HAYATUL MAHAYAT 23-24

Advertisement

 

🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸

         πŸ¦šπŸ¦šπŸ¦šπŸ¦š

               πŸ¦šπŸ¦š

                 πŸ¦š

_Story and written_

            “`By“`

*NPEEDY A AJI* 

_Dedicated to_

Advertisements

*My yar amana*

“`My Novels 

1-NAYI RAYUWA DAKE

2-SANADIN ACCIDENT

    2019

3-SAKAYYAR CUTA 

4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA

 HAYATUL MAHAYAT

Advertisements

         typing……✍🏻“`

 *_____________________________________*

 *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER’S✍🏼*

*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

πŸ…Ώ 23 & 24

Muzaffar bakinshi d’auke da sallama sukashiga cikin parlour ganin babu kowa a parlour yasashi  nufar cikin bedroom d’in yana shiga yahango maimartaba kwance gawata irin muguwar rama dayayi ganin numfashin shi bayako sauka yadda yakamata saurin sauke Shureem yayi yanufi bakin bed d’in cikin gigita 

” innalinlahi wa’inna ilaihirrazu’uuuu Dad ya Allah da mai yasaka cikin irin mawuyacin halin ? amma akabarka anan kamar ba Sarkin masarautar HAYAT ba ?

Wani irin kuka yaji ya’kwace mishi cikin fad’a yajuya yace 

” tabbas kun cutar dani aduk lokacin danace ina dad cemin kukeyi yana lafiya danayi ‘korafin idan nakira wayar shi bata shiga kai yaya Ahmad kaine kacemin yadena amfani da sim d’in dukda nayi mamaki amma senadena sabida nasan yayana bai ta’bayimin ‘karyaba haba sekace ba mahaifina ba “

Cikin raunin murya yaya Abubakar yace 

” kayi ha’kuri muzaffar maimartaba ne yace kar a sanar da kai amma muba laifinmu bane kuma wannan ciwon nashi bana asibiti bane ayanzu haka su kawu Yusuf sunanan  shigowa da wani malamin dazaiyimai addu’a koza’a dace dukda cewa ankira malamai dayawa amma har yanzu babu wata nasara “

Cikin matu’kar damuwa muzaffar yajuya kan maimartaba hannun shi yakamo yasaka cikin nashi hawaye nasauka saman kuncin shi ahankali maimartaba yake bud’e idanun shi zubasu yayi kan muzaffar amma yakasa koda d’aga lab’ban shi balle yace wani abu

Dedenan su kawu Yusuf da waziri sukayi sallama suka shigo tareda Malam wato boka ganin muzaffar kamar daga sama yasasu matu’kar razana cikin ‘kasada murya waziri yacema kawu Yusuf 

” shikuma wannan yaushe yadawo ? lalle idanfa akayi wasa zai’bata mana shiri “

Jinjina kai kawu Yusuf yayi yace 

” barshi nasan yadda zanyi “

Aje wani ‘ko’ko boka yayi sannan yayima kawu Yusuf magana cikin wata irin murya mai nuna matu’kar tausayawa kawu Yusuf yace 

” Malam yace kowa yafita zaiyi ayki ba’a bu’katar kowa cikin bedroom d’in kukoma parlour “

Mi’kewa sukafarayi  cikin izza muzaffar yace 

” kamar yayafa wane irin maganine daharse kowa yafita ina tunanin addu’a yazoyi sekuma kowa turare ko ? to wallahi babu inda kowa zashi sede idan yafasayin aykin “

Cikin fad’a kawu Yusuf yace ” kai muzaffar bafazaka hana Malam aykinshiba kasan da yadda nasamu yazo ne ? shine kakeso ka’bata komi ? to dole kowa yafita kamar yadda Malam yace kuma hadda kai “

Jinjina kai muzaffar yayi yace ” bafa kowa zai fitaba kawu kakalli kowa dake gurinnan daga matanshi se yaran shi se kuma ku tay…….. “

Cikin hassala kaka tace ” lalle muzaffar kayi mugun renani wato kana nufin baka gannibane ? dabazakace da mahaifiyar shiba tode  daban haifeshiba dabakuzo duniyar ba kud’in “

Fuska tamke muzaffar yace ” ay banga shigowar ki bane kaka ” jin haka yasa kaka jinjina kai sannan tace ” nimafa Yusuf bangoyi bayan mufitaba idan har  malamin gaskiya ne to yayi aykin shi agaban kowa tunda shideba likita bane kuma ayko likita yana zuwa duba marassa lafiya tareda wasu  daga cikin ma’aykatan shi dan haka kai Malam maza kafara ayki “

Wani irin ba’kin ciki su kawu Yusuf sukaji shiko boka tuni yafarayin nadamar zuwan shi cikin tashin hankali Rayhana tace 

” innalillahi ina yarana ? “

Jin haka yasa muzaffar saurin juyowa kafin yace komi yaji kukansu cikin ‘kar’kashin bed d’in maimartaba saurin du’kawa yayi hannu yami’ka  Shureem yafito dashi sannan yami’kama  Sudees ‘kin mi’ko hannun shi yayi dole muzaffar yadu’ka sosai yajawo shi cikin mamaki kowa yake kallon Sudees hannun shi rungume da wata farar ‘kwalba wadda aka cikatada kayan surkulle cikin ta 

Cikin razana boka yarad’ama kawu Yusuf magana kai wannafa itace kwalbar sihirin gata hannun yaron nan kayi gaggawar amsar ta tun kafin mushiga cikin masifa dan wallahi idan najiwuya gaskiya zan fad’i “

Cikin sauri kawu Yusuf yanufi gurin muzaffar hannu yasa zai amshi kwalbar yana nuna tsananin mamaki cikin sauri muzaffar ya amshi kwalbar daga hannun Sudees cikin nuna matu’kar ‘bacin rai kawu yabud’e baki zaiyi magana kamar daga sama  sukaji muryar maimartaba yana salati had’ida yin mi’ka 

Juyawa kowa yayi yana kallon ikon Allah tashi maimartaba yayi zaune fuskarshi d’auke da murmushi kallon ‘kwalbar hannun shi muzaffar yayi cikin fushi da fusata yace 

” nagane wato wannan kwalbar itace sanadin wannan masifar gud my Twins daga shigowar ku harkun fara warwaremin wani ‘kulli tabbas zaku nunamin munafukai da ma’kiyan cikin masarautar HAYAT “

Murmushi maimartaba yayi dukda jikin shi babu ‘karfi wata 5 akwance wasane cikin sanyin murya yace

” tabbas naga alamar alkairi taredasu Allah yasa Twins d’in jikokinane akagani Farooq da Haidar mi’komin su Muzaffar “

Mi’ka mishi Sudees yayi sannan ya’amshi Shureem yami’ka mishi cikin farin ciki kaka tace 

” tabbas sunzoda alkairi dan haka na amince dazaman mahaifiyar su yaredasu “

Tashi Momy tayi takoma bakin bed d’in d’aukar Shureem tayi tarungume tanajin wani irin farinciki marar misali kawu Yusuf da waziri wata irin zufa sukaji tana keto musu shiko boka jiyakeyi kamar yazura aguje cikin nuna farinciki kawu Idris yace 

” Alhamdulillah gaskiya wa’innan yaran kun ceci min yayana badan kuba haka zaitafama daciwo dan babu wanda zaiyi zaton akwai wannan kwalbar sihirin ‘kasan gadon maimartaba Allah mungode maka “

Ya’ke kawu Yusuf yayi yace ” masha Allah ” shika’de ya’iya fad’i itako Ummi bataji dad’in warkewar maimartaba ba sabida harta hangi uwar dukiyar dazatasamu idan yamutu su yaya Ahmad kuwa farinciki da murna baya misaltuwa ‘ko’karin bud’e ‘kwalbar Muzaffar yashigayi cikin sauri maimartaba yace 

” a’a Muzaffar bakai yakamata kabud’e wannan ‘kwalbar ba sabida bud’e Sihiri se malamai dan haka kabama wannan malamin dayazo dan yimi magani yabude tunda shi malami ne yasan addu’o’in dazaiyi kafin yabud’e “

Jinjina kai Muzaffar yayi shiko boka tuni yaji wani irin murd’awar ciki yasan idan har yabu’de to tabbas zaigamu damasifa cikin in ina da daburcewa yace 

” maimartaba ay kunsan malamanma kalakalane nide banida sani akan addu’o’in bud’e sihiri musamman irin wannan mugun sihirin gaskiya sede anemi wani “

 Cikin sauri kawu Yusuf yace ” to ay babu damuwa semu nemi wani kawai kunsan shi ilimi kogine ? ta’inda wani yasha batanan wani yashaba muje kawai malam nasallameka ” dasauri Muzaffar yace 

” haba malam ay dole seka bud’e wannan sihirin kasan kai bakacika malamiba kazoyima mahaifina magani gaskiya ni banma yarda dakaiba dan haka kabud’e wannan kwalbar sihirin sannan mubaka damar tafiya idan kuma baka bud’eba to wallahi rufeka zanyi nayi bincike akanka amshi maza bud’e mug………”

Afad’ace kawu Yusuf yace ” lalle muzaffar wato kaiga fitsararre kowa baiyi maganaba se kai dukga yayyanka basuce a’a ba se kai tunda yace bai iyaba ay bai zamadole seya iyaba dan hak……….. “

Dakatar dashi kaka tayi dafad’in ” ay abinda muzaffar yace yayi dede dan haka dole yabud’e idan har ba munafiki bane ” wani irin fitsari boka yaji yafara zubomai shiko kawu Yusuf wani irin bugu zuciyar shi keyi waziri kuwa sharar zufa kawai yakeyi cikin azama boka yajuya yafita aguje cikin sauri mu’azzam da muzalbil da yaya Abubakar sukabi bayan shi shima Muzaffar juyawa yayi zaibi bayansu Momy tace ” dagata Muzaffar barsu sukamoshi  yana fita ‘kofar parlour dogarawan dake tsaran gurin sukayi saurin ri’keshi sha’ko wuyan shi muzalbil yayi yafara dukanshi cikin sauri Sarkin gida yarugo yace 

” Allah ya taimakeka Yarima kabada izinin dukan shi karka wahalar da kanka  ” afusace muzalbil yace ” kai Sarkin gida wannan huruminmu ne banakuba dan haka dakanmu mukeson nayimai mugun duka ” cigaba da jibgarshi sukayi idan wannan yaduka wannan yajibga aguje kawu Yusuf da waziri suka fito nufar wajan sukayi sunayi musu tsawa ki’ro hannun mu’azzam kawu Yusuf yayi wani irin naushi muzalbil yasaukema kawu Yusuf abaki wanda  yasa ha’korin shi fita lokaci d’aya hantsilawa yayi yafad’i yana waiyo Allah cikin sauri muzalbil yayi kanshi yana fad’in ya Allah dan Allah kawu kayi ha’kuri nazata wannan malamin ‘karyarnne nakawoma naushi “

Kasa magana kawu Yusuf yayi kamashi mu’azzam yayi yanufi parlour shi dashi dan bashi gajin gaggawa sedasu muzalbil sukaga boka yayi lilis sannan suka rabu dashi sawa sukayi aka kulleshi awaje mafi tsaro tsayin lokaci suna cikin parlour maimartaba suna cigaba dayin farincikin samun lafiyar shi fitowa maimartaba yayi parlour bayan yayi wanka yashirya tsaf bayajin komi ajikin shi se rashin kuzari zama maimartaba yayi cikin soyayya ya kalli su Sudees yace 

” har sunyi bacci kenan ? masha Allah addu’a ” maimartaba yayi sannan yafarayin jawabi Alhamdulillah a yau  ina matu’kar farinciki da Allah yakawo ‘karshen wannan kalular tawa wanda jikokina suka zama silar warkewata kai Muzaffar mahaifiyar ka tasanar dani komi akan wannan matar taka dakuma yaranka Alhamdulillah nayi matu’kar farinciki haka kuma inayi muku fatan alkairi a cikin zamanku 

Kowa yasheda nayima wa’innan jikokin nawa kyautar wannan babban gidan nawa dake  wajan masarautar HAYAT da kimanin kud’i nera million 20 kowa 10 million sannan kowa yasheda bazanyi sassauci ba gaduk wanda yayi ‘ko’karin cutar dasu dan haka kowa yakiyaye inaso ashirya walimar dawowar muzaffar dazuwan matar shi dakuma babban farinciki wato samun Sudees da Shureem kowa yasan irin yadda akeyin bikin murna vaduk wacce tahaihu to su Shureem basusamu hakanba sabida basa taredamu dan haka yanzu za’ayi musu shgalin murnar zuwansu duniya harna tsayin sati 2 inaso acibada datsare wannan malamin har zuwa bayan kammala wannan bikin murnar da’alama yanada masaniyar wani abu gameda wannan kwalbar sihirin sabida naji yana fad’in zaifad’i komi kowa yatashi yaje ya kwanta “

Mi’kewa kowa yayi amma wasu cikin rashin kuzari suka mi’ke  bayan fitar kowa kilishi kawai akabari cikin part d’in sabida itakeda girki tashi tayi tanufi kan cushion d’in da maimartaba yake zaune zama tayi cikin farin ciki tace 

” Nayima Allah godiya dabaka lafiya maimartaba Allah ya’kara tona asirin ma’kiyanka “

Ameen maimartaba yace hira sukacigaba dayi irinta mata da miji kallon Zarah Muzaffar yayi yace 

” waike mai kikeyi ne har yanzu cikin gidan nan baki tafi gidan mijin kiba ? “

Tuni zuciyar Zarah takarye cikin damuwa tace ” yaya tun bayan tafiyarka da kwanaki 3 Aliyu yasakeni k……. ” dakatar da’ita yayi dafad’in ” saki shi Aliyu ? lalle yayi kuskure jeki kwanta zuwa safe zamuyi magana “

Rai’bace Muzaffar yawuce itako Rayhana binshi kawai takeyi ga yaro saman kafad’ar yayi bacci part d’in shi suka nufa har cikin bedroom d’in shi yashiga da Sudees kwantar dashi yayi saman bed d’in shi waigowa yayi ganin babu Rayhana yasashi nufar hanyar parlour rai ‘bace kiranta yayi bayan tashigo ya amshi Shureem ya kwantar dashi saman bed jawota yayi da’karfin tsiya tafad’o jikin shi saurin janye jikin shi yayi daga nata kunnanta yakama yamatseshi  da’karfi yace 

” kinwani tsaya daga parlour bana gaya miki anan zaki d’inga kwanaba ? tun daga yau kinaso kinunamin bakyajin magana ko ? to wallahi kibini ahankali kawai kayan baccin Nabila cikin wardrobe d’ina ga toilet cen kije kiyi wanka kibud’e kid’auki d’aya daga ciki kisa idan kinsa ki kwanta kusada Sudees sune zasu zama mana katanga tsakanina dake da nayi ‘kud’in a’kasa zaki dinga kwanciya amma darajar yaranki yasa najanye haka dan sun taimakeni sunzama silar warkewar dad “

Juyawa yayi yafita parlour System d’in shi yad’akko yabud’e komawa yayi cikin bedroom d’in yazauna saman sofa 

Cikin sanyin jiki take d’aga kayan duk babu wadda zata iya sawa sabida duk masu bayyana surar jikine da’kyar tasamu wata doguwa mai kauri amma tanada tsagu daga ‘kasa zuwa ‘kugu shiga tayi da’ita cikin toilet d’in shiko bai masan tanayiba dan gaba d’aya hankalin shi yana kan system 

Tsayin lokaci sannan Rayhana tafito hannu tasa ta’ri’ke wajan tsagun nufar wajan bed tayi cikin tsaurin murya yace ” zonan ” fad’uwar gaba taji sosai amma kuma yaya zatayi dole tanufo inda yake kallon ta yayi yahad’a rai yace 

” wai mai kike rufewa lalle yarinya nikam mai zangani ajikinki kina ‘kwala to dama kindena boye  wannan jikin naki dako kallo bai isheniba balle ta’bashi fita parlour zakiyi inaso nashiga wanka sabida bakiyi girmanda zaki’iya kallon koda sumar ‘kafataba kuma duk ranar dakika sake kikaga koda kafad’atace to wallahi senayi miki  hukunci a wannan ranar fita “

Sosai Rayhana taji zafin wannan kalaman nashi dan har seda sukasata ‘kwalla shiko ko’ajikin shima har seda bacci yafara d’aukar Rayhana sannan Muzaffar yafito afurgice tatashi zaune sabida jin kiran tadayi asaman kanta gaba yatasata suka shiga cikin bedroom d’in hawa yayi saman bed yakwanta had’ida rungumo Shureem yaja blanket sabida akwai sanyi sanyi ga tafkatafkan windows d’inshi abud’e masu ‘bakin glass daga amma daga ciki farine ana iya hango komi daga ciki amma daga waje ba’a iya ganin kowa zuwa tayi taja labulayen jikin windows d’in sabida itakam tsoro takeji idan tahangi wajan a cikin daran nan dukda cewa akwai hadahadar mutane musamman dogarawa da Security cikin tsawa yace mata ” maza kimayar dashi yadda yake kizo ki kwanta ke nifa banason takura da damuwafa dan haka bibini ahankali kinji nagaya miki “

Jiki a sanyaye tamayar dashi yadda yake sannan taje tahau ssaman bed d’in rungume Sudees tayi tarumtse idanunta kamar maiyin bacci amma takayin hakan sabida cikin matu’kar tsoro take 

Washe gari tun misalin 7 aka gama shirya komi ko’ina kabi cikin masarautar HAYAT abin shi’awa sabida an ‘kawata gurin da ‘kyalekyale da abubuwan  ban shi’awa cikin sauri abokin Aliyu yashiga cikin parlour shi cikin sa’a kuwa yasame shi azaune zama yayi ko gaisawa basuyiba yace 

” Yarima nazoma dawani mihimmin labari yau anayi wata gagarumar walima cikin masarautar HAYAT nasan kowa yana cikin farinciki babu wani ‘bacin rai kaga kasamu hanyar ganin Zarah cikin sau’ki sekace gayyatarka akayi tunda masarauta ce basedole anji waye yagayyacekaba “

Mi’kewa Aliyu yayi yana jinjina kai murmushi yasaki yace 

” tabbas nasamu dama abokina lalle kakawomin gud news kaje kashirya tare zamu bari nashiga wanka  “

Mi’kewa yayi cikin zuciyar shi yana fad’in ” yau senaji d’umin jikinki  da laushin jikinki danayi mugun kewarshi tsayin watanni “

To Aliyu barimugani ko hakan zai yiwu 

Cikin tashin hankali waziri yace ” Allah yabaka nasara sarkin gobe  munacikin tashin hankali fa wallahi idan boka yafad’i gaskiya tofa kashinmu yabushe dan natabbatar kashemu za’ayi “

Mi’kewa kawu Yusuf yayi cikin rashin sonyin  magana sabida kumburin dabakin shi yayi ga’azabar ciwo yace 

” ay se idan yana raye sannan zaifad’a ko ? Waziri kasan duk yadda zakayi akashe boka cikin wannan shgalin nasan hankalin kowa zai d’auku  wajan hidimar babu wanda zai ankara “

Jinjina kai waziri yayi alamar gamsuwa 

Cikin damuwa Ummi tace ” tur’kashi gawani saban  aykin kuma gagarumi ” 

A’bangaran Aunty Sumayya kuwa cikin fad’a tace 

” kwantar da hankalin ki Islam inde Muzaffar ne sekin aure itakuma waccen shegiyar Rayhana senasan yadda nayi tabar cikin masarautar nan tareda samun mugun wula’kanci daga  Muzaffar “

Tofa Rikici kenan 

Daga Al’kalamin…..πŸ–Š

NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸

Comments and shire please

Leave your vote

-2 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like