Advertisement
πΈ *HAYATUL MAHAYAT* πΈ
π¦π¦π¦π¦
π¦π¦
π¦
_Story and written_
“`By“`
*NPEEDY A AJI*
_Dedicated to_
Advertisements
*My yar amana*
“`My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA
5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA
HAYATUL MAHAYAT
Advertisements
typing……βπ»“`
*_____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER’SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
π Ώ 63 & 64
Hannu yaya Ibrahim yasa yadakatar da’ita dole Aunty Sumayya tadakata sabida yadda taga fuskar shi zaunar da Islam yayi kan kujerar dining sannan yadawo gurinta babu zato taji yasureta tsakiyar parlour yanufa da’ita zaunar da’ita yayi kan cushion shima yazauna rungumota yayi cikin sanyin murya yace
” Haba Honey duk wannan fushi kuma akaina zakisaukeshi ninefa Ibrahim naki tabbas nasan nayi lefi agareki amma kisani duk kece kikaja komi banyi niyyar ‘kara Aure ba amma kikasa nayi ra’ayin haka gaskiya inajin ciwon yadda kike takura Muzaffar akan dole seya auri Islam hakan yasa kika tsani Nabila tsana mafi girma har tabar duniya da ba’kin cikin ki amma koda tarasu baisa kinyi nadamaba kika koma kan Raihan dukda irin taimakon datayima d’an uwanki haba Sumayya wallahi idan kikayima Raihan wula’kanci inajin zafi har cikin Raina fiyeda yadda nikejin zafi idan kika wula’kanta Nabila narasagane dalilin haka amma inajin Raihan tamkar jinina
Sumayya kece kikace bazakiyi kishi da Islam ba ashe abin bahakabane to amma meyasa kikeso ayima wasu kishi ke kuma bakiso yaya haka Islam fa ‘kanwarkice tayaya zakibari zuciya tasa ki aykata abinda zaisa girmanki yazube ? Sumayya inasonki fiyeda tunaninki kuma babu sama dake cikin zuciyata da idanuna amma kisani ada na auri Islam ne dan kikoyi darasi badan inasontaba amma maganar gaskiya ayanzu ina son Islam sosai Honey ni Ibrahim inamebama matata ha’kuri dan Allah kuzauna lafiya zantafi zuwa jibi idan akwai abinda kuke bu’kata keda yara kisanar dani ”
Kuka sosai Aunty Sumayya takeyi tanayin nadamar yarda datayi dasu Islam tabbas batayi tunanin su zaliha zasuci amanarta hakaba mi’kewa tayi tanajin wani’iri jiri yanad’ibarta bata kalleshiba tace
” ina jiranka a babban parlour kakaini nayima yara Shopping wajan Islam tanufa kallonta tayi tawatsar tace ” ni zakicima amana Islam hmmmm wallahi sekinyi nadama ” daga haka tajuya tafita dawowa yaya Ibrahim yayi yazauna kan d’aya dagacikin kujerun dining d’in cikin shagwa’ba Islam tace ” yaya gaskiya inajin tsoran Aunty Sumayya ” Murmushi yaya Ibrahim yayi yace haba keda Aunty ki karki damu kede karyi renata kuma karkizama mai yimata rashin kunya dan tanagabadake kuma tabbas kinsan kinyi mata lefi mijinta kika aura fa dole kizama mai binta sannu Islam har abada babu wula’kanci ko cin fuska atsakanina da Sumayya idan kika ‘bata mata tabbas raina zai’baci auroki danayi bayana nufin wula’kanci ga Sumayya bane a a sedan natsayar da takunsa’kar dake faruwa tsakanin yaya da ‘kani wato Sumayya da Muzaffar amma karkiyi tunanin banasonkine eh gaskiya abaya badan so yasa nanemi aurankiba sedan insa Sumayya tagane wata Rayuwar amma ayanzu ina sonki sosai amma yanada kyau kiciba da kiyaye abinda zaisa nacigaba dasonki zanshiga nashirya yanzu zamufita ayima yara shopping kinsan gobene tafiyana ” dagahaka yami’ke yanufi bedroom d’inshi ajiyar Zuciya Islam tasauke dan kam batasojin hakaba amma babu yadda zatayi binshi da kallo tayi tana tunanin abubuwa dayawa cikin zuciyar ta tace
” lalle yaya Ibrahim namijine tsayayye gaskiya abinda Aunty Zaliha takeson muyima Aunty Sumayya bafazai yuwuba idan har basonikeyi nayi wajeba yazama dole nayima mijina biyayya dan ina matu’kar sonshi ”
tana nan zaune yafito cikin shiga ta alfarma se kamshi yakeyi wajanta yanufa rungumota yayi yasumbaci kuncinta yace ” dear senadawo ko tsarabar mai kikeso ? amma bamasekin fad’iba nasan maiyadace nasiya miki bye bye yayi mata yafita yana fita yasamu Aunty Sumayya a parlour tayi jigum tana tunani had’ida matu’kar mamakin yadda Zaliha da Islam sukaci amanarta yaya Ibrahim yakatse mata wannan tunanin babu zato taji yarungumota sosai fuskarta yakamo yasakar mata Murmushi bakinshi yazura cikin nata yasakar mata wani kiss namusamman dandanan Aunty Sumayya taji jikinta yamutu sabida raban jikinsu yahad’u itada yaya Ibrahim tunkafin yafara neman aure
Cikin ‘karfin hali tamike datatuna daga wajan wata yake watanma wadda tad’auka matsayin ‘kanwa hanyar fita tanufa tashi shima yayi yace dole kiji zafi Honey na amshi lefin muje kinji matata nasan zakiyima dadyn Amfal ha’kuri ko ”
Seda suka biya part d’in Momy suka gaida ta nasiha tayimusu sosai sannan sukafita shi dakanshi yake driving dagashi se ita suka fita dan bayason idan wani yahanashi lallashinta a ‘bangaran su Muzaffar kuwa
Kwance suke kan makeken bed d’in su Muzaffar rungume da’ita tamkar za’a ‘kwace mai ita cikin sauri Rayhana tami’ke toilet yanufa aguje amma kafin ta’karasa amai yakufce mata dole ta tsuguna tashiga kwarashi cikin sauri Muzaffar yasauka daga bed d’in zuwa yayi yakamata cikin tausayawa yakeyimata sannu duk yagama rikicewa sosai Rayhana tadad’e tanayin amai sannan yalafa gyaramata jikin yayi sannan yakamata kwantar da ita saman bed yagyara gurin
Komawa yayi cikin tausayawa yakamo hannunta wani irin zafi yaji cikin sauri yakai hannun shi jikinta yadda yaji jikin nata yad’auki zafi sosai yasa Muzaffar sake rud’ewa cikin rud’u yashiga tambayarta amma takasayin magana sede girgiza kai sabida jitakeyi idantabud’e bakin zatasakeyin wani aman
Sauka Muzaffar yayi daga bed d’in fita yayi yana isa parlour yacigaro da Momy da wata hadima d’auke dasu haidar sefaman kuka sukeyi cikin sauri Muzaffar ya amshi Farooq cikin sauri Momy tace
” lafiyarka kuwa Muzaffar naganka duk a rikice ina Raihan d’in ? ” cikin damuwa Muzaffar yace ” Momy batada lafi…. ” kafin ya’karasa tuni momy tanufi cikin bedroom d’in zamatayi bakin bed d’in takamota sosai itama tarazana dajin zafin jikin nata cikin damuwa Momy tace
” Muzaffar maza muje gara akaita asibiti dan jikin yayi zafi dayawa cikin sauri yazari key yafita kamata Momy tayi suka fita hadimai 2 nari’ke da Farooq da haidar Muzaffar yake driving dakanshi tofa Maike damun Raihan
Masarautar Yazeed cikin kissa Salimat tanufi inda Ummi take zama tayi tasa hannu tayi tagumi hannu 2 batare datace komiba cikin damuwa Ummi tafuskanceta sosai tace
” lafiya kuwa Salimat meke damunki ? ” cikin muryar kuka tace ” doctor ne yacemin wannan cikin nawa yanacikin had’ari sabida akwai matsala idan har anaso yazauna dole kullum senasha wata ‘kwaya kuma duk 1 50k take har natsawon 6 months shine nashiga cikin damuwa matsananciya ” Murmushi Ummi tayi tadafata tace
” haba Salimat ay wannan abune mai sau’ki karki manta jinin Aliyu nefa yaron danafiso duk duniya ina matu’kar son ganin d’an Aliyu musamman wannan dazaki haifa maiye 50k akullum dan ankashe su akan jikan cikin masarautar nan kuma jika nafarko wajan maimartaba karki damu nawa kenan adadin kud’in duka kinga se abama doctor d’in yazama kawowa kawai zaidingayi kinasha ”
Cikin murya ‘kasa’kasa Salimat tace to Ummi zansanar dake zuwa anjima tashi tayi tanufi part d’inta tanajin wani irin ba’kinciki binta Ummi tayi dakallo cikin zuciyarta tace ” Allah yasaukeki lafiya Salimat senafi kowa farincikin ganin dan Aliyu
Tofa
Aunty Zaliha zaune cikin parlour Islam itada ‘kawarta cikin murya ‘kasa’kasa tace
” ke Islam bafa zama zamuyiba dole munemi mafita kotawace hanya danki mallaki Ibrahim ” cikin mamaki Islam tasaki baki tana kallon Aunty Zaliha
Iname baku ha’kuri akan shirun dakukaji amma in sha Allah komi yazama dede yanzu zakudinga ganin posting kullum koda babu yawa nagode sosai masoyana
Daga Al’kalamin….π
NPEEDY A AJI πΈπ¦πΈ
Comments and shine please
GIPHY App Key not set. Please check settings