KIBIYAR AJALI 10

Advertisement

 

              *10*

 

 

   *Tun* daga wannan malam Auwal yake dan yi min mutunci ba wai da yawa ba, saboda a cewar sa kada na raina shi dan ba kunya ce dani ba idan yana sakar min fuska zan dena ganin mutuncin sa. Yanzu ta kai ta kawo da kai na nake zuwa makaranta ba sai an tuna min ba dan sosai nake jin dad’in yadda ake koyar damu hanyoyin da zamu yi tsafta, kula da iyayen mu da ma jin maganar su.

 

Yau ma kamar yadda malama Mardiyya ta koya mana, muna tashi daga makaranta na koma gida na cire kayan makarantar nasa wasu riga da skirt wanda malama Mardiyya take kawo min, na yarta ne da kuma ‘ya’ yan yan uwan ta shine take kawo mana nida su Uwande dan kar su ce ni kawai take yiwa shi yasa take hadawa dasu. Naje na dauki bokiti na debo ruwa a rafin durb’un, na dawo tare da dakko ragowar sabulan wanki na da nake boyewa idan ya ragu, na wanke kayana tas suka yi kyau na shanya can inda hannun Gajiyalle ba zai kai ba bare tayi min mugunta ta yarmin dasu. Sannan ne na fara tunanin abinda zanci, dan dazu da safe tas na cinye buredin da malam Auwal ya bani jiya.

 

Advertisements

Babban buri ne ya sake mamaye zuciya ta shi yasa nake son dagewa wajan ganin nayi karatu wato na zama cikakkiyar yar jarida, wannan shi ne mafarki na a duk lokacin da na samu ina shakar numfashi. Muryar Dara’ifa ne ya fito dani daga cikin daki ina daura mayafi na a kugu duk kuwa da cewar malama Mardiyya da malam Auwal sun hana ni yin hakan, amman sabo da kuma ganin al’adar kauyen mu ne yin hakan yasa na kasa denawa, ko na yafa idan na fara tafiya sai na zaro na daure a inda na saba. Na saki murmushi lokacin da na ganta da faranti a hannunta, ina ta addu’a Allah yasa ni ta kawowa.

 

“D’an malele ne nayi shine na kawo miki, Na rasa yaron da zan aiko shi yasa na taso da kai na kici shi da zafinsa.”

 

“Walle naji dadi Dara’ifa, nagode Allah ya hi miki albarka. Sittin ta Ubangiji ina ha’awar dan malele sosai.”

 

“Toh gashi nan kuwa ai ta sha Dijen Baffa.”

 

Nayi murmushi tare da karbar filet din ta tafi ni kuma na samu guri wajan dakin Baffa na zauna ina ci ina santi dan yajin ba karamin dadi ya yi ba. Cikin ikon Allah Gajiyalle ba ta fito ba har lokacin tana daki tana baccin asara. Ina gamawa na dauraye filet din naje na kai mata tare da godiya sannan na tafi wasa na gidajen kawaye na, wasu muyi fada na tafi wani gidan, idan naje muyi ta musu da su a kore ni na fito a haka har dare yayi na koma gida na kwanta.

 

Babu abinda yafi ilimi dadi a rayuwar dan adam, saboda tun da aka bude makarantar boko da islamiya a kauyen mu muka fara samun sauye-sauye da yawa. An dan rage kauyancin da ake fama dashi, ana barin yara mata suna karatu dan sun fara ganin alfanun karatun a cikin rayuwar mu mata. Duk da cewa bana yin na farko a ajin mu, amman ina yin gaba ina kuma zama mai kokari har ta kai ta kawo ina zuwa ta daya ko ta biyu ko uku, da taimakon malaman mu da basa fushi akan duk wani shirme da muke yi musu. Har na kammala primary muka shiga bangaran secondary, nan din ma dai malam Auwal sai da ya bimu can yana koyar damu, A hankali kuma yana ta jefa sakon soyayyarsa gare ni inda ni kuma naki bashi fuska dan gani nake tamkar so yake ya sake samun dama ta yadda zai horani iya son ransa.

 

Advertisements

*BAYAN WASU SHEKARU*

 

 

    *’KAUYEN DURB’UN*

 

 

Nana Khadijaa (Dije, Dijangala ta mai gari/Oganniya yar Baffan ta!) Duk sunaye na ne na yanka dana lakani. Da farko dai: Baba na na kira na da Ummi na, Saboda kasancewar sunan mahaifiyar sa da naci. Matar baba na na kira na da Dije itada wasu tsirarrun mutane a karkarar mu. Mafi yawancin yan karkarar mu na kira na da Dijangala ko Ta mai gari. Kawaye na da matasan karkarar mu na min laqabi da Dije Oganniya. Kasancewar a lokacin ina karama ina da kiriniya da siyan fadan da ba’a kasa da ni ba.

 

Duk wani cincirindon ruguntsumi idan ka cakuda zaka ga ni ce akan gaba. Lamari na dai addu’a ce kawai ta kare ni. Na kasance ni kadai ce awajen iyaye na. Tun ina ‘kankanuwa mahaifiya ta ta rasu, Mahaifina ya auro wata matar, Ya zamto riko na ya koma hannun kishiyar uwa. Na taso cikin wata irin kuntatacciyar rayuwa wanda alqalami yayi ka’dan wajen bayyana muku ita, Manufa dai na sha wahala sosai. Duk da azabar da kishiyar uwa ke gallazamin, Sai Allah yasa mahaifi na yakan kyautata min a duk sanda yake da iko.

 

A yau January 1, Zan kammala jarabawar kare karatu na na secondary, Alhamdulillah Allah kai ne abun godia. Na karanta b’angaren art saboda inaso na karanci fannin Mass-Com/journalism. Na kanyi daria a duk sanda na tuno kuruciya ta ta da. Lalle Allah qadirun ne ala manyasha’u, Na sake daga kai na dubi allon zayyana ta wanda nayi sauka bara a tahfiz din da su Malama Mardiyya ke koya mana.

 

Shekaru na goma sha bakwai a yanzu. Ina kuma sana’ar kitso, Na kuma fara koyon dinki a gidan Bara’atu tela (Babbar mace bata ajin mu ba) Alhamdulillah da wannan yar sana’a tawa nake rik’e da kai na dama Baffan mu. Wanda a yan shekarun nan ya kamu da lalurar nakasar shanyewar barin jiki (hemiplegia/hemiparesis.)

 

Hijabi na na janyo sabo fil dashi Bara’atu ta dinka min, Wuta ta ruru na zubata a dutsen guga, Cikin kwanciyar hankali na shiga goge hijabi na. Na kammala na shasshafa turaruka masu sanyin k’amshi dana siya a shagon Falalu.Ban tsaya wata kwalliya ba na dai goga farar hoda da basilin a lebe na. Gashi na mai matukar tsawo da cika naita ko’karin daurewa, Dak’yar ya dauru. Domin ina daure shi yana kuncewa saboda santsin sa, Ko kitso ake min kasan na warwarewa. Zura hijabin nayi, Na goggoge takalmi na samfarin sandal. Safa tama sabuwa ce sai sheki take. Wajen Baffa na nufa na coka biro a gefen kunne na, Ji na nake on top yau zan kammala sakandire, Sai kuma fanni na biyu.

 

Yana malale a taburma kamar ruwa, Dakyar yake iya magana. Gajiyalle na gefen d’akin girki tana kwashe tuwo. Na san ba zata bani ba bare Baffa na. Domin tunda rayuwa ta ta sauya daga bak’a izuwa fara Gajiyalle ta dena bani abinci, Duk abinda zan sanya a ciki na tadena min shi. Ko banda hantara da kyara yanzu babu abunda ke shiga tsakani na da ita. Zan gayshe ta Sau dubu ba zata amsa ba, Sosai take jin haushin karatun da nake yi. Kullum cikin yada min da magana take. Kan naki aure ina yawon ta zubar, Ga k’awaye na nan duk sun hayayyafa. Ni da Siyama da Uwande da Nafisa ne kadai ke yin karatu yanzu a sa’oin mu. Gaba d’aya sunyi aure sun tara yara. Ajiyar zucia na sauke ina kallon Baffa na, Dama ance sai ka rasu ake gama canza maka halitta. Yanzu Kalli Baffa da sumul k’alau yake. Tashi d’aya ya samu wannan ciwon,

 

 “Baffa na..! Sannu ya jikin naka?”

 

Baffa ya lumshe idanu ya bud’e alamun lapia. Kafin ya bude bakin sa hankali,

 

 “Allah… Ya bada sa’ar jarabawa Ummi na.!”

 

 “Aamin Baffa na! Allah ya tashi kafad’un ka yasa kaffarane.”

 

Rufe idanu yai. Na mike dakyar jikina duk yayi sanyi.

 

 “Na tafi Gajiyalle.”

 

Harara ta dankaramin ta cigaba da kada miyar ta.

 

 “Na tafi jarabawa Gajiyalle.”

 

 “Ko an tafi yawon ta zubar ba. Mude kada a kawo mana abun kunya gida, Atoh!”

 

Girgiza kai kawai nayi na fice rai na babu dadi. Nera dari da hamsin din hannu na na tsaya na mikawa Safarau me sayar da abinci,

 

 “Gashi ki zubamin a kwanon jiya ki wanke dan Allah sauri nake zan tafi jarabawa, Idan na dawo zan tsaya na karb’a.”

 

Saurin Karb’a tayi ta koma wajen zaman ta. Iyayen ta sun hanata karatu sai dai tallen abinci, Wai ta haka zata tara kudin kayan daki. Abun takaicin ma mazan yar kasuwa sun mai da ita tamkar matar su. Su yita bata kudi suna taba ta. Haka na shige da tunanin da safarau ke ciki na tafi makaranta. Lalle na godewa Allah daya kadarta za’ai makaranta a kauyen mu, Da hakimi daya samo mana tallafin yi, Dama mai gari daya wayar da kan dattawan karkarar mu, Sai Baffa na, Jigon rayuwa ta. Wanda ya tsaya min a komai, Ya so ni bai kyamace ni ba kullum cikin min adduar shiriya yake. Ga bani shawarwarin yadda rayuwa ke ciki. Da yadda zan gudanar da al’amura na ba tare da na gunduri kowa ba. Bayan Baffa na sai Malamai na. Musanman Malama Mardiyya data dauke ni tamkar ‘yar data haifa, Itace mace ta farko data gyaramin rayuwa ta. Gaba d’aya acikin duhu nake. Zuwan Malama Mardiyya shi ya samar da yadda na zama a yanzu. Ba abinda zance da kowa sai fatan alkhairi.

 

*_GOVERNMENT JUNIOR/SENIOR SCHOOL DURBUN*_

 

Kide kide muka fara da bencina muka d’akko muka kawo su farfajiyar makaranta, Yau munyi candy. Mun kammala makarantar secondary. Allah mungode maka. Wakoki muka fara na candy, Muna yi fuskokin mu dauke da farin ciki da annushuwa,

 

 _2005 muna tare, 2006 muna tare, 2007 muna tare.. 2014 zata raba mu. Malam Auwal mude kayafe mu, Mude mun yafe, Muma ka yafe mu, Malama Mardiyya mude kiyafe mu, Mude mun yafe mu de kiya fe mu..🎶_

 

Haka Mukai ta yi har akazo kan sunayen dalibai, Nima na mike ina hawaye,

 

 _Khadija Basheer Inuwa inayin ban kwana, Nide ku yafen, Nima na yafe ku.🎶_

 

Ina k’arasawa na fashe da kuka, Saura na ban haku’ri, Mu kaita koke har aka kammala, Aka babbawa prefects kyaututtuka. Ni ce ‘sanitary prefect’ kasancewar nafi kowa tsafta. Domin tunda na Kile na koma yar gayu, Har kawaye na ke kira na da ‘Dije wanka-wanka’ Idan zanzo makaranta ko banida kudin guga tun dare nake yiwa uniform dina ninkin guga na kwanta akai da safe kuwa sai kuga sunyi ‘das dasu tamkar nasa dutsen guga.

 

 ‘’ Ina sanitary prefect? Nana Khadija Basheer..”

 

A hankali na mike daga zaunen da nake na isa gaban makaranta inda Malam Habu ke kiran mu dai-dai, Sunana ya tashi daga Khadija Baffa ya koma na ainihi wato Nana Khadija Basheer. Tun a Jss3 na canza lokacin da mu kai jarabawa. Malam Auwal na gefen Malam Habu yana min wani kallo tunda ga sama na har kasa,

 

 “Dan iska…”

 

Na furta ahankali ina gatsine baki. Murmushi yai yayi magana da labban sa bansan meya ce ba. Malam Habu ya dankamin kyauta ta, Na tsaya muka dauki hoto da sauran malaman kamar yadda ake da kowa. A haka aka kammala komai bayan anyi walima mekyau. Mardiyya bata bari mun kara sallama ba ta tafi bayan ta dankamin number wayar ta a paper, Kan cewar zata dawo ta dauke ni muje birni nayi jamb. Nasan idan muka kara had’uwa kafin tafiyar ta sai nayi wani sabon kukan itama haka, Shi yasa ta tafi. Amma Malam Auwal ya ki tafiya yananan ya kasa ya tsare. Da wani Malamin ya kira wo ni zai dakatar da ni. Sai kace wani miji na.

Ko ta kansa ban sake bi ba, Na bi su Uwande muka dauki hanyar gidan su ganin kayan barar ta da aka kawo,  Kamar hadin baki Siyama ma jibi Za’a kawo nata, Nafisan kansila kuwa an kusa bikin ma, Wani dan uwan su na birni zata aura yanada mashin dinsa Lifan. Ni kuwa ko oho. Banda Malam Auwal da kama sunan sa haushi yake bani ma sai Mubarak dan gidan Bala driver, Shi kuwa babar sa ta dira tsallen albarkar danta ba zai auri wadda tai boko ba. Muna tafe a hanya ina tunanin duniya, Malam Auwal ya shiga zabga min kira tamkar wadda naci bashin sa na gudu. Nifa gaba d’aya haushi yake bani, Ada babu wadda ya tsana iri na, Yana kallo na tamkar kashi. Duk abunda nayi bana birge shi. A kullum cikin kuntata min yake. Amman yanzu ya nanike min kamar super glue. Duk inda nai bina yake sai kace rak’umi da akala.

 

 “Na’am..”

 

Na amsa masa bayan ya kira sunana a karo na ba adadi. Ya sake marairacewa yana zuba hannayen sa a aljihun jeans dinsa,

 

 “My Baby K! Meyasa kike wahalar da zuciar masoyin ki ne? Na gaya miki tunda Allah yasa son ki ya mamaye bargon jiki na da tsoka, Kullum da begen ki nake kwana nake ta shi. “

 

Namiji mayaudari ji wata karya dan Allah! Duk da a k’auyen kayau na tashi, Naki jinin irin kalaman soyayyar nan. Konamin rai suke. Gashi duk karyar banza ce. Don takaici rasa me zance masa nayi.

 

 “Baby K!”

 

Wai Baby K! Kamar wata diyar cikin sa. Murtuke fuska nayi na juya gefe ina dagawa su Uwande hannu alamar su tsaya ni kar su tafi.

 

 “Malam Auwal jira na ake..”

 

 “Naki jinin yadda kike ambatar sunana Baby K! Ni ba malamin ki bane, Masoyi ne agare ki. Ki tallafawa zuciya ta ki karbi kokon barar soyayyar ta. Shekaru nawa ina rokon ki, Ya kamata ace kin tausaya min, Gashi yau zan koma inda na fito. Kuma ba naso na koma batare da kwakkwarar amsar ki gare ni ba.”

 

Ajiyar zuciya na sauke, Ni kai na nagaji da kulaficin da yake yi min, Mutumin da sam baisan darajar dan adam ba, Rashin mutuncin da yai wa Baffa na bazan taba mantawa dashi ba, Yazo zance Kwana ki, Baffan mu ya fito zai tafi gona da y’ar fatanyar sa bai ko kalle shi ba. Ina tsaye ina gwada hankalin sa. Dana tambaye shi meyasa bai gaida wanda ya wuce ba? Wai ya dauka me gyara ne. Gyaran uwar baban sa? Ranar naci masa mutunci sala-sala bansan meyasa baida zuciya ba ya nanuke min.

 

 “Kayi hak’uri Malam! Gaskia bana ra’ayin soyayya, Karatu zanyi. Allah ya baka wadda ta fini komai. Ina maka fatan alkhairi. Allah ya kiyaye hanya.”

 

Ina gama fada nai gaba abuna, Na barshi a tsaye ya sandare. Mukai tafiyar mu dasu Uwande, Wannan itace rana ta karshe tsakani na da Malam Auwal. Ina wa dukkanin mu fatan alkhairi a rayuwa. Muka je gidan su Uwande muka gano kaya, Wallahi Uwande tai goshi, Kaya nasha-nasha. Daga nan na tsaya na karb’i abincin dana bada Kud’i dazu, Gida na nufa, Ina shiga na hango Baffa na a inda na barshi ya kwarara amai yana numfarfashi dakyar, a sukwane na zubar da kyautar hannu na kwanon kuma na ajiye a gefe na shek’a da gudu na isa wajen sa ina tallafo shi da karshen karfi na,

 

 “Baffa na…! Sannu! Amai kayi! Sannu! Jinjiri (Almajirin dake kula dashi Idan na tafi makaranta ko bana nan) bai zo ba? “

 

D’ankwalin hijabi na nasa na gogge masa fuskar sa, Kafin na debo ruwan dumi dana ke had’a masa shayi na surka na gogge masa jikin sa, Riga na d’akko na sauya masa da Wadda ya b’ata, Ina ta faman masa sannu. Gajiyalle ta fito daga d’akin ta tana wake wake, Ta shiga kitchen ta ebo abincin ta ta wuce ko kallo bamu ishe ta ba. Ni bansan meyasa Baffa ya auro taba. Silar ciwon sama itace ta haushi da kokawa ya zume a bandaki.

 

 

Abincin dana sayo na janyo, Na raba shi kashi biyu, Na shiga bashi a hankali dakyar yaci rabin sa, Ni kuma na cinye sauran. Na wanke tulin kwanukan da na gani awajen, Kafin na ha’da wuta na dora ruwan wanka na. Baffan mu na shiga nunnunawa kyaututtukan yai murna kwarai tare da kwarara min addu’a. Ruwa na na zafi na shiga band’aki na yo wanka. Ina futowa mu kai kicib’is da Mudi na koma ciki da sauri, Domin kwanan nan haka yake yi. Sai yaita kallo na yana lashe lebe hade da kashe min idanu. Ya zama direban hayis, Ya siyarda tumakin Gajiyalle da sauran jarin ta ya sai mota yana lodi gari gari, Ga shaye shaye da yake yi du ya bata maza yaran karkarar mu da yi.

 

Sai danaga ya fuce sannan na shige daki da sauri na canzo kaya na, Bana sallah. Hakan yasanya na canza auduga na zura hijabi na d’auki kayan koyan d’inki na mufi gidan Bara’atu me koyamin dinki. Baffa na yana ta baccin sa. A hanya muka had’u da Balki da gayyar yara rab’e rabe wasu na bin wasu har su bakwai. Ta manyanta sosai tamkar ba Balki ba.

 

 “Balki..”

 

Na fada cike da mamakin ganin ta.

 

 “Dijengala!! Rai kanga rai? Yauhe rabon da na saki a ido na?.”

 

 “Ai kuwa dai an jima, Ina wuni Balki, Yaran ki ne wannan?”

 

 “Eh nawaje na ne, Biyu sun rasu ma..”

 

 “TubarkAllah. Allah ya raya su. Balkin Haladu, Ina Haladu?(mijin ta)”

 

 “Uhm dan bankadaddiya, Mayaudari. Ke fa kihiyoyi na biyu. Namiji ba tabbas ingaya miki an sa ranar sa da y’ar gidan babire farkon watan gobe. Mu hud’u kenan. Ke shika biyu yamin saura d’aya auren mu ya datse.”

 

Na rike baki ina mamaki,

 

 “Subahanallahi! Allah ya tsare, Yasa ku zauna lapia.”

 

 “Amin dai. Walle ki tsaya ki cigaba da karatun ki. Yanzu ba hi nan ba tamkar na haife ki. Aure ba dadi kud’in cefa nema nera talatin.”

 

Sirrin gidan ta data fara fad’amin yasa na dan gyara tsayuwa ta ina kallom agogon hannu na,

 

 “Allah sarki! Bara na wuce Balki sai gani na biyu.”

 

Na zaro ragowar hamsin din jakata na mikawa yaran, Kafin su karb’a ta wafce tana cusawa a kanta,

 

 “Mungode Dije. He anjima.”

 

 “Mu jima dakyau.”

 

Gaba nayi abuna na wuce gidan Bara’atu, Hankali kwance ta cigaba da koyamin d’inki, Sosai nake ganewa. Sai bayan magriba na koma gida.. Haka rayuwa ta cigaba da garawa yau da dad’i gobe babu…

 

..

 

______________________

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA’ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.

 

To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.

 

        Ina ma’abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

 

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.

 

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana’arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

 

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 1

Advertisement  *KIBIYAR AJALI…..!!!!* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_            🏹👑👩‍❤️‍👨💝 *MALLAKAR:- NANA…

KIBIYAR AJALI 28

Advertisement   28….*      _*KIBIYAR AJALI…..!_* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_                  🏹🥰😍    …

KIBIYAR AJALI 8

Advertisement   _*BABI NA: 8_*     _*Wattpad:missxoxo00_*                 ***   Advertisements “Hannu malama Mardiyya.”  …