HAYATUL MAHAYAT 45-46

Advertisement

 πŸŒΈ *HAYATUL MAHAYAT* 🌸

         πŸ¦šπŸ¦šπŸ¦šπŸ¦š

               πŸ¦šπŸ¦š

                 πŸ¦š

_Story and written_

            “`By“`

*NPEEDY A AJI* 

_Dedicated to_

Advertisements

*My yar amana*

“`My Novels 

1-NAYI RAYUWA DAKE

2-SANADIN ACCIDENT

    2019

3-SAKAYYAR CUTA 

4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA

 HAYATUL MAHAYAT

Advertisements

         typing……✍🏻“`

 *_____________________________________*

 *πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER’S✍🏼*

*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

πŸ…Ώ 45 & 46

Zaune suke cikin jirgin sunad’an hira jefijefi amma banda Muzaffar daya kwantar da kan saman kujerar yalumshe ido tamkar mai bacci kallon shi Muzanbil yayi dafashi yayi yace 

” sekayi ha’kuri Muzaffar kuma kacire damuwa kayima Allah godiya da akagane gaskiya kashi kuma har zamuje tahowa damai lefin ” 

Jinjina kai Muzaffar yayi cikin zuciyar shi yace ” Muzanbil bakasan meyake damuna bane shiyasa amma zansamar makaina mafita bayan sun sauka suka iske masu tarbarsu babu ‘bata lokaci suka shiga cikin motocin wani kyakkyawan gida akanufa dasu suna shiga Muzaffar yanufi cikin wani bedroom suko zama sukayi saman curious dake parlour yana shiga yazauna kan sofa wayar shi yaciro harya danna kiran Rayhana sekuma yayi saurin katsewa zuwacan kuma yashiga tura text 

_ke yaya su Farooq suke ? ki kulamin dasu sosai zan kira zuwa anjima sekibasu naji muryarsu su kwai_

Yana turawa yami’ke yashiga toilet Rayhana nazaune kusada Zarha suna hira taji shigowar text bud’ewa tayi taduba Murmushi tasaki mi’kama Zarha wayar tayi tace ” d’an ajemin wayar nan agurinki duk wanda yakira kice ina aykine amma idan yaya Ibrahim ne ko yaya Mu’azzam  kisa akirani jankoma part d’in Momy akwai abinda zanyi ” Murmushi Zarha tayi tace ” toshi yaya Muzaffar fa? ” girgiza kai Rayhana tayi tace ” nasan bazaikiraba kuma koda yakira kinsan halinshi fad’ane kawai zaiyi dan shi abin fad’a bashida wuya agurin shi kinga kuwa ni yau ina cikin farinciki banason damuwa ” dariya Zarha tayi tace gaskiyar ki nima idan naga shine bazan d’agaba kar a saukemin fad’an ” 

Murmushi Zarha tayi tami’ke fita tayi cikin zuciyarta tace hmmm ” wallahi senabaka mamaki Muzaffar nalura kanada mugun taurin kai wato kana nufin babu macan data isa karusina mata har kafurta mata kalmar so to zamugani ” 

Bayan Muzaffar yafito wanka kayan shan iska yasaka yafito parlour hannun shi ri’ke da waya yana duba ko text yashigo sabida yayi tunanin Rayhana zatayimai barka da sauka tunda taji sun sauka lafiya amma baiga komiba tashi Mu’azzam yayi yami’kama Muzaffar waya yace ” samin number Raihan inaso naji yaya take ” wani irin kallo Muzaffar yayi mai cikin tamke fuska yace banida ita ” kallon mamaki Mu’azzam yabishi dashi dariya yaya Ibrahim yaguntse yace ” kawo nabaka Mu’azzam ni inada ita 

Kallon yaya Ibrahim Muzaffar yayi cikin ‘bacin rai mi’kewa yayi yabar gurin harabar gidan yafita kiran wayar Rayhana yashigayi amma ba’a d’agawa har sau 3 cikin jin haushi yamayar da wayar aljihu yakoma ciki babu kowa cikin parlour da alamu kowa yashiga watsa ruwane zama yayi yana nazarin ‘kin d’agawayar shi da Rayhana tayi dan kam yanada tambacin ‘kin d’agawa tayi Muzanbil  yafara fitowa shima sanye dakayan shan iska sefama kiran waya yakeyi shima ba’a d’agawa wani irin tsaki yaja yace ” ohhhh haba Samha tayaya bazaki d’aga kiranaba ? kamar….. ” 

Ganin Muzaffar zaune yasashi yin shiru sabida bayason kowa yasan halin dayake ciki shiko Muzaffar cikin zuciyar shi yace ” hmmm yarinyama ta’iya wula’kanci balle babba mace hmmm ” zama Muzanbil yayi daga gefanshi yace ” ashe kadawo ? d’aga kai kawai yayi fitowar yaya Ibrahim yasa Muzaffar sake tamke fuska sabida yabashi matu’kar haushi akan bama Mu’azzam number Rayhana dayayi shiko yaya Ibrahim waya yakeyi cikin nishad’i badakowa yake wayar ba seda Islam  adede lokacin tana zaune a parlour daga gefan Aunty Sumayya sun dade suna waya bayan sunyi sallama Aunty Sumayya tadubeta tace 

” waye wannan ? banahanaki kula kowaba ? jinjina kai tayi tace ” to Aunty yaya zanyi wani d’an uwa nane kuma Abba yace lalle nakulashi kinga yazama dole nabi umarnin Abba kuma kinga har yanzu hankalin Conal yakasa zuwa gareni shekaru tafiya sukeyi Aunty karnazo nayi biyu babu idan bansamu Muzaffar ba senayi ha’kuri na auri yaya I’b ” 

Jinjina kai Aunty Sumayya tayi tace ” karki damuwa Muzaffar nakine idan kuma hakan yagagara shikenan zanbaki goyan baya akan auran shi I’B amma senayi duk yadda zanyi wajan ganin kin auri Muzaffar  ” Murmushi Islam tayi cikin zuciyarta tace ” Aunty kenan ay nasan bazan samu Muzaffar ba sabida yaciga taurin kai gadama tasameni senayi watsi da’ita ina sede kiyi ha’kuri Aunty dan bazan iya barin yaya Ibrahim ba ayni babbar sa’a nayi wai namiji mai tsada haka hmmmm Allah nagode maka ” dafata Aunty Sumayya tayi tace ” tunanin mai kikeyi haka ? Murmushi Islam tayi tace 

” a’a naga yaya Ibrahim bai kiraki bane har yanzu kuma kema bakiyi maganar shi ko kikira shin ba shine nike tunanin abin ” ta’be baki Aunty Sumayya tayi tace ” kar Allah yasa yakira kuma nima bazan kirashiba sede muzauna ahaka ” d’an canza fuska Islam tayi tace nikam aunty  barinakira yara mukira shi muji yaya suka sauka ” ku kuka sani Aunty Sumayya tafad’a tana mi’kewa barin parlour tayi takoma cikin bedroom Murmushi Islam tayi tami’ke tanufi bedroom d’in yaran 

Kallon yaya Ibrahim Muzanbil yayi yace ” amma de yaya wannan irin waya haka nalurafa ba Aunty mubace kode wata kake shirin kawomana ? to gaskiya bazamu yardaba ” Murmushi yaya Ibrahim yayi yace ” ayko dole kuyarda danni mijin mace 4 idan ina ra’ayi amma de iya 2 sun isheni kuma ay nabar Aunty taku tasha miya dayawa ” Allah yaya nabaka goyan baga πŸ’― dan nima 2 nan in sha Allah  cewar Mu’azzam dayafito daga bedroom  harara Muzaffar yawurga mishi suko dariya sukasaki zama Mu’azzam yazo yayi kusada Muzaffar wayar shi yaciro number Rayhana yakira bugu 2 aka d’aga cikin sanyin murya Rayhana tayi sallama wata irin ajiyar Zuciya Mu’azzam yayi yace 

” _kema amincin Allah yatabbata agareki my Apple inamai farincikin sanar dake mun sauka lafiya kowa yana gaidaki yaya yaran nawa ina Haidar da Faro…….  ” cikin azama Muzaffar yafige wayar dan kam shi ada baiyi tunanin da Rayhana Mu’azzam yakeyin wayaba yazata da Arfat ne rai ‘bace yakai wayar kunnan shi adede lokacin Rayhana tace ” masha Allah Sweet brother  haid…. ” katseta yayi dafad’in ” Allah ya’isa dakikayi magana dawani ‘kato kuma wallahi kisaurari dawowata senayi mugun hukuntaki idan kuma kika sake d’aga wayar wani Allah sena…. ” kashe wayar tayi cikin fusata yad’aga wayar ze bugata da ‘kasa yaya Ibrahim yayi saurin ri’ke mishi hannu yace

” haba Muzaffar yayahaka kahanashi number anbashi kuma kahana shi kiranta lalle wato har wani Allah ya’isa kakeyimata ko ” azafafe Muzaffar yace ” eh sabida nasan dole takamata idan har bayafewa nayiba sabida matata ce Mu’azzam kafita hanyar Raihan idan ba sokake musamu matsala a tsakanin muba ” 

Mi’kewa Mu’azzam yayi cikin mamaki yace ” hmmm matarka kace to ay naga agaban kowa tabayyana cewa babu aure tsakaninku ko ? kuma bakace komiba se yanzu  hmmm kaga idan kaima sonta kakeyi to kashiga sahu Allah yabamai rabo sa’a ” 

daga haka Mu’azzam yajuya yanufi dining cikin sauri yaya Ibrahim yashiga lallashin Muzaffar dan yasan halinshi yana iya barin ‘kasar a wannan lokacin ” haba Muzaffar karkayi haka idan har son Raihan kakeyi kafad’i semu sasantaku anemi ra’ayin ta akanku wadda taza’ba shikenan ” 

Fuska tamke Muzaffar yace dolene senace inasonta toni bason Raihan nikeyiba amma ina bu’katar ta cikin rayuwata sabida yarana kuma dani Raihan yakamata tazauna sabida nine nakawota cikin gidan badan rayuwar kowaba sedan tawa rayuwar dan haka duk wanda yashiga cikin rayuwar Raihan wallahi sena bashi mamaki ” 

Afusace yanufi bedroom kallo yaya Ibrahim yabishi dashi yace ” wai wannan irin kishi haka ? Muzaffar ayko Nabila banga kanayimata irin wannan kishin ba amma kamusanta cewa sonta kakeyi to tunda kai basokakeyiba sedan wani dalili to ko dole kabar maisonta yasota tunda mude bamuga shedar tabbacin itad’in matar kabace tunda bamuji abakintaba ” 

Rumtse idanunshi Muzaffar yayi dan yaji duk abinda yaya Ibrahim yace cikin ‘bacin rai yace hmmm dole sekin fad’i gaskiya Raihan to waima maiyasa nadamuda ‘karamar yarinya haka har nikeso nazama kamar wani marar tunani ina akwai sake wayarta yashiga kira amma bata d’agawa tsaki yaja yawurga wayar saman bed  sake shiri yayi yafito kallonsu yayi yace” idan kungama hutun sekufito mujeyin abinda yakawomu “

Daga haka yanufi hanyar fito girgiza kai yaya Ibrahim yayi yace ” kutashi muje ko ? komawa kowannensu yayi cikin bedroom dan sauya kaya 

To bari mukoma masarautar sarki Yazeed 

Cikin yanayin damuwa Salimat tanufi part d’in Ummi zaune tasameta a parlour gaidata tayi sannan tafashe da kuka tace ” Ummi yaya zanyi sefaman kiran wayar Aliyu nikeyi amma batashiga dan Allah  Ummi kikiramin shi ina bu’katar yin magana dashi cikin gaggawa banaso nafarayima kowa wannan albishir d’in se shi ” 

Dubanta Ummi tayi tace ” haba Salimat ay tunda Aliyu bayanan ni yakamata kisanar makoma meye balle albishir duk abinda akace albishir to abune mai dad’i dan haka sanar dani nima konakira number shi batazuwa ” Murmushin kissa Salimat tayi tad’an rufe fuskarta itanan mai kunya tace ” Ummi dama cikine dani ” 

washe baki ummi tayi cikin farinciki tajawota jikinta tace ” masha Allah wannan babban albishir ne dole abada babbar kyauta nasan ma maimartaba zaiyi farinciki sosai Salimat Allah yayi miki albarka  Allah yakawomin jikana lafiya ” Murmushin jin dad’i Salimat tayi cikin zuciyarta tace ” yauwa nasamu wata hanyar zama hamsha’kiyar mai arziki kafin Aliyu yadawo sannan  dole ya amshi wannan baby kuma yayi mai hidima tamkar jinin shi ” mi’kewa tayi cikin jin kunya tabar parlour  bintada kallo Ummi tayi tanajin matsanancin farinciki afili tace ” nagode ma Allah dama akan dole zamuje amsar babyn Zarha to shegashi Allah yakawo mana wanda mukeso ” tashi tayi tanufi part d’in maimartaba cikin farinciki tasanar dashi sosai yayi murna dandanan cikin masarautar yad’auka da murnar samun cikin Salimat cikin lokaci kad’an aka shirya walimar murna 

Tofa lalle wannan babyn yanada farinjini ayanzu toko zai d’ore har nan gaba baride mugani 

India 

Cikin ‘bacin rai Muzaffar yace ” tabbas akwai wanda yasanarma Nura zuwanmu shiyasa yasamu damar ‘boyewa ‘kilama yabar ‘kasar yau kimanin 2 weeks muna india amma munkasa kama mutun 1 haba sekace wasu ragwaye ” mi’kewa yaya Ibrahim yayi yace ” kwantar da hankalinka  Muzaffar yau zamubar india zamukoma BIHAR dan nariga nakama Nura nahad’amai tarko irin na marassa waye kumayafad’a dan haka kowa yatashi yashirya jirgin 3 zamubi Nura yana cikin but d’in motar wannan abokin nawa kai Muzanbil jekashigo dashi ” 

mi’kewa Muzaffar yayi cikin sauri yaya Ibrahim yari’ko hannun shi yace ” a’a Muzaffar karkaje sannan banaso akayima Nura komi har semun bar india idan akaganshi jinajina to zebamu matsala kafin mu isa BIHAR dan haka kadanne zuciyar ka har semun koma kaji aboki ” wayar shi yaya Ibrahim yaciro kiran Raihan yayi cikin farinciki tad’aga kiran gaishedashi tayi ya amsa cikin fari’a tambayar ta yara yayi tace suna nan lafiya yadauwar dacewa ya ba’kuntar skul Murmushi tayi tace ay yaya babu wata ba’kunta inajin dad’in skul d’in sosai Murmushi yaya Ibrahim yayi yace to masha Allah muma gamunan dawowa gida yau in sha Allah kuma munyi nasara Raihan ga Muzaffar kugaisa ” 

Mi’kamishi wayar yayi amsa Muzaffar yayi babu musu amma ko kunnan shi bai kai wayar ba yakashe ya’ajeta saman cushion yatashi cikin bedroom yashiga yafarayin shirin tafiya

Binshi da kallo yaya Ibrahim yayi ya girgiza  kai shima Mu’azzam kallon yabishi dashi itako Raihan ta’be baki tayi tace ” matsalar kace badan yaya Ibrahim ba ayni dababu abinda zaijamin amsa wayarka ” 

Misalin 05:42 su Muzaffar suka iso BIHAR tareda Nura babu ‘bata lokaci motocin dasukazo tarbarsu suka shiga kowa kaga fuskar shi d’auke da walwala amma banda Muzaffar da fuskar shi take atamke babu alamar fari’a suna isa cikin masarauta akashiga yimusu kirari  cikin ‘bacin rai Muzaffar yabude murfin mota tun kafin ayi parking balle yajira abud’e mai ganin haka yasa driver tseda motar kai tsaye part d’in momy yashiga yanashiga ya iske su haidar se kuka sukeyi a hannun masu ronon su cikin mamaki yashiga cikin sauri suna ganinshi suka shiga zullo amsarsu yayi sannan rai ‘bace yace 

” ina Momyn tasu ? ” cikin girmamawa d’aya daga cikin hadiman tace ” tana skul saurin kallon agogon hannun shi yayi yace ” skul hmmmm ” dede lokacin Momy tafito daga bedroom Murmushin jin dadi momy tasaki tace ” barkanku da dawowa ina sauran ‘yan uwan naka ? ” suna wajan maimartaba kawai Muzaffar yace fuska tamke Murmushi Momy tayi tace ga abinci can Raihan tashirya maka kafin tatafi skul ” mi’kewa Muzaffar yayi yace kibar mata abinta momy idan tadawo taci bana bu’kata amma inaga tanagaf dabarin wannan skul muddin zatad’inga tafiya tanabarmin yara suna kuka kum……..  “

Sallamar Raihan tasa Muzaffar saurin juyawa dan jinta yayi har jikin kanshi kallon shigar jikinta yashigayi daga sama zuwa ‘kasa doguwar rigace tawata tsadaddiyar atamfa wadda tayi masifar amsar jikinta se wani gyale madedeci gawani kamshi dake tashi cikin jikinta tsantsar ‘bacin rai yabayyana cikin idanunshi sauke yaran yayi kusada Momy rai ‘bace yafizgi hannun Rayhana yanufi cikin bedroom  d’inta da ita 

Tofa Muzaffar koka manta akwai Momy a parlour ne 😊😜

daga Al’kalamin…..πŸ–Š

NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸

Comments and shine please

Leave your vote

-10 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like