Advertisement
πΈ *HAYATUL MAHAYAT* πΈ
π¦π¦π¦π¦
π¦π¦
π¦
_Story and written_
“`By“`
*NPEEDY A AJI*
_Dedicated to_
Advertisements
*My yar amana*
“`My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA
5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA
HAYATUL MAHAYAT
Advertisements
typing……βπ»“`
*_____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER’SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
π Ώ 27 & 28
Cikin zafin rai da mugun ‘bacin rai Arfar tajuya afusace tabar cikin bedroom d’in jiki a sanyaye Muzaffar yatashi zaune itako Rayhana rawa kawai jikinta keyi sabida jin ‘ba’kon yanayi cikin jikin ta sakkowa tayi tanufi hanyar fita jitayi yace
” ina yaran ? ” murya a sanyaye tace ” suna gurin momy ” idasa fita tayi komawa yayi yakwanta ahankali yake furta
” Senayi maganin waccan yarinyar tajamin yima yarinya ‘karama abinda bai kamataba salan tajamin raini Allah sarki Nabila kinbarni gashi rashinki yana neman illata rayuwata “
Mi’kewa yayi yanufi toilet ranshi a’bace cikin zuciyar shi yace ” yarinya ‘karama tajamin yin wanka lalle Arfat sena baki mamaki sabida duk ke kika jamin ” itako Arfat tana fita tasaki kuka sosai tana shafa cikinta d’ayan bedroom d’in Rayhana tashiga toilet tanufa dan watsa ruwa sabida jikinta rawa kawai yakeyi bayan tafito tagoge jikin ta bakin mirror tanufa tashafa maya mayan dake gurin hadda turaruka bakin wardrobe ta’isa sosai tarazana daganin irin kayan dake ciki masu kyau da tsada komawa bakin bed tayi tazauna
Magana taji wannan aljanar tafarayimata ” barkanki dashigowa cikin masarautar HAYAT Raihan ayau naga irin wula’kancin da Muzaffar yayi miki banji dad’in hakanba amma karki damu komi zai wuce kitashi ki d’auki wasu daga cikin kayan nan kisa su zasu zamar miki kariya daga mugun wula’kancin Muzaffar dukda bazai bar wula’kan takiba sabida yatsani mace ayanzu amma zakisamu sassauci sosai sannan sekinyi taka tsantsan dakowa cikin masarautar nan kinga wadda tashigo yanzu wato Arfat tanada yun’kurin cutar dake dan haka ki kiyaye da duk wani motsinta
Bazan iya hana ‘kaddarar Allah yin ayki akankiba amma zanyi iya ‘ko’karina wajan kareki kid’auki wannan box d’in amma kicire ring d’in dake ciki ki aje agurinki kikai box d’in cikin wancan part d’in nagefan hakunki idan kin fita cikin bedroom na ‘karshe ki’aje saman bed kifito karki bari kowa yaganki mahaifiyar ki tana lafiya sannan mahaifin ki sunanan suna neman ki sunason gano inda kike da’alamu kuma zasuyi nasara anan gaba ‘kadan amma kafin lokacin zamusan abinyi nabarki lafiya “
‘Dan jim Rayhana tayi kallon hotunan dake jikin bangon d’akin tashigayi cikin sanyin murya tace ” tabbas nanne bedroom d’in Nabila gaskiya nayarda babu wacce Muzaffar zaiso kamar Nabila duba da irin yadda sukayi hotuna ko wanne yanayi kamar zai had’iyeta ji wancan yadda yasumbaci kuncinta ko kunya ” cikin sauri takoma bakin wardrobe d’in wata Arabia gowt taciro mai masifar kyau tasaka simple makeup tayi tafesa turaruka kama kashinta tayi zuwa baya tayi rolin d’in d’ankwalin woow ni kaina nayaba Raihan πππ» fita tayi jiki asanyaye
Cikin sauri Muzaffar yayi saukin waigowa sabida jin kamshin turaran Nabila saurin tashi yayi dayaga Rayhana ce ganin kayan jikinta yasa shi wani irin jan numfashi ‘karasowa yayi gurin ta rai ‘bace yace
” wayabaki izinin shiga cikin bedroom d’in Nabila har kisa kayan ta dama turaran ta ? ” hannu yasa zai jawota muryar Momy tasa yayi saurin sauke hannun shi
” haba Muzaffar ay hakan shine dede nasan kai kanka zakasamu sau’kin kewarta Raihan da nasa ayimiki Oder kaya sabida naga bakizo danakiba amma yanzu zansa abarshi senan dawani lokaci kiyi amfani dana yar uwarki kinji Nabila batada matsala kema naga kamar hakane Raihan zanso kizama kamar ita ke wane mataki kike akaratu sabida nasande ke baki ‘karasaba dubada yarintarki bakikai shekarun Nabila ba “
Murmushi mai ciwo Rayhana tayi murya asanyaye tace ” Momy matakin Secondary kawai gareni nafarayin tagaba da Secondary amma ko 100 level ban ‘karasaba akasamu matsala ”
Jin jina kai Momy tayi tace ” karki damu zakicigaba anan in sha Allah ” mi’kamata yaro tayi tace ” amshi wannan rigimamman shikama yafi d’an uwanshi rigima ya’ki zama gashi nakasa gane waye Sudees ne ko Shureem ? “
Murmushi Rayhana tayi tace ” Shureem ne shi’ay ‘kiwa gareshi shima Sudees idan yaga ba Shureem d’in kuka zaiyi ” d’an ri’ke kunnanshi Momy tayi tace ” ayko sekaitayin ‘kiwarka kanagani zantayin auran da Sudees amma banda kai barima kaga nakoma wajan Sudees karyatashi yayi kuka ” murmushi suka saki suduka hadda Muzaffar fita Momy tayi
Sake tamke fuska muzaffar yayi tamkar bashine yayi murmushi yanzuba zama Rayhana tayi tanayima Shureem wasa ta’ki yarda suhad’a ido da Muzaffar farinciki takeji cikin zuciyar ta na albishir d’in da Momy tayimata akan karatu sabida tana masifar son tayi karatu du’kowa Muzaffar yayi ya amshi Shureem sosai kamshin turaran yasake bugar hancin shi wanda yasa har seda yalumshe idanun shi saurin zama yayi kan cushion d’in gefan Rayhana yanajin wani irin yanayi
Kwantar da Shureem yayi saman ‘kirjinshi ya kwantar da kanshi saman hannun cushion d’in tsayin lokaci yad’ago kanshi fuska a tamke yace
” ke jeki had’amin Lipton ki matsa lemon tsami aciki guda 4 ” tashi Rayhana tayi cikin zuciyar ta tace ” har guda 4 to wane dad’i zaiji ahaka bin bayanta yayi da kallo ganin yayi takoma mai tamkar Nabila
Samha tana farkawa muzalbil yayi saurin zama kusada ita hannuwanta yakamo duka 2 yace ” yaya jikin ” Aunty Sumayya zatayi miki wasu tambayoyi akan kwayoyin dakike sha karki sanar da ita komi idan tasan maganar cikin nan asirinmu yatonu kinji “
A matu’kar mamaki take kallon shi cikin ‘karfin zuciyar tace ” gaskiya Yarima nagaji kar’in hallaka kaina gara kowa yasani se’a nemarmin mafita kaji tsoran Allah kasanar dani wanna cikin kanada ala’ka dashi ko a’a idan nakane semusan abinyi idan bakason shine idan kuma banaka bane se anemi mafita mai yasa kake zuwamin bayan kabani abinda zai gusar da hankalina ? haba Yarima duk rashin son dakake yiminne yajawo haka ? dan …….. “
shigowar Aunty Sumayya yasata yin shiru sosai takeyimata fad’a kuka Samha takeyi amma takasacewa komi har Aunty Sumayya tagama fad’anta tabar part d’in mi’kewa Samha tayi wani irin kallo tayima muzalbil tashiga cikin bedroom d’in ta zama yayi yadafe kanshi yana nazarin yadda akayi Samha tasan yana zuwamata
Hankali tashe kawu Yusuf yake kai komo cikin parlour shi yamarasa yadda zaiyi dan duk wani tunanin shi yatsaya matar shi tashiga tambayar shi lafiya amma yayi mata banza ta’be baki tayi tabar mai parlour
Jin kukan Zarah yasa kaka shiga cikin bedroom d’in zuciyar ta cike damatu’kar fargaba zama tayi tajawota jikinta lallashin ta tashigayi dankam ayanzu mugun tausayin Zarah takeji sabida tasan duk itace silar shigarta cikin wannan damuwar
Sedataga tayi shiru sannan tashiga tambayar ta abinda yasata kuka amma Zarah ta’ki sanar da ita dole kaka taha’kura mu’azzam zaune kan cushion duk tunanin duniya yagama isarshi dede lokacin Arfat tashigo hanyar bedroom d’in ta tanufa kiranta yayi yatsina fuska tayi sannan taje kusadashi tazauna seda yayi d’an jim sannan yace
” Arfat gaskiya zan ‘kara aure sabida bazan iya rayuwa babu mace ba har yanzu zuciya ta takasa natsuwa nakasa yarda cewa Muzaffar zai aykata hakan wannan cikin najikinki yana tada hankalina amma banta’ba jin cewa shid’in na Muzaffar bane Arfat ke kike da amsar duk wata tambaya tawa amma kinkasa cireni adamuwa to zan barki kiyi duk yadda kikeso tabbas aure zanyi babu fashi ke kuma idan kin haihu seayi gwajin jini na babyn dana Muzaffar anan ne zangane gaskiyar komi “
Yana kaiwa nan yami’ke afusace yabar part d’in duka dafe ‘kirjinta Arfat tayi tace ” nashiga uku kadafa nayi bawan bawan narasa mu’azzam kuma bansamu Muzaffar ba yaya zanyi kenan idan nafad’i gaskiya wata matsalar ce idan kuma na’ki fad’i shima matsalar ce yaya zanyi kenan ? “
bayan Muzaffar yagama shan Lipton d’in yakoma cikin bedroom d’in shi kasa zama yayi afili yace ” haba Momy tayaya zakibama wannan yarinyar damar amfani dakayan my Nabila hakan cikin wani hali zaisani ina ganin tamkar Nabila ce sha’kar kamshin turaran ta kawai yasanaji matsananciyar bu’kata gaskiya bazai yiyuba ” sallamar Rayhana tasa Muzaffar saurin zama kan bed tsugunnawa tayi kusadashi cikin sanyin murya tace
” kayimin izini zanje part d’in Momy ? ” d’aga mata kai yayi alamar taje dan gaf yake dayakasa jurar wannan kamshin turaran itako kanta yana ‘kasa bataga alamar dayayi mataba wata irin tsawa yadaka mata ” nace kije ko dallah tashi kifita daga cikin bedroom d’in nan ” cikin sauri Rayhana tami’ke tabar bedroom d’in tashi yayi tsaye yakaima d’ayan hannun shi naushi yanufi toilet
Kuyi ha’kuri da wannan babu yawa nayau ππ»
Daga Al’kalamin….π
NPEEDY A AJI πΈπ¦πΈ
Comments and shire please
GIPHY App Key not set. Please check settings