KIBIYAR AJALI 4

Advertisement

 

*BABI NA 4*

(Free page)

 

 

  *Cikin* kankanin lokaci aka fara kawo malamai daga cikin birni wadanda zasu koyar da mutanan karkarar mu karatun boko, a cewar mai gari harda na addini duk za’a koyar kuma kyauta, abinda kawai ake bukata shine iyaye su yarda su dinga tura yaransu makaranta. Yaran mai gari dana mai unguwa da liman da sauran masu faɗa aji a kyauyan mu su aka fara sakawa a makarantar saboda ma kar wasu

iyayen sunce gashi gashi, su ance su kai yara makaranta amman wadanda suka ce ayi su basu saka nasu can ba, hakan yasa suka fara yiwa tufkar hanci.

 

Tun daga kan su kuma ba’a kara kai wasu ba, ba wai rashin yaran zuwa makarantar ne babu ba. A’a tsabar su yan garin basu yarda da karatun bokon ba shine ya hana su kai yaran su. Ganin haka ne yasa hakimi da kanshi ya yi magana cewar dole ne kowa ya kai dansa makaranta tun daga kan dan shekara uku zuwa goma sha biyar maza da mata. Amman iyaye mata suka ki barin yaransu mata suyi, a cewar su babu abinda ya kamaci suyi irin talla dan su tara abin da za’a siya musu lokacin aure. Ni kuwa da dama bani da wani mafadi idan ba Baffa na ba, kuma shi ɗin ma ba wani tsoro yake bani ba. Sai ya zamana babu mai cewa Dije shirya na kai ki makaranta, ko kuma Dije zoki je makaranta.

Advertisements

 

Ranar da aka fara yin karatu naje makarantar amman ba wai shiga nayi ba, lekawa nayi ta taga na hangi su Abu yar gidan mai unguwa zaune a kan benci ta kurawa malamar ido kamar zata hadiye ta, na kwashe da dariya tare da sake yin ɗage yadda zan dinga hangowa sosai nace.

 

“Kai Abu hekace kin samu talabijin sai kallon matar can kike yi.”

 

A dai dai lokacin malamar ta juyo da yake rubutu take yi a jikin allo. Ita kam Abu turo baki tayi ko bata fada ba nasan bacin rai ne a zuciyar ta dan itama ba son makarantar take yi ba. Malamar ta saki murmushi cike da tsantsar kulawa ta kalle ni tace.

 

“Zagayo ki shigo kema.”

 

Cikin dafe kirji da zaro ido duk a lokaci guda nace mata.

 

“Wa?” Malamar tace,

Advertisements

 

“Ke mana, shigo ki zauna a yi karatun dake.”

 

Budar baki na sai cewa nayi.

 

“Allah sitiri buƙi, inci tsohowar….”

 

Ban kai ga karasawa ba naji wani irin abu ya sauka a tsakiyar kai na, babu arziki na yi kasa ina kuka ina ihun a kawo min dauki. Kafafuwa da na gani sanye cikin wani cover sheo shine ya tabbatar min da cewar wani ne ya yi min abu. A hankali na dinga dago ido ina karewa jikin kallo, kafin daga bisani na sauke idanuwa na biyu na dora su kan fuskar shi, gabana ya buga ras! Saboda tsananin tsoro da naji. Sam fuskarshi babu annuri bare kayi tsammanin fara’a a kai, ya kalle ni fuska a murtuke tare da cewa.

 

“Bar nan gurin ko na babbalaki.”

 

Sam ban san daga ina furucin ya fito ba, dan ban maji kalmar a baki na ba bare nace ni nayi, kawai saukar furucin nayi a cikin kunnuwa ne ina cewa.

 

“Saboda me?!”

 

“Ohh tambaya ta kike yi?”

 

Cike da gasgata tambayar da ya yi min nace,

 

“Eh walle talle ban gane mekake nuhi da cewa na bar gurin ba.”

 

Bacin rai ya kuma ziyartar zuciyar shi, ya dan matsa kusa da bishiyar darbejiyar dake bayan shi, ganin yana niyar tsinko bulala yasa nayi saurin rugawa da gudu tare da yi masa gwalo. Shi kuwa gabaki d’aya haushin yan kauyan namu yake yi, tunda yazo yake faman korar masu zuwa gulma wato iri na kenan, bamu shiga anyi da muba, gashi mun hana wadanda ake koyawa suyi cikin nutsuwa. Malamar ta leko ta taga tana yiwa malamin magana cikin dariya.

 

“Malam Auwal kana ta fama kaima.”

 

Yaja dan karamin tsaki,

 

“Ni anya zamu shirya da yan kauyan nan kuwa? Wallahi malama Mardiyya baki ji yadda rai na yake baci ba, gashi sam basu da tarbiya mazan su da matan su.” Dariya malama Mardiyya tayi.

 

“Wallahi kuwa malam Auwal sai dai kawai muyi hakuri tunda Allah ya kaddara cewa nan zamu dawo, ni dama mai gida na da kyar ya yarda wallahi dan cewa ya yi sai dai na ajiye aikin saboda nisan dake tsakanin mu da wannan Kauyan.”

 

“Mtwww! Ni abin da yake bani haushi malama shine, yadda kina ganin yara a kauyan nan maza da mata sunfi dari biyar duk wadanda basa zuwa, dubi ko class d’aya mun kasa samu saboda wulakanci, babu abinda suka sani sai tallah shegun.”

 

Malama Mardiyya ta kwashe da dariya tana gyara zaman mayafinta tace,

 

“Lallai malam Auwal kafi mai gida na jin haushin wannan kauyan, kasan shima ya taba zuwa nan yin aikin ƙidaya, nake gaya maka suka ki amincewa a yi musu haka suka tattara suka koma gida ransa a mugun bace. Shi yasa da nake gaya masa anyi min transfer zuwa nan ya fara masifa, da kyar na samu ya amince, tunda gaskiya ni dai albashin da nake karba yana rufa min asiri sosai.”

 

Malam Auwal ya tabe baki kai kace shi ba da albashin ya dogara ba, mugun dan kwalisa ne dan irin samarin nan ne da suci a cikin su gwara su sanya a jiki ace sunyi abu iri kaza a rayuwar su. Matashi ne dan a shekaru ba zai wuce ashirin da bakwai ba, dogo ne baki irin mai kyau din nan mai dauke da yar siririyar fuska, idanunsa mici-mici kamar wanda aka sauwa, habarsa dauke da d’an guntun gemu wato tabani kasha hadisi da samari ke yi. Ya kuma taɓe baki tare da cewa.

 

“Ai kuwa ni zanyi maganin su wallahi tallahi, dan babu shege ko shegiyar da zata sanya ministry su zo suyi mana dibar albarka.”

 

“Da kyau malam Auwal ina bayan ka wallahi dari bisa dari.”

 

Cewar malama Mardiyya tana ta dariya.

 

Wucewa ya yi ya tafi ita kuma taci gaba da koyar dasu kamar yadda ta soma yi.

 

Ina ta gudu ban tsaya ba, duk a zato na yana biye dani ashe bai ma biyo ni ba, sai da naje kofar gidan mu na turo kofa tare da lekawa sannan na tabbatar da cewa gudun banza nayi. Gajiyalle ta damko min wuya na tare da tun kudani cikin gida tana masifa.

 

“Gantalalliyar yarinya kawai, babu abinda kika sani sai yawo da bin lunguna yin dambe. To zaman banzarki ya kare daga yau, maza dauki gashi nan na soya nayi miki kullin biyar, goma da ashirin. Tun dazu na hangi su Lami sun tafi tallar wainar roga da wainar gero nasan zuwa wannan lokacin ko basu siyar ba toh sun kusa. Amman ke da yake ba ƴar mutunci bace, baki taba yin tunanin abin arziki ba, tashi maza ki tafi yar kasuwa ki sai sa min.”

 

Wani sassanyan dadi ya mamaye rai na, yau na samu abin da nake so wato damar yin tallah, saboda tan matukar bani sha’awa, musamman idan naga yadda kawaye na suke sha’anin su da kudi. Carab na dauki farantin gyada ina murmushin farin ciki nace da Gajiyalle.

 

“Daman fa Gaji kece baki sani ba, ina ta so na gaya miki ki dinga yin wani abu ina fita yar kasuwa dashi. Toh sai na yi shiru dan karki doke ni, yanzu kuwa kinga kema zaki zama mai kudi kamar Innarajo, dama har ta fara tarawa Balki kayan aure, nima kinga sai ki fara yi min tanadin nawa.”

 

Ta sakar min wani banzan kallo wanda ya tabbatar min da cewa taji haushin kalamai na, sai dai bata ce komai ba har na tashi na fice daga gidan. Wayyo ranar jina nake tamkar a gidan aljanna saboda farin ciki, gashi tun kafin na karasa yar kasuwan na fara ciniki a majalisar Sallau mai tsire.

 

Cas! Suka bani kudin gyadar naira saba’in na dauki farantin na dora a kai na ina digirgine ga kuma kudi a hannu ina kuma lissafawa. Ta kusa da makarantar da aka bude na bi, har zan wuce sai kuma na sake shiga ina mai kulle kudin a gefen mayafi na da nayi damara a kuguna. Wasu malamai suka kira ni suma suka siya, naga na dazu da ya biyo ni amman wannan karon ko kallo na beyi ba, har zan tambaye shi ko zai siya, sai nayi shiru dan na lura kamar bashi da mutunci.

 

Na tafi yar kasuwa kasan cewar ni sabuwa ce kuma gyadar sabuwar suya ce sai ya zamana ta kare da wuri. Ina kudin Gajiyalle? Na same su ci banza ci wofi tamkar nawa ne, ni har mantawa ma nayi cinikin ba nawa bane saboda rufewar idanuwa. Ban lura cewar kudin sun kusa karewa ba sai da naje siyan kankana kwallo daya aka ce min naira saba’in, jiki na yana bari na zaro ina kirgawa naga arba’in da biyar ne kawai. A lokacin gabana yayi mugun faduwa na dafe kirji na tare da furta.

 

“Na shiga uku da Gajiyalle.”

 

Babu shiri na dauki farantin gyadar na tafi gida, sai da na kusa zuwa sannan na fashe da kuka ina tafiya ina yi kamar wacce aka yiwa dukan tsiya. Na shiga zaure na samu kasa duk na zuba a jikina da gurin baki na idan ka gani ba zaka taba kin cewa ba na jaki na sha ba a gurin manyan maza, na shiga ina dora hannu aka. Gajiyalle na zaune tana dinkin hula gani a wujejjige yasa ta saurin mikewa tana tambaya ta.

 

“Lafiya Dije?”

 

“Na shiga uku Gaji zasu kashe ne.”

 

“Suwa ye?”

 

“Yan sholisho… Wayyo Allah na Gaji sun kwace cinikin na shiga uku.”

 

“La’ilaha illa lahu ni jikar mutum hudu me kike son sanar dani Dije? Kina nufin kice an siyar da gyadar yan iskan gari sun turmusheki sun kwace cinikin?”

 

Na gyada kai na ina share maina da bayan hannu, tace.

 

“Na shiga uku Dije kin cuce ni, dan kaniyarki ina karfinki da har kika bari aka kwace kudin? Shikenan daman gyadar rantowa nayi nace zan yi gwaji gashi nan kin gwadani Dije, wallahi Kedai banza ce sakarai shashasha. Allah ya isa ban yafe ba, gashi dole na biya.”

 

Tana magana rana duka na ni dai ban da bata hakuri babu abinda nake yi, cikin dashasshiyar murya nace bayan na zaro ragowar kudin.

 

“Wannan kawai suka bani, suma din sai da suka mare ni da suka ji nace ba tawa bace ta babar mu ce.”

 

“Uban babar ku, nice babar taki dan malafar gyatuminki? Da ace kin dauke ni uwa ai da ba zaki bari su karbe miki ba bakar munafuka kawai, tashi ki bani waje ko na karya ki, bana son ganin ki Dije na tsane ki.”

 

Na tashi kamar munafuka na fita, zama nayi a zaure ina tikar dariya ta ganin yau na rainawa Gajiyalle hankali. Tun daga lokacin kuwa bata sake gigin dora min komai ba, duk nacin da nayi mata kin yarda tayi haka na hakura, na koma gidan jiya wato yawace-yawace kwararo-kwararo ina gurin.

 

*SASHEN MAI GARI JAMILU*

 

Gaba d’aya kusan duk maza dattawan dake karkarar Durbun suna zazzaune a karkashin bishiyar darbejiyar da mai gari jamilu yake zaune. Yana hakimce akan kujerar sa yasha rawani na masu gari, Sauran mutane na daga kasan taburmi sun yi gurfane suna sauraron mai gari. Malam Bashari (baban Dije) shi ma yana gefe kansa a kasa. Mai gari ya sake jan majina kafin ya cigaba da cewa,

 

 “Toh nagode da abunda wasun ku suka yi min, Wato ina matsayin mai garin nan ban isa na zartar da hukunci ba kenan sai an gayawa magabata na? Saboda an rena ni shine Za’a kai ‘karata wajen hakimi? Kai bara na fito muku a Mutum. Kauyen nan tsatso na ne suka kafa shi, Babu wasu wa’enda suka isa su zartar da hukunci bayan namu. Ku ba farin cikin ku bane ace ‘ya’yayen ku suna boko? Yanzu ‘yayan kansila su biyu ina har alfindi yake kai su kullun suyi bokon? Gata ya samu yanzu za’a zo amana makarantu shine kuke bakin ciki? Wannan wane irin kidahumanci ne? Toh dai,

 

 “Ni da hakimi mun gama magana, Za’a cigaba da karatun  nan, Sannan ‘yayayen ku su amfana kuma ku amfana dasu nan gaba. Amma babu tilas wanda yaga baya ra’ayi shikenan. Amma kada nan gaba nasara ta samu yaran da sukai karatun nan kuzo kuna dana sani. Zan baku kowanne takaddu na shiga makarantun nan guda bi-biyu ku bawa ‘yayan ku domin shine fom na gurbin karatun. Kunga masu wayo tuni ‘yayan su sunyi nisa da karatun, Kuma wannan makaranta da naku zasu fara itace Idan suka kammala zasu samu fannin shiga jami’oi. Hakimi ya tabbatar min cewa sarki dake birni yayi alqawarin samawa yaran mu guraben karatu a jami’oin su dake birni. Saboda haka yanzu zan bawa kowannen ku takardun nan guda biyu. Ruwan ku ne ku sanya su a makarantun nan, Ruwan ku ne ku kyale su suyi ta hargitsa mana gari, Tunda kunnu na bani da martaba a idanun ku..”

 

 “Tuba muke ranka ya dade..”

 

Cewar malam sagiru dake gefen mai gari a durkushe. Sauran suma suka fad’a da karfi Kan su a kasa. Mai gari yaja tsaki kafin ya janyo takaddun a gefe ya shiga kiran sunayen su yana babba su. Har akazo kan Malam Bashari mahaifin Dijangala. Mikewa yai ya isa gaban mai gari ya durk’usa kana ya mika hannun sa cikin girmamawa. Mai gari ya mika masa yana murmushi,

 

 “Malam Bashari, Har abada nasan baka cikin masu yimin zambo cikin aminci. Ba zaka taba zuwa kayi dani ba awani wajen. Tilasta ka akai, Kaje a yan cikon masu korafi, Ko’ina ne zan shedaka wallahi..”

 

Malam Bashari yayi murmushi kafin yace da mai gari,

 

 “Godia nake yallabai, Allah ya saka da alkhairi.”

 

Mai-gari yayi murmushi kana ya mika masa takaddun guda biyu. Hannu biyu Malam Bashari yasa ya karba, Da ganan aka shiga muhawara kowa yana tofa albarkacin bakin sa akan makarantun da yaran su zasu fara yi. Kafin a watse kowa ya kama hanyar sa. Malam Bashari ya taho gida zuciar sa ayyana yadda Gajiyalle zata karb’u maganar. Kafin ya k’arasa gida yaci karo da dandazon yara anata tafa hannaye,..

 

Fada ya kaure tsakanin Dijengala da Ummin Nasiru mai guga. Sai kaurewa suke suna tima juna a kasa. Na kururuwa kafin na daga hannu na watsa baya.

 

 “A hayye! Ke Ummin gwaigwai, Ba tsoron ki nake ji ba. Da wani gahin ki a tsaitsaye kawa hammatar dan iska. Banza bazara iskar damuna.”

 

Na karasa fada ina karkadawa Ummi hannu. Ummin ma taja shewa kafin ta finciko ni muka kara haurawa,

 

 “‘Ni an gaya miki tsoron ki nake ji? Kazama kawai me warin kwata.”

 

 “A hayye nanaye! Kece kazama ai. Banziya wadda ke hamamin doyi. Ummi gwaigwai. Yanzun sai na caskala ki a wajen nan.”

 

Na karasa fada ina  jan tsaki. Na shatalo kafar Ummi na nakata da kasa. Ummi ta hau kuka, Dai dai sanda Baffa na Malam Bashari yazo wajen. Duk rashin ji na ina tsoron Baffa na sosai, Ko kadan banason b’acin ransa.

 

“Kai ku bari, Maza kowa ya tafi gida, Tashi kinji! Yi hak’uri. Bata hak’uri, Ummi na muje gida..”

 

Baffa na ya karasa fada yana nuna Ummin Nasiru mai guga da hannu, Cuno baki na nai gaba, ciki ciki nace,

 

 “ ‘ki hak’uri”

 

 “Yasin ca tai ‘ki hakuri ba Yi hak’uri ba..”

 

Ummi tafada tana tafa hannaye, Zare min idanu Baffa yai alamun na bata hak’uri. Wayyo Allah na. Bana son bata hak’uri, Idan ba Baffa ba, Ko Gajiyalle ko Idan nayi ba dai dai ba shine nake bada hakuri, Amman ya za’ai itace da lefi ace na bata hak’uri. Nasha mur kana na juyar da kai na,

 

 “Baffa yar gala-gala muke yi, Kaga gidan dana zana kuwa? Kawai Ummi tazo ta tarwatsa mana ta tattake. Kuma ace na bada hak’uri? Haba Baffa dan Allah kada kace na bata hak’uri.”

 

Baffa ya janyo hannu na gefe ya dafa kai na kafin yace,

 

 “Wanda yabada hak’uri baya faduwa Ummi na, Ko bake bace da laifin kiyi hak’uri kinji? Ki bata hak’uri, Saboda mutanen wajen nan siyi koyi dake. Kinga nan gaba za’ai shedar ki.”

 

Daga kai nayi badan wai naji dadi ba sai dan gudun bacin ransa, Har gaban ta naje, Na wulkita idanu na na zabga mata uwar harara, Na mata kallon zata sani bata sha ruwa ba, Kafin na watsa hannu baya na buga zani hade da murgud’a baki nace,

 

 “Kinci saar Baffa na wallahi, Da wallahi sai na caskali ki, Nayi kullin tara sisi dake, Gajabura kawai. Badan halin ki ba.. Kada Allah Ubangiji yasa ki hakura. Aikin banza kawai. Mts! Allah ya…b..”

 

Baki na ya shiga min nauyi, Har ga Allah banason bata ha’kurin nan. Amma ala dole na bata Saboda Baffa yace dole ne na bata. Na bata rai kafin na sanya karamin danyatsa na na sosa hanci na. Dakyar naja iska. Wai ni Dijengala ni zan bawa wata hak’uri.? Iska na sake ja na sauke kafin nace,

 

 “Kiyi hak.. h.. hakuri.”

 

Ina gama fada nai gaba ina hawayen bakin ciki ganin yadda Ummi ke murna harda shewa, Tab ai kuwa bashi taci. Sai na yagalgalata narantse da Allah . Baffa ya cimma ni, Na cuno baki gaba dak’yar nace,

 

 “Sannu da zuwa Baffa..”

 

 “Yauwa yar baffan ta.. ko kefa! Gwara da kika bata hak’uri kinji? Kinga mutanen dake wajen laifin ta zasu gani.. Mahakurci mawadaci.”

 

 “Toh Baffa..”

 

Na bashi amsa bawai don maganar sa ta hige niba, Gida muka higa , Gajiyalle na tsaye a turken dabbobin ta tana kirga yawan su, Kullum haka take yi sai ta kasafce kansu hankalin ta yake kwanciya. Daganan ta koma kan kajin ta da zabbin ta. Tabe baki nayi, Nayi gaba abuna. Baffa ya karasa bakin dakin sa ya zauna dakyar yana salati. Wasu takardu ya zaro a aljihun wandon sa dake lilo zai yage ya ajiye akan taburma,

 

 “Salamatu.. (Sunan Gajiyalle)”

 

 “Na’am Malam! Ya akai?”

 

Tabashi amsa tana daga tsaye gandar-dar..

 

 “Kya dai zauna ko? Abun arziki ne ya tunkare mu.”

 

Gajiyalle ta washe baki. Nima na ajiye robar dana kamfaci ruwa na kwasa a guje. Ban dire a ko’ina ba sai gaban Baffa. Duk azato na duddugar tsire ya sayo ko Kan babban kifi. Gajiyalle ta dankaramin harara nima na rama ina gatsine..

 

 “Guzumar ubanki! Kaga yar bankadaddiya.”

 

Na mike ina cuno baki,

 

 “Yasin Baba ta ba bankadaddiya bace ehe, Allah ya jikan ta.”

 

Tayo kai na zata dake ni na goce ina watsa hannu baya, Mudi ya shigo yana jin rediyon sa ta naci. Cikin daga murya yace,

 

 “Ke ga wani yaro can awaje yana kuka wai kin jefamas taya a kwata. Shi da yayan sa..”

 

“Tashi kije ki san yadda zaki ki dakko masa tayar sa, Uwar yan jawo masifa. Wannan yarinya sam bakida kirki.”

 

Tabe baki nayi na kalli Baffa kafin nace,

 

“Kana ji ko Baffa, Ina cikin tafiya shi ya fara tsokana ta. Musa ne fa dan Malama Harira me siyar da wainar yar bagalaji. Haka kawai ya tsokane ni wai Dijangala tsogalgala me kama da zankala ‘koki. Shi ne ni kuwa na kwace tayar dayake wasa da ita nai cilli da ita a kwata. Ai ba lefi na bane ko?”

 

Baffa na ya cire tagumin. Kafin ya mike ya fuce kawai, Ina jiyo shi shida Musan da yayan sa. Da alamun hak’uri ya basu. Can naga ya dawo ya zauna. Ya kira Mudi shina ya zauna.

 

 “Yauwa Salamatu ga takardu nan daga birni sarki ne ya mana hanya daga shugaban kasa. Tallafin karatu ne da yaran mu zasu yi. Kyauta har su kare su shiga gurbin jami’a..”

 

Gajiyalle taja tsaki kafin ta mike tana zabgawa baffan mu harara,

 

 “Ai karatun arna? Kan babban bala’i! Yasin ba dai agidan nan ba? Karatu fa kace? Mudi ko zakai boko?”

 

Mudi ya mike yana girgiza kai,

 

 “Ni lodin mota zan fara. Gajiyalle zata sayamin mota idan na kara manyan ta. Bazanyi boko ba gaskia “

 

Tab tunowa nayi nima naga yadda ake boko a talabijin din gidan su Nafisa. Yara kamar a bursun din kauye. An hanasu Fita anata koya musu shirme wai shine karatu. Mikewa nayi nima na dire tsallen albarka, Kafin na kwararo rantsuwa na dire ina watsa hannu na,

 

 “Gaskia bazan yi bokoko ba, Yan bokoko ba basa karatu basa sallah, Sai Karatun arnaye. Idan nayi boko na nutse.. “

 

Baffa ya duka yana rok’on mu,

 

 “Ku temaka min kuje karatun nan. Wallahi Za’a amfana. Ina jin kunyar mai gari na mayar masa da takardun nan. Salamatu kisa baki.”

 

Gajiyalle taja tsaki akaro na ba adadi kafin tace,

 

 “Salon iskanci akeso a koyawa yaran karkarar nan. Suyi ta cikin shege ko? Akan me Za’a ce yaran mu suyi boko? Saboda hanyar neman abincin mu su lalace ko? Gaskia Mudi bazai yi boko ba. Idan yar ka zata yi to? Amman dai ai Gwara Kiyi talle da boko ko Dije?”

 

Kad’a Kai na nayi na dashe baki.

 

 “Sau dubu miliyan Gwara nayi talle da dai nayi boko. Bazan yi ba gaskia. Ni talle zan yiwa Gajiyalle. Na girma ayi aure na ko Baffa?”

 

Baffa na yayi ajiyar zuciya kafin ya dube ni dakyau yace,

 

“Yanzu da kiyi karatun gwara kin d’au talla kina yawo a gari? Ba kince min kina sha’awar yadda kike sauraron na radiyo idan suna magana ba? Kuma kikace na Abun kallon gidan kansila ma yana burge ki. ? Kinason ki rika ri’ke musu abun da suke magana ko? Yanzu bakyaso kin watsar ba zaki cinma burin ki ba?”

 

Tunani na shiga yi, Gaskia bazan iya zama kamar a bursun ba, Gwara nayi tallen.

 

“Nide gwara tallen..”

 

Gajiyalle taja guda da shewa kafin tace,

 

“Yauwa yar gari. Zanci gaba da baki kayan talla kina yi min.”

 

Baffan mu ya kad’a kai hade da mikewa ya dube ni,

 

 “Bazan tursasa ki ba. Allah yaba da sa’a.”

 

Yana gama magana yai fucewar sa. Ni kuwa dadi nake ji zan fara ci gaba da talla ina samun kudin kashewa koda cikin dabara ne. Acikin satin Gajiyalle tafara doramin tallen kayan koli dana turaruka da take sarowa a birni. Inata talle na har aka bude makaranta. Nayi mamakin ganin kawaye na duk sun fara zuwa. Na sheke da dariya na kance,

 

“Mahaukata, Banda shirme me akai da boko? Sun zama arnaye. Harda Siyama kawata aminiyata. Lalle siyama batada wayo. Tabdijan.”

 

Ni kuwa likafar talle na taci gaba, Kaf karkarar mu ba inda bana zagawa don asai kayana. Idan naga zai yi kwantai ma har fada nake janyowa ta yadda dole mutum ya siya asarar sa.. Ho ni Dije- Dijengala Yar Baffan ta. Ta Gajiyalle mai yar hakiya.. Dijama mai kayan koli. k’anwar Mudin bakin tasha..”

 

Kirarin da nakan yiwa kai na kenan aduk sanda nayi ciniki. Gajiyalle kan bani kudin batarwa. Idan kuma banyi kasuwa ba ta lakadamin duka ni kuwa na rama akan dabbobin ta na targada shegu…

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 1

Advertisement  *KIBIYAR AJALI…..!!!!* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_            🏹👑👩‍❤️‍👨💝 *MALLAKAR:- NANA…

KIBIYAR AJALI 11

Advertisement                  *11*         *Ranar* wata sanyayyar asabar da damina, Muka tashi da babban tashin…