HAYATUL MAHAYAT 41-42

Advertisement

 

🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸

         πŸ¦šπŸ¦šπŸ¦šπŸ¦š

               πŸ¦šπŸ¦š

                 πŸ¦š

_Story and written_

            “`By“`

*NPEEDY A AJI* 

_Dedicated to_

Advertisements

*My yar amana*

“`My Novels 

1-NAYI RAYUWA DAKE

2-SANADIN ACCIDENT

    2019

3-SAKAYYAR CUTA 

4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA

 HAYATUL MAHAYAT

Advertisements

         typing……✍🏻“`

 *_____________________________________*

 *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER’S✍🏼*

*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

πŸ…Ώ 41 & 42

Tsayin lokaci Muzaffar yana cikin toilet sannan yafito d’aure da towel dawani  a hannu yana goge kanshi bayan yatsane jikin shi jallabiya kawai yazura yazauna bakin bed juyawa yayi yazurama bed d’in ido dede inda Rayhana take kwanciya da yara tashi yayi tsaye yatana kai komo yakasa kwanciya wayar shi yad’auka dukda yasan bashida number ta amma yashiga dubawa tsaki yaja layin Zarha yakira har kusan sau 3 amma bata d’agaba sakekira yayi seda takusa katsewa sannan tad’aga cikin muryar bacci tace 

” Hello yaya lafiya kuwa ? tsawa yadaka mata yace ” itace takawo haka maza kituro min number Raihan  ” baijira mai zataceba yakashe wayar bin wayar Zarha tayi da kallo tana mamakin yadda bashida number Raihan kuma yake nemanta cikin daran nan tura mishi tayi takashe wayar sabida gudin masifar shi dan bata bu’katar yasake kiran ta musamman yadda tajishi cikin fad’a 

Jin ‘karar shigowar text yasa Muzaffar saurin duba wayar shi ajiyar Zuciya yasauke tamkar Raihan d’in yagani kiran wayar yashigayi amma ba’a d’agawa yakuma kasa ha’kura dakiran cikin mamaki yace 

” yau ni Muzaffar niketa kiran number  har sau babu adadi amma babu piking ” harya cire rai dazata d’aga babu zato yaji muryar ta cikin bacci ” Assalama alaikum ” shiru Muzaffar yayi sabida yarasa mai zece nemo natsuwar shi yayi yace ” mijin kine Muzaffar ina bu’katar Lipton yanzu ” kallon agogon d’akin tayi 02:26 cikin muryar bacci tace 

” haba dadyn Haidar kayi ha’kuri dare yayi sosai kabari zuwa safe kaji ” shiru natsayin lokaci sannan yace ”  bazan iyayin hakan ba ajiyar Zuciya  Raihan tayi tasake cewa to tayaya zanfito yanzu kasanfa Momy bazata barniba amma in sha Allah zuwa safe dawuri zan had’a maka kaji dadyn Farooq ” a hassale Muzaffar yace banason wannan sunan idan muna magana tsakanina dake kibari se gaban su Momy kifad’i wannan cikin d’an mamaki tace to se wanne ? ajiyar Zuciya Muzaffar yayi yace se wanda kikaga damar sawa kuma kiyi gaggawar fad’ar gaskiya idan kuma kika’ki zakija abubuwa dayawa kinji nagaya miki ” kashe wayar yayi yawurgata saman bed yanasakin huci kamar wanda yayi dambe 

Bin wayarta Rayhana tayi da kallo tana mamakin ‘karfin hali irin na Muzaffar shida yace bayasonta kuma bazai iya rayuwar aure da ‘karamar yarinyaba to tayaya yadamu akan seta bayyana makowa shi mijin tane ‘ gaskiya bazan iyaba bazan zauna da wanda bayasona ba ” kashe wayar tayi takoma ta kwanta amma takasa komawa bacci cikin ‘bacin rai Muzaffar yahau saman bed cikin muryar fushi yace ” tayaya kikayimin tsaye cikin zuciya Raihan maiyasa nikeson cigaba dazama dake? ok nagane sabida su Farooq  kinacan kina bacci amma ni inanan nakasa hmmm ” 

Kwanciya yayi yaja blanket amma kokusa yakasa runtsawa cikin farinciki Mu’azzam yashiga cikin parlour shi zama yayi yana Murmushi cikin mamaki Arfat take kallon shi kasa jurewa tayi tataso tazo kusadashi tazauna cikin d’an sakku tace 

” doctor wane abune yasaka cikin farin ciki haka ? rabandanaga Murmushin fuskarka harna manta ” sakeyin Murmushi Mu’azzam yayi yace ” dole nayi Murmushi sabida nasamu wadda nikeso yarinya mai tarbiyya ga hankali da natsuwa ga sirrin kyau kay gaskiya nayi matu’kar sa’a ” 

Wani irin ba’kin ciki Arfat taji amma setayi saurin dannewa tace ” natayaka murna sosai Doctor  wacece wannan mai matu’kar sa’a haka ? ” Murmushi Mu’azzam yayi sannan yami’ke taku d’aya biyu yayi yace ” Raihan ce tunda babu aure tsakaninta da Muzaffar ay nikam tagyarumin kishirya idan har ta’amince kizauna a d’akinki to babu matsala idan kuma tace bazata zauna da kishiyaba tofa zakiyi waje ” 

Yana gama fad’in haka yanufi cikin bedroom wani irin ‘bakin ciki da razana Arfat taji cikin sauri tabi bayan shi amma kafin ta’karasa haryasama ‘kofar key dur’kushewa tayi agurin tana kuka mai tsuma zuciya yanajinta dukda cewa yanajin kukan nata cikin ranshi amma yadake tsayin lokaci yanajin kukan nata har yadenaji 

Shiko Muzanbil tausayin Samha ne yayi matu’kar kamashi  yadda yaga take kuka mai tsuma zuciya  bayan yayi shirin bacci yakoma cikin bedroom d’in hawa saman bed yayi yarungumo ta yashiga lallashin ta 

” haba kiyi ha’kuri kibar kukan mana idan aka tambayi Nura akaji batada saka hannu cikin wannan kisan za’a saketa kinji nayi miki al’kawari zantsaya wajan ganin anyi adalci kinji ” 

Kuka Samha tasake saki tace ” shikuma yaya Nura kasheshifa za’ayi shiyasa naketa gargad’in mami akan wannan lamarin gashinan abinda son zuciyar su yahaifar ” cigabada  lallashin ta Muzanbil yayi har seda yaga tayi shiru cikin muryar jin bacci tace ” barrister yakama kaje ka kwanta nima kwanciya zanyi kaga dare yayi sosai ” cikin mamaki yake kallonta dan beyi tunanin zataso yabar cikin bedroom d’inta ayau ba d’an dakewa yayi yace zaki’iya kwana ke kad’ai gaskiya bazan iya barinki ki kwana ke kad’ai cikin damuwa ba ” 

Sake jawota yayi cikin jikin shi kafin tasake cewa komi jin wani yanayi yana fusgarta yasata tashi zaune juyawa tayi had’ida matsawa can gefe tayi kwanciyar ta babu jimawa bacci yayi gaba da’ita shiko Muzanbil tashi yayi yazaune yana tunanin yadda zaishawo kanta

Jin kiran sallar asuba yasa Mu’azzam tashi dan bawani baccin kirki yayi ba alwala yayi yafito daniyyar tafiya masallaci cikin mamaki yake kallon Arfat tade kwance abakin bedroom d’inshi ga dukkan alamu anan tayi bacci har yayi niyyar tsallaketa yawuce sekuma yatsaya d’aukarta yayi yakoma da ita cikin bedroom kwantar da ita yayi saman bed tsurama cikin jikinta ido yayi wanda yafito fili ayanzu saurin juyawa yayi yafita 

A’bangaran Muzaffar kuwa ko runtsawa baiyiba jin kiran salla yasashi tashi amma da’kar yami’ke sabida wani’irin ‘kullewa mararshi tayi alwala yayi yanufi masallaci bayan sunfito sallah kai tsaye part d’in Momy  yanufa ganin babu kowa cikin parlour yasa yanufi cikin bedroom d’in da Rayhana take zaune yasameta akan abin sallah tana lazumi zama yayi kan bed d’an zuba mata ido yayi kafin yamaida duban shi kan yara bacci sukeyi sosai hawa yayi saman bed d’in sosai ya kwanta lumshe idanunshi yayi yana sha’kar kamshin turaran Rayhana daketashi saman bed d’in  tsayin lokaci sannan Rayhana tami’ke daga kan abin sallar tanunke sannan ta’iso bakin bed d’in cikin sanyin murya tace 

” barka da asuba dadyn Farooq ” yi yayi kamar baijiba sake fad’a tayi nanma shiru ganin bashida niyyar amsawa yasa tami’ke hanyar waje tanufa cikin sauri yatashi jawota yayi tafad’o jikin shi rungumeta yayi sosai yana sauke ajiyar Zuciya kawo bakinshi yayi kusada kunnanta cikin wata irin murya yace 

” banaso idan muna mu 2 ba karki sakecemin dadyn Farooq  ko haidar ba gaskiya nalura bakijin magana amma barinasa kid’ingaji ” juyoda fuskarta yayi suka fuskanci juna sosai bakinshi yasaka cikin nata kissing d’inta yashigayi dandanan yashiga cikin wani yanayi juyarda ita yayi yarufamata baya hannun shi yad’aura saman breast d’inta wani irin numfashi yaja yasauke shi da’karfi cikin rawar jiki yashiga romantic d’inta tsananin tsorone yakama Rayhana tafara ‘ko’karin tureshi jin maganar Momy tana knocking yasa Rayhana sake tureshi cikin sauri yasake jawota cikin muryar tsoro tace 

” My Noor  Momy tana knocking fa ” cikin wani yanayi yasaketa cikin karfin hali yad’akko Sudees yad’aurashi saman ‘kirjinshi  yana sauke wani irin wahalallan numfashi jiki asanyaye Rayhana taje tabud’e ‘kofar shigowa Mommy tayi kai tsaye ganin Muzaffar kwance yasatayin mamaki ‘karasowa tayi bakin bed d’in tace

” Mai zangani haka Muzaffar ? yaushe kazama haka ” maza tashi kafita daga yau karkasake zuwa cikin bedroom d’in Rayhana  a irin wannan lokacin sabida yaranka yasa har zanbarka kanashiga cikin bedroom d’in nan amma bazan lamunta zuwanka a irin wannan lokacinba yara kotashi basuyiba maza katashi kasan maimartaba yasaku ayki Ibrahim yace dawuri zakutafi India wajan tahowa da Nura  Kaje kashirya ” 

daga haka Momy tajuya tafita tashi Muzaffar yayi zaune kallon Rayhana yayi rai ‘bace yace 

” kingani yanzu duk wannan kike bu’kata adingayimin nida matata ko to barikiji daga yau idan har baki fad’i gaskiya ba nadena shiga harkarki kuma wallahi  duk ranar danasamu dama senarabaki da abinda kike ta’kama inga ‘karyar rashin kunya kuma bazan ta’ba sakin kiba sede kitazama da igiyar aurena akanki  kuma wallahi  nagakin kula wani senayi mugun ‘batamiki rai sannan kijamakowaye wahala sannan dole kidingayimin abinci dan bazan iya cin abincin hadimai ba kiyi maza kihad’amin breakfast da Lipton zamutafi ” 

Daga haka yafita afusace cikin wani irin yanayi Rayhana tabishi da kallo cikin zuciyarta tace 

” haka kawai bakasona nayarda nacigaba dazama da kai ina salon kaita cutata sede kagaji karabu dani amma bazan iya cigaba dazama da kai ba inda najidad’in zama dakai ne sena’amince amma wahala kawai nasha ” 

Juyawa tayi ta kalli yaran baccinsu kawai sukeyi canza kayan baccin jikinta tayi tafita parlour  kai tsaye kitchen tanufa 

Kuyi ha’kuri da wannan naso yafi haka kasancewar nayi kwanaki banyi typing ba sabida rashin lafiya to amma rashin caji yahana hakan kunsan yanzu wutar nefa tazama abinda tazama ina godiya sosai πŸ’―πŸ‘πŸ»

Daga Al’kalamin……πŸ–Š

NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸

Comments and shine please

Leave your vote

-2 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like