KIBIYAR AJALI 3

Advertisement

 

BABI NA UKU*

(FREE PAGE)🏌️‍♀️

 

     ••

Kukan akuyoyi da tunkiyoyi shine ya farkar dani, saboda ji nayi tamkar a tsakiyar kai na suke yin kukan. Ina bude ido naga cincirindon mutane tsaye a kai na suna kallo na kamar sunga mai hauka sabon kamu. Na tashi ina ‘kifkifta idanuwa ina kuma turo baki, kafin nayi magana sai na fara jera atishawa kusan guda shida a lokaci guda.

 

”Oganniya Dije yau kuma me ya hado ki da Gajiyalle har ta kore ki daga gidan?”

Advertisements

 

Malam Muttaka ya yi min maganar yana ri’ke da gemun sa. Haushi ya kamani na sake daure mayafi na dake kugu na tare da cewa.

 

”Waya sanin mata.”

 

”Kina nufin ba ki yi mata komai ba ta hanaki kwanan gidan ku?”

 

”A gida na kwana, kawai fitowa nayi nan ko zan samu na Allah ya bani abin da zan yi karin kumallo dashi.”

 

“Allahu Akubar Dijangala kina ganin rayuwa, toh Allah yasa ki samu.”

 

Ganin yana shirin tafiya ba tare da ya bani ko sisi ba, yasa nayi tsalle na dire a gabansa ina mai kallon cikin ido nace.

Advertisements

 

“Cewa nayi fa na Allah ya bani kuma naga ka tafi ko kai bana Allah bane?” Malam Muttaka ya yi sauran kallon mutanan dake wajan, aikuwa naga shi suke kallo, naji dadi dan nasan da kunya yace min shi ba na Allah bane yanzu a kafirta shi.

 

“Toh ai ni Dijengala yanzu haka bani da kudi, sai dai ki bari wata rana idan Allah ya sake hada mu sai na baki.”

 

Aljihunsa na kalla zuciya ta sam taki yadda da cewa ba kudi a ciki, na kalli mutanan wajan tare da cewa.

 

“Allah dai ya hana babu, kuma duk wanda yace a gurin nan yana da kudi ya boye yace babu Allah yasa idan ya fara tafiya su fadi, dan Allah kuce amin.”

 

Yara ne kawai suka amsa da amin sabanin manya da kuma matasan da suka san suna da kudin, kafin kace mene tuni sun gudu kamar wadanda suka ji karar bomb. Na kama kugu na rike ganin banyi nasara ba, gashi gari ya yi haske dan na dai Allah ya taimake ni naci dambun nan jiya da sai nafi haka wahala wlh. Hanyar gidan mu na bi da kallo, zuciya ta nason zuwa saboda ina son shiga bandaki, tsoron abinda Gajiyalle zata yi min duk da nasan ba zata kashe ni ba iya kaci ta buge ni kilama harda ciwuka. Ban samu kwarin gwiwa daga jarumar zuciya ta ba dake son na koma gida, sai dai na samu damar daga kafa nayi tafiya har zuwa gidan mai gari, inda na taki sa’a ina shiga ana gama damun koko. Na karasa wajan Ramma wato uwar gida da yake ita ke damawa, na durkusa kusa da ita ina washe baki.

 

“Inna Ramma sannu da aiki, dame zan taya ki?”

 

Sai naga tayi kicin-kicin da fuska da alama ta gano cewa wani abun nake son a bani, dan itama tasan hali na bana yin abu dan Allah sai dan a taimaka min. Ta sake matsar da bokitin kokon zuwa gabanta, na yi murmushi a raina nasan bazan bar gidan ba sai na samu abinda zan sakawa ciki na. Haka aka yi kuwa duk rowar Ramma a ranar sai da nasha koka da wainar rogo, ina gamawa kuma na kara gaba abu na, duk wanda ya ga yadda nake rayuwa yasan cewar ba’a gaban mahaifiyata nake ba, saboda rayuwa nake yi kai na tsaye, kuma alhamdulillahi duk iya rawar kai na da rashin nutsuwa ta babu wani fasiki da ya taba nuna zai yi lalata dani.

 

Muna cikin wannan rayuwa aka zo aka fara gina mana makarantar boko, ana ginin nan ne na fara samun goma ashirin a wajan wani bawan Allah da yake leburanci a gurin. Allah ne ya sanya masa jin tausayi na hakan yasa yake kyautata min, dan ko abinci aka kawo musu daga gidan mai gari sai ya ajiye min idan nazo ya bani. Ranar da aka buɗe makarantar harda manyan mutane suka zazzo daga birni, da hakimi mataimakin gwamna shine yazo ya wakilci gwamnan sakamakon shi baya kasar. Munyi murna tamkar anyi mana wahayi da gidan aljanna saboda ganin manyan motoci da ganin yan gayu, gaskiya kauyanci beyi ba, komai muka yi sai an gane cewa akwai karancin wayewa a tattare da mu.

 

Bayan an kammala komai baki suka tafi ragowar ruwa, lemuka da abincin da suka bari yara da manyan kauyen muka durfafar musu, ni da yake na iya rigima sai da na samo lemon kwalba uku da ruwa jarka biyu na kulle a gyale na sannan na kuma daurewa a jikina. Na nufi wajan kololin abinci na sunguma nayi gida da gudu harda masu biyo ni. Kai tsaye na shige bandaki ina ta faman nishi, ko Gajiyalle bata san da shigowa ta ba sai hanayi da ta jiyo ta fito tana tambayar.

 

“Danladi lafiya?”

 

“Dije ce ta dauke mana abinci, kuma mai gari cewa ya yi duk a rarraba.”

 

“Almura kace sata tayo?”

 

“A’a kwacewa tayi daga hannun Ayuba gashi nan.”

 

Danladi ya fada harda nuna Ayuba wanda yake ta faman huci kai kace da gaske kwato musu nayi.

 

“Toh ina take almurar yarinyar?” Gajiyalle ta tambaye su.

 

“Ai ta shigo nan gidan da gudu.” Ayuba ya fada yana sosa cikin hancinsa.

 

Gajiyalle ta shiga nemo ni longu-longu amman Allah besa zata duba bandaki ba, ta fito daga dakin Mudi tana cewa.

 

“Wallahi kuka bibiya ta haura ta katanga, kunsan ta iya tsallake ta tunda ba tsaho katangar gare ta ba, kubi bayan gari kila can ta buya.”

 

Ina jin lokacin da suka fita, na saki wata nannauyar ajiyar zuciya dan ba ƙaramin wahala nake sha ba a tsaye. Sum-sum-sum Gajiyalle ta ganni ina fitowa daga cikin ban daki, ta kasa magana sai kallo na da tayi tana rike habar ta alamar mamaki tsantsa.

 

“Iyeeeee! Kaga almurar yarinyar nan, dama kina cikin gidan nan?”

 

Ta fada tana sake kare min kallo irin na zaki yi bayani d’in nan, banji komai ba dab nasan ta akwai son banza, dan haka na ajiye kular dannan na kwance lemokan da ruwan ina cewa.

 

“Yo dan Allah Gajiyalle kowa yana diba ni bazan debo na kawowa iyaye na ba?”

 

Gajiyalle tace,

 

“Eh mana yar albarka, ai daman nasan kina cikin bandakin, shi yasa ma banje nemanki can ba. Ah! Lallai baki sun samu dadi irin wannan hinkafa harda hanta.”

 

Tana maganar tana luma katon hannunta cikin abincin, ta debi gurin naman ta kai bakinta tana lumshe ido. Na dinga buga mata harara ina miƙa mata jarkar lemo guda daya da ta ruwa. Amman matar nan ta sake dauke wasu ta barni da guda daya-daya tana cewa.

 

“Haba Oganniya Dije! Nima dai yau na ‘dan dana wannan kirararin da ake yi miki. Baffanki da yayanki fa duk baza ki bayar a ajiye musu ba? Haba ai ban sanki da haɗama ba autar Baffa.”

 

Haushi da mamakin ta suka tokare min a wuya na, matar da taki jinin taji mutane suna ce min yar fari yar autar Baffa, tana jin an fada zata fara masifa da jaraba race bani bace itama tana nan zata haifawa Baffa yara jira take yi ya maro daga talaucin da yake fama dashi. Amman yanzu dubi yadda take ta faɗa tamkar gaske, gaskiya mata makirai ne wallahi, kuma nasan da sun kare zata maida ni gidan jiya wato duka da zagi. Haka na hakura ba dan rai na yaso ba sai dan tafi karfi na, kuma a ranar bacci nayi harda minshari sai kusan karfe biyar da rabi na yamma sannan na farka, fitsari kawai naje nayi daga nan na dauki kular gidan mai gari zan mayar, na haɗu da su Ayuba dasu danladi sun dakko sanduna, gaba na ya buga na fara waige-waigen inda zan samu makami nima, can na hango gatarin malam Iro na faskare a jikin bishiyar kofar gidan sa, na ruga na dauka tare da nannaɗe siket d’in jikina nayi shirin yin dambe.

 

“Yanzu sai ki gaya mana wa muka kama?” Cewar Danladi yana nuna ni da sandar hannunsa.

 

“Cabdijan! Lallai ma yaron nan, kana nufin zan tsaya ku jibge ni ne sai kace wata shegiya? Wallahi tallahi duk yaron da bai fasa duka na ba nima bazan fasa buga masa wannan gatarin ba. Me nayi muku da zaku doke ni iyeee?”

 

Ganin yadda nake buga gatarin a kasa ina kuma yin tsalle ina direwa yasa duk suka tsaya daga nesa, sun san tsab zan iya dukan su dashi dan wani lokacin ba hankali gare ni ba.

 

“Yarinya idan ba tsoro ba ki ajiye gatarin hannunki kiga idan bamu yi miki tsinannan duka ba.” Laminu ya fad’a.

 

“Hahahaha ahaiyeeee nanaye! Bazan ajiye ba d’in kun dauka bani da wayo ni ma, kuma ku fara gaya min abin da nayi muku dan ni nasan banyi muku uban komai ba.”

 

Duk sai suka zagaye ni, kusan su bakwai ni kadai kamar wacce tayo musu wani abu. Na sake gyara gatari na ina nuna su idanuna a waje kamar wata zakanya. Da yake Danladi yafi cewa a doke ni hakan yasa na nufeshi da gudu da nufin kwala masa sai kuma yace kafa me naci ban baki ba, ganin haka da nayi ne yasa duk na bisu zan kwala musu suka gudu, ina huci na ce.

 

“Da ku tsaya mana ku gani yan iska kawai, kun dauka zanji tsoran ku ne?”

 

“Ke Dije kin fiye masifa wallahi, babu wanda baki taba fada dashi na a cikin kauyan nan, wallahi ki dena idan ba haka ba wata rana zaki sha wahala dan kowa haushinki yake ji.” Cewar malam Iro yana karbe gatarinsa da na dauka.

 

Ko kula shi banyi ba saboda daman haushi yake bani, mokotan mu ne amman suna ji Gajiyalle zata zane ni basa zuwa su taimaka min. Na dauki kular na tafi ina ƴan wake-wake na har naje gidan mai gari na basu sannan na fito na tafi yar kasuwa dan yin hira da kuma wasa da ƴan talla. Ban koma gida ba sai kusan karfe goma har da wani abun.

 

*BIKIN JUYA BAI*

 

Gaba d’aya karkarar ‘Durbun’ ta dauka da shirye shiryen bikin juya bai da zata yi. Kowanne lungu da sak’o na karkarar mutane ne ne keta hidima. Bikin juya bai yana gudana ne Bayan an samu alkhairin abubuwan da aka shuka na noma. Kamar yadda mai karatu yasani hausawa sukan ce :Na duke tsohon ciniki, ‘Kowa yazo duniya kai ya taras.’.

 

Noma na da ma’anoni da dama kasancewar irin amfanin sa a fannoni daban-daban. To amma dai a fassara mafi sauki, zamu ce, Noma wata hanyar sana’a ce domin samun abinci da kudin shiga. Haka zalika noma wata babbar hanya ce ta samun karuwar tattalin arziki da al’ummai suka raja’a akan ta. A kasar hausa ko kuwa, noma shine babbar hanya ta samun habakar tattalin arziki. Da noma ne hausawa suka fi samun kudin shiga da abinci dama kayayyakin da ake sarrafawa a masana’anta kamar tufafi da sauran su. A wajen hausawa musamman mazauna karkara noma ya zama kamar wajibi (dole) a wajen kowanne bahaushe musamman magidanci. Kusan muce ma ko wanne bahaushe ya iya noma yasan yarda ake yin shi. Noma ya kasu kaso biyu akwai: Noman rani da Noman damina. Noman rani: noma ne da ake yin shi a lokacin rani ba da damina ba. Sabanin noman rani, shi noman damina ana yin sa ne a lokacin damina.

 

Toh *BIKIN JUYA BAI* wasu kwanaki ne da mutanen karkara ke diba suna dandalar cimar kayan dadi, Mafi akasari cimar ta kunshi nama, Na kaji, Zabbi, Talo talo, Wasu kan yanka dabbobin su ayi dabgen miya. Wannan bikin dabdalar rakashen nama dai na faruwa ne a duk shekara bayan manoma na kauyuka sun ebe/kwashe amfanin gonar su.

 

   *A* yau ranar asabar, Saboda haka naji mutan garin mu na yau asabar. Domin ni ba sani nai ba, Ba kuma damuwa nai nasani ba. Illa dai nasan yau zamu ci dadi mu godewa Allah. Domin gaba d’aya karkarar mu miyar ja zasu yi. Tun duhun safiya Gajiyalle ke safa da marwa tana lalleka zabbinta da kajin ta da yan dabbobin ta kar wani yai awun gaba dasu.

 

Bokiti na dauka nai gangare dan ebo ruwa a rafi. Ina tafe ina wake-wake na. A haka na ebo ruwan na dawo na fada bayi. Ba sabulun wanka ba nida soso rabo na da wanka mekyau inaga sai sallar bara da baba ya bani sabulu kafin Gajiyalle ta k’wace. Don haka yau so nake nayi kyau. Na ebo tokar murhu na duddurje jiki na da ita, Na kwara ruwa. Ina fitowa na sake dakko gawayi Mudi na farfasa na durje baki na dashi. Kai na sai tsami yake. Narasa ya zanyi dashi. Ruwa na kwarara masa na tsane da dankwali na. Kayan kuncen da Adama ta bani na saka. Kamar ranar sallah haka nake ji na. Iska sai kada ni take yi. Yunwa ce kawai ke addabar ciki na. Ina ta jera hamma sai ga baffa ya dawo hannun sa rike da leda,

 

 “Baffa! Sannu da zuwa.”

 

 “Yauwa Ummi na.. Ungo mika mata ledar nan.”

 

Leka cikin ledar nayi na hango kayan miya ne da mayi na ‘kuli sai tashin kamshi yake. Kai mata nayi ta amsa a dakile tana kallon Baffan mu a dakile,

 

 “Haka za’ai miyar lami?”

 

 “Ki dau zabo na d’aya da ya rage ai miyar dashi.”

 

Baffan mu ya bata amsa yana mai kwanciya akan tabarmar gefe na. Baki na tsuke da tafin hannu na ina murmushi. Yau zamu sha dabgen dadi.  Baffa ya bani wazobiya yace na siyo koko. A dari na fece na siyo na dawo . Ko kadan ban tsaya siyan fada ba yau. Ina kawowa Gajiyalle ta kwace ta barmin dan mitsitsi. Jiki na rawa na karba na kwankwade shi tas. Na hada wanke wanke nayi, Duk aikace-aikacen da zanyi nayi, Daga nan na fece yawo na. Gidan su Zubaida kawata naje mu kaci abincin gidan su, Daga nan muka tafi gidan yan gayu gidan su Nafisan kansila. Sunada wuta, sun kunna talabijin. Gurfane nayi Ina kallon talabijin din, Wallahi yadda mutanen ciki ke magana sunyi shiga cikin birgewa abin ya sake burge ni, Naji inama ni ce. Matar an bata wani abun karfe ta rike tana magana ta cikin sa,

 

“Lasifika ce ko Nafisa?”

 

Na tambayi Nafisa ina mai nuna talabijin din da yatsan hannu na. Nafisa ta daga kai tashiga kwararo min bayani. Cikin haka yayan ta Bello ya shigo ya same mu. Ya zabga min harara nima na rama hade da gatsine fuskata. Wata kwalba ya mik’awa Nafisa ta karba tana tsalle,

 

 “Dijangala! Zaki sha?”

 

Daga kai nayi na shiga motsa baki na, Daga gani zai yi dadi tun kafin ma taba ni. Zubawa tayi a kofi ta mikomin na karba jiki na sai rawa yake yi, Ina ayyana garar dadin da yan hanji na  zasu ji, Yaushe rabon duniya da ayyaraye? Karba nayi da sauri na kafa a baki na. Kurba d’aya nayi na dawo dashi, Ji kake ‘phussss..’ a fuskar Bello. A zabure ya mike zai doke ni Nafisa ta shiga tsakanin mu. Ni kuwa gaba d’aya a rude nake. Na zazzago harshe na ina ife-ife,

 

 “Wuta baki na, Wuta.. Wuta baki na. Wuta..”

 

Gaba d’aya ji nake tamkar harshe na zai zazzago saboda tsabar yadda yake radadi, Kirji na sai suka yake. A guje na tafi wajen rijiya na tinjimo ruwa ina kwararawa baki na, Ji nake tamkar harshe na da ciki na ake bankawa wuta. Sam banbi takan Nafisa ba dake tambaya ta menene? Sai da naji sa’ida sannan na zube awajen ina fiffita baki na, Na zabgawa Nafisa harara, cikeda jin haushin lemon wutar data bani nace,

 

 “Gaskia Nafisa baki da kirki, Dan bakin munafurci shine kika bani abinda zai konamin yan hanji?”

 

Nafisa ta kece da dariya, Na mike ina gyara damarar kan zani na, Ji nake tamkar na karairaya ta tsabar haushi. Bello ya yo kai na yana karkada min hannu,

 

 “Kede gaba d’aya baki da hankali, kidahumar banza. Dan tsabar reni lemon kazamin bakin ki kika zubamin a fuska. Ni sa’an ki ne?”

 

“Wannan ne lemo? Walle ba dai lemo ba. Kawai dai mugunta akeson hadamun.”

 

Bello da Nafisa mai zasuyi ba dariya ba. Suka shiga kyakyatawa. Na murtuke fuska ina gatsine baki.

 

Nafisa ta ri’ko hannu na tana murmushi,

 

 “Be lemon wuta bane kawata. Lemo ne na sha, Sunan sa coke. Tsaya kiga ma na sha.”

 

Tana gama fada ta dauki kwalbar ta kafa a bakinta Sai da ta shanye tas sannan ta ajiye. Ganin dagske ta shanye hakan yasa na danji sanyi a rai na. Murmushi na mayar mata nima na dashare hakora na,

 

 “Ayyo! Lemon yan gayu ne dai. To ai kuwa dai zanba su Larai labarin lemon nan. Tab.”

 

Bello yai tsaki kafin ya sakar min rankwashi a kwanyar kai na,

 

 “Mugu azzalumi..”

 

Na fada ina sosa wajen. Har ya fara tafiya ya juyo yana kallo na,

 

 “Me kika ce?”

 

 “Ca nai adawo Lapia”

 

Na karasa fada hade da mai zunde, ya fice ba Tare da yace komai ba. Nafisa taja hannu na muka koma cikin parlorn su. Maman su ta zuba mana abinci fal da naman kaji. Abincin juya ban su na yan gayu. Muka hadu da sauran k’awayen Nafisa muka cinye tas . Suma mukajajje gidajen su muka ci muka koshi, Daga nan naja zugar yara k’awaye na muka tafi gidan mu. Muna tafe muna neman magana. Kafata tayi busu busu ba silipas.

 

 “Oganniya ta Gajiyalle me yar hakiya.”

 

Cewar lantana yar gidan rumasa’u me kitso. Na kece da dariya kafin na buga tsakiyar zani na na ja guda,

 

 “Sai ni Dijangala ta mai gari yar Baffan ta..”

 

 “Gajiyalle ai ba babar ki bace ko? Ita bak’ace bata da kyau.”

 

Nafisa ta tambaye ni tana cigaba da irga duwatsun hannun ta. Na tab’e baki kafin na bata amsa,

 

 “Yarinya Dagaske ba ita ta haife ni ba. Ni baba ta ta mutu dan kiji tun ina karama. Kuma ita kyakkyawa ce yarinya.”

 

Haka dai mu kai ta shirmen mu akan hanya har muka Karasa gidan mu. A tsakar gidan mu zugar k’awaye na suka zauna muka shiga yin yar carafke, Na lek’a gefen murhu inda Gajiyalle ke girki, cikin sa’a ta kammala tana karkasa shi.

 

 “A zuba mana da kawaye na.”

 

Harara ta dankara min ta cigaba da karkasa abincin. Komawa nai cikin yara muka shiga hirar mu. Can Gajiyalle ta callarawa sunana kira. Na mike a sukwane har ina bal da robar ruwan dan akuyan Gajiyalle. Ina zuwa ta mikamin wani kwano cike da abinci yasha nama. Yawuna yatsinke, kunnuwa na sai rawar dadi suke.

 

 “Ungo.”

 

Wayyo Allah na dadi! Yanzu duk namu ne wannan? Nama nasha nasha akai. Gudun kar nayi katobara Hakan yasa na sake tambayar ta namu ne da kawaye na.

 

 “Na mu duka ne?”

 

Gajiyalle ta daga kai tana mai cigaba da kasa abincin gaban ta.A sukwane na karasa wajen kawaye na da kwanon. Muka hau ci sai da muka cinye tatas muka gyatse Sannan kowacce tatafi gidan su. Haba tsabar yadda yau naci na koshi kasa tashi nai nabi lafiyar tabarmar da nake zaune na kwanta sai bacci. Cikin daddadan baccin da yai awun gaba da ni na jiyo wani azababban dundu da aka sakarwa gadon baya na tamkar zai burma saboda yadda aka duma masa dundu. A firgice Na mike Ina sosa bayan. Ina bud’a idanu na na hango Gajiyalle da Mudi, Sai huci take, 

 

 “Dan guzumar uban ki ina abincin dana mika miki ki bawa Mudi?”

 

Idanuna suka kawo ruwa . Wane abinci taban na Mudi? Girgiza kai nayi Saboda hakikanin gaskiya kenan ni bani ta bawa abincin Mudi ba,

 

 “Ba ni .”

 

 “Zaki shiru ko sai na lakada miki na jiki. Yanzu dai dan guzumar uban ki ina abincin yake.?”

 

“Wallahi Gajiyalle bani kika bawa abincin Mudi ba. Iya abinci na da kawaye na kawai kika bani. Nace miki na mu duka ne? Ki Kai shiru alamun Eh. Amman bayan haka baki bani abincin Mudi ba”

 

“Dan guzumar uban ki. Ca ki kai na Mudika ne? Na daga miki kai. Uban wa zan zubawa abinci haka Idan ba Mudikalle naba?”

 

Na sake girgixa kai cikin hakikanin gaskia nace,

 

“Sai da na tambaya nace na mu duka ne? Kika daga kai alamun Eh”

 

Kukan kura Gajiyalle Tai ta shak’o wuya na tana huci.

 

“Amma wannan yarinya ko yar bankadaddiya. Abincin Mudikallen zan baki ku cinye keda yuyar kawayen ki? Nace abincin Mudikallen? Zaki magana ko sai na lakada miki na jaki?”

 

Ruwan ciki na ta hau bugu tana yakushi na. Takaici da zugin da ciki na yake yasa na fara kuka mai kara, Cikin haka ‘Dara’ifa makociyar mu ta shigo da alamun kuka na ne ya kawota. Dakyar ta banbare Gajiyalle daga jiki na,

 

 “Haba Gaji! Haba! Kashe ta zaki yi? Yarinya kamar wannen fisabilillahi ya za’ai ki dinga hayewa ruwan cikin ta kina duka? Tsakani fa da Allah.  Shi fa da na kowa ne Gajiyalle, Idan ka kyautata wa dan wani sai a kyautatawa naka kai ma. Marainiya c…”

 

“Ishiru dakata, dakata min ‘Dara’ifa, kefa dama akwai ki da shisshigi da gutsiri tsoma, Ina ruwan ki? Dan tsabar tsagwaran gulma irin ta ki menene na shiga abinda babu ruwan ki? Shysa akeyi dake a garin nan.. Kinsan meta min ne da zakizo kina min wa’azi?”

 

Dara’ifa ta girgiza kai cikin takaici tace,

 

 “Koma meta miki Gaji sai ki hak’uri, Amma akan me zaki dinga dukan ta kamar kinsamu katako? ‘Ya mace kamar wannan da zaki kyautata mata bafa kisan inda rana zata fa’di ba. Shi maraya kokarin kyautata masa kake ba kuntata masa ba.”

 

“Yau za’ai tsallen badake. Abincin Mudikalle na fa mumugunciyar yarinyar nan ta kaiwa kawayenta suka cinye. Tafa tambaye ni nasa ne? Na daga mata kai alamun eh amman yarinyar nan dake ba tsoron Allah a ranta sai tai mirsisi takai musu suka cinye.”

 

Ina daga kwance na mike dakyar saboda yadda jiki na ke tsamin jibgar da tamin.

 

  “Walle ba haka bane, Kina ji Dara’ifa? Sai dana tambaye ta nace na mu duka ne? Ni da kawaye na nake nufi. Saboda tun farko sai dana ce mata tazuba mana ni da su. Bayan ta kirani ta mikomin abincin na tambayeta fa ta daga kai alamun eh”

 

Gajiyalle taja tsaki tana bubbuga hannu a katangar gidan mu, Har gefen dake lilo ya zubo a kasa.

 

 “Guzuma. Yarinyar nan ko yar makaryaciya. Aina akai haka? Na mudika ne? Kika tambaye ni? Na daga kai alamun Eh. Dara’ifa ki ky’ale ni na kacaccala yarinyar nan”

 

‘Dara’ifa ta shiga tsakanin mu tana janye Gajiyalle tana bata hak’uri,

 

 “Toh Kiyi hak’uri akasi aka samu. Ke dije ita Gajiyalle na nufin abincin Mudi. (Na Mudika) ke kuma Gajiyalle, Dije na tambayar ki ne (Na mu duka?) ma’ana nasu itafa kawayen ta? To adai Yi hak’uri . Abinci dai anci sai kasayarwar sa. Bazai dawo ba, Duka bashi bane. Ke kuma dije Idan kinyi laifi Ki zama mai bada hak’uri kinji”

 

Daga kai nayi alamun Toh, haka Dara’ifa tagama maganar ta ta tafi. Tana fita Gajiyalle ta hau rankwashi na ji kake ‘qwas’ gwaf’ Kif’ duk a kwanyar kai na. Da alamun Dara’ifa ta jiyo. Ai kuwa ta sake yo sallama ta kirawo ni wai zan kai mata nik’a. Arcewa nai a guje har yin karo da dan akuyar Mudi. Rike hannu na Dara’ifa tayi muka shiga gidan ta, Koina yasha siminti abun sha’awa wallahi kamar na lashe shi. Zama nayi a gefen kitchen kofar dakin ta Ita kuma ta shiga ciki,

 

“Dara’ifa ina ku’din aiken?”

 

 “Ki hutawar ki Dije babu abunda zaki siyo min, Kawai kiran ki dai nayi naga yadda take nadar ki.”

 

Dashe baki nayi kawai na cigaba da shasshafa simintin dake malale a k’ofar dakin. Dara’ifa nada kirki, Ita ba tsohuwa bace irin Gajiyalle, Amarya ce amma bata taba haihuwa ba. Daga kauyen alfindi mijinta ya aurota, Shine dan karkarar mu. Sam batada gulma ko biyewa mata n auren karkarar mu dake yawon gidajen juna suna gulma, Ita kullum tana gida tana harkokin gabanta bata shiga lamuran su. Shiyasa suka tsane ta, Kullum cikin yi da ita suke, Wai tacika girman kai, Takance ba girman kai bane gudun zucia ne.

 

Ina nan zaune har aka kira sallah, Dara’ifa ta fito tayi alwala tayi sallar ta, Inata bin yadda take Sallah gwanin sha’awa. Ta mike ta cire hijabin jikin ta,

 

 “Dije ta shi kiyi alwala kiyi sallah.”

 

Baki na na bude kafin na rufe shi Ina mai jinjina kai na,

 

 “Ban iya ba. Daga alwalar har sallar.”

 

 “Wai har yanzu bakya sallah dije? Shin ba’a saki a Islamiyya bane ko allo?”

 

Na daga kai hade da kafad’a ko ajiki na.

 

“Tashi kiyi alwala mu gani.”

 

Mikewa nai dakyar na kamfanci ruwa a buta tamkar yadda naga Baffa yana yi wani lokacin. Na wanke hannu na da k’afa sau dai dai sannan na kuskure baki na na zuba ruwa a gashi na, Na gantsare na mike zan bar wajen Dara’ifa ta hanani,

 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! Koma ki zauna, Haka ake alwalar? Shikenan har kin kammala? Oh ni Dara’ifa!”

 

“Shin dije, Gaji bata koya miki? Anya kin iya karatun sallah ma kuwa?”

 

Na tabe baki kafin nace

 

“Itama fa battai, Yasin seta kwan nawa batai ba. Yo alhaki akanta tunda bata koyan.”

 

Dara’ifa ta girgiza kai kawai, Ta sake debo ishasshen ruwa a buta ta mikamin, Na karba na koma na zauna. Ahankali take koyamin tana min bayani tamkar malama da daliba, Ba lefi na fara ganewa gaskiya. Daga nan tace nayi sallah, Nan ma ban iya ba, Na dudduka kawai na mike na jefar da hijabin data bani a gefe, Nan ma sai data sake koyamin yadda zan dinga yi. Na gane wani abun, Wani kuma ban gane ba. Mudi ne ya leko yace gaji tace naje, Na mike dakyar banso zan koma gida ba har ga Allah. Saboda sam Dara’ifa bata da fada ko hantara irin na Gaji. Har na Kai kofa zan fita ta yafito ni da hannu na koma. Wazobiya ta mikomin hade da radamin a kunne,

 

 “Ki sai sabulun wanka kinji? Sai da safe nagode.”

 

 “Nima nagode Dara’ifa. Allah dai ya biya ki da alkhairi.”

 

Sallama mu kaiwa juna na tafi gidan mu zuciya ta sam ba dadi. Ji nake dama Dara’ifa ce babata dana more. Take ummata ta fadomin arai na. Uwa mai dadi, Da ace tana raye nasan bazan taba tagayyara kmar haka ba. Wasu zafafan hawaye ne suka zubomin, Cikin sarkakiyar murya nace,

 

 “Allah ka jik’an Umma tah..!”

 

Tun daga zauren gidan mu nake jiyo sautin suratan Innarajo mahaifiyar Balki K’awata itada Gajiyalle. Sam innarajo bata sona batasan kawancen da muke da Balki ‘yarta. Shiyasa nima na dena shiga harkar Balkin. Wai ashe barar (kudin aure) Balkin aka kawo. Mamman mai shayi ne zai aure ta. Gajiyalle sai guda take tana yada magana.

 

 “Ai wallahi innarajo Gwara ka aurar da yar ka tun tana karama kana iya tankwarata. Yanzu ba gashi ba xatai auren ta tabar yuyar su hannu na mai kafada( Wai ni)”

 

Ta karasa fada tana mun zunde da baki. Yi nayi tamkar Bansan suna tsakar gidan ba na kauda kai na gefe. Band’aki na shige na rage ciki na kafin na fito nai ficewata yar kasuwa siyo sabulu da kayan k’walam da wazobiyar (hamsin/50 Naira) da Dara’ifa ta bani.

 

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 28

Advertisement   28….*      _*KIBIYAR AJALI…..!_* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_                  🏹🥰😍    …