Advertisement
πΈ *HAYATUL MAHAYAT* πΈ
π¦π¦π¦π¦
π¦π¦
π¦
_Story and written_
“`By“`
*NPEEDY A AJI*
_Dedicated to_
Advertisements
*My yar amana*
“`My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA
5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA
HAYATUL MAHAYAT
Advertisements
typing……βπ»“`
*_____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER’SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
π Ώ 29 & 30
Rayhana tana fitowa daga cikin bedroom d’inshi tasaki wani irin kuka mai tsuma zuciya sosai takeyin nadamar shigowarta cikin wannan masarautar jin kukan Shureem yasata saurin share hawayen idanunta d’aukarshi tayi tasake komawa cikin bedroom Muzaffar tana shiga tausake ajiyar zuciya sabida jin ‘karar ruwa cikin toilet dasauri tadu’ka ‘kasan bed d’in wannan box d’in tad’akko saurin d’aukar Shureem tayi dede lokacin Muzaffar yafito daga toilet tamke fuska yayi sosai yace
” mai kika du’kayi a ‘kasan bed d’ina ? ” wata irin faduwar gaba Rayhana taji cikin d’an in’ina tace ” abin wasan Shureem ne yafad’a tun d’azu gashi yanzu se kuka yakeyi shine nazo d’aukar mishi ”
Nuna mata hanyar waje yayi batare daya ce komiba cikin sauri tafita tana sauke ajiyar Zuciya cikin bedroom d’in Nabila tashiga ‘boye wannan box d’in tayi sannan tafito part d’in Momy tanufa tana shiga Zahra tayi saurin mi’kewa fuskarta d’auke da Murmushi tami’ka hannu zata amshi Shureem saurin kwantar da kanshi yayi saman ‘kirjin Rayhana alamar bazaizoba
Tsawa Aunty Sumayya tadakama Zarah ” ke Zarah maiye haka kika wani mi’ke cikin zumud’i sekace kinga ‘kanwar uwarki wannan dakike gani mai kamada aljanar muguwar munafukace kina gani zata rabaki da d’an uwanki amma kike wani shige mata shasha kawai k…… ”
” ke Sumayya maiye haka? ” cewar Momy data fito yanzu daga cikin bedroom maiyasa ke har abada bazakiji magana ba to wallahi idan bakifita hanyar iyalin Muzaffar ba senayi mugun sa’ba miki haka kika addabi Nabila gashima tabar miki duniyar amma kinkasa saduda shine zakikoma kan Raihan ko to gaskiya ina zaton baki ‘kaunar Muzaffar duk cikin ‘yan uwanki shi kika sama ido h….. ”
” Haba Momy tayaya zan’kin d’an uwana nibana’kin Muzaffar sede ina mugun jin haushin irin za’banshi yarasa matan dazai dinga kwasowa se mararsa aji Momy kalli wannan yarinyar fa? Yar ficiciya da ita wai itace matar Muzaffar tur abin kun…… ”
” !!!!!!! Sumayya tashi kifita daga cikin part d’in nan ko ranki ya’baci ”
Rai ‘bace Aunty Sumayya tafita kamo hannun Rayhana Momy tayi kan cushion tazaunar da ita itama tazauna lallashin ta tashigayi sosai hankalin Rayhana ya kwanta ko babu komi Momy tanuna mata soyayyya
A’bangaran Aliyu kuwa suna isa gida ko gamayin parking ba’ayiba yabud’e marfin motar yafito afusace kai tsaye party d’in Ummi yanufa zaune yasameta hannnunta ri’ke da Cup tanashan madara ganin yanayin shi yasata aje cup din tafuskanceshi sosai tace ” lafiyar ka kuwa Aliyu waye yata’bamin kai haba gadanga tell me your problem my big Son ” shiru Aliyu yayi babu alamar ma zaiyi magana tashi Ummi tayi daga kan cushion d’in datake takoma kusada Aliyu fuskar ta d’auke da damuwa hannuwan shi takamo cikin muryar lallashi tasake cewa
” haba Aliyu sokake katadamin hankali ? Kasan bazan ta’ba samun batsuwaba idan har ina kallon fuskar ka cikin damuwa ” sake tamke fuskar shi Aliyu yayi rai ‘bace yace
” Ummi kune musabbabin matslata musamman ke kun rabani da Zarah alokacin daya dace nazauna da ita dukda babu sonta cikin raina amma zamanta taredani babbar kariyace agareni dan babu macan dazata iya d’aukar lalurata batare da nuna gajiyawa ko damuwa ba Ummi kudawomin da Zarah idan kuma kuka ‘ki to duk halin da Rayuwata tashiga kune silar komi “
Mi’kewa Ummi tayi rai ‘bace tace ” Aliyu kalleni da kyau duk da irin son danikeyi maka to wallahi zan iya mugun ‘bata maka rai akan maganar Zarah kayi gaggwar mantawa da ita koda kaji muna neman tadawo dan d’an dake cikin tane bawai dan itaba nalura sonta kafarayi shiyasa to bari gaji najanye maganar dawowarta sede idan ta haihu kaje kai dakanka ka amso min yaron kaji nagayamaka shashancin banza kawai Salimat batafi Zarah komiba dahar zakace wannan yarinyar itace zata iya d’aukar lalurarka to wallahi tun wuri idanma sonta kafarayi kayi gaggawar cireshi cikin ranka Salimat yakamata kaso so mai tsanani ”
Mi’kewa Aliyu yayi cikin raunin murya yace ” kiyi ha’kuri Ummi bazan kuma zuwa mikida maganar Zarah ba amma ayanzu duk duniya babu wacce natsana kamar Salimat tabbas nafara yarda dacewa son Zarah ne yafara kamani amma zannemi mafita ”
Aliyu yana ‘karashe fad’ar haka yafita daga part d’in gaba d’aya yana fita Ummi takoma tazauna dafe kanta tayi afili tafurta ” tabbas akwai matsala tayaya nabari Aliyu yafara son Zahra ? ” tunanin mafita tafarayi shiko Aliyu yana fita kai tsaye cikin part d’inshi yanufa cikin bedroom d’in Zahra yashiga kwanciya yayi saman bed d’in yana tuna irin abubuwan dasuka wakana abaya tashi yayi yaune yafesar da iska mai zafi daga bakinshi yace
” tabbas nasan bazaki dawo gareniba Zahra nacutar dake iya cuta tayaya zanyi tunanin zaki soni amma nikam bazan ta’ba iya sake sakin kiba sede rayuwar auranmu ta’kare ahaka ” wayar shi yaciro yashiga turamata text kamar haka
” _Assalama alaikum Momyn baby na yaya kike ya babyna ina fatan duk lafiya dan Allah kikulamin da babyna inaji ajikina tamkar shi kad’ai zan haifa a aduniya Zarah nasan zakiyi mamakin ganin wannan text d’in to kidena mamaki ina tsananin son ina matu’kar son ina kewar ina burin kasancewa da shi wato Baby na idan yakasance kin haihu bana kusa please idan namijine kisamai sunan mahaifina wato Yazeed idan kuma macace sunan mahaifiyarki Kilishi wato Sadiya ina ‘kara jaddada miki kikulamin da babyna ina matu’kar sonnnn nabarki lafiya daga Yarima Aliyu mijinki nahar abada_ ”
Yana turawa yadafe kanshi afili yace ” maiyasa bansanar da ita cewa ina sontaba kai zuciyata bazata iya zubarmin da ‘kimataba akan mace Zarah dole kisoni so mai tsanani ”
mi’kewa Aliyu yayi wata yar madedeciyar bag yad’akko kayanshi yashiga zubawa aciki duk wani abinda zai bu’kata yad’auka pen da paper yad’auka yayi gajeran rubutu guda 2 bedroom d’in Salimat yanufa ya aje mata d’ayar Paper part d’in mahaifin shi yanufa sabida yasan adede lokacin yana fada ajemai d’ayar paper yayi yafito komawa yayi cikin bedroom d’in Zarah yad’auki bag d’in sannan yanufi cikin bedroom d’inshi yakwashi kud’i masu yawa yad’auki ATM d’in shi guda 3 na bank daban daban yafita ta’kofar baya bayi se zubewa sukeyi suna kwasar gaisuwa amma ko kallonsu baiyiba yafita abinshi
jin ‘karar shigowar text cikin wayarta yasa tad’auki wayar cikin mamaki tabud’e ganin number ce babu suna sabida batama da Number shi karanta text d’in tayi tana gamawa tasaki tsaki afili tace
” watoma shi ta babyn shi yakeyi Allah yasauwa’ke nasama d’ana sunan mugun Sarkin mahaifin ka kuma wallahi baka isa kabarni da igiyar aurankaba dan kam nida zama dakai har abada nasan maganinka da yaya Muzaffar zan had’aka wallahi zama duk kusan halinsu d’aya se shegen nuna isa su akullum sune gaba ” tsaki tasake ja
Murmushin takaici Rayhana tayi tace
” toya zakayi Zarah Allah yabasu mulki da jagoranci akan mace sune sama damu kinga kuwa babu yadda zamuyi dole muyi biyayya idan har munason ganin dede karki manta aljannar mu tana ‘kar’kashin kafarsu kinga kuwa idan munaso dole muyi biyayya Zarah idan kikayi ha’kuri watarana zai zama labari “
Tashi Zarah tayi tadawo kusada Rayhana murmushi tayi tace ” hakane Aunty Raihan gaskiya zuciyar ki mai kyauce tabbas maganar ki haka take kuma nayi kudirin yima mijina biyayya wanda zan aura nan gaba ” cikin mamaki Rayhana tace
” kamarya mijinki fa ba zaman jego kikazoyiba? ” dan danan hawaye suka wanke fuskar Zarah labarin duk abinda yafaru tasanar da Rayhana tun daga auranta har zamanta cikin masarautar Yazeed raunin Zuciya irinna Rayhana seda tayi kuka tanamai tausayama Zarah cikin zuciyar ta tace ” kowa da irin tashi ‘kaddarar hmmm Zarah dakinsan wacece Rayhana dakin tausayamin nima ” haka suka cigaba da hirarsu
Shiryawa Muzaffar yayi yafito cikin shigar manyan kaya idan ka kalleshi seka sake kallon shi masha Allah hanyar fada yanufa kasancewa antara baki ko ina Muzaffar yayi binshi da kallo akayi hakan ba’karamin haushi yabashiba cikin sauri tawa hadima daga cikin hadiman Arfat wadda ta aminta da ita taruga cikin part d’in Su Arfat tana shiga tazibe takai gaisuwa tace ” Allah ya’kara miki lafiya ga Yarima Muzaffar can yafito cikin shiga ta alfarma da alamu fada yanufa ”
Cikin sauri Arfat tami’ke abayarta tazura mai matu’kar kyau a saman riga da wandan jikinta dasuka kamata tsam hular rigar taja saman kanta tafita cikin sauri take tafiya tawani corridor tabi wanda zai iya sadaka da hanyar shiga fada cikin sa’a suka kusayin kicibis da Muzaffar shiko yabiyo hanyarne sabida yawan jama’ar daketa damunshi saurin shan gaban shi tayi cikin sauri Mu’azzam yala’bai dawowar shi kenan yahangi Arfat d’in tanufi hanyar cikin sauri shine yabiyo dan yaga mai zatajeyi cikin raunin murya Arfat tace
” Dan Allah Muzaffar katsaya ka saurareni wallahi son danikeyi maka yasa na aykata haka haba conal Muzaffar nakasa bama d’an uwanka kulawa sabida kai tun farko kai nikeso tun kafin nasan maiye so dan Allah kaceci rayuwata nasan bakada ala’ka da wannan cikin amma ko Doctor yana d’aukarshi amatsayin naka da Momy please help me Conal I begging u ka amsamin cewa kana sona zan warware wannan kullin da kaina I promise u Conal Muzaffar ”
wani irin zazzafan mari yasauke mata rai ‘bace yanunata yace
” ke Arfat kiyi gaggawar shiga hankalinki wallahi koda Mu’azzam mutuwa yayi bazan iya aurankiba dan bakidaga cikin tsarina har abada bazan ta’ba sonkiba nalura ke kam dabbace kar Allah yasa ki warware komi banida matsala da hakan kisani ina raga mikine sabida Mu’azzam dan shi nayarda nashanye bulala 100 sabida naga tsantsar soyayyyar ki cikin idanun shi badan hakaba da senayimiki abinda sekin gammaci mutuwa akan rayuwarki idan kuma kika sake tarata da irin wannan maganar senasa Mu’azzam yarubuta miki saki 3 dukda son dayake miki bazai’ki aykata hakanba idan nabu’kata dabida tsananin soyayyyar dake tsakaninmu ”
Turata yayi saura kad’an tafad’i tabaya wucewar shi yayi cikin sanyin jiki Arfat tajuyo idanunta sunciga tab da hawaye ganin Mu’azzam agabanta yasata zaro ido Murmushin takaici Mu’azzam yayi yace
Alhamdulillah dama Zuciyata takasa amincewa d’an uwana zai aykatamin haka yau gashi naji aynahin gaskiya da kunnuwana tabbas Muzaffar baiyi ‘karyaba Arfat ina tsananin sonki amma ayanzu natsaneki bazanyi saurin sakinkiba yanzu sena d’an d’ana miki irin ba’kin ciki da damuwar dakika sani kikasa d’an uwana aciki sannan kiyi gaggawar sanar dani wannan cikin najikinki nawaye Arfat tabbas kin cutar dani nami’ka miki daukkan soyayyya ta ke kuma kinci amanata cin amanarma hadda cikin shege dukdan kulla makirci to wallahi bazan ta’ba yarda da wannan cikinba sanin kan kine kinsan ban ta’ba kusantarkiba na yarda dashine sabida ina zaton na d’an uwanane to yau naji tabbacin bashida ala’ka dashi kamar yadda banida shi ”
Ya’karashe maganar cikin rawar murya yajuya saurin ri’ke rigarshi Arfat tayi tace
” Doctor wallahi wannan cikin nakane bashida wani uba se kai ka saura r……… ”
Juyowa yayi afusace yasauke mata mari idanunta cike da hawaye tad’ago ta kalleshi ganin hawaye saman fuskarshi gawani irin red da idanunshi sukayi sabida tsananin ‘bacin rai saurin rumtse idanunta tayi afili tace
” Doctor yau kaine nike ganin hawaye saman fuskar ka ? Nashiga uku ni Arfat ”
Barin gurin Mu’azzam yayi cikin sauri itako dur ‘kushewa tayi saman gyuwoyinta Muzaffar yana shiga cikin fada maimartaba yafad’a Murmushin shi su wajiri kuwa wata irin fad’uwar gaba sukaji kasancewar kayu Yusuf baya gurin yasa waimbai jin kamar yasaki fitsari gaisuwa Muzaffar yakai gurun mahaifin shi sannan yazauna gaisheshi aka shigayi saurin dakatar dasu yayi fuskantar mahaifin shi yayi yace
” Allah ya’karamaka lafiya mahaifina nazomaka da wata magana amma batana nufin shiga cikin hukuncin kabane inaso kabani damar tuhumar wancan azzalumin mutumin dasuke kirada malami dan nalura akwai lauje cikin nad’in akan zuwanshi wajan yima magani ”
Jin jina kai maimartaba yayi yasauke ajiyar Zuciya yace
” karka damu Yarima Muzaffar zanbaka damar haka amma kabari zuwa gobe idan munyi magana da hajiya kaji “
Jin jina kai Muzaffar yayi yami’ke sallama yayima mai martaba yafito daga fada dafe setin zuciyar shi waziri yayi dan ji yake kamar zata fito sabida tsananin bugawa datakeyi Part d’in Momy Muzaffar yanufa
Cikin sanyin jiki Muzanbil yashiga cikin parlour zaune yasamu Samha tanashan fruit sallamar shi kawai ta amsa tacigaba dashan fruit d’inta kallonta yayi yai saurin kauda kanshi sabida irin shigar datake jikinta ji yayi tsigar jikinshi tatashi cikin bedroom d’in shi yanufa cikin zuciyar shi yace
” lallema yarinyar nan wato yau ko bag d’in bazata amsaba wanka yayi yashirya yafito dining yanufa zama yayi yanajiran tazo tazubamai amma shiru shikuma girman kai yahana yayi mata magana ‘kwafa yayi yazuba abincin Spoon d’aya yayi yai saurin furzar da abincin yami’ke afusace yanufi gurinta cikin fad’a yace
” waine irin abincine wannan ? Sekace za’abama dabba ” mi’kewa Samha tayi tace ” daga cikin gida yake wanda hadimai sukayine dama bani yadace nadingayin abinciba kaima Kasan haka inayimakane sabida kyautatawa to nalura baka bu’katar haka shine nabari idan katashi bu’katar haka sekayimin magana idan naga zan iya ” tana ‘karashe fad’ar haka tanufi hanyar fita daga parlour cikin mamaki Muzanbil yabita dakallo dan yakasacewa komi
Fuska tamke Muzaffar yazauna saman cushion d’in dake kusada Momy gaidata yayi ko kallon inda Aunty Sumayya take baiyiba itama shigowarta kenan yanzu tashi Rayhana tayi tanufi freezer lemon ta d’akko had’ida yanka nau’ikan fruit acikin fulet tanufo gurin Muzaffar ganin haka yasa Momy tashi barin part d’in tayi tanufi part d’in kaka dede lokacin islam tashigo gurin Aunty Sumayya tanufa
Zama Rayhana tayi kusada Muzaffar d’aukar yankan watermelon tayi tanufi bakinshi dashi tagefan idanunshi ya kalli Aunty Sumayya ganin shi take kallo yasa shi bud’e bakin tasame cikin wata irin murya Rayhana tace
” woow Sojana kayi kyau sosai dole nasiya wannan wankan ” wata irin fad’uwar gaba Muzaffar yaji cikin zuciyar shi yace kajimin yar duniyar yarinya tayaya tasan wannan kalmar hmmmm senaci uban Zarah nasan itace zata sanar mata ” saurin ‘ka’kalo Murmushi yayi tunawa dayayi su Aunty Sumayya suna gurin yace
” haba wane biya zakiyi bacin danke nayi kemafa kinyin kyau sosai shiyasa nasake biyoki nan dan nasake ganinki ” Murmushi Rayhana tayi tasake samai fruit abaki abin watermelon d’in yazubar mai ajiki tayi saurin yun ‘kurawa zata goge mishi akayi rashin sa’a tafad’a saman jikin shi saurin rungumoshi tayi sabida jidatayi zata fad’i d’ankwalin dake kanta yazame kamshin irin mayamayan gyaran kan Nabila yadaki hancinshi ga kamshin turaranta wani irin tashin hankali Muzaffar yaji saurin cije lip’s d’inshi yayi cikin zuciyar shi yace
” wannan yarinyarfa idan nayi wasa kasheni zatayi amma senayi mugun sata tashiga cikin hankalinta tuni idanunshi suka canza launi itako sake ‘kan’kameshi tayi tsakaninta da Allah ita tsoro yasatayin hakan badawani daliliba afusace Islam tami’ke tafita daga part d’in itako Aunty Sumayya zuciya tagama kasheta
Kuyi ha’kura najina shiru jiya batare dana sanar mukuba wani uziri yatsareni ina yinku fans ana mugun tare ina godiya da irin ‘kaunar dakuke nunamin Allah yabar zumunci ππ»π
Daga Al’kalamin….π
NPEEDY A AJI πΈπ¦πΈ
Comments and share please
GIPHY App Key not set. Please check settings