Advertisement
πΈ *HAYATUL MAHAYAT* πΈ
π¦π¦π¦π¦
π¦π¦
π¦
_Story and written_
“`By“`
*NPEEDY A AJI*
_Dedicated to_
Advertisements
*My yar amana*
“`My Novels
1-NAYI RAYUWA DAKE
2-SANADIN ACCIDENT
2019
3-SAKAYYAR CUTA
4-RUFAFFIYAR ZUCIYA
5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA
HAYATUL MAHAYAT
Advertisements
typing……βπ»“`
*_____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER’SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
π Ώ 67 & 68 69 & 70
LAST PAGE
Cikin sauri yaya Ibrahim yafito daga mota nufar wajan Aliyu yayi cikin mamaki yace
” Aliyu inafatan de lafiya gobe nike shirin tafiya ina mama da Abba ? karkacemin wani abu yafaru dasu ” Murmushi Aliyu yayi yace
” lafiya lau suke kuma tare nike dasu kaga ikon Allah ko ” cikin sauri yaya Ibrahim yabud’e murfin mota jiki asanyaye Alhaji Jamilu yafito daga mota rungume yaya Ibrahim yayi baya bu’katar sewani yacemai shine d’anshi tsananin kamarshi tanuna hakan hawaye Alhaji Jamilu yashigayi shima yaya Ibrahim haka
Dede lokacin maimartaba ya’iso ganin yayanshi yasashi saurin rumtse ido yabud’e dan jiyake kamar mafarki yakeyi ‘karasawa yayi ganin tabbas hakanne yasa maimartaba rungumarshi yanafad’in ” yaya damakana raye akace kamutu ? ”
Murmushi Alhaji Jamilu yayi yace ” adakam namutu amma a yanzu gani araye ina mama jan hannunshi yayi cikin farinciki sukanufi part d’in kaka itako mama zuciyarta cike take da alhinin rashin Rayhana tanajin idan babu ita tofa komi zai iyafaruwa da ita
Cikin matu’kar farinciki yaya Ibrahim yarungumeta Murmushi mai sanyi tayi tace ” inafatan kana lafiya ? ” jinjina kai kawai yayi sabida farinciki yahanashi magana janye jikinta tayi tashafa kanshi tace Aliyu yakamata kanunama murna sosai sabida shine sanadin dawowarmu ”
daga haka tanufi part d’in kakar itama rungumo Aliyu yayi yace ” Aliyu banida bakin dazan gode maka amma nabaka damar kafad’i duk abinda kakeso nayima wanda zaisakayin farinciki kamar yadda kasani “
Murmushi Aliyu yayi yace ” Zahra nikeso kadawomin da ita dan Allah yaya Ibrahim wallahi ina matu’kar sonta ” ganin yananiyyar yin kuka tabbas yaga soyayyyar zahra cikin Idanunshi dafashi yayi yace karka damu nayima al’kawari babu zato yaji Aliyu yarungumeshi sabida murna dede nan motar Muzaffar tashigo cikin sauri yayi parking sabida ganin Aliyu fitowa yayi yanufoshi janyeshi yayi daga jikin yaya Ibrahim yad’aga hannu zaisauke mishi mari yaya Ibrahim yari’kemai hannun yace
” A yau iname bada ha’kuri amadadinshi dan Allah ayimai afuwa Aliyu yadawomin da farincikina cikin masarautar nan wato mahaifina da mahaifiyata cikin mamaki Momy tace ” mahaifiyarka da mahaifinka ? dagaske Ibrahim suna ina ? kafin yace wani abu Aliyu yakalli Rayhana dake gefan Momy cikin mamaki yace ” Rayhana kece anan masha Allah yau gaki ga mama dama sekuka takeyi sabida rashinki cikin mamaki yaya Ibrahim yace kamar yaya fa Murmushi Aliyu yafad’ada yace itad’in ‘kanwarkace ”
Cikin sauri kowa yadubi Rayhana shiko yaya Ibrahim jiyayi kamar yayi ihu sabida farinciki babu zato yashureta yanufi part d’in kaka cikin matu’kar farinciki bin bayanshi sukayi suna murna yana shiga yasauketa kan cinyar mama cikin matu’kar mamaki mama tace Rayhana dama kina raye kuka tasaki itama Rayhana haka seda kyar akasamu sukayi shiru nanfa kowa yashiga bada labarin yadda abubuwa suka kasance kallon mahaifinta tayi cikin tausayawa tace ” Abba dan Allah kayafemin bansan bakada lefiba shiyasa nadauka kaci amanarmu cikin raunin murya Alhaji Jamilu yace
” balefinki bane auta ta nine nayi kuskure rashinbin maganar iyayena shine yajawomin wannan masifar nagodema Allah dayadawo dani mahaifata ” cikin damuwa Muzaffar yace to Abba yanzu ina su wa’innan miyagun mutanan suke ajiyar Zuciya Alhaji Jamilu yasauke yace cikin dare bayan sunkawoni gidana kamar yadda suka saba kullum Aliyu yaje har gidan tsafin nasu yakunna wuta tatashi cikin gidan tsafin nasu ta’konesu suduka babu wanda yatsira amma dataimakon wata Aljana baiwar Allah “
Ajiyar Zuciya Muzaffar yasauke yace ” Alhamdulilh Allah ya’kara tsaremu cikin sauri yaya Ibrahim yace ” ina ro’konku dan Allah kumayarma Aliyu da matar shi cikin sauri kaka tace wannan ay yazama dole namayarmai da ita dariya suka saki suduka cikin nadama Aunty Sumayya tashiga ro’kon Rayhana
” dan Allah Rayhana kiyafemin ashe jininace ke nike cusguna miki dan Allah kiyafemin ” Murmushi Rayhana tayi tace babu komi Aunty nayafe miki hamdala kowa yayi dede nan maimartaba Yazeed yashigo shida Ummi harmada mahaifinshi tareda dogarawan maimartaba Abdurrahaman cikin mamaki kowa yake kallonsu tashi mama tayi tarungume mahaifinta da yayanta zama sukayi shiru nawani lokaci maimartaba Yazeed yace
” iname baku ha’kuri akan abubuwan dasuka faru dan Allah kuyafemana komi yawuce dan Allah zahra tadawo gidan mijinta kai Aliyu iname baka umarnin kasani matarka Salimat ” cikin nuna mamaki Aliyu yace ” to ay Abba tunkafin nabar BIHAR nasaki Salimat ” ajiyar Zuciya maimartaba Yazeed yayi yace masha Allah taci amanarka itada kawunka ta bayyana mana cikin jikinta amatsayin naka ashe ‘karyane sejiya mahaifiyarka takamasu dumudumu cikin aykata fasad’i nima shedane dan nagani da idanuna ayanzu haka suna gidan yari ”
Sosai kowa yagirgiza da wannan lamarin cikin kuka kawu Yusuf yadurkushe gaban maimartaba yashiga ro’konshi cikin kuka yabayyana duk wani makirci daya shirya jin haka yasa waziri neman yafiya shida sauran munafukai sosai kowa yagirgiza bayan kowa yanumfasa sabida girman lamarin maimartaba yayafema ‘kaninshi komi yawuce nan taro yatashi
Bayan kwanaki 3 aka maida zahra dakin mijinta murna wajan Aliyu abun ba’acewa komi sosai yakebama zahra kulawa da tsananin soyayyya ayaune sarki yasamu labarin mutuwar boka wanda har yafarayin wari babu wanda yasani sawa sarki yayi aka d’auki gawar aka kaita can daji aka jefar kunji ‘karshen mushiriki dan Allah muguji aykata shirka
Bayan 10 yrs
Agajiye Rayhana tashigo cikin part d’in ta dakugu Farooq da haidar yan kimanin 11 yrs ayanzu se su Sudees da Shureem yan kimanin 9 yrs se yan uku duka mata yan kimanin 5 yrs rugowa sukayi suna ‘kokarin rungumeta rumtse idanunta tayi jin shiru yasata bud’e ido ganin Muzaffar agaban yaran yasata sakin ajiyar Zuciya had’ida Murmushi tace
” wai ay harna sada’kar dasun mur’kusheni dan wannan oyoyon nasu ni wahalar dani yakeyi dariya Farooq yayi yace to ay Momy idan bamuyi yauba tunda dady yahana gobe ay mayi ” amshe zancan haidar yayi yace nikam ko yanzu ban ha’kuraba senayi kozuwa anjimane tsalle Shureem yayi yace nima shima Sudees hakan yace suko yan uku dariya suka saki shigowar yaran Samha dana Arfat harma dana islam yasa yaran fita suduka suka nufi part d’in Momy
Cikin farinciki Muzaffar yasuri Raihan yace ” dama cikin matu’kar bu’kata nike doctor dan naga har yanzu babu alamar wasu ‘yan uku bafazan yarda da tazarar haihuwaba tun yanzu dan nasan halinku ku doctors kun iya wayo ” Murmushi Rayhana tayi tace ” ina ay tunda mijina bayaso bazanyiba haihuwa 3 fa kawai yara 7 nima inason ‘kari muje naji dake dan banason karasa komi ” Murmushi Muzaffar yayi yace ” shiyasa akullum sabuwa kikezama cikin zuciyata Allah yayi miki Albarka Allah yabaki Aljanna mafificiya pretty “
TAMMAT BIHAMDULLAHI
Anan nakawo ‘karshen wannan book d’in inayima Allah godiya dayabani ikon gamawa lafiya Allah kayafemin idan nayi wani kuskure acikinshi Allah darasin dake ciki da fad’a’karwar Allah kasa yazama sanadin samuwar Rahama agareni Ameen ya Allah
Jinjina da d’inbin godiya gareku masoya ina matu’kar yinku semun had’u cikin saban book
ππ»MUGUN TSARTSEπ
daga Al’kalamin….π
NPEEDY A AJI π¦πΈπ¦
Comments and shine please
Love u all sisters π₯°π€π»
GIPHY App Key not set. Please check settings