe ciwo, ga shi baya wani iya cin abu mai nauyi daga lemu sai ruwa sai tea shi ma can ba a rasa ba, sai dai tana addu’a kuma tana fatar idan an je check up din nan a gano matsalarsa. A dinning din take zaune amman ta kasa taba komai balle ta ci kamar ba ita ta dafa abun karyawar ba, yadda yake fito daga part dinsa ya zo part dinta su karya ko kuma idan ba shi da lokaci sai ya dauki breakfast din ya tafi da shi ko mug ne abunda yafi tsaya mata a rai, yau kusan 7 days yana asibiti mutumen da bata bari yai nisa da ita, and the most saddest part is aurensa aka daura yana cikin farinciki wannan abun ya same shi. 

A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta dora hannayenta saman dinning din ta dafe kanta kamin ta kike tsaye ta nufi upstairs dan jin tai bata bukatar cin komai. 

HALIMATU POV. 

Ba karamin tsoro ne ya kama ni ba, na san ban tana kiran Ahmad ba tun da nake a rayuwata, amman mi zai saka yanzu na kira shi yaki dagawa? Amman ya kamata nai masa uzuri, after like seven minutes a sake gwadawa still be daga ba na sake gwadawa be daga ba haka nai ta yi har kusan 20 miss calls amman be yi picking ba, a lokacin ne fargabana ya karu tsoro ya auri zuciyata na fara sake sake kala kala, ji nai bana da natsuwa kwata kwata a rayuwata jikina ya bani cewar akwai abunda Ahmad yake boye min. 

Tashin nai na shiga dakina na canja tufafin jikina na saka wata rigar yadi na dauki medium veil na yafa na saka talkamina na dauki yar purse dita cikin dabara na fice na bar gidan domin na san idan nace zan fadawa Mama zata iya cewa ba zan fita ba tare da izinin mijina ba, tun da ba fada mata zan yi gurinsa zan je ba, ina tafe ina waige waige kar wani dan gidan mu ya gan ni kamar wata marar gaskiya, Allah ko ya bani sa’a har na tari napep na hau ban hadu da kowa ba, zuciyata bata raya min na je ko’ina ba sai gidansu Ahmad, duk kuwa na san hakan be dace ba amman ba ni da wata mafita wacce ta fi wannan ko dan samun natsuwar zuciya dole naje na ga halin da yake ciki, tun da yanzu yamma ta yi ba na san baya kamfaninsa. 

  Sai da mai napep din ya kai ni har kofar gidan na sallame shi sannan nai knocked din gate din gidan cikin sa’a kuwa mai gadin ya bude min, sai da muka gaisa da shi sannan na tambaye shi ko masu gidan suna ciki, ya amsa min da suna ciki har ma da bude min kofar, sai da na doshi harabar gidan sannan na soma tambayar kaina to idan na shiga ciki me zan fada musu? Idan ma mahaifiyarsa ce tai masa katanga da ni fa? Kuma gashi na shigo har cikin gidan anya shi ma kansa zai jidadi? No wait idan ma babu duk wannan anya ban yi rashin kunya ba na tukari idansu kai tsaye? A take duk na ji wani iri hakan yasa ban karasa ba na juyo na dawo gurin mai gadin. 

“Dan Allah Malam ko zaka shiga ciki kace ana sallama da Ahmad?”

“Wai Alhaji… Alhaji ai…. ”

Sai kuma yai shiru ya kalleni. 

“To bari a fada musu”

Ya nufi cikin gidan ni kuma na bude gate din daker saboda shegen nauyinsa na fita daga waje na tsaya, kamin ya fito har na matsu bugun zuciyata ya karu ga tsoro ga fargaba da tunanin rashin dacewar zuwana sai suka taru suka tsaya min a rai. A tsammanina Ahmad din zai fito ko mai gadin amman ga mamakina sai kanwarsa ta fito waton Siyama, tana ganina ta saki far’a ta karaso ta rike hannuna. 

“Laaaaa In-law shine kika tsaya a waje”

Nima nai mata murmushin daya kasa boye damuwata cike da kunya na ce. 

“Bana son shiga ciki ne”

Sai taja hannuna tana fadin. 

“Dan Allah shigo ciki magana, sai ku gaisa da Hajiya”

“A a dan Allah ki bari, ba sai na shiga ciki ba amman Ahmad na zo….”

Sai kuma kunya tasa na kasa karasawa, sai tai murmushi.

“Ai baya nan ya tafi jos…..”

Da sauri na kalleta domin ni ba jos yace min ba. 

“Jos kuma?”

“Amman ba can yace min ya tafi ba”

Wani abu tai da ido tana yar dariya kamar marar gaskiya. 

“Eh na tuna daga jos zai wuce can garin da yace miki zai tafi…”

“Wane gari?”

Na sake tambaya ina ta kokarin gano gaskiyarta, sai ta fara kame kame wanda hakan yasa hankalina ya kara tashi. 

“Can inda yace miki, Kadu…. Na….”

“Ni Abuja yace min”

“Eh eh daga Jos din zai je Kaduna da Abuja, daman Abujar ya kamata nace tun dazun sai na fadi wani gari”

Ta karasa tana murmushin rashin gaskiya. Hannayenta na kama biyu na rike cikin wata irin siga ta magiya na shiga rokonta. 

“Dan Siyama idan akwai wata matsala ki fada min”

A iya abunda zuciyata ta raya min Ahmad na cikin gidan yace ace baya nan, hakan na nufin Hajiyarsa ta hana shi ganina kenan ko kuma wata matsalar ce ta dabam daga sashenta. Sakin hannayen nawa tai tace. 

“Ina zuwa”

Juyawa tai ta koma cikin gidan, ni kuma na tsaya a gurin zuciyata kamar zata fito, hawaye sai wanke min fuska yake ina sharewa, a yanzu kam idan har ta tabbata Hajiyarsa ta shiga tsakanina da Ahmad ban san ya zan yi ba, wata kila akwai matar da take son ya aura ba ni ba shi kuma ya aure ni ba d amincewarta ba, indan sabon da tsanar uwar miji na saba sai dai bana jin cewar zan iya jure wannan idan har ya tabbata abunda nake zargi ne. 

  

“In-law Hajiya tace ki shigo”

Dagowa nai na kalleta idona da hawaye na girgiza mata kai. 

“A a zan tafi dai, ki ce ina gaishe da Ahmad din”

“Ba zata jidadi ba idan kika tafi ba ki shigo ba, bayan kuma ita da kanta ta bukaci haka”

“Ina tsoro kuma ina jin kunya”

“Akwai maganar da Hajiya take son fada miki dan Allah ki shigo ko kuma naje na kirata”

Na yi saurin dakatarta ita. 

“A a dan Allah”

“To muje”

A dole na bita a baya bayan na share hawayena, babu abunda zuciyata take raya min sai irin cin mutuncin da Hajiya zata min ko kuma gargadi, a lokacin ne naji ina ma ace ban zo ba, kamar wata marar gaskiya haka na shiga falon sai na tsaya daga bakin kofar na zauna jikin wata karanar kujera mai kamar ta kwalliya dake jikin kofar, ita kuma Siyama ta nufi dakin Hajiyar, ni kam gabana sai faduwa yake har yawun bakina daker nake hade su, ina jin motsin saukowar Hajiyar gabana ya kara faduwa. 

“Ahhhh Haba dai Siyama ya zaki barta a bakin kofa? Yanzu idan Yayan ki yana nan Wallahi kin san sai yace mun wulakanta masa mata”

“A a Hajiya ita ta zauna a can daker ma fa ta shigo cikin falon nan”

Siyamar ta fada tana rigan Hajiya zaunawa. Hakan yasa na dan dago kadan na kalli Hajiya tare da mika mata gaisuwa sai ta amsa min da murmushi. 

“Lafiya kalau taso dawo nan Yata”

Ta fada tana taba kujerar da take zaune wacce ta zaman mutum uku ce, ban iya musa mata ba na tashi na koma a inda ta bukata wato kusa da ita na zauna a kasa wata irin kunya na kara rufe ni, ai kam da kunya ace na so neman miji har gidansu!

  

“Kawo mata abinci da lemu Siyama”

Umarnin Hajiya Siyama ta bi a gabana ta jera min kula biyu wacce nake kyautata zaton tuwo da miya ne ko shinkafa da miya, sannan ta kawo min lemu da ruwa da kofuna ita da kanta ta bude lemun ta zuba min a kofi sannan ta koma ta zauna. Kunya ta hanani ko da kallon nemun balle na dauka na sha. 

“Hajiya zan tafi”

Na fada ina mikewa tsaye cike da kunya.

“A a ko abincin ba ki ci ba?”

“A a koshe nake”

“Ba Ahmad kika zo nema ba? Zauna mana”

Hakan da tace sai yasa kunya ta kara rufe ni. 

“A a daman… ”

“Zauna Yata ke ma kina da hakkin sani”

Cewar kina da hakkin sani yasa na koma na zauna cike da son jin ko minene. 

“Yata… Mijinki ba shi da lafiya Siyama ta fada min cewar yace miki ya tafi Abuja, be je ko’ina ba yana asibiti, yace miki haka ne saboda baya son a tashi hankalinki, ni da Siyama duk ya roki kar mu fada miki halin da yake ciki, sai dai na fada miki ne saboda ke matarsa ce kuma kina da hakkin sani, na san ya mace na da kunya da kawaici tun da har kika iya zuwa nan dan jin lafiyarsa aiko kin nuna mana kauna, ya kamata ke ma ki san halin da yake ciki”

Tun da ta fara maganar na ji zazzabi ya rufe ni, a razane na kalleta. 

“Hajiya me ya same shi? Dan Allah ku fada min”

Na juya gurin Siyama ina hawaye. 

“Rashin lafiya ce ki kwantar da hankalinki da sauki ai sosai, yanzu haka na gama shirin fitar da shi waje jibi zamu tafi”

A take jikina yai sanyi gaba daya sai na nemi kunyar da nake ji na rasa na kama kafafuwan Hajiyar na rike. 

“Dan Allah ku kai ni na gan shi, ina bukatar ganinsa dan Allah”

“Siyama tashi ki kaita”

Hajiya ta fada ita ma hawaye na sauko mata kamar yadda Siyamar ma take balle kuma ni da kuka ya zame min abinci. Da sauri Siyama ta tashi ta nufi dakin da nake kyautata zaton nata ne bata dade ba ta fito rike da dan mayafi da makullin mota, ni kam jiki na rawa na tashi na bi bayanta, kusan a tare muka shiga motar domin zuciyata sa ya soma raya min abubuwa marasa dadi. Wayarsa na soma kira wannan karon ma sai da tai ringing ta katse ba a daga ba. 

“Idan yana cikin azabar ciwon baya iya daukar kira”

Siyama ta fada tana tuka motar tana kallon sunan yayanta dake gaban wayata, ji nai kamar ba zan iya hakura ba sai na sake kiran na ci sa’a ya daga. 

“Hello Lims…”

Sai na kasa magana saboda bana son yaji kukana.

“Lims…. Lims…. Lims….”

Haka yai ta kirana amman na kasa amsawa daga karshe na kashe wayar gaba daya, sannan na kalli Siyama na ce. 

“Tun yaushe ne ba shi da lafiya”

“Wacan asabar din da ta wuce, yace ya ji abun yana driving be ma iya kawo kansa gida ba sai da ya kira driver ya tuka shi ya kawo shi gida saboda hannun da ke masa ciwo, yace mana be yi kwana ba saboda azabar ciwo kuma da aka je asibiti aka auna sai aka ce ba a ga komai ba”

“Mi yake damunsa?”

“Ciwon Hannuna ne, wani lokacin har cikin jikinsa yace yana jin abu, idan ya taso masa sai an daure ko kuma an masa allura sannan yake samun sauki”

“Hannun ya bugu da wani abu ne?”

“Mu dai be fada mana ba gaskiya, yace cikin dare ya soma jin abun”

A gurin da aka tanada dan aje motoci ta aje motarta muka fita kusan har na fita sauri ma duk da ban san inda yake ba har sai da ta shiga dakin da kanta ina binta a baya. A zaune muka same shi an daure hannunsa na dama da belt dayan hannunsa kuma rike da waya. Yana ganina ya watsawa Siyama wata muguwar harara wacce ta saka ta kasa karasa cikin dakin. 

“Zuwa kikayi kika dauko ta ko?”

“A a Wallahi ita ta zo…”

“Shut up…. Ban fada miki kar a fada mata ba? Ko ban fada miki tana da hawan jinin ba?”

“Yes amman….. ”

“Fita ki ba ni waje…. And if wani abu ya samu matata i swear sai kin yabawa aya zakinta”

Cikin tsawa sosai yake mata fadan ya ma kasa tsayawa ya saurareta, da sauri ta juya ta fice tana kuka. Nima da nake tsaye bakin kofar kuka nake ina kallonsa yayi wani irin mugun rama sosai kuma kana ganinsa kasan ba shi da wani kuzari.

“Kin gani ko? Saboda kukan nan yasa nace kar a fada miki yanzu sai ki tashi hankalinki….”

“Amman ina da hakkin sani, ni matarka ce, a iya tunanina babu wani boye boye a tsakaninmu, be kamata ka boye min wannan ba…. ”

Na fada cikin kuka, sai ya aje wayar ya miko min hannunsa na hagu, ni kuma na taka na karasa kusa da shi na kama hannun na rike. 

“Can you please hug your husband”

Na rumgume shi kamar yadda ya bukata ina fashewa da wani irin kuka mai taba zuciya. Da dayan hannun ya rika shafa bayana yana min magana a hankali kamar yadda ya saba. 

“Babe please kukan kin nan yana taba min zuciya, bana son wata damuwa ta same ki shiyasa na ce kar a fada miki”

“Daman na sani…. Shiyasa nake tsoron rabar mutane ko kuma mutane su rabe ni… Saboda wani…. ”

Ban karasa ba yasa hannunsa na hagu ya dago fuskata ya hade bakina da nashi, we spend more than 5 minutes muna abu daya kamin ya cire bakinsa ya hade goshinsa da nasa. 

“I miss you….”

Ya fada cikin rada.

“Daman can ina fama da ciwon kirji kuma kin sani, to shine yanzu ya sauko min har a hannu, so ki daina canfa kanki idan kina haka haka ne zai ta sakancewa da ke, Allah yasa dai baki fadawa Hajiya wannan maganar ba? Kar ki sa ta fara zargi ta tsorata ta dauka da gaske ne”

Na girgiza kai a hankali hawaye na sauko min. 

“Ban fada ba… Amman….”

“Amman…. ”

Yaja hancina sannan ya saka hannun ya share min shawaye. 

“Karki sake irin wannan maganar, tun before na aure ki nake jin wannan ciwon yafi min tsanani a yanzu kawai pls smile”

Ya fada yana jan kumatuna, all what i try to do is na tsayardar zubar hawayena. Tashi nai na zauna saman gadon kusa da shi, a yau kam ni nake masa irin kallon da yake min wani irin jinsa nake a raina gaba daya tausayinsa ya gama mamaye min zuciya. Kissing forehead dina yai sannan ya saka hannunsa na hagu ya kama hannuna ya rike gam. 

“Sarkin kuka i love you”

Kwantar da kaina nai kafadarsa ta hagu ina jin wani sabon kukan na son fito min. A hankali na fara jin yana motsi da na kalleshi sai na ga ya rufe ido yana cizon baki, a take hankali yai mugun tashi cikin sauri na mike tsaye ina tunanin abunda zan yi, dayan hannunsa yasa ya rike hannunsa na dama yana wani irin nishi yana ambaton Allah. 

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”

Shine abunda na furta ina fashewa da kuka, a yanayin yadda nake ganin fuskarsa da kuma yadda ya rike hannun ya isa ya sanar min da irin azabar da yake ji, wacce nake jin kamar ace akwai abunda zan iya a dauke masa ciwo gaba daya, da sauri na fito daga dakin da zimmar zuwa dakin da Doc Nura yake domin na san asibiti tun da ba yau na fara shigowa ba, a kujerar dake kusa da dakin na yi arba da Siyama zaune tana latsa wayarta tana ganina ta mike tsaye. 

“Ciwon ya tashi kenan?”

Ban ko kula ta ba na nufi hanyar da zata sadani da dakin likita ina kuka, kamin na karasa mutumen da ke gadin kofar office din ya tare ni. 

“Likita nake nema ciwon Ahmad ya tashi”

“Baya office dinsa tun dazun ya fita”

Juyawa nai da gudu na koma dakin sai na samu likitan da wasu likitoci biyu suna tsaye a kansa, Siyama kuma tana gefe tsaye tana kuka, belt din suka kwance suka sake saka masa wani sannan sukai masa allura. 

“Dan Allah ku je waje….. ”

Ni da ita muka fito daga dakin muka tsaya a waje, ita kuka ni hawaye.

“Ki yi hakuri zai samu lafiya in Allah ya yarda” 

Na fada ina dafata domin a yadda ita take kuka dole ne ni tasa ni na hade nawa kukan na zama jaruma na lallashe ta.

“Ina fatar hakan, baya son muna zuwa kusa da shi saboda kar mu ga halin da yake ciki, tsoro na ke ji ina jin kamar…. kamar…. Yaya mutuwa zai yi…..”

Na yi saurin rufe mata baki.

“Haba dai cuta ai ba mutuwa ba ce, zai samu sauki In-Sha-Allah”

A lokacin ne wani kukan ya zo min, tana da gaskiya ni da ita za mu iya rasa shi, saboda haka suka rasa yarsa, idan har ya kasance ni ce sila fa? What if ya kamu da wannan ciwon ne saboda ya aure ni? Ban raba dayan biyu ba Doc Nura ya fito daga dakin, ya nufo inda nake tsaye ni da Siyama yai mana maganar da zata kwantar mana da hankali cewar Ahmad zai samu sauki. Sai da ya wuce zuwa wani gurin sannan Siyama ta bude dakin ta shiga, ni kuma na bi bayan likita na cika kafa kamin ya shige na cin masa. 

“Doc dan Allah ina son magana da kai”

Juyowa yai ya kalleni. 

“Ina jin”

“Dan Allah miye abunda yake damun Ahmad?”

Shiru yai kamar mai nazari.

“Hajiya bata fada miki ba?”

“Ta fada min tace ba a san ko minene ba amman ina son kara ji daga bakinka”

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce.

“Gaskiya ne, an yi duk wani hoto daya kamata amman ba a ga komai ba, kuma shi yace yana jin ciwo yana masa yawo a hannun”

“Amman tun yaushe abun ya fara?”

“Yace min ranar assabar da dare, ya fito daga gurin abokinsa da dare, wai be iya kai kansa gida ba sai da ya kira direbansu ya kawo shi, na tambaye shi ko ya ci wani abu ne ko kuma hannun ya bugu da wani abu? Yace min a a yanzu jibi za a fita da shi, asibitin da za a kai shi tana da kyau tana daya daga cikin asibitoci masu kyau da iya aiki a duniya, ina sa ran ko minene za su gano In-Sha-Allah ki kwantar da hankalinki”

Na gyada masa kai sannan na juyo na fara tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa, babu komai a zuciyata sai tausayin Ahmad da kuma zargin kaina domin a wannan assabar din guri ya fito, ban san ko ya biya ta wani gurin ba, amman tabbas na san ranar ce abun ya same shi. Jinginawa nai jikin wani gini ina hawaye, wayata tai ringing da na duba sai na ga number Hafiza, share hawayen nai na dauki kiran. 

“Hello”

“Halima kina ina?”

“Dan Allah kina kusa da Mama?”

“Eh ita tace a kira ki ai ta duba bata gan ki ba”

“Bata wayar”

Ina jin sallamar ta a kunnena sai na fashe da kuka. 

“Mama na fita na zo nan asibiti Ahmad ba shi da lafiya”

“Subhanallahi miya same shi?”

“Hannun shi ke ciwo, kuma likitan yace ba a gano matsalar shi ba an yi hoto ba aga komai ba, Mama tun ranar assabar din daya bar gurin be sake lafiya ba har yau”

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, kina asibitin ne?”

“Eh Mama tsoro nake ji”

Na fada ina kuka domin har ga Allah tsoron nake ji.

“Ikon Allah abu kamar na iska? Ki kwantar da hankalinki za ku zo yanzu In-Sha-Allah”

“To”

Na kashe wayar ina share hawayena, sannan na nufi dakin da yake na tura na shiga, ban samu Siyama a dakin ba shi kadai na samu a zaune kamar dazun, a take hawaye suka fara wanke min fuska amman shi murmushi yake min wanda zai kwantar min da hankali, karasa nai kusa da shi na saka hananyena duka biyu na rika fuskarsa ina ta kallonsa har ga Allah ban tana jin son sa da tausayinsa a raina ba irin yau.

“Tun ranar da ka bar gurina baka sake lafiya ba, ba a gano dalilin ciwon nan naka ba, Ahmad ba zan daina zargin kaina ba, idan wannan ciwon be barka ba zan yafewa kaina ba, na dade ina jin tsoro bana son mutane suna samu matsala saboda ni, kuma ina ji a jikina cewar ni ce sila….”

“Shiiiiiiiiiiiiiiiiii”

Ya dora hannunsa saman bakina. 

“Ke baki dogara da Allah ba ne? Kin gani saboda gudun hakan yasa nace kar a fada miki, zaki saka damuwa a ranki har ciwonki ya taso, sannan za ki so ki fara magana marar kyau har ki sa a fara zargin wani abu, musamman ma Hajiya ta ko Siyama, dan Allah Lims ki bar wannan a matsayin sirrin mu, bana son wani yace zai ga laifinki ko ya tsane ki a yanzu, kina bukatar farinciki ko bana raye, and I’m sure idan ba ki samu a gurina ba Hajiya da Siyama za su ba ki, saboda sun san ina son matata sosai…”

Ya karasa yana sumbatar hannuna. Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, na rumgume shi ina jin kamar akwai abunda Ahmad ya boye min, har ga Allah ba zan daina zargin kaina a kan ciwon Ahmad ba domin a lokacin da be aure ni ba abun ba haka yake ba, why sai yanzu? Ko dai ni din ba alheri ba ce a gurin jama’a? Sanadina ya rasa yarsa, yanzu kuma ace ya zama mijina kuma ta kamu da ciwo?  Ina kokarin tsayar da kukana zancen Siyama da na Doc Nura ya fado min a rai, cewar a daren assabar din data gabata abun ya same shi and a wannan assabar din yana tare da ni ai kuma daga ita ne be dawo ba, hakan na nufin a ranar ne ya kasa kai kansa gida? Kuma a wannan ranar he hold my hand wata kila daga nan abun ya same shi.

 “Abu kamar na iska”

 Maganar Mama ta dawo min, no wait a daren ma ai ya gaisa da Abdallah, kuma Abdallah zai iya masa wani kofi, indai har ransa ya bace, i can remember ni ma ya taba min a lokacin da ya bukaci na shiga motarsa na ki sai an rasa mai napep din da zai dauke ni, and i lokacin da na auri Abdulhamid ma ya taba min na kasa girki, ya taba min wayata tsage ba tare da ta fadi ba, and yayi ma Abdulhamid ma, tabbas zai iya yi ma Ahmad inda har za a duba ace ba a ga komai ba tabbas Abdallah ne.

  Shine abunda zuciyata ta raya min kai tsaye, domin a wannan ranar Ahmad ya rike hannuna har gaban Abdallah kuma na san hakan ba dadi zai masa ba, secondly the way da ya ba Ahmad hannu su gaisa ba dan Allah bane, how Abdallah zai yi wani murna ya aure ni? Wanin ma wanda ya bukaci na daina aiki a kamfaninsa saboda baya son taraiya mu… 

Ban san lokacin da na mike tsaye da sauri ba hankalina yai mugun tashi.

“What…?”

“Ya kamata naje gida ba su san na zo nan ba gashi yamma ta yi”

Kallona yai from head to toe. 

“Ji veil din da kika fito da shi Lims, nasa doguwar riga ce amman ina bukatar ki rika rufe min jikina”

“Zan saka next time, zan dawo anjima kadan…”

Na fada ina nufar kofa da sauri sai ya kira ni. 

“Hey Lims are you okay?”

“I’m fine”

Na fada ina kokarin kwantar da hankali. 

“Okay come here and kiss me”

Dawowa nai na yi kissing dinsa sai ya rumgume ni da dayan hannun nasa. 

“I love you”

Ya rada min sannan na sake shi na mike tsaye na dauki purse dita na fice daga dakin. A phone list dina na shiga na nemo numbersa da ke kan gmail nawa na danna masa kira da sabon line na, ringing rai sai da ta kusa katsewa sannan ya daga da muryar da ke nuna be san mai magana.

“Abdallah kana ina?”

Yana jin muryarta ya gane ni ce mai magana. 

“Halima…..”

Yayi shiru sai kuma ya amsa. 

“Ina gida”

“Wane gidan?”

“Gurin Hajiya” 

Kashe wayar nai na nufi hanyar fita daga ward din ina ta sauri kar na hadu da su Mama. 

*Where are are the classy ladies 🤔  mata yan kwalissa ga awwaba scent tazo maku da hadadun turarukan wuta humra body oil turaren jiki na tsuguno da kayan gyaran jiki kaman dilka scrub organic soap 🧼  da sauransu akan farashi daidai aljihu say no karnin da warin damshi na lokacin damina zaaiya samunmu a wannan lqmbobin 09137294470 08034236800*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

GOBE NA 43

Advertisement GOBE NA…* By Khadeeja Candy  4️⃣3️⃣ ABDALLAH POV.  Advertisements He’s walking slowly tun daga inda ya aje…